SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Abuja, 12:00pm.
tun zamansu a dining dan yin break fast idon Madam Gloria ke kan Emanuel, da dukkanin tunaninta na son gano abinda ke damunsa a kwanaki biyun nan, wani abu na damunsa, kuma yana ɓoye wani abu, tabbas tasan da hakan domin ba haka yake ba, shi mutum ne me walwala amma acikin kwanakin da suka shuɗe taga duk ya sauya, koma ta kira canjin nasa da tun ranar da shegiyar yarinyar nan ta bar gidan, alƙawari ne tayiwa kanta indai ɗanta ya sami matsalar damuwa akan yarinyar to tabbas saita shafe rayuwarta da rayuwa ahalinta sun zama tarihi.
kuma ta ƙara tabbatar da akwai matsala tare da shi tun sanda aka zauna don cin abincin, amma shi ya kasa ci, illa aukin juya fork ɗin da yake akan wainar ƙwan. tayi gyaran murya hakan yasa duka yaran suka karkata hankalinsu kanta hatta kuwa Granny, yau babu Dad ya tafi wata seminer acan india.
“baka da lafiya ne?”. t tambaye shi sanda ya ɗora idonsa akanta, sai ya girgiza ma ta amsar a’a. “to mene ka tasa abinci a gaba kaƙi ci?”. ya shafi gashin kansa ta baya da hakan yake ɗabi’arsa kan yace,”ina tunanin meeting ɗin da zamuyi a gobe ne”. ya faɗa yana miƙewa yaja kujerar baya, agogon hannunsa ya kalla yaga ƙarfe sha biyu an kusa sallar azahar ma kenan, cikin dabara yace da Mom ɗin,”i want to rest, zan kulle ɗakina kar a dameni”. baki kawai ta taɓe ta bishi da ido har ya haura sama. kuma tunda ya shigo ɗakin yasa lapton agaba da zummar yin aiki sai yaji ya kasa, komai nema yake tsaya masa cak, ya saka duka hannayensa a sumar kansa ya yamutsa sannan yasa ƙafa ya ture table ɗin dake gabansa, kamin nan ya kwanta akan gadon.
tun a ranar daya musulunta yake jinsa tamkar wani sabon halitta, tamkar ba Emanuel ɗin da yake a baya ba, kuma tun a wannan ranar yake jinsa da wata iriyar natsuwar ruhi da kwanciyar hankali a tare da shi, ga kuma wani farin ciki na babu dalili da yake yini a cikinsa, komai nasa sakayau ba kamar da ba da yake jinsa da nauyi. ko a jiya da sukai waya da Amadu abunda yace masa,”Sir ka kasance me godiya ga Allah da wannan ni’ima da yay maka, ka zama me gode masa daya sa ka rabauta, ka gode masa da ya kuɓutar da kai daga duhu zuwa haske, ka ci gaba roƙonsa akan ya tabbatar da kai acikin addinin da yake na gaskiya ba tare da wannan ni’imar ta yanke maka ba har ƙarshen numfashi”.
a yauma abinda ya haddasa masa rashin nutsuwar nan da yake da faɗuwar gaba ta yanda zai tunkari iyayensa da maganar cewar ya musulunta, da waɗanna kalamai zai fahimtar dasu cewar ayanzu shine akan hanyar dai-dai su kuma suna kan hanyar ɓata, shi kuma a gaskiya ya gaji da wannan ɓoye-ɓoyen, bai saba ba ko kaɗan…ga maganar Malam da yay masa ayau na zancen aurensa da diyarsa, sai kawai ya rumtse idanunsa ya shiga karanto adu’ar daya gama haddarta ajiya, wadda ya yini a masallaci wani mutum na biya masa ita, dan Amadu ne ya turo masa ita ta waya shine shi kuma da yaje sallah sai ya nemi wani yay masa bitarsa. kuma bai manta ba da faɗin Malam dake ce masa,”duk lokacin daka ji wani al’amari ya cunkushe maka, ka kasa nemawa kanka mafita, to ka karanta Allahumma la sahla illa ma ja’altahu sahlan, wa anta taj’alu-l-hzana idha shi’ta sahlan. ma’ana Ya Allah! Babu wani abu mai sauƙi sai abinda Ka sanya shi ya zama mai sauƙi, kuma Kai kana sanya tsanani idan Ka so ya zama sauƙi”.
sai kuma ya tashi yay azamar shiryawa ya suri keys ɗinsa ya fita, kowa na zaune a parlo a sanda ya sauko ƙasan, kuma bai kula kowa ba ya fice sai raka shi da idanuwa da suka yi da mamakin sauyawar da yay cikin kwanakin nan.
kamar yanda Kulu bata so fitowata ba, haka nima ba’a son raina na fito ba, dan har cewa tayi zataje taiwa Baba magana nace babu ruwanta karta shiga lamarin da bai shafeta ba, na riga na amince ba auren dole zaai min ba.
a zaure muka haɗu da Adawiyya itama zata fita ta tambayeni,”ina zaki da tsakar rana haka?”. a harzuƙe nace da ita,”ki shaƙeni saina faɗa miki”. “Allah baki haƙuri”. ta faɗa tana kyaɓe baki, na harareta da faɗin,”da haƙurin ta mutu sadaƙar nawa kika bani, ni kaucen a hanya ko na bi ta kanki wallahi”. babu shiri ta kauce na wuce.
daga gaban gidanmu na hango arniyar motar tasa baƙa sai sheƙi ta ke, na ƙarasa inata faman ɓata raina kamar na kurma ihu. da kansa ya buɗe min wai na shigo ciki, ni kuwa nace babu inda zan shigo ni ba ƴar iska bace, idan yana iya fitowa ya fito, in bai iyawa na koma becouse i have alot to do. murmushi yay sannan ya buɗe ya zago daga ɓangarensa zuwa inda nake, da yake da yamma ne idon mutane duk a kanmu, kasancewar an daddawo daga kasuwa, kuma duk banji daɗin tsayuwar ba, na haɗiye haushina nace da shi,”faɗi da sauri”. oho na manta ba bahaushe bane, sai da naji yay shiru na dube shi ina zabga masa harara sannan na tuna, dan haka cikin yaren da zai gane me nake nufi nace,”yau kuma ina sarƙan cross ɗin?”. sai yay murmushi yace min, “ina Al-Mustapha ina sarƙan cross, sai kace wata Gift a baya”.ya faɗa da sigar tsokana, dan haka na jiyo ina ƙara haɗe fuska cike da tsiwa nace,”ni karka ƙara dangantani da wani Gift idan ba haka ba kuwa zanyi maka ɓarin mahaukaciya, waya san ma da zuciyar da ka bar ƙazamin addinin naku, Gaskiyar Yagana ma da tace Uwar bari ka gani”. a wannan karan kam siririyar dariya yayi kan yace,”ai ba saboda wani na karɓi musuluncin balle asa naji haushi na sauya ra’ayi…ba wannan ya kawoni ba, zuwa nayi ki bani shawara saboda ke ɗin me kifin basira ce”. nace,”aikuwa dai kayi farar dabara, dan babu abinda zaisa na bika na zauna acikin arna, saboda haka ka san da cewa in an ɗaura a gidanmu zanci gaba da zama, idan haɗuwarmu da kai ta zama dole ma ke gaisawa ta waya”. “idan baki bar min tsiwa ba zan cafe wannan ƙaramin bakin nan naita kissing ɗinsa har sai jamaa sun taru a wurin nan”. na sa ke ɓalla masa harara nace,”iskanci dama ai ba baƙonka bane”. yana kallona da wani makirin murmushi yace, “nan gaba kaɗan ai za ki so iskancin kema”. wani haushinsa ya tuƙeni, dan haka na bar masa wajen na ɗauki hanyar gidan Yagana, dan karma na koma gida Baba ya saito ni, dan yau gaba ɗaya ma sallah ce kawai ta ke fito da shi waje, gidan kuma ba kowa Kulu ce kawai, Innata da Inna Zulai duk sunje anguwa yara kuwa duk sun tafi makaranta, sai Sadiya da Adawiyya da ban san inda tsinannan yawonsu ya kaɗasu ba.
ban dawo gida ba sai bayan an idar da sallar magriba, kuma har lokacin gidan shiru babu kowa, Kulu ma ba ta ɗaki sai nayi zaton ko banɗaki ta shiga. dan haka na wuce ɗakin Baba sai dai ina zuwa ƙofar ɗakin na dakata da shiga a sanda naji murya Baba sama-sama kamar yana faɗa.
naja burgi na tsaya jin ya ambaci sunan Kulu yana cewa,”Hauwa wannan hukuncin da kika yanke kan Mairo da Kabiru babu inda zaije, ba kuma shine samun mafitarki ba, illa ƙara dagula lissafin komai, abinda ake gudu kuma yazo ya faru, saboda haka ki kauda ido ki bari na aura ma ta Al-Mustapha kawai, zuwa wannan lokacin da bayan na mutu sirrin komai zai bayyana zata fi samun sauƙi, tunda da aure akanta, akan wannan lokacin da ta ke ciki…banda an sami tsaiko daga ɓangaren Al-Muspha da tuni tun azahar na jima da ɗaura musu aure”.
cikin matsanancin kuka da muryar da ta fara dakushewa Kulu tace,”Malam ni kaina na gaji da ɓoye wannan sirrin, duk da cewar har yanzu bana so Hussaina ta san gaskiyar komai dan bana so rayuwarta ta ƙuntata, amma bani da yanda zanyi, ita gaskiya duk inda aka kai ga ɓoyeta watarana saita bayyana kanta…kayi haƙuri ban taɓa ƙin maganarku ba, amma ba zan iya bari Kabiru ya rasata ba, ba zan iya zuba ido inaji ina gani a ɗaura ma ta aure da wani ba bada Kabir ba, na riga nayi masa alƙawarin aurenta, ba kuma zan iya saɓa wannan alƙawarin ba”. sai tai shiru, Baba kuma ya ɗora da faɗin,”to ni ban yarda ba, ban kuma amince ba in har na isa kamar yanda kike cewa, in har ina da iko akan ƴarki to ban amince da wannan alƙawarin naki ba, ki ɓalla shi. dan sai bayan raina kaɗai na yarda Mairo tasan cewar ita shegiya ce, ta san da cewar an samar da ita ta hanyar zina ne bada aure ba, ta kuma san cewar ni da Marigayiya bamu ne iyayenta ba. lokacin da bana nunfashi kaɗai na yarda Mairo tasan ita ƴar gaba da fatiha ce ita, amma ba yanzu da nake raye ba, saboda haka batun aurenta da Kabiru da kike magana na soke shi, insha’Allah idan Allah ya bamu tsawon rai gobe zan ɗaura ma ta aure da Al-Mustapha, in yaso daga baya yasan yacca yay ya sanar da iyayen nasa”. sai kuma ta ƙara fashewa da kukan daya fi na ɗazu, a yanzu kuwa muryarta ta gama dakushewa, domin da ƙyarma ta ke fita,”a’a Malam, aurenta da wanda kake ikirarin zaka bata shima kuskure ne. idan har da gaske ɗan gidan Major Tosin ne to babu aure a tsakaninsu, domin Major shine silar zuwansu duniya ta ƙazamar hanya, hanyar da ba aure”.
sai naja ƙafata da naji ta daskare, na jingina da jikin garun ƙofar ɗakin, gaba ɗaya kunnuwana sun kasa yarda da abinda suka ji, na sulale na zube a ƙasa. muryar Kulu kuma naci gaba da shiga kunnena,”Major Tosin Afafa shine mahaifinta, dattijun da babu imani acikin zuciyarsa, shi ne silar komai Malam, shi ya zama mafarin koma…na shiga uku ni Akila, ban san ta yanda Hussaina zata karɓi cewar ita ɗin shegiya bace”.
tamkar saukar tsawa akan dutse cikin duhun dare, tamkar kaɗawar guguwa acikin iska, haka nake jin maganar acikin kaina. Mairo shegiya ce, Mairo ƴar gaba da fatiha ce, Mairo an haifeta ne ta hanyar zina, kuma wani kafiri can daban shi ne ubana, ni Mairo!. sai kawai na tsinci kaina da ƙwalla wata uwar ƙara tare da buga kaina ajikin garu, domin na farka daga wannan mummunan mafarkin mara kai mara gindi.