SIRRIN ƁOYE COMPLETE

***tunda Ya Kabiru ya rufeni bai ko waiwayeni ba, tun ina hawayen har suka ƙyafe, kawai sai na karayar da kaina ajikin bangon ɗakin, na rufe idanuwana ina tunanin irin ƙaluban da zan fuskanta a sabuwar rayuwar da zan shiga, ciki kuwa harda aurena, auren dana tabbata sai an rufa asiri sannan za’a yishi, idanma na sami me auren nawa kenan, ɗaya ɓari na zuciyata yace,“to ke Mairo banda abinki tunanin za kiyi ma yi aure ai bai taso ba, dan babu ɗan halak ɗin da zai auri shegiya, baki ga misali ga uwar taki bane, da tayi cikin shegen ai babu wanda ya aureta gata nan har yanzu a zaune…ci gaba da zaman gidan nan ma bai taso ba, yanda ƴan gari suka gama jin kowace ke shikenan kowa zai fara tsangwaramarki, ai ki tashi kawai ki tafi ki nemawa kanki mafita, shege ai sai shiga duniya. kije kema ki ɗauko musu abin kunyar kizo ki dire musu a gabansu kowanne cikinsu ki bashi ɗai-ɗai.”. sai kuma ɗaya ɓarin zuciyarta tawa ta gargaɗeni da,“kul, karki soma, itama mahaifiyar taki da hakan ta kasance da ita ƙaddara ce”. sai kawai na rumtse idona gam da ƙarfi na furta,”a’a ƙarya ne ba ƙaddara bace, kawai dai ta zaɓi ta fito dani ta wannan hanyar ne, kuma wallahi saina sata kuka ba zan janye daga ƙudurina ba”. sai nai shiru naci gaba da saƙe-saƙen neman mafita a gareni, mafitar fita daga cikin wannan ɗakin, banda ace Ya Kabiru ya ɗaureni da ko daƙiƙa ɗaya ba zan ƙara ba acikinsa, dan yanda nake jin wani mugun ƙarfi ajikina tsab zan jijjige ƙyauren ɗakin na ɓanɓare shi nai ficewata, kuma ba tare da kowa yay min burki ba, dan yanzu a shirye nake wajen karawa da kowa.
Akila ta riga ta goga min baƙin tabon da babu ta yacce za’ai na goge shi, sam ba zan iya ci gaba da zaman cikin gidan nan ba balle cikin garin, to idanma na tafi ina zan nufa?, ai kawai na biyewa shawarar zuciyata na shiga duniya shine kaɗai ya fimin, dan da shi na dace. duk da a duniya ba zan taɓa mantawa da Baba ba, amma shima ba zan ƙara waiwayarsa ba tunda ya ɓoye min sirrina, dan mene yasa tun farko basu sanar min wace ni ba sai da akazo wannan gaɓar, shima kuma da banji ba shikenan haka zasu ci gaba ɓoye min, ba zan kuma waiwaiyen wannan gidan ba illa kawai nasan duk inda zan shiga Baba da Gwaggo suna nan maƙale a zuciyata, kuma ba zan fasa binsu da adu’a ba.
wani guntun murmushi me ciwo da takaici ya subce min a saman leɓe, wato Akila ma bata da tunani, da har ta ke tunanin ta ƙaƙabawa Ya Kabiru ni ya aura, saboda dai ita zuciyarta azzaluma ce har yanzu bata rissina daga saɓon Allah ba. banda haka ina Kabiru ina ni Hussaina shegiya, dole Baba yaƙi amincewa dan shi yasan ɗansa bai cancanci auren mace mai gurɓataccen asali irina ba. kuma ni kaina ko da zan mutu babu aure ba zan taɓa aurensa ba, dan yafi ƙarfina, ni shegiya shi kuwa cikakken mutum me cikakken usili, abunma babu gami.
ina cikin wannan tunanin naji an buɗe ƙofa, ban ko waigi wajen ba. Adawiyya na gani tsugune a gabana tana kiran sunana, ni dai da ido kawai nake binta dan ko motsi banba. tasa hannu ta shiga warware ni da igiyar tana ɗan shashsheƙar kukanta, kukan da ko ban tona zuciyarta ba nasan na munafurci ne, ƙasan ranta fal frinciki, yanzu kuwa ko babu asiri sai su karɓe Al-Mustapha da hannunsu, ko ba shi ba ma ni na bar musu kowa ne.
“sannu kinji ƴar’uwata”. ta faɗa tana rungumeni. sai kawai naji saukar wasu sabbin hawayen na sakko min, na buɗi baki murya na rawa nace,”ashe kema kin jima kina min kallon ƴar zina shine ba ki taɓa faɗa min ba”. itama muryar tata rawa ta ke tace,”wallahi ban sani ba. ni ban taɓa sanin da wannan zancen ba”. na haɗiye guntun yawu da cewar,”taya akai kika buɗeni?”. tace, “dagani sai Inna ne a gidan, Baba dasu Yaya da Yagana sun wuce kai Ummanki asibiti tana ta aman jini har ta kai ga ta suma, kuma an yayyafa ruwan amma bata farfaɗo ba, shine Idris me chemist yace su wuce asibiti…Ya Kabiru bai sani ba na zare maƙullin a aljihun wandonsa”. sai na sake yin murmushin da sautinsa ne kawai ya fita, na furta,”Allah yasa ma mutuwa tayi, ta hutawa kanta daga hukuncina. na gode miki”.
nasa hannu na hure ma ta ido daga tsareni da shi da tai, na ɗaga ma ta gira da cewar,”yane, ki tashi ki fita kar tsautsayi ya dawo da Ya Kabiru ya tadda ke anan, kin san halinsa sarai”. sai tai azamar miƙewa da cewar,”to kema ki fito dan Allah, Inna ma tace karki zauna ki gudo ɗakinta, ko me ki kai ai ba laifinki bane”. “jeki kawai, ki ja min ƙofar yanzu zan fito”.
bayan fitarta na tsawon daƙiƙa uku kamin zuciyata ta gama ayyana abinda ya dace dani ayanzu, dan haka na miƙe na ƙarasa ga ƙatuwar akwatin Ya Kabiru me shegen kyau, na buɗeta na shiga binciketa, har nai nasarar samun wasu kuɗaɗe masu yawan gaske da ban san iyakar adadinsu ba acikin wani envelop, na gyara zaman trolly ɗin yanda ba zai fuskanci an taɓa masa wani abu aciki ba.
sannan na ɗauki p-cap ɗinsa na saka na fice daga gidan ba tare da ko su Adawiyya sun sani ba. gidan Yagana na wuce kai tsaye, da zuwana na ɗauki ɗaya daga cikin ɓaƙaƙen abayata da Ya Kabiru yay min tsarabarsu na saka, na lulluɓe jikina ruf ta yacce babu me shaidani balle ya nunani yace ga shegiyar can, na ɗauki akwatun kayana nayo waje, harna saka ƙafata akan dakalin ƙofar ɗakin sai idona ya zuƙo min wallet ɗin Ya Kabiru da ya ban ajiya ɗazu haɗe da wayata a ajiye akan shimfiɗar dana tashi, na koma na ɗauko ina goge hawayena ta cikin niƙabi, Allah ya sani zanyi kewar wannan ɗakin da mamallakiyarsa.
zuciyata bata yanke shawarar inda zan dosa ba saida na shigo garin kano, na samu wuri na zauna gefen wani me saida idomie, ban san wace unguwa bace, ni dai kawai nace a saukeni a wurin. warin taba sai tasowa yake daga wurin me indomien da alama ƴan shaye-shaye ne mafi yawanci zaune a gun, kuma sai na jiyo ɗaya daga cikinsu na faɗin,”Baaba kaga wata mace da lulluɓin baƙin kaya ajikinta, anya ba ɓarauniyar yara bace”. hantar cikina ta kaɗa, kamin na ɗago na kalli inda suke sai ganinsu nai tsaye a gabana suna tuhumata. na yaye niƙab ɗin ina zazzare ido nace,”wallah ni ba me satar yara bace, matafiya ce dare ne yay min a hanya kuma ban san kowa ba anan”. sai baƙin cikinsu wanda duk gashin kansa yafi muni yace,”kuma shine saboda ki jawa me so asara zaki zo ki zauna a irin wuraren nan”. yana tangaɗi ya kama hannun trolly ɗina yana cewa,”muje na baki masauki zuwa wayewar gari”. duk su du na bisu da ido, dan da ganinsu ba mutanen arziƙi bane, sai nai saurin gyaɗa kaina da cewar,”a’a zanje hotel na kwana acan..”. ban ƙarasa ba na tsakiyarsu yay wata iriyar dariya yana faɗin,”au ashema ƴar hannu ce, kawai to kizo muje muma can ɗin da zaki zauna muhalli ne me kyau. inda sabo ai an saba zamu mo re dare ne kawai”.
a wannan karan ba ƴaƴan cikina kaɗai ba, ni kaina saida na kaɗa, na shiga rarraba idanuwana ina tunanin ta yanda zan rabu dasu lafiya, ga titi sai ɗaikun motoci dake wucewa.
babu shiri na shiga sakawa napep ɗin data zo wucewa hannu, Allah ya taimakeni kuwa ta tsaya, banko faɗa masa inda zai kaini ba na faɗa ciki ina ce musu na gode, nace da me napep ɗin ya shigo min da trolly ɗin, ban sami natsuwa ba saida naga mun bar wurin gaba ɗaya sannan na shiga sauke ajiyar zuciya ɗaya bayan ɗaya.
sai da mukai tafiya me nisa sannan me nepep ɗin ke tambayata,”Hajiya ina zamuje ne, dare fa yayi ƙarfe goma yanzu”. ina zance ya kaini ne?, ni gaba ɗaya ma ban san wurin da zan dosa ba, kamar nace masa ya kaini matattarar karuwai sai kuma zuciyata ta kwaɓeni da hakan, ban san sanda bakina ya furta masa airpot.
“amma kin san kuɗinki zai ƙaru ko?”. nace masa,”babu komai muje”. a filin jirgin Malam Aminu Kano na sauka, saida na sauka kuma na shiga tunanin wurin zuwa, dana zo nan da sunan hawan jirgi wacce ƙasar zan nufa?, tayama za’ai nai bucking a wannan lokacin?, ba lallai kuɗin dana ɗebo su isheni ba. dama na ɗauka ne dan siyan abincin da zan riƙa ci, da ƙananun buƙatuna.
security ya ƙaraso inda nake yana min magana akan na matsa daga wurin, naja trolly na na shige cikin reception, na ɗauko envelop ɗin kuɗin na shiga ƙirgawa, tun ina lissafin dai-dai harya ƙwace min saboda yawan kuɗin, sai kawai na zuba musu ido ina kallo. can na miƙe na ƙarasa wurin cashier ya ƙirga adadin kuɗin naira dubu ɗariyar da hamsin, na tambayeshi wacca ƙasa zasu iya kaini?, yace min zasu kaina ƙasashe da dama in har bani da wani kaya da yawa, har zance masa ai min ticket na saudiya sai kuma maganar Akila ta haska acikin kaina, Qatar!, dan haka kai tsaye nace masa Qatar. yace min akwai jirgin da zai tashi ƙarfe sha biyu da rabi, amma na sani indai ticket nake buƙata ayanzun nan kuɗin da zan biya saiya haura ɗari biyar, babu yanda ban da shi ba akan ya haƙura ya samin duka 550 ɗin yace sai nayi addition ɗin 100k. na buɗe wallet ɗin Ya Kabiru na zaro atm ɗinsa na bashi, nace ya zara aciki.
ƙarfe sha biyu da rabi jirginmu ya tashi, kuma ƙarfe shida na safe jirginmu ya sauka a ƙasar Qatar. saukarmu a airpot na ciro wayata nayi serching hotel nearby. “Hilton Doha, Diplomatic District”. nace da texi drivern a sanda na shiga na zauna na daidaita zamana.
online booking nayi dan haka ina isa kai tsaye stairs na hau zuwa room ɗin dana kama, ina shiga nai wanka na shirya sannan na kwanta ina tunani kala kala, tunanin dake neman tarwatsa zuciyata, hakan yasa na tashi na fito dan naga gari ko na sami sassauci a zuciyata.
tafiya nake ina kalle-kallen yanda ƙasar ta ke gwanin sha’awa, ba irin nigeria ba, kowanne bulding nasu me kyau da tsari, gasu kansu mutanen garin masu burgewa. ina tafe ina karanta wani symbol ban sani ba kawai naji nayi karo da mutum wayoyin hannayenmu duka suka faɗi, muka sunkuya muka ɗauko munaiwa junanmu sannu, sai dai a sanda hannuna yay gogayya da farin hannun dake ɗauke da jan lallai sai naji zuciyata tayi bugawar da ko a sanda naji cewar ni shegiya ce batai ba, haka kuma naji ina shakkar haɗa ido da koma wace idan muka ɗago.
ko dana baro gida bana faɗuwar gaban da nake yi a halin yanzu.
“Sannu, kiyi haƙuri bada sanina na bigeki ba”. abinda na faɗa kenan cikin harshen turanci, sai dai ita abinda tace min da larabci ta faɗa. dama nayi goggling akan yaren ƙasar english da arabic kawai suke ji saboda haka ne ma yanzun na bata haƙuri da english.
ɗagowar da zanyi da kaina kawai sai naga Kulu a gabana, kallonta nake da maɗaukakin mamakin dake haskawa a ƙwayar idona, tare da wani kallo na daban da ni kaɗai nasan ma’anarsa. itama kallona ta ke da mamakin, mamakin da zan iya kiransa na rainin hankali, dan ko ban rantse ba yacce idanuwanta ke nunawa shaida min yake basu gane ni ba.
saina buɗi baki nace,”hmm mayaudariya kawai”. na faɗa tare da bangajeta zan wuce, ba ganinta a ƙasar ne mamakina ba, yanayin canjawarta shine abin mamakina, kai bakace ba matar dana baro cikin wani hali ba, ta gudo ta barsu cikin tashin hankali.
sai naji ta dafo kafaɗata, na dakata da tafiyar ta zagayo gabana. cikin fusata nace,”wai nufinki hakan da kike shi zaisa na sauka akan ƙudurina ne. ko kaɗan bana tausayinki, kije kiyi rayuwarki nima nayi tawa, kije ki ɗora daga inda kika tsaya, nima zan shigo sahunku”.
da mamakina na rainin hankalinta sai ji nai tace,”bana jin abinda kike faɗa cikin yaren da kike magana, yare biyu nake ji arabic and english, kina iya min magana da su”. nai mata wani kallo na kin raina min hankali, naja tsaki zan wuce maganarta ta dakatar dani. “please who are you?”. na zuƙi numfashin fusata na sauke sannan nai juyo gareta nace,”ni ce shegiyar ƴarki da kika haifa a yawon tazubar ɗinki, ƴar da sai da ku kai tarayya da ƙazamin abokin karuwancinki wato Major Tosin sannan kuka samar dani. Akila ina fatan yanzu kin shaida wace ni”.
idan na lura kamar tayi suman tsaye ne, saboda haka saina buɗe jarkan swan water ɗin dake hannuna na fesa ma ta shi duka a fuska dan ta samu ta farfaɗo daga duniyar tunanin da ta faɗa. sai dai me! kamar yanda na tsammaci dawowarta, haka na sami saukar marin da sai daya kaini har ƙasa, marin da shigarsa ya haddasa ganin tartsatsin wuta acikin idanuna, marin da saida yasa jina da ganina suka ɗauke gaba ɗaya, dan haka ne nai zaman dirshan a ƙasa ina jiran dawowar hayyacina, sai dai ji nai kamar a lokacinne ta ke wankeni da marin, dan haka nai saurin dafe kuncina duka ina maida numfashi da sauri sauri.
a ƙalla na ɗauki tsawon daƙiƙa biyar kamin na dawo duniyar dana bari, kuma ina ɗago kaina naga har lokacin tana tsaye a gabana, da yanayin fuskar dana kasa fassara abinda ke shimfiɗe akanta, tunanina ya tsaya cak sanda naji ta ambaci sunan.
“Maryam”. ta faɗa da kakkausar muryar dake shaida min da gargaɗi ne zai biyo bayan sauran furucin. sai dai nima zuciyata ta kai maƙura, dan ta jima da bushewa, ko kaɗan bana ma ta kallon wannan sunan na uwa da ake ambata, na miƙe a fusace zan kai hannuna fuskarta ta riƙeni ta watsar da hannun tare da sake sauke min wani sabon marin daya sani natsuwa kamar yanda tace,”ki tsaya ki saurareni kamin na illata fuskarki da yatsun hannayena”.
idan da ace ban san Akila, to tabbas zan rantse wannan ba ita bace, sai dai tsmbayar da tai min ita ta wanzar da maɗakakin mamaki da al’ajabi a tre dani. “ina Akila?”. tambayar da ta min kenan, kuma saida na ƙara maimaitata acikin raina kamin nace da ita, “rainin hankalin naki har ya kai nan?, ko a duniyar karuwancin naki ma…”. a wannan karan marin da ta sakar min maganata ce ta ɗauke gaba ɗaya, kuma zan iya rantsewa idan na buɗe bakina babu harshe balle haƙori.
cikin tsananin ɓacin ran da zan iya rantsewa a duniyata ban taɓa ganin wani acikinsa ba ta fara ce min, “dan uwar da tai silar ubanki zuwa duniya, Akilan da kike kira da waɗannan kalaman rashin ɗa’ar taki ba itace ta haifeki ba, ni da kika ganni a gabanki nice uwar da kika fito daga cikina, ni ubanki yaywa ciki ba Akila ba, ni Aaliya ni ce na haifeki. ita kawai sadaukarwa tayi, kuma akanta babu mahaluƙin da ba zan iya ɗaukan kowanne mummunan mataki akan aibantata ba, saboda haka ki iya bakinki kamin ki harzuƙa zuciyata.
ina kallon zuciyata ta bani ke ƴata ce, kuma sai kika zo da maganganun da suka tabbatar min da hakan”. ta ƙara matsowa gabana ni kuma ina ja da baya, har ƙarshena ya kai jikin motarta, ina jin yanda zafin numfashinta ke sauka ajikina, ta miƙo hannu kamar wadda zan bawa wani abu tace min,”ina Akila?, dan tsawon wannan shekarun ita nake nema bake ba, duk da cewar na san zan ganku tare”. shirun da nai yasa ta bugan tsawan,”ba za ki faɗa min ba?”. ta faɗa tana zare min idanu. a tsorace nace da ita,”ai tana nigeria”. “uban me ya rabaki da ita da har kika zo nan”. cikin saurin bada amsa nace,”ai sai yanzu ta faɗa min asalina shine na gudo nan zan shiga yawon duniya”. sai naga ta juya tana duban drivern da suke tare da shi. “ka kira Al-Hassan an min buking tafiya nigeria yanzu ba tare da ɓata lokaci ba”. sannan ta dawo kaina,”karki fasa shiga duniyar. abu ɗaya da zan gargaɗeki idan bakinki ya kuma furta Akila saina sa an datse shi, sunanta Ummi daga yau ɗin nan”. a tsawace tai min maganar, tsawar da sai da tasa jikina duka kyarma, kuma babu shiri nabi bayanta muka shiga mota kamar yanda ts umarceni da idanuwanta.