NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Bayan Kwana Goma.
“ni kuwa Jummai duka kayan Marigayiya ta haɗa ta tafi da su?, dan jiya naga kamar wani fallan atamfarta a kan gado”. Yagana ce ke wannan maganar, ni da Adawiyya muna zaune muna fige kaji guda biyun da Baba Mujibu ya kawo aiwa Yagana ferfesu. a karo na biyu maganarta ta sa ke giftawa ta cikin shirun da nai zurfi aciki.
“ikon Allah da yawa yake, ni kuwa Mairo kamar dake nake magana ko?”. muryata a sanyaye nace ma ta,”Yagana ta gama ɗiba duka, waɗanda kika gani nawa ne na ɗauka”. ta kuma cewa,”Ya rasulillahi, to ke me zaki yi dasu?, ina zaki kai kayan Suwaiba ajikinki Mairo duk da kin ciko ba kamar da ba, magana ta Allah ki fito dasu a bayar sadaƙa ba’aje su su mutu a banza ba”. bance ma ta komai ba, dan yanzu ni magana sam ba ƙaunar yinta nake ba, Allah kaɗai yasan halin da nake ciki na irin faɗuwar gaban da nake yi a kullum, ga mutuwar uwata da bata sakeni ba.
ta kuma cewa,”ni kuwa gashi bana so ina yiwa mutum magana yay sautin mahaukaciya dani, ke kuma gashi sararki ce Mairo, Kabiru ya goga miki fentin rashin kyautawar nan, alhalin ba abu me kyau bane kuke yi, ni wallah ma nayi zaton zaman gidan arnan ba surarki kawai ya sauya ba harda halinki, ashe hali na nan saima ƙara gaba gaba da yake, ko da yake dama me hali baya fasa halinsa”. Adawiyya tace da ita,”Yagana ke kuma gaki da magana, ki barta taji da abinda ke damunta, Uwarta ce fa raru amma kinbi kin kwazazzafeta. kaya idan ta ɗauka mene aciki, ba kayan Babarta bane, su zata dinga gani suna ɗebe ma ta kewa”.
tace da ita,”uwar sawa da iyawa ai ba dake nai magana ba, dan haka ki rufe min baki…kuma da kin gama aikin ki miƙe ki tafi gidanku dan ba nemanki nake ba, inaji jiya Uwarki na faɗin wai na riƙeki ina hanaki zuwa ki tayata aiki, da yake ita bata da godiyar Allah, duk sauran ƴaƴan dake gabanta suke ma ta hidamar basu isheta ba saike ɗaya da ike wurina kike zuwa ita kuma ba ƙaunar hakan ta ke ba, to Allahn da yake sona ya dawo min da ɗiyar albarka, sai ta jiƙaki ta cinye”.
daga dukkan alama Adawiyya ta ƙulu da maganartata, ni dai jinsu kawai nake, kafin na bata amsar da ta takura min da tambaya akai wai kayan Gwaggon har kala nawa na ɗiba.
“Yagana babu fa yawa, kala uku ne, sai wannan dungun atamfar da bata ɗinka ba Baba ya bamu kuɗi muka kaiwa Shamsiyya ta ɗinka mana ni da Basma”. “to ai shikenan, suma sai ki kai a rage miki ɗinkakkun tunda nasan sunyi miki yawa”. “haka zanke saka su ba saina rage ba”. “to hakan ma ba laifi ai tunda ke ba jin shawara kike ba, ita dai Allah ya jiƙanta…ke kuma ya sauya miki halin kafiyarki”. na amsa da,”Amin”.
ta kuma cewa,”shi Liman ɗin me yace a ga me da sallolin da suka bar kanki?”. Ya Salam, na rasa kunnen Yagana wane irin kunne ne, da ace yanda bakinta ke da magana haka kunnenta ke da ji da magana ɗaya ta gamsar ba saika ƙara ba. a gabanta fa Liman yace,”Ai a Musulunci an ɗauke alƙalamin rubuta lada ko zunubi ga mutane 3. 1- Yaro ya sai ya balaga. 2-Mai bacci har sai ya farka. 3-Da mahaukaci har sai ya warke.
Kuma shi irin wamda yay ciwona na mantuwa ana sanya irinsu ne a fannin mahaukata tunda dai ba shi da hankali. Kuma duk abinda ya aikata na lada a yanayin ba za a rubuta masa ba, haka ma na zunubi ba za’a rubuta masa ba, Yana farkawa zai ɗora ne daga inda yabari a farko, duk abinda yafaru a tsakanin nan ba zai ramasu ba”. kuma a sanda yay shiru da bayanin nasa ita ta karɓe da Kabbara, amma yanzu kuma tana ƙara tambayata ya akai.
tare da Adawiyya muka ɗora sanwar dahuwar kazar, dama tunda bayan sadaƙar ukun Gwaggo na tattaro kayana na dawo gidan Yagana, dan bana jin zan iya ci gaba da zaman gidan duk da cewar akwai Inna Amarya, gidan gaba ɗaya ba daɗinsa nake ji ba, saboda Basma ma tabi bayan su Anty Ma’u gidan da ta ke zaune acan kano, Ya Kabiru ma kuma yana ikirarin zai koma a sati na gaba, su Adawiyya ma komawa zasu yi dan hutunsu ya ƙare, ni kuma Ya Amadu yace ba zan bisu ba na zauna anan za’a nema min wata private school ɗin naci gaba da zuwa, Ya Kabiru yace kuɗin makaranta ko ya kai dubu ɗari ne akaini zai biya, tunda har yanzu duk ban manta da karatuna ba, komai yana kaina.
dan har yanzu ma hausar bakina kamar bata cikakkiyar bahaushiya ba, maganarmu da Ya Kabiru da Ya Amadu ma yanzu da turanci muke yi, hatta Kulu ma wadda nayi matuƙar mamakin hakan daga gareta, ta iya turanci sosai dan idan tana yi ma zaka rantse wata baturiyar ce, naso kuma nayi ma ta wasu tarin tambayoyi akanta da suka tarar min akai, to amma ba ayanzu ba, nafi so mu gama sabo da ita tukunna.
“wai da gaske ne shekaranjiya Suhail yazo miki gaisuwa?”. maganar Adawiyya ta shigo cikin tunanin da nake, nace ma ta,”umm sunzo, ai yana da matuƙar kirki”. da ace na kalli fuskarta a lokacin da zanga abinda ban taɓa gani a fuskarta ba aga me dani, to amma maganar da ta biyo bayan amsa ma ta ɗin da nayi shi yasa ni waigowa na dubeta babu shiri. “nima ya min gaisuwa, har yake ce min wai ai har fyaɗe ma anyi miki, baki ji yanda maganar ta sosa min rai ba har ƙwalla saida nayi. kuma na tambaye shi aina yaji zancen yace ai maganar ma ta gama baza garin bichi, kuma ya za’ai ma nace masa ban san maganar da ta fito daga cikin gidanmu ba”. ban san sanda na haɗiye wani baƙin yawu a maƙoshina ba, wani babban abu ya tokare a ƙirjina, na tafi tunanin sanda Ya Amadu ke zayyanawa su Baba labarin komai tun daga lokacin da Emanuel ya bugeni har sanda yaje gidan ya sameni, kuma nima na basu labarin abinda ya faru damu acan dajin da aka kaimu, kuma Inna Amarya ta dage akan akaini asibiti a dubani, muka je asibitin Malam Aminu kano akai min gwaje-gwaje, aka tabbatar musu da babu abinda ya taɓa budurcina, kuma babu abinda ya sami lafiyata, sai kuma a sannane kowa nutsuwarsa akaina ta gama dawowa.
sai dai a lokacin na shiga wani babban mamaki na tsintar rashin jin daɗin sakamakon a fuskar Inna Amarya, da har ta dage ta tubure akan sai an ƙara gwadawa ko kuma aje wani asibitin, a haka har saida muka asibiti uku, kuma duk sakamako ɗaya suke badawa, alamun rashin jin daɗin bayanai ya fito ɓaro ɓaro a saman fuskarta da kuma yanda duk ta ke neman ta rikice, na shiga zuzzurfan tunani akan hakan, dan hatta a maganar da ta faɗa min a ranar uku me ɗaure kaice, tana kuka ta ke ce min,”ta wani ɓangaren sai naji dama ba’a ganki ba Mairo, saboda ina gudun yanda mutane zasu yi ta kallonki, da rabon Suwaiba ba zata shaƙi wannan takaicin ba”. ina cikin yanayin da bana iya magana ma kwata kwata a lokacin, shi yasa ban sami damar ɓarar ma ta da abinda zuciyata ta kwararo min ba. haka kurum a yanzu sai nake jin Inna Amarya bata shigewa har cikin zuciyata da wasu sabbin ɗabi’un da nake ganinta dasu, sai nake ganin kamar dama can ma tana riƙe dani ne saboda wata manufa tata, to amma duk sanda baya ta hasko min cikin kaina, kyakykyawar zamantakewarsu da Gwaggona sai na ture duk wani kokonto a gefe, zuciyata ta koma tuna min wannan Inna Amaryar ce da ta ɗaukeni kamar ƴar cikinta, Inna Amaryar da kullum Gwaggona ke sawa albarka, Inna Amaryar da komai ta rakito na Mairo ne da Gwaggo, to akan me zuciyata zata fara wasi-wasin banza akanta?.
“ke tunanin me kike?”. na kore mamakin da yay tsalle ya dira a saman fuskata na yacce na karancin maganar da Adawiyya ke faɗamin ƙarya ne, dan fuskarta da yanayin maganartata sun nuna hakan. na ƙaƙalo murmushi nace da ita,”ba komai”. sai kuma ta ɗora zancen daga inda ta tsaya,”ni wallahi ma yanzu fargabata a gaba ta ke Mairo, idan akazo maganar aurenki wannan soki burutsin ya shiga kunnen mijin da zaki aura…shi kansa Suhail ya faɗa min abinda baki sani ba, yace tuntuni yana sonki kuma aurenki zaiyi, yaso ma ace bayan mutuwar nan ai maganar aurenku, to amma tunda yaji anyi miki fyaɗe yaji ba zai iya ba”. nai wani guntun murmushi me ma’anoni biyu nace da ita,”au Fyaɗenma har anyi min kenan?”. tai wani murmushin da zan iya kiransa dana munafurci dan yayi kama da hakan, sannan tace.
“to Mairo abinda ake ta cewa kenan, kuma kowa ya yarda”. “harda ke kenan?”. da nuna alamar rashin gaskiya tace min,”haba in yarda da wannan banzar maganar, sai kace ban san wace ƴar’uwata ba, ni dake fa duk mun san cikin juna, idan gaske ne ai tuni kin faɗa min… ai shi yasa da ake ta cewa wannan hasken da kika yi na me ciki ne naji daɗi da Ya Amadu ya kora bayanin komai, kowa yasan gidan hutun kika faɗa ba hannun wahala ba shi yasa kikai kyan gani, wallahi ban san mun tara maƙiya ba sai a dawowar nan taki…ke baki ji yanda aketa baƙinciki da sauyin rayuwar da kika samu ba, harfa da masu zugani wai na fita harkarki tunda kin iya turanci ni ban iya ba…ni duk ba wannan ba, yanzu taya zamu goge baƙin fentin da mutane ke miki kallo da shi?”.
na sake yin wani murmushin nace,”to ma dai ko me za ai ta faɗa aita faɗa, ni ba zai dameni ba, dama tunda na dawo na shiryawa jin waɗannan ƙananun maganganun, dan haka wanda bai faɗa ba ma ya faɗa, wanda yake faɗa kuma yaci gaba da faɗa ni ko a gefen yatsana”. da alama maganar da nai batai ma ta daɗi ba, taso ace na tashi hankalina ne, dan tun dawowata na gama fahimtar sabuwar zuciyarta, Adawiyya ba irin ta da bace akaina, ta yanzu da banbanci, waccan pure ce, amma wannan cike ta ke da tsatsa.
na sauke tunkuyar daga kan murhu ita kuma ta kashe murhun, sannan muka wuce ɗakin Yagana. ta ke min naganar Nafi’u ɗan gidan me unguwa daya zo da maganar aurena, tana roƙona akan na yarda na amince.
“shi kuwa kamar wanda bai san mutuwa ba, sai kace gidanmu neman kai dani suke, daga mutuwar uwata sai maganar aure, ai ya bari na huce zafin mutuwar tukunna ya tunkare ni yaji idanma zan amince masa, amma ba kai tsaye ya kai maganar wurin manya ba. ko da yake dama yanzu ni sai abinda na dinga gani, tunda jajirtacciyar mahaifiyata me tsayin daka akaina she is no more, i have to be patient akan duk wasu challengies da zan fuskanta”. na faɗa a sanda nake yafa mayafi ina cewa da Adawiyya ta tashi mu tafi gida, yau gaba ɗaya ban leƙa ba. Yagana ta zabgan harara da jan ƙaramin tsaki. “ai na faɗa miki ki daina samin ɗan banzan turacin naku acikin magana tunda ba iya shi nayi ba. ke baki san ma ni yanzu wannan hausar taki ma ba sonta nake ba, ba yanda na iya ne kawai…amma da kinyi zance kaɗan saiki fara za da mo da yo, haka kawai ki dinga ƙunshe min kai”.
murmushi kawai nai na nufi wajen da nayi sallah ɗazu zan ɗauke ƙaramin ƙur’anin dana karanta, sai ce min tayi,”kice ash hadu”. a dole tasa nai ƴar ƙaramar dariya, haka ta ke min yanzu ko alwala zanyi saita tace ki faɗi kalmar shiga musulunci.
saboda na ƙara kunnota nace,”Don’t worry Hajiya Yagana i will say it”. aiko kamar jira ta ke na rufe baki naja tsaki, ta kuma hau sababi, ta kuma bani dariya sose, da yake yanzu gaba ɗaya ma da turanci muke magana da Ya Kabiru, to idan zamuyi zaman awa guda agabanta muna magana, taita jan tsaki tana mitar an isheta da ɗan banzan yaren da bana uwa da uba ba.
a hanya muna tafiya Adawiyya ke ƙarasa min zancen da ba ta ida ba a ɗazu, wai Suhail yace shi yana so ya auri wadda ta fito daga gidanmu, kuma gashi ba zai iya aurena ba, saboda haka idan har ita ta amince masa zai aureta.
ba ƙaramin daɗi naji ba da jin zancen, har na ɗora hannuna a kafaɗarta ina zolayarta da cewa,”waya ga gimbiya Adawiyya…dilla ki amince masa mu raƙarƙashe, kinga shikenan muma mun zama jinin sarauta”.
tai min wani banzan kallo tana cewa,”Allah raba gatari da saran shuka, me zanyi da mutum me ɗaukar maganar mutane”. nai murmushi ina kama hannunta nace,”kema dai Adawiyya baki so gaskiya ba, magana ta Allah who ever gets in to the situation am in dole mutane su zarge shi, balleni da nake mace, shi yasa nace miki na toshe kunne na da duk abinda mutane zasu akaina…amma dan Allah ki bar batun wai ba zaki amincewa aurensa ba, Suhail mutumin ƙwarai ne, kuma gidansu ma mutanen ƙwarai”.
kamar ba zata ce min komai ba, sai kuma ta numfasa tace,”naji”. da haka muka ƙarasa gida inata tsokanarta, ita kuma sai ciccin magani ta ke.
ɗakin Gwaggo daya koma ɗakin Kulu a yanzu na shiga, tana zaune da hisnul muslim a hannu tana karantawa, nayi sallama na shiga ta amsa min tana hararata. ina murmushin daya bayyanar da dukkan haƙorana na ƙarasa gareta ina rugumeta nace,”am sorry my second Gwaggo, Allah yau aiki mukaiwa Yagana shi yasa baki kalleni ba tun safe”. duk da haka taƙi ɗago da kai ita alalla tana fushi, saina karɓe hisnul muslim ɗin na ajiye shi na kwantar da kaina bisa cinyarta, na shagwaɓe fuska ina kama kunnena nace,”Am so sorry, Allh nima tun ɗazu hankalina na kanki”. sai tayi murmushi a sanda ta ke kallona, ta shafo kumatuna tana cewa,”ai idan nayi fushi dake ko duka jamaar kano zaki tara su tayaki bani haƙuri ba zan haƙura ba…shikenan haka akeyi fisabilillahi sai kusa na ƙara zama marainiya, ita Basma na ma ta uzurin makaranta, amma ke kin tattara kin gudu wurin Yagana kin barni ni ɗaya a ɗaki kamar mayya, bayan sarai kin san bani da kowa a gidan nan yanzu sai ke, ke kaɗai nake gani naji daɗi, kuma kece ke ɗebin kewar Yaya, dan Allah karki kuma yini baki zo na ganki naji sanyi a zuciyata ba, wallah bana samin nutsuwa idan ba kya cikin gidan nan”.
nai wani fari da ido nace,”to Gwaggo 2″. sai taja hancina tana gajeriyar dariya, sannan kuma muka shiga hira, tana bani labarin taji Baba ɗazu yana faɗa akan ba zata bar gidan nan ba, amma bata san acikin Inna Amarya da Inna Zulai wa yaje masa da zancen ba, wai sun gaji da zama da mahaukaciya tunda dama dan Gwaggo ta ke zaune to yanzu saita bar gidan tunda babu Gwaggon, Baban yace karsu ƙara ce ma ta mahaukaciya, da lafiyarta, zanen ƙaddara ne ya maida ita hakan, kuma zamant a gidan nan babu fashi, sai dai idan bayan ransa.
tausayinta ya kamani, nayi ɗan jim kafin nace,”to kema Kulu ki koma gidanku mana indai kin san inda ƴan’uwanki suke”. sai naga tayi murmushi me kama da ciwo kan tace,”lokacin hakan yana tunkaro ni, na kusa nan bada jimawa ba”.
Muryar Ya Kabiru ta shiga kunnuwanmu a sanda ya ɗaga labulen ɗakin, muka kai dubanmu gare shi, shima na lura yanzu yasan Kulu na magana, tunda bata shayin yi agabansa kuma shima babu mamakin hakan a tare da shi, muryata a ƙasa nace, “da ɗaya bayan ɗaya kowa na gidan nan sai ya gano gaskiyar kina magana”. da ƙaramar dariya ta rakani, ni kuma na miƙe na isa bakin ƙofar da Ya Kabiru ke tsaye, na miƙa hannu na amsa ledar kaza da youguht ɗin daya siyo min, na ɗago kai zan masa godiya ya matse hancina yaja, nai ƴar ƙara ina kama hannunsa zan cire daga hancin nawa.
sai ya kawo goshinsa ya ɗan doki nawa goshin,”kin wani ƙunshe a gidan Yagana, kin bar mutane anan da kewarki”. nace da shi,”to ba saika bi sahuna ba Ya Kabiru, ai sai kaje kaga ko lafiya tunda kasan safiya nayi nake tahowa nan”. yace,”tabɗi! Yaganar nace min me hannun ɓera zanje gidanta, ai ba zan sake komawa ba saita neme ni da kanta”.
na ƙyalƙyale da dariya na juya ina bawa Kulu labarin diramar Ya Kabiru da Yagana, ya siyo ma ta dambun nama ya kai ma ta ya ɗiba sai cewa tai yaje da halinsa, ita bata san hannun ɓera gare shi ba da bata ce ya siyo ma ta ba, amma ai gwara daya nuna ma ta halin ɓerayen da yake da shi, gaba ta dinga kaffa-kaffa da kayanta idan ya shigo gidan, yanzuma dan Allah ya tashi ya fita, kamin ta nemi kayan jama’ar da aka bata ajiya ta rasa, ya barta da tsilla tsilla, ita ta ƙaguma ya koma ƙauyen daya fito.
Da daddare bayan anyi magriba ina shirin tafiya gidan Yagana Baba yace na dakata zaiyi magana dani. a ɗakinsa na same shi Inna Amarya na zaune a gefensa, sai Ya Amadu shima daga gefe, na ƙarasa ciki na zauna kusa da Inna Amarya, gabana ya shiga dukan ukukun dan na san wannan zaman ba ɗaya ba, musamman dana ji Baba yace,”zauna sosai Mairo, zaman naki ne…dukkanmu da kika gamu anan muna zauna ne saboda ke”. na ɗago duk na dubesu kafin na mayar da kaina ƙasa naji shi da maganar da banyi tsammani ba.
“maganar aurenki ce Mairo…”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button