NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

ME KUKE TUNANI, ME KUKE TSAMMANI?

Comment&Share.

SIRRIN ƁOYE

By Oum Ramadhan✍????

31)
tun bayan dana idar da sallar asuba zuciyata ke faɗamin tabbas mafarkin da nayi gaskiya ne kuma zanga gaskiyar ta bayyana a zahiri nan bada jimawa ba. a wayewar garin yau inaji tamkar an buɗe min kundin rayuwata ne ina karanta haƙiƙanin abinda zaiyi tasiri akaina a yau. sai naji wata iska me zafi ta shura ta fuskata kamar yanda iska me ɗumi ke bin cikin iskar guguwa, kuma a hankali sai naji wani abu na ɗiga ajikina me zafi kamar ruwan dake tafarfasa acikin tukunya, tabbas akwai abinda ke shirin faruwa da ni, sai dai ban san menene ba tunda shi ɗan Adam baya sanin lokacin da masifar rayuwa zata kasance da shi, sai dai kawai ya tsinci faruwar musifar akansa. na zuƙi wata iska a hancina wadda nake jin ta banbata da irin iskar da nake shaƙa tun bayan zuwana duniya, Ya Rabb! kasa koma meke shirin faruwa dani na iya tunkararsa, ka bani ikon ɗauka, ƙaddarata a rubuce ta ke kuma ban isa na guje ma ta ba, ya ubangiji ina roƙonka da ka juya mummunar ƙaddarar da zata sameni zuwa me kyau.
na ɗago daga tagumin da nayi na kalli Kulu dake gefena, acikin idanuwanta da basu ƙarasa rufewa gaba ɗaya ba na hango tarin baccin dake cikinsu, nai guntun murmushi dan da alama gyangyaɗi ma ta ke bata sa ni ba, sai na miƙe daga kan sallayar na ɗauko bargon rufarmu na shimfiɗa a ƙasa, na kamata zan kwantar da ita saita farka, muka haɗa ido nai ƴar dariya ina cewa,”gyangyaɗi fa kike, ki kwanta kinga dai bacci ba’a ɗaukar bashinsa”. murmushin daya tsaya iyakar leɓenta tayi,”ai tare muka raya daren dake, kema zoki kwanta ga idanunki nan duk a kumbure”. “ki fara kwanciya nima yanzu zan kwanta”. na faɗa ina gyara ɗaurin zane na. naji tace,”ina za ki hala gari ko gama wayewa bai ba, yara ma gasu can ina jiyo dabdalarsu basu gama wucewa makaranta ba”. “wurin Baba za ni”. sai tai saurin yunƙurawa ta miƙe zaune,”karki sa ke ki bashi labarin mafarkin da kikai, kin dai ji na faɗa miki”. da sigar faɗa tayi min maganar, kuma naji na ɗauka, domin ina ganin girmanta, dan haka na bata amsa bayan sauya ra’ayina da cewar,”ba zan faɗa masa ba wallahi, ina so ne na koma makarantar asuba saboda na ƙarasa cike haddata, shine zanje naima Ya Amadu zancen tunda kinga yace gobe zai wuce da wuri”. ta gyaɗa min kai,”hakan yayi kyau, Allah ya taimaka, sai kin dawo, ki kula da kanki, Allah ya tsare”. “amin”. na amsa ina nufar hanyar ƙofa, duk jikina yay sanyi kamar yanda nake aiwatar da komai cikin sanyi tun mafarkin jiya da nai.
a tsakar gida na tarar da Inna Amarya tana shimfiɗa tabarma, na saka takalmina sanda kuma har ta kai kicin ta ɗauko botikin koko da ta dama, na ƙarasa da sauri na amsa,”sannu da aiki Inna”. “yauwa har an tashi?”. “ehh Inna, yau kin kammala sanwa da wuri”. nai maganar a sanda ni da ita muka ƙaraso kan tabarmar ina ajiye botikin kokon ita kuma tana ajiye kofunan zuba kokon, ta ke ce min,”wallah zan fita ne ina so naje jigawa, kin san Babanku kuma baya son tafiya da rana, shi yasa nai himmar gama komai da wuri tunda ke yanzu ba zaman gidan kike ba balle na bar miki aikin”. “aikuwa dai kinyi dabara, dan kina kaiwa sha biyu Baba zaice ba za ki ba. Inna amma dai ba bikin gidan Umman Abbas za ki ba ko?”. “bashi bane, ita ɗince dai ta kirani kuma ina tsammanin ba zai wuce akan bikin zamu tattauna ba”. na ɗan ɓata fuska ina cewa,”Inna kince fa idan za kije zamu tafi tare”. “kiyi haƙuri sai gaba idan zan koma tukunna…shiga ɗakin Zulai kice ta bada kwanon abincinta, idan Adawiyya ta tashi ta fito kuci naku, Sadiya ma tazo ta ɗau nata”.
Na shiga falon Inna Zulai da sallama, duka basa nan suna cikin ƙuryar ɗaki, kuma daga can ɗin na jiyo muryar Adawiyya na faɗin,”Inna yanzu shikenan inaji ina gani saita rigani aure ban fara cimma muradina ba, kina ji fa abinda Baba yace wai yau zai ɗaura ma ta aure”. Sadiya ta amshe da cewa,”ni gaba ɗaya Adawiyya na rasa gane akanki a al’amarin kishin da kike da Mairo, ina ce dama shi ɗan gidan Sarakan kike so kuma an shiga an fita kin gama samunsa, to mene kuma za ki ɗaga hankalinki akan batun aurenta tunda bada shi za’ai ba, ke ba ma dama kika samu na goranta ma ta ba ta auri mutumin da yake kafiri a ada”. Adawiyyan ta kuma cewa,”nifa duk inda za’ace Mairo zata ji daɗi baso nake ba, shi ɗin fa da zata aura ba ƙananan mutane bane, babba ne shima dan ubansa shine major general na ƙasa baki ɗaya kamin yayi retire, wallahi inaji Ya Amadu na faɗar mahaukatan kuɗi ne dasu, hatta gidan da suke zaune idan kaje zaka rantse ba’a ƙasar kake ba..me kike tunani idan Mairo ta koma rayuwar can gaba ɗaya?, wallahi sai tafi yanda ta ke ɗin nan kyan gani, kuma bada jimawa ba kiga ana haskata a gidan talabijin, aike kin gani ma a vediyon da Ya Amadu ya nuna mana sanda tana kafira”. a wannan karan da tayi shiru kuma Inna Zulai ce ta amshe da cewa,”Adawiyya idan kika kaini bango zan fita a lamarinki, na faɗa miki ki bar asarar hawayenki ki zuba ido ki gani idan auren zai tabbata, na faɗa miki muddin ina raye rayuwar yarinyar nan a wahala zata ƙare, bana faɗar abinda ba zan cika ba, ba kuma na tunkarar abinda ba zai kaini ga nasara ba, a wanne dalili zan zuba ido ina ganin suna ci gaba ni kuma rayuwar tawa ƴaƴan a dakushe kullum, ƴaƴana su ƙare a auren manomi, ai ba zai yiwu ba…wannan kuɗin da kuka ga na amsa wurin Amadu naira dubu hamsin ƙarya nai masa da cewar zanja jari, boka zan kaiwa ya magance mana komai, yanzu nan zan shirya na wuce dan a kammala aiki da wuri, yau ai sai dai Malam yaji kunya a idon jama’a, dan sai jama’a sun gama taruwa yaron zaizo yace ya fasa, ban damu da duk ƙananun maganar mutane da zasu biyo baya tunda ba akan ƴaƴana bane”. naja numfashi nai tattaki na ƙarasa bakin ƙofar ɗakin, sannan na buɗe baki na kwarara sallama, hakan kuma yasa sukai tsit da abinda suke son ƙara cewa.
Inna ta taso ta fito tana washe min baki da murmushin makirci, na tsuguna na gaisheta. “yau da sassafe haka, ko kunyi halin da ƙawar taki ne?”. nace da ita,”a’a Inna ai anan gida na kwana. dama Inna ce tace ki bada kwanon abincinki tana sauri zata fita ne”. “to shikenan bari na ɗauko miki”. ta faɗa tana komawa cikin ɗakin, na ƙara cewa da ita, “Inna su Adawiyya sunje makaranta ne?”. “a’a kin ganta anan tana aikin kukanta na gaira babu dalili, na rasa uwar da akai ma ta”. na saki murmushin daya fitar da sauti ina cewa,”ke dai Adawiyya kin shiga uku da damuwa, to idan kin gama kukan ki fito muyi break fast…Sadiya kema Inna tace kije ki ɗauki naki”. Adawiyya ta fito jikinta a sanyaye, fuska duk ta kumbura saboda kuka. “ai gwara ni sau dubu akanki, idan ina ciwo bana kwakwazo”. a wannan karan dariya nayi bayan na amshi kwanon abincin da Inna ta miƙon, nayi gaba ina ce ma ta,”ai kuka yanzu kika soma indai ba za kisawa zuciyarki haƙuri da salama ba…kuma ki sauri ki fito dan tafiya zanyi gidan Yagana”.
abincin muke ci amma gaba ɗaya na lura cin dole ta ke yi masa, damuwarta ta fito fili ƙarara taƙi ɓoyuwa. bata san tawa damuwar taci uwar tata ba, hasalima ni ƙatuwar matsala ce dani da ban san ta inda zan tunkari al’amarin ba, al’amarin shirinsu na kunyatar da Baba akan fasuwar ɗaurin aurena. tabbas nasan duka zuciyoyinsu babu imani, musamman Inna da idan tace zatayi abu to saita aiwatar hankalinta ke kwanciya, tunani nake kamar naje na sami Baba na faɗa masa ko kuma na faɗawa Innata, to amma kuma idan na faɗa ɗinma babu amfani, dan babu me yarda da maganar da babu shaida.
a can gidan Yagana tunda na shiga na sameta tana bacci na kwaso kayan wankinmu na fito dasu, a cikin kayayyakin da Ya Kabiru ya siyo min na ɗauko wani sabulun wanki me ƙamshi, ina wankina ina sauraron karatun ƙur’anin da aka saka a gidan radio ina kuma binsa, da yake izu talatin ɗin ƙasa ne kuma mun sauke a makarantar allo, sai naji zuciyata ta fara washewa daga dukkan damuwarta da fargaba.
na gama shara na fito daga wanka saiga Saddiqa ta shigo, na tafi da ɗan saurina na rugumeta ina yi ma ta oyoyo. Saddiqa sabuwa ƙawar da nayi ne a lokacin rasuwar Gwaggona, jika ce a wurin Baba Lami a kano suke tazo hutu ne gidan Malam Liman. munsha hira sose da ita kafin ta tafi, sallama dama tazo min akan zata koma gida hutunsu ya ƙare, kuma hirar da mukai da ita duk saita ɗebe min kewa, tana ta bani labarin makarantar bokonsu me suna turkish international school, kuma naji makarantar ta burgeni sosai harna ƙudurta a raina zance Ya Kabiru can za’a kaini, tunda dama har yanzu yana tunanin wadda za’a kaini ne, shida Ya Amadu sunce sunfi son private school me kyau da inganci, wadda ba za’ayi dana sanin biyan kuɗinta ba, kamar dai irin tasu Adawiyya, amma ni basa so nayi bording saboda matsalar idona da kuma firgita da nake yawanyi cikin dare.
“ke ƙaro mana radiyon nan”. Yagana ce ta faɗa tana daga zaune tana karin kumallon da Saleh ya kawo ma ta yanzu, babu yanda banyi da ita ba ta ɗauki sabon brushi ɗina ta ke amfani da shi taƙi, wai ita tafi ganewa gawi ko kuma tasa ruwa ta kurkure bakinta, ita bata yarda da wannan abin me yaji na bature ba, haka kawai ya ɗaɗe ma ta dasashi, ko kuma shi brush ɗin ya karya ma ta ƴan haƙoranta da Allah ya bar ma ta.
“ku guji munafurci domin yana daga cikin manyan kaba’irai, wanda Allah SWT yaywa masu yinsa tanadin wutar jahannama. a littafinsa me tsarki yana cewa,”innalmunafikina fil darkil asfali minannar, fabashshirhum bi’azabin azim”. munafurci yana nufin cin naman mutane, ka ɗauki zancen wani ka kaiwa wani, ka haɗa husuma a tsakanin mutane da kuma zama da mutum da zuciya biyu…”. wa’azin dake ta shi ta cikin radion kenan daga bakin wani Malami, kuma jiyo sallamar Ya Amadu daga waje yasa na rage sautin radiyon ina amsa sallamarsa, dan Yagana tuni ta tada sallar wadha sallar da bata wuceta, ni kuma kasancewar cikin jini shi yasa banyi ba domin nima bata wuceni, dan na koya daga wurin Gwaggona. “tsohuwar gidan nan saiki dinga wani ƙunshe kanki a ɗaka kamar wadda taiwa kishiya laifi, aita kwaɗa sallama baki sa ni ba, ranar da wani ya shigo yayi wuff da turken awakinki naga ta tsiyar ƙunshe kai kamar daddawar ɗaƙa”. maganar yake a sanda yake sanyo kansa cikin ɗakin, kuma tunda yay maganar za’ai wuff da awaki Yagana ke tai masa gyaran murya, sarai yasan da shi ɗin ta ke, dan har ya zauna dariya yake ƙasa-ƙasa yakeyi. na duƙa na gaishe shi kamar wata munafuka, dan ni Allah ya gani ina matuƙar shayin wannan bawa nasa, ya amsa min a daƙile, ban damu ba inda sabo mun saba.
“za kiyi baƙo zuwa anjima, aina zaizo ya sameki na faɗa masa?, danni yanzu kano zanje”. maganar a ƙasaƙasa yayi, kuma na fahimci baya so Yagana taji, na haɗiye wani yawu a maƙoshina daya wuce min da ƙyar, kamin na bashi amsa da cewar,”ya sameni acan gida”. Yagana ta sallame daga sallar a lokacin ta juyo tana shafa adu’a, adu’ar da ko yinta baai ba saboda sababi na cinta. “Amadu fata na gari lamiri, kuma insha’Allahu babu abinda zai sami awakina, indai ba so kake mu sami saɓani da kai ba to ka daina ja musu jafa’i…na rasa wannan abu duk abi a sawa al’amuranka ido, alhalin kai baka damu da bawa ba, ni acikin jikokina ma mantawa nake ina da kai, tunda dama kai ba mutumin da zaa iya zama da shi ba ne, Uwarka ma banda ƴar kanta ce ai da tuni kasa ma ta hawan jini da wannan tsinannan miskilancin naka da na rasa aina ka gado shi, kana ganin ɗan’uwanka Kabiru fuskarsa kullum a sake duk wurin daya shiga faran faran da shi, amma kai duk wanda ya zauna tare da kai sai zaman ya gundure shi, sai kayi wani gumm kamar wanda ke fama da cutar warin baki…Allah ya gyaraka, amma ka sauya hali ni shawara nake baka, idan kayi aure a haka Matarka yaji zata dinga yi”.
yay murmushi yana cewa,”Hajiya Yagana ikon Allah, ai daɗi dake a tsiya dake”. saida ta gama jan carbi kan tace,”ka rabani da tsiya dan wannan kalmar a gindin Zulai ta ƙare, ahh tou”.
yace,”Yagana wai ba kya kara ne?”. saita ɗaga murya tana faɗin,”har Uwarka fa ta gama cin amarcinta bata taɓa kawo min farantin shinkafa da sunan abinci ba, ƙarshe ma sai cewa tayi ita ba zata iya girki da uwar miji ba…da labarin yazo kunnena naje har gidan na cashe ma ta, sai da taga ina da iko da igiyoyin da ta ke taƙama dasu sannan tasha jinin jikinta dani ta hankalta…Amadu ba wannan ba ma, yanzu me ya kawoka gidana da sanyin safiya haka ko gama wartsakewa ban ba?”. na dubi agogo naga har ƙarfe sha ɗaya da rabi amma ta ke kiran sanyin sassafe.
ya ciro kuɗi a aljihu ya miƙa ma ta,”gashi kici goro, sallama dama nazo yi miki dan gobe jirgin sassafe zan bi”. “to kuma sai akace maka babu rana babu dare da ba zaka iya biyo wannan lokacin ba tunda sallamar ta zama dole a wurinka”. ta karɓi kuɗin,”to an gode Allah ya shi albarka, yasa afi haka. dawowa ta gaba dai sai a dawo da himmar aure, zaman ya isa haka in ba so kuke ku shiga sahun tuzurai ba, sa’anninku duk sun tara ƴaƴa jiyama sai da naje sunan matar Saddiqu”. yace,”Yagana aimu da sauranmu har yanzu yara ne, shekara 30 fa kacal”. ta kwaɗa wani salati tana riƙe haɓa da cewa,”ina zancen yara anan, kana ganin yanda Kabiru jin daɗi da hutu yacce ya maida shi wani babban mutum, jiya fa dana dawo daga unguwa na shigo ɗakin nan na tarar da shi saina zube ina kwasar gaisuwa ce nake wani babban me faɗa aji ne a ƙasar nan, ko fa fitila ban kunna ba jiya a ɗakin nan saboda yanda hasken fatarsa ya gauraye ɗakin nan, ƙamshi kuwa kace shine kamfanin turaren, baka ji ba daka shigo?…to shi matsalarsa ɗaya hannun ɓera gare shi, shi yasa ban cika son zuwansa gidana ba”. bani kaɗai ba, hatta Ya Amadu sai da yay dariya, dariyar da ta lotsa dimple ɗinsa har ciki, ita kuwa kamar ba ita tai maganar ba, tana ɗaure kuɗin da ya bata a gefen zane ta ƙara cewa,”ba batun dariya bane Amadu, indai Kabiru ne yana da halin ɓeraye shi yasa ma yau zanje wajen Malam Kabiru ai masa rubutu ya samu yasha kamin ya koma, kar yaje can ya ɓallo mana wani ɓallin…jiya fa da zan fita Zannira ta min aiken tuwon masara da lafiyayyar miyar kuka taji man shanu, na tura abuna ƙasan buhun can saboda ma kar Yarinyar nan ta shigo ta ganshi, ashe ajiyar banza nayi, dan ina dawowa na tarar da ɗan banzan yaron nan ya gama aikawa da shi cikinsa, kai kuwa Amadu kace min Kabiru bai kamu da cutar ɓeraye ba, dan sune masu zaƙulo ajiyar da ba tasu ba…kuma fa saboda rashin kirkinsa ya kai intaha ko haƙuri bai bani ba, saima mita da yake min wai nayi shiru kansa na ciwo. ni kam Rakiya aina gaji da zaman Kabiru, lokaci yayi ya koma can dama ni bamu samu haɗuwar jini da shi ba”. na buɗe ba ki nace,”Kai Yagana, da Ya Kabirun ne ba kwa jituwa?, ranar fa daya kawo miki gasashshiyar kaza kika ce kaf jikokinki kinfi ƙaunarsa”. ta waigo ta ɓalla min harara,”aku uwar magana wa ya saka dake…wannan ai haɗa fitina ne baccin yanzu kika gama jin wa’azi, irinku ne masu ji basa aiki da shi. ni Kabirun ma ya shigo ya san yanda zaiyi a haɗa dake a tafiyar su Adawiyya ku koma tare, ba zai yiwu ki dinga haɗani da mutane ba…ai sai kisa Amadu yaga baƙina, ya ɗau kuɗinsa dubu biyu ya ban kuma kina wani batu na daban, ke dai sam baki da hali kina da ƙatuwar matsala”. dariya kawai Ya Amadu keyi, kan ya bata labarin musuluntar Emanuel, ta kuwa bushe da dariya harda kifawa, “shegiya ƙaniya! ɗan banza duk yanda akai mafarki yay ana cin ubansa a ƙabari har aka hasko masa zurfin gidansu shi yasa ya karɓe kalmar Shahada…to na masa barka, idan ka koma ka miƙan gaisuwa kace ina gaishe shi tunda yanzu ya zama namu”.
Ya Amadu zai tafi Ya Kabiru ya shigo, tun daga tsakar gida da Yagana ta jiyo sallamarsa ta ke kiran,”ɗan halak kaƙi ambato, ɗan albarka shigo ka ganni da baƙin asuba kamar korarru”. ya shigo ɗakin yana amsheta da tasa tsiyar shima. sanye yake cikin coffee ɗin yadi me ƙaramar riga, yay kyau sosai acikin ɗinkin, sai zuba ƙamshin da Yagana ke faɗi yake, yana sanye da baƙin glass ɗin dake ƙara ƙawata kyawun halittar fuskarsa. ya ƙaraso ciki yana sawa Ya Amadu ƙafa kan ya wuce inda Yagana ke masa nuni da kusa da ita. “Matar ya dai?”. ya faɗa yana taɓa kumatunta. itama ta shafo fuskarsa tana koɗa kyan da yayi, harda cewa ba zata bawa yarinyar ƙauye shi ba, idan ya koma yaga ta aure acan ya aure kawai, ta san ƴan’uwan nasa daga baya. sai kuma tace na shiga ɗaki na ɗauko ma ta ƙwaryar zuma, na kawo ta karɓa ta dire a gabansa tana faɗin,”Zuma ce farar saƙa, jiya bayan fitarka Mujibu yay min aikenta, ko sha banyi ba nace sai ka fara sha tunda nasan kai ma’abocinta ne, sha kaji me kyan ce”. ta faɗa tana gutsurowa ta kai bakinsa ya karɓa, ni dai kallonsu kawai nake ina murmushi, kuma kallon bana Yagana bane na Ya Kabiruna ne, da kallon nasa ke hadda tasirin wanzuwar wani abu a tare dani da ban san ko menene shi ba. ban san lokacin da wata dariya ta suɓuce min ba harda ƙwalla, a sanda Yagana ta tura ƙwaryar zumar gaban Ya Amadu tana faɗin,”gashi nan uban kwazazzafa saika gutsira, in faɗa maka Kabiru tunda ya shigo ya dameni wai dole saina ba shi ai kai ba sai kasha ba, naƙi nace kai na ajiyewa, shine fa dalilin wannan uwar harar daka ga yana watsa min…dama tun kuna yara haka yake sai a zuba muku abinci ya wawashe ya barka da ƴar ƙaramar murya kana kuka, ƴaƴan Zulai ai akwai cin tsiya cikinsu a buɗe yake”.
tabbas Yagana sai ta kashe auren dake da soyayya ma, ba mara soyayyar ba, yanka sharri a wurinta baya da wani wahala, kuma idan tana yi saita ɗaure fuska ka rantse da gaske ta ke, duk tabi ta ɗaure mutum da jijiyoyinsa. da taga yanda Ya Amadu yay kicin kicin saita bushe da dariya tana faɗin,”Allah sarki Amadu, Allah ya jiƙanka ba dan ka mutu ba…kai Kabiru da wasa nake yi, kar naje ya ƙullaceni idan ya koma garin arna yasa su ɗaure min baki na shiga banu”. kiran sallar azahar ɗin da akai ita tada su Ya Amadu suka fita zuwa masallaci, kuma sanda Ya Kabiru ya dawo shi ɗaya lokacin na gama kwashe shanyarmu zan shige ɗaki, na rasa dalili, na rasa me yasa yanzu indai na gansa sai nake jin ina faɗawa cikin wani irin yanayi me wuyar fassaruwa, gabana yayta faɗuwa. har ya iso gabana ban sani ba, dan nayi nisa a zuzzurfan kallon da nakewa bakinsa dake motsawa da salon murmushi, ya lakuce min hancin yana faɗin,”kallon fa?”. “Ya Amadu nima ka sammin abinda kake sawa kana ƙara kyau”. murmushi yay ya kama hannuna da ba kayan, mukai ɗakin Yagana. “duk kyauna ai ban kai Balarabiyar da Gwaggo ta haifa ba”. a sanda nake ajiye kayan nace,”tab ana cewa yanzu nafi kama da inyamurai kana haɗani da larabawa”. “inji uban wa?”. ya faɗa yana ɗaure fuska kuma yana tsareni da ido. su Sadiyya naji suna zancen, yanzu kuwa idan na faɗa masa ai babu wanda zai hana shi ɓaɓɓala ƙasusuwan yarinya ayau, dan haka sai na fizge da faɗin,”a jikina kawai nake jin kamar mutane xasu ke faɗan hakan”. har yanzu bai saki fuska ba, kuma bai bani amsa ba, sai ya kamo hannuna ya zaunar dani a kusa da shi kamar wanda zai ɗorani a saman cinyarsa, kafin ya ɗora bayan hannayena akan tafukan hannunsa yana binsu da kallo.
“wancan ranar na faɗa miki fatarki bata son wanki karki ƙara, ashe baki ji ba, shine harda yin wanki me yawa haka”. muryar tasa ta fito cikin sautin faɗa yana me shafa fatar wurin da ta kusa ɗaɗewa, ƙwarai an jima ana faɗa fatar jikina bata son wahala, shi yasa ko lokacin da Gwaggona na raye ban fiya aikin ruwa ba, aiki ma ko da Ya Amadu ya raba mana shara aka bani, idan kuma zaai wankin yara ni nake shanya, aikin taɓa ruwa baya wuce irin ɗan kaɗan ɗin nan. Yagana ta sako baki,”to kai an faɗa maka wannan yarinyar tana jin magana ne bayan ta zuciyarta”. sai ya ɗago ido ya dubeni, ni kuwa Allah yaji ya gani ina cikin wani hali, dan yanzu ko ido bana son haɗawa da shi, tunda Ya Kabiru ya soma shafa fatata da tai ja ta ɗaɗe naji numfashina ya katse a ƙirjina.
“kinyi amfani da Sol de Janeiro Coco Cabana?”. sai dai nai ƙoƙarin saita tunanina kan na kaɗa kai na amsa masa,”a’a, wanda na buɗe ma ai bai ƙare ba”. a yanzu cikin ƙwayar idona yake kallo kamar me son karanto wani abin, sannan yace,”je ki ɗauko”. na miƙe jiki kamar mara laka na shiga uwar ɗakin Yagana, na ɗauko akwatin daya shaƙo min ita da tsaraba da zai dawo, na buɗe na ɗauko cream ɗin da yake nufi, sannan na fito na ba shi. ya ɓare robar sannan ya shafa min man a hannuna duka. “yau ta zama rana ta ƙarshe da zan ƙara ganin kinyi wanki da kanki. idan ke ba kya ƙaunar lafiyarki to akwai wanda ya damu dake, ya kuma damu da lafiyarki, ya kuma ƙi jinin duk abinda zai taɓa masa lafiyarki”. a wannan karan muryar tasa a hankali ta fita, murya da ta shiga bin kowacce jijiya ta jikina tana neman ƙassara ɗan sauran kuzarin daya rage min. yawu kawai na haɗiya na kaɗa kai wajen bashi amsa. kuma har yanzu dai bai saki fuskarsa ba, saima ƙara tamketa da yay, ya ɗauke wuta kamar babu shi a wurin, nima kuma na kasa wani ƙwaƙwƙwaran motsi, sai bugun zuciyata dake ƙara tsananta, na kai yatsa zan goge ƙwallar dake neman saukowa, sai dai kamin na kai ga hakan hannun Ya Kabiru me ɗauke da hanky ya goge min. na kalle shi naga yana kallon wani gefe na daban. a raina faɗi nake na shiga uku, wai zuciyata wacce iriyar zuciyata da bata da lissafi, Yayana ne fa, Yayana da muke ciki guda, amma ta ke wani ƙazamin tunani akansa. na zuƙi wata iska me ɗumi sannan nai ƙoƙari ture dukkan wani abu da tunani ke haddasa min shi a raina, na gyara zamana na saƙala hannuna ta cikin hannunsa, ina leƙen wayar da yake shafawa. “lectures kuke?”. “umm”. ya bani amsa a taƙaice, nk kuwa nan duk neman shiri nake yi. kuma alokacin saina tuna da lambar wayar Saddiqa da ta bani ɗazu, na ɗauko ina ce masa,”Ya Please save this number for me on your phone, ta ƙawata ce ina so na kirata zuwa anjima naji if she arrives home safe and sound”. wayar kawai ya miƙo min bai tankani ba, na amsa nai dialling number nayi saving sannan na miƙa masa. “taki ce ai”. jin abinda yace na gyara zama babu shiri, na kai hannu na juyo da fuskarsa daya kauda gefe, bakina yaƙi rufuwa saboda murna. “you say what?, Ya cewa fa kai tawa ce?”. na tambaya ina jujjuya wayar da nasan tasa ce, mamaki kuma ya lulluɓeni a sanda ya fito da wata daga aljihunsa, iri guda exactly da ta hannuna, kuma sai yanzu na lura ta hannuna tafi tasa sabunta, sai na saki baki nama rasa wanne irin farin ciki zanyi. na shiga kwararo masa adu’a kamar yawun bakina zai ƙafe, sai kawai ya miƙe yay ƙofa yana faɗin,”ban siya dan ayi shirmen banza ba. research only”. “an gama Yayana na kaina, Allah ya jiƙan mahaifiya yasa afi haka”. daga haka kuma ya fita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button