NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

A Ɗaya Ɓangaren.
saukar jirginmu a airpot ɗin Malam Aminu Kano muka fito hannuna na cikin na Al-Hassan yana riƙe da ni, kuma tun bayan wasu daƙiƙu bayan tasowar jirginmu daga can Qatar nake zubar da hawaye, hawayen da har yanzu suka ƙi tsayawa.
Mami na gaba muna biye da ita a baya har muka ƙaraso bakin farar motar da akazo ɗaukanmu acikinta, sai dai a sanda aka buɗewa Mami murfin motar zata shiga a sannan na zube gwiwoyina a gabanta, cikin amon muryata da ta gama raunana, cikin sautin muryar da ke fitowa da rawa, cikin sautin muryar da zuciya ta ke a karaye, cikin sautin muryar kuka, na tattaro busassun yawun bakina da suka ƙafe na shiga roƙonta.
“Mami dan Allah kiyi haƙuri, dan Allah kiyi haƙuri kar naje wajen police, wallahi ban san a inda zan nemo kuɗi na biya Ya Kabiru ba, kuma idan naje wajensu tsare ni zasu yi”. kaina na ƙasa nai maganar, inda ƙwayar idona ke akan doguwar farar ƙafarta me ɗauke da zara-zaran yatsu. a jikina naji kallon da ta ke bina da shi, kuma har tsawon daƙiƙa 1,2,3,4, bata ce komai ba, ko ba’ace ba nasan nazari ta ke, haka zuciyata ta faɗa min, kuma acikin wannan ƙunar dake zuciyata, ta cikinsa naji gilmawar furucin Al-Hassan daya ce da ita,”Please Mami, ki min alfarmar idan munje wajen Kabir ɗin ni zan biya shi kuɗaɗensa”. kuma shirunsa ya haɗu da maganar da nai,”balle ma ba zai taɓa cewa na biya shi ba”. sai kuma Mamin tace,”sanin cewar ba zai ce ki biya shi ba shi yasa kika sata kenan?”. nai saurin girgiza kaina da sauri,”a’a wallahi Mami, ba haka ba ne, sharrin zuciyata ne”. sai ta ƙara cewa,”to ni ba ɓarauniya bace, dan haka ba zan yarda na haifi ɓarawo ba”. sai na ƙara fashewa da kuka ina faɗin,”Mami wallahi tallahi ban taɓa sata ba, ban taɓa ɗaukar abin wani nai amfani da shi ba, yanzuma tsautsayi ne, dan Allah kiyi haƙuri kar naje gaban ƴan sanda”.
zuƙar nunfashi ɗaya tai sannan tace,”ku shiga mota mu wuce”.
dai-daituwar zamanmu a motar Al-Hassan yasa handky ɗinsa yana goge min hawayena, kuma muryarsa a hankali ta fito ta cikin shirun motar.
“ba za ki daina kukan ba kuwa”. amon muryar ya fito da sautin nuna damuwa da kuma kulawa. nima muryarwa tawa ta fita a hankali wajen ce masa,”zan daina, amma sai Ummi tace ta yafe min abinda nai ma ta tukunna”. sai yace,”bana tunanin Ummi zata ƙi yafe miki akan wannan laifin da nasan ɗan ƙarami ne a wurinta, abinda kullum Mami ke faɗa min shine, Umminka tana da haƙuri, tana da kirki, kuma ƴar aljannah ce insha’Allahu”.
na fesar da wata iska daga bakina, tare da sauke gajeran numfashi, dukkan tunanina ya tafi kan rayuwata ta baya kamin na san komai a yanzu, lokacin dana girma na fara wayo, zuwa lokacin dana mallaki hankalin kaina, bakin Ummina a rufe yake da yin magana, idanuwan nan kullum akaina suke cike da so, ƙauna da tausayi, ta takure kanta a waje ɗaya, acikin ƙunci da damuwa, ta hana kanta walwala balle ta sawa kanta jin daɗin rayuwa, a gida ɗaya muke rayuwa, tana so ta kasance tare da ni, amma gudun halin da zan shiga idan naji wace ni, ta haƙura ta nisanta kanta da ni, ba don komai ba sai dan saboda ni naji daɗin rayuwa, ta fara tsufa tun da sauran ƙuruciyarta kuma wai duk saboda ni.
amma na rasa da me zan saka ma ta sai da waɗannan kalamai na rashin tarbiya, na rashin ɗa’a, na rashin ya kamata. ko da yake ba laifina ba ne, i was very shock a lokacin da naji cewar ni ƴar zina ce, shi yasa na kasa controlling zuciyata, amma wallahi bada son raina ba, nayi nayi na lanƙwasa zuciyata amma sam na kasa saboda tafi ƙarfina a lokacin, tabbas na aikata babban kuskure, na aikata abinda nake yin nadamar aikatawa ayanzu, amma ko kaɗan, ko kaɗan na san Ummi bata cancanci abinda nai ma ta ba, uwata ce, a koma yata sameni ya akamata ace na martaba ta.
to wai ma aina na dinga samo waɗannan ƙazaman kalamai da na dinƙa jifanta da su ne?, ko da yake kamar yanda na faɗa ba laifina ba ne, zuciyata ce, babban tashin hankalina a yanzu shine, idan na tuno wannan barazanar dake shimfiɗe a ƙwayar idon Mami sai naji kamar na haɗiyi zuciya, a yanda nake bana taɓa tunanin Ummi zata iya yafe min abinda nai ma ta, ga Al-Hassan ya tabbatar min da Mami bata barazana, tana faɗar abinda tasan cewar zata aikata shi ne, kuma ya tabbata, shi yasa a kullum kuma a ko da yaushe alƙawari yake biyo bayan furucinta…to ni kuwa Maryam idan haka ne na shiga uku, dan tabbas nafi kowa rashin dacewa a duniyar nan.
kuma sai kalaman Al-Hassan suka shiga haskawa acikin kaina, a wannan lokacin da muna cikin jirgi, lokacin da Mami ta tashi ta koma seat na daban don gudanar da aikin office ɗinta acikin system, Al-Hassan ya shiga toilet ya fito, kuma daya zo wucewa ta gabana ne ya tarar da ni ina zubar hawaye, idanuna a rufe suke a lokacin saboda haka har ya tsuguna a gabana ban sa ni ba sai da naji yana faɗin.
“a rayuwata hawayen mace yana ɗaga min hankali, ki tambayi Mami na kiji, yanzu-yanzu hawayen mace zai hargitsani, ya kiɗima ni, ya gigita ni, saboda haka ki taimakeni ki goge su.
shin ma me akai miki a duniyar nan da har kike zubar da hawaye masu gudu irin haka?”.
ban amsa masa ba illa iyaka buɗe nauyayyun idanuwana da nai na saukesu akansa ina binsa da kallo kawai, ina kallonsa da hoton fuskar Al-Mustapha, naga lokacin da wani abu ya wuce ta maƙogwaronsa kafin ya ƙara buɗe baki yace min.
“Mami bata taɓa yi min wata magana da wasa ba, duk abinda ta faɗe shi to haka yake da gaske. shi yasa ko a yanzu da ta faɗa min kece ƙanwata banyi tantama ba na amince da hakan, duk da zuciyata tana cike da mamakin ta yanda akai ta sameki bayan tsawon shekaru goma sha bakwai da aka ɗauka, alhalin kuma tun kina jaririya rabonta da ke da mahaifiyarmu, sai dai kuma a sanda nake kallonki yanzu zuciyata ta kore duk wani tunani da kokonto, na ƙara amsar maganarta, duba da kamanninki, kamanninki zam irin nasu ne, siririyar fuska kawai kika fisu”.
sai nace da shi,”yanzu kai kenan baka damu da ta hanyar da aka bi aka haifemu ba?, ka ganka fa hankalinka a kwance, ko baka san komai ba ne?”. murmushi me ciwo naga yayi da ya tsaya iyakar leɓensa, kafin ya bani amsar,”nasan da cewar ba ta hanyar aure aka haifeni ba, na san da wannan tun banma san me hakan ke nufi ba har zuwa sanda na girma na san ma’anar kalmar zina, na kuma san ta wannan hanyar aka bi aka haifeni, kuma bayan haihuwar tawa mahaifiyata ta gudu ta barni saboda kunyar duniya. kin san a lokacin da Bella ta tareni da wannan maganar me nayi?”. da mamaki na zaro ido waje ina tambayarsa, “aina kasan Bella kuma?”.
“Bella Kaka ta ke a wurinmu. kuma ita ta shaida min waye ni, kuma a wannan ranar da ta faɗa min kwana nai ina aikata abinda ban taɓa tunkarar yinsa ba a rayuwata, kwana nai ina shan abinda Allah ya haramta saboda baƙin ciki, idan da ace giya na yin tsiro da yanzu tayi rassa ajikina. to amma daga baya da Abi yay min nasiha akan karɓar ƙaddara sai naji zuciyata ta washe. duk da cewar sai da Mami tai min barazanar yankani idan na kuma yunƙurin shan giya ko kuma na kuma furta zan shiga duniya balle na furta kalmar ɗaukar fansa akan Aaliya, ba barazana ta ke min ba, zata aikata ɗin kamar yanda ta faɗa. ta kuma gwada na gani, dan sai da ta nuna min, banda zuwan Ammi wajen da alokacin da ta kwantar da ni ta ɗora wuƙa a wuyana tsab saita yanka maƙogorona na zama tarihi”. furuncinsa na ƙarshe yasa na saki guntuwar dariya da ban san lokacin da naita ba, da mamaki nace da shi,”yankawa dai!, ita Mamin saita yanka ka?, wace kalar mata ce ita ne?”. tashi yay daga tsugunen da yake ya zauna kujerar kusa da ni yace,”idan aka tashi rubuta sunan masu faɗawa da cikawa to sunan Mami ne zai zo a farko. haka kuma tana sahun masu zafin zuciya, irin zuciyar da bata son wargi. uwa ce ita me daɗin sha’ani, amma kuma sam bata tolerating wani iskanci daga ɗa”.
nai shiru ina nazarin kalamansa, kamin na jefa masa tambayar, “to dama su biyu ne da gaske?”. sai ya juyo ya kalleni,”ba ki sa ni ba dama?”. kaina kawai na ɗaga masa ba tare da bakina ya furta komai ba.
“twins ne su kamar yanda muke, basu da wani banbanci a kamannin halittarsu, sai dai kuma a halayya da ɗabi’u. Mami itace ƙarama wadda ta haifemu kuma itace Babba me suna Aaliya”. “Aaliya kuma?”. ya jijjiga min kai don ba ni tabbacin amsata. sai na shiga girgiza kai ina faɗin,”ya ake neman a rikita min lissafi ne. wadda na tashi a wurinta fa tace sunanta Akila, ita kuma Mami tace min sunanta Aaliya. kai kuma yanzu kana ce min Mami ce Akila, ya haka kenan?”. sai yace,”nima a ɗazu dana fuskanci tana kiran waccan da Akila na shiga cikin duhu, kuma Mami ba me son yawan tambaya bace shi yasa kika kalla nayi shiru, amma har zuwa yanzu kaina a ɗaure yake da sunan da ta kira”.
sai kawai na zuƙi wani numfashi kamin na furta,”to ni dai kome za’ai ba zan fasa ɗaukar fansar shegantani da akai ba”. na faɗi hakan har zuwa lokacin zuciyata bata rissina ba.
sautin murmushin takaicinsa na jiyo ta gefen kunnena tare da cewar”a kanwa za ki ɗau fansar?”. ina rumtse idona nace da shi,”akan Akila da Major, Al-Hassan idan kai ka yafe wallahi tallahi ni ba zan taɓa yafewa ba, saina ɗauki fansar rayuwata akansu, sai na saka su kuka fiye da wanda suka sa ni, saina saka sun wulaƙanta a duniyar nan, wannan alƙawarina ne”.
sai yay saurin katse maganar tawa ta hanyar rufe min baki da tafin hannunsa,”shhh, Hussaina waɗannan kalaman fa har ina?, ina kike so ki kai ɗumbin zunubi?.
to bari na faɗa miki abinda haƙuri bai bada ba rashinsa baya taɓa bayarwa, kuma ai idan hankali ya gushe hankali ake sawa ya nemo shi, nima nayi waɗannan kalaman a sanda aka faɗamin ni ɗan zina ne, amma sanda na sami tarihin nasihohi da wa’azi daga bakin Kakana Shaik Tamin, kuma na zauna nai nazari da tunani sai naga ɗaga hankalina ma nace saina ɗauki fansa babu abinda zai haifar min fa ce ƙara dagula rayuwata…Hussaina wallahi Allah yana sonmu da Rahma, idan ba ki san da wannan ba to ki sa ni ayanzu, Allah yay mana ni’imar da bai kamata mu butulce masa ba. kina ina, kina ina Hussaina ake haifar irinmu a watsar da su, wasu kuma asa su a kwalin indomi a rufe, wasu kuma asasu a masai a floshing ɗinsu, wasu ma suna jarirai shagaf a kashesu ta dole, kije gidan marayu ki kalla irinmu sunfi a ƙirga, waɗanda basu san iyayensu ballantana danginsu, wasu kuma suna nan suna gantali a duniya, suna ƙasƙantacciyar rayuwa, bakin duniya na binsu…amma mu da ubangiji ya tashi, sai ya rufa mana asiri, bai sa mun wulaƙanta ba, bai sa mun tozarta ba, bai sa mun ɗanɗani wannan ɗaci da baƙin cikin a zuciyoyinmu ba tun muna ƙanana, sai ya barmu acikin gatanmu, ya barmu acikin ni’imarsa, to kuma dan me zamu butulce masa Hussaina?…Hussaina babu macen da zata so ace ta haihu bata hanyar aure ba, haka ma banda ƙaddara babu abinda zai sa mahaifiyarmu ta samar damu ta wannan ƙazamiyar hanyar, na sami tabbacin hakanne ta irin shaidar da mahaifiyar ta samu daga wajen mutane, idan har kuwa haka ne akan mene ba zamu yi ma ta uzuri mu yafe ma ta ba?, mu tayata goge wannan ruwan hawayen baƙin cikin da ta jima tana yinsa tun bayan zuwanmu duniya…a barshi ma da gangan tai, amma shin ko kin san wannan lamarin tsakaninta ne da ubangijinta, kuma da zarar ta roƙe shi zai yafe ma ta, to idan har shi zai yafe ma ta dan me mu ba zanu yafe ma ta ba?, kuma da kike ikirarin sai kin saka sun wulaƙanta, to ki nutsu da kyau, ki sakawa zuciyarka salama na lokaci kaɗan, sai ki dawo da hankalinki gareni”. a wannan lokacin sai yay shiru, ni kuma sai na ɗan kalle shi, fatarsa tai jaa, manyan idonsa irin nawa sunyo waje.
a hankali na rufe idona, na zuƙi doguwar iska kamar yanda yace, sannan na fesar, sai dai hakan har sau uku kamin na shiga biya, “innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, hasbunallahu wani’imal wakil”. ashe a fili na faɗa, ba’a zuci ba kamar yanda nai tsammani, sai naji Alhassan na ce min,”yauwa, kiyi ta maimaita hakan a fili, akan laɓɓanki da kuma cikin zuciyarki”.
wucewar daƙiƙa 1,2,3,4,5 sai naji wani sanyi na daban yana ratsa zuciyata, kuma sai naji Al-Hassan yaci gaba da cewa,”to ki faɗa min shin za ki so ace mahaifiyarki ta wulaƙanta a duniya?, shin za ki so yau ace mahaifiyarki ta tozarta?, to idan ma kinyi hakan ke mene makomarki? kuma mene ribarki?…haba Hussaina, yanayinki bai yi kama dana yarinyar da bata da ilimi ba, ko kuma bata sami tarbiya ba, idan ace tunaninki ya gushe, to ina iliminki fa?, ki tattaro hankalinki wuri ɗaya ya dawo miki da iliminki, wannan ilimin naki ya tuna miki cikin rukunan musulunci akwai yarda da ƙaddara me kyau ko mara kyau tare kuma da fawwwalawa Allah komai.
sannan ilimin naki ya tuna miki faɗar Allah SWT da yake cewa, “kuyi haƙuri, haƙiƙa ubangiji yana tare da masu haƙuri, kuma yace ku zama masu afuwa ga wanda ya saɓa muku, haƙiƙa ubangiji me afuwa ne”. Fansa! Fansa dai! Hussaina idan har za ki tuna wannan faɗin na ubangiji to ki faɗa min mene amfani ɗaukar fansar?
kuma ma abu mafi muni da tashin tashin hankali ɗaukar fansar taki akan uwa, wadda saita ɗaga miki digadiganta ne tukunna zaki samu wucewa zuwa aljannah. Macen da ita ce ma’aiki ya faɗeta har sau uku kamin ya ambaci uba, Uwa Hussaina, Uwa ba’a bar wasa ba, ki shiga hankalinki, ki kuma shiga nutsuwarki, domin ɓacin ranta shi zai kaiki wuta, hawayenta kuma ya turaki jahannah.
shin ni kin san tsawon shekara nawa na ɗauko ina roƙon Allah ya haɗani da ita, na jingina a kafaɗunta, na goge mata dukkan wani datti na damuwa dake cikin ranta, na maye ma ta gurbinsa da farin ciki, ba don komai ba sai dan kwaɗayin wannan ɗumbin ladan na kyautatawa iyaye.
to wallahi Hussaina inda ba so kike ki ɓata lahirarki ba? tun wuri ki tuba, yo zunubin ki kaishi har ina?, kiyi ƙoƙari ki gyara lahirarki tun wuri, kuma tun lokaci bai ƙure miki ba, mutuwa na nan zuwa, ko ta ɗauke ki ko ta ɗauke Mahaifiyarki…Hussaina dukanmu masu laifi ne in one way or the other, kuma a kullum burinmu da fatanmu shine a yafe mana, kiyi tunani, ki ƙara tuna wannan girma da darajar na iyaye kamin ki zartar da hukunci”.
tunda ya soma maganar naji numfashina yana yin sama sama da har ta kai ga na gagara wajen in fesar da shi, ƙwaƙwalwata kuma naji tana bugawa da wani irin duka dum dum, kaina ya cushe.
“kice astagfirullah, kiyi istigfari ko kya sami sauƙi a zuciyarki, dan wallahi wannan mummunan ƙudurin kaɗai da kika ɗauka ba zai barki jin daɗi ba”. Alhassan yace da ni a sanda ya lura da yanayin da nake ciki, kuma cikin wata iriyar murya da ba zan iya kwatanta yanayinta ba na shiga faɗin,”Astagfirullah, Allah na tuba, Allah na tuba”. faɗa nake ina ƙara maimaita, a lokacin babu a inda nake so na ganni illa agaban Ummi nah, babu abinda idanuwana ke son gani sama da Ummi nah, ita kawai, ita kaɗai don inje in nemi yafiyarta.
a hankali na shiga buɗe idanuna ina mai jin zuciyata a matse, na sauke idona akan titin da muke cikin go slow, sai naji Alhassan na saka min earport a kunnena, suratul yusuf ce ke tashi cikin ƙira’ar Shuraim, kuma a hankali sai naji ina samun nutsuwa.
“ranki ya daɗe gamu mun shigo garin bichi”. security ɗin da aka haɗa Aaliya da shi ya faɗa, yana daga gaban motar a zaune.
sai tace da Maryam,”ke gamu a garinku, sai ina kuma”. na buɗe idanuwana na sauke su acikin garin bichi, garin da na fita da niyyar barinsa har a bada, na haɗiye abinda ke dunƙule a maƙogorona sannan naiwa driver ɗin nuni da hanyar da zai ɗauka.
tsayuwar motarmu a ƙofar gida na riga kowa buɗe murfin motar, Mami na fitowa abinda bakinta ya furta shine,”anan Akila ta ke rayuwa?”. na ɗaga ma ta kai kawai, sannan na wuce zuwa cikin gidan. a tsakar gida na sami Inna Zulai da Adawiyya da Sadiya sai Zubaida, kuma dukansu sai suka miƙe a razane saboda ganina kamar wacca aka jefo.
“Mairo”. Inna Zulai ta faɗa, kan Adawiyya ma dake dafe da ƙirji tace,”me kika dawo yi? hankalin kowa ya tashi anata cewa kin gudu kema kin shiga duniya”. na sharesu na wuce zuwa ciki, dan bata su nake ba, hasalima a yanzu bana son wani abu wai shi ɓacin rai, sai dai ƙofar ɗakin Gwaggona a rufe da kwaɗo, saboda haka na dawo nace da su,”ina Ummina?”. da mamakinsu suke tambayata,”wace kuma haka?”. “Babata ta ainihi”. Inna Zulai tace,”ohh ai tun jiya da suka wuce asibiti basu dawo ba, ɗazun nan ma Kabiru yazo ya ɗiba kayanta wai an basu kwanciya”.
“innalillahi kwanciya kuma, a wane asibiti?”. “asibitin bichi, za ki je ne?”. kamin na basu amsa sai ga Mami ta doko sallama, kuma kafin wani cikinsu ya amsa Inna Zulai dake daga bakin ƙofa tace,”ikon Allah ba dai ma sune suka dawo ba, kinji maganarta ƴar halak”. sai nace,”ba ita bace”. “amma kuwa maganar zam ita…wa’alaikum salam, shigo”. Innar ta faɗa tana dawo daga inda nake tsaye tana leƙan zaure, a tsorace kuma taja da baya tana dafe ƙirji kamar wadda taga mugun abu,”na shiga ni Zulai, Kulu kece haka?”.
na ƙara bata amsa da,”ba ita bace Innah, ƴar’uwarta ce”. sai ta kalleni tana ƙifta idanu da cewar,”me?, ke kinji yarinya zata manna min haka…Kulu yanzu da gaske kece acikin wannan shigar ta alfarma, a’a ke ni nama kasa ganewa, kamar fa ba wadda ke kwance hajaran majaran ba”. na sake cewa da ita,”Innah wannan ba Kulu bace”. nai ƙoƙarin kallon Mami dake bin gidan namu da kallo, sai na kasa saboda kwarjinin da ta ke da shi me kassara kallon mutum.
kaina a ƙasa na shiga ma ta bayanin cewar tana asibiti, kuma a kiɗime tace da ni muyi waje, acikin sakan ɗaya nema ta ke ta firgice daga jin batun rashin lafiyar ƴar’uwarta. direct kuma bichi general hospital muka nufa, muna zuwa muka ji batun cewar jikin nata yay tsanani an turasu asibitin AKTH. hankalinmu duk ya ta shi, ban ankare ba naji saukar wani gigitaccen mari a saman fuskata.
“duk da ace ba ki gudu kin barta ba da ba ta shiga wannan halin ba, haka zuciyata ta ke faɗa min”. kuka nake sose kuma micijin da na gani ta wajen ƙafata shi yasa ni razana na doka tsalle zuwa bayan Alhassan na maƙalƙale shi ina ihu, muryar Mami kuma ta fito da furucin cewa,”ba abinda zai miki a yanzu, amma ki san da cewar ni na miki ƙofinsa…kuma ki sakawa ranki matsawar ya zama kece silar kwanciyar ƴar’uwata saina saka ya shiga jikinki, haka idan na sameta a yanayin da zuciyata ba zata ɗauka ba Maryam ba miciji kaɗai ba, sai kinsha mamakin abinda zan miki”. duk saina tsure na nemi fita acikin hayyacina, da alama dai Mami so ta ke ta haukatar dani da tsoronta.
muka shiga mota driver yaja, kuma kamar na san zata iya kasancewa, saina ce da security ɗin da aka haɗomu ya bani aron wayarsa, ya miƙo min na saka lambar Ya Amadu, dan nasan ko na kira Ya Kabiru ba zai tsaya saurarona ba. yana ɗagawa kuwa na tambaye shi inda suke, baima shaidani ba, dan kai tsaye ya bani amsa da, “muna international hospital”.
da zuwanmu asibitin na hango Yagana a bakin ƙofar room ɗin tana alwala, kuma tun daga nesa na ƙwala ma ta kira, ta ɗago tana dubana kamin ta kai dubanta ga wadda ke biye da ni, sai naga ta miƙe daga sunkuyen da ta ke ta leƙa cikin room ɗin ta window, sannan ta kuma dawo da kallonta kan Mami, kamin tayi fatali da butar da ta ke alwala ta faɗa cikin ɗakin da gudu tana zabga salati me haɗe da kururuwar ihu tana faɗin,”Yau naga ta kaina ni Rakiya”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button