NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

A can ɗaya ɓangaren.
Amarya ce zaune akan kujerar dake cikin matsakaicin falon gidan, yayin da wata ma ta ke fuskantarta, yanayinta na nuni dana wanda ya tattara hankalinsa gaba ɗaya ga mutumin dake masa bayani.
a wannan lokacin babu abinda zaka tsinta a saman fuskar Amarya fa ce zallar ɓacin rai, babu walwala balle yanayinta ya nuna maka tana tare da wani abu wai shi farin ciki.
ta kai hannu ta zame ɗankwalin dake kanta zuwa baya, sannan ta fuzgar da iska daga bakinta, ta dubi matar dake gabanta da irin kallon da zai shaida maka girman matsayin da ta ke da shi ga waɗanda suke ƙasanta. wucewar daƙiƙa biyu tana dubanta kamin ta ɗauke idonta daga kanta ta mayar da shi kan wayarta dake gefenta tana ringing, kuma tana ɗaga wayar ta kara a kunnenta da cewar,”bana son wani abu wai shi kuskure ya kuma shigowa cikin lamarina, ka faɗa min kawai anyi nasara Musbahu?”. ban san me na cikin wayar ya faɗa ma ta ba sai naji tace da shi,”ka tabbata raunin daya samu ba zai barshi ya ƙara shurawa ba?”. wucewar wasu sakanni kamin na cikin wayar ya gama bata amsar tambayarta sannan ita kuma tace da shi,”da kyau!, yanzu abunda za kai kaja abinda zaija tsaiko a wajen mutanen da suke ƙoƙarin kaishi asibiti, kuma tunda kace sun kira waya nasan Amadu suka kira, kuma Amadun zaice zai taho wurinsa, ka kafa ka tsare Musbahu kar Amadu ya ƙarasa wajen nan, domin duka su biyun nake so a rasa a lokaci guda, ta yanda zanyi aikin kwashe duk wata dukiyar da Kabiru ya tara ba tare da hankalin kowa ya kawo kanta ba…sannan a ɗazu dana koma gida na tsinci maganar su Zulai suna batun kamar ita wadda ta zauna a gidan namu ɗiyar wata ƙusan ce, dan sunga alamun hakan a jikin ƴar’uwarta da tazo, to da zarar ka kawar da Amadu shima, ina so ka shiga yi min binciken wace ita, yanzu zan san yanda nai Malam ya faɗa min asalinta ta yanda aikin zaizo maka da sauƙi….”.

Plss Share&Comment and also vote.

SIRRIN ƁOYE

By Oum Ramadhan✍????

Please Avoide Any Mistakes.

(37)
“an gama ranki ya daɗe, zanyi kamar yanda kika faɗa, ba za’a sami kuskure ba, wannan alƙawari ne nayi miki”. Musbahu ɗin ya faɗa daga can inda yake.
“shikenan sai naji daga gareka, komai ake ciki kai saurin sanar da ni”. ta sauke wayar daga kunnenta tana me yasar da ita a gefenta. sannan tai wani murmushi mai ciwo, irin murmushin nan na takaicin cimma wani abu da kai burin samu, sannan ta kwantar da kanta ajikin kujerar. “Amma Yaya kina tunanin za ki cimma nasararki a wannan karan?, sai nake ganin kamar lokaci ya ƙure miki ko kuma ma nace lokacin ya tsaya miki cak, domin anzo gejin da ba zai barki kici gaba da amfani da shi ba”. Khadija wadda ta ke ƙanwa ce gareta tayi maganar. Amarya ta ɗau lemun soɓo dake cikin kofi ta kafa a baki, sai da ta kusa shanyewa sannan ta ajiye shi tana mai sauke numfashi.
sannna ta dubi Khadija tana murmushin dake bayyana irin yaƙinin samun nasarar da ta ke da shi akan dukkan wani abu da ta rubuta shi a lissafinta sannan tace,”nasara bata taɓa juya min baya ba, kuma zan iya cewa tayi kaɗan ta juya min baya a wannan lokacin, kan wannan gaɓar, akan wannan gaɓar da nake tunanin na kammala dukkan shirina dana lissafa…tukunna ma! me kike nufi da lokaci ya tsaya min?”. Khadija tace,”tun lokacin da kika shirya cewar zaki kauda Kabiru da Amadu na faɗa miki hakan kaman ganganci ne, shi yasa a yanzu da aka zo gaɓar da Kabiru ke kwance a asibiti nake ganin kamar asirinki zai tonu…”. ba ta kai ga ƙarasawar ba Amarya ta dakatar da ita,”ke za ki fallasa ni ko?”. ta girgiza kanta,”a’a ko ɗaya ba haka bane…idan aka kai Kabiru asibiti a wannan yanayin da yake ciki dole sai hukuma ta shiga cikin lamarin, shi yasa nake tsoron me ka iya zuwa ya dawo”.
cikin tsananin ɓacin rai Amarya ta dakatar da ita wajen kiran sunanta a tsawace,”karki ƙara min wannan zancen, karki ƙara idan ba haka ba kuma ranki idan yayi dubu sai ya ɓaci…ta ya za ai ki dinga kutso min da wata magana mara daɗi cikin sha’anina, ke kin san kuwa tsawon shekarun dana ɗiba ina gudanar da aikina domin cikar burina, babu boka babu Malam da irin dabaruna kawai da suke cikin kaina nake aiwatar da komai nawa da babu wanda ya isa ya gane ina da wata fuskar bayan wacce kowa yasan ni da ita, wannan kyakykyawar innocent fuskar, bari kiji na faɗa miki, ko da lokacin ya yanke, duniyar Amarya ba zata juyawa ba daga yanda ta ƙawatata kuma ta tsarata, duniyar nan da kike gani itace al…”. caraf Khadija ta dakatar da ita daga abinda zata faɗa, wannan kalmar ce da kullum ta ke faɗa ma ta a matsayinta na wadda tai imani da Allah da kuma manzonsa bai kamata ta ke faɗar irin wannan kalmar ba, wanda hakan zaisa ta iya fita daga imaninta, cewa da ta ke duniyar nan itace aljannarta, “saboda ta gina ta da abubuwan da ko da an shafe tarihin kowacce halitta zata ji daɗinta ba zata wahala ba”.(auzubillah), ƙwarai matuƙa Khadija na jin takaicin wannan kalmar shi yasa sau tari ta ke kutso da wani zancen a duk sanda Amarya tai yunƙurin furtata.
“Khadija a da ni mutum ce kamar kowa me anfani da zuciyar da ubangijina ya halicceni da ita, amma a yanzu sam ba haka nake ba, tuni na sauya wannan zuciyar zuwa irin wadda nake so ta zama, ta yanda zan cimma burina a gidan Malam, ba dan komai ba sai dan bana so na tashi a tutar babu a sanda Malam yay sallama da wannan duniyar, bima’ana ba zan iya zuba ido naga wasu da ƴaƴansu kaɗai sun wawashe dukiyar da Malam ya tafi ya bari ba, ba zan iya ba!, shekarata ɗai-ɗai har goma sha biyu a gidan Malam amma kullum abinda yake faɗa min ga me da rashin haihuwata shine Amarya ki ƙara haƙura, ubangiji shine me yi, yana sa ne dake, kuma duk wani jinkiri da kika gani a rayuwar mumini wallahi alkhairi ne, dan haka kar muyi azarɓaɓin da zaisa mu iya kauce hanya, saboda kiji daɗi yasa na baki Mairo, wannan Mairon da kike jin tamkar ke kika tsuguna kika haifeta…ni ba ciwo ba, lafiyata ƙalau amma ace tsawon shekarun nan da nake gidansa banyi shukar da rassanta za suyi irin yaɗon da ba zaisa na jigita ba a sanda bana tare da shi, ehh haihuwa ta Allah ce amma abin yana damuna”. tai shiru tana mai jan nunfashi, ta kai hannu ta damƙe glass cup ɗin dake kan taburin dake gabanta, wanda da ta ƙara sa masa wani ƙarfi zai iya tarwatsewa.
“inda Malam yay kuskure shine yacca yake bayyana irin soyayyar Suwaiba ɓaro ɓaro ga kowa, da kuma kasa ɓoye irin matsayin da ta ke da shi na daban akanmu a wurinsa, da fifitata da yay ya bata wani linzamin matsayi daban da namu acikin fadar zuciyarsa, da irin yanda baya yabon kowacce acikinsu sai ita, komai it ta iya, haƙuri itace, hali itace, nagarta itace, sanin ya kamata itace, iya kula da tarbiyar yaro itace, idan wani sirrin nasa ne itace, dukkan yabawarsa da bajintarsa duka nata ne…wannan dalilin shi yasa na kasa danne zafin kishin dana ɗebi shakara da shekaru ina yi akanta, na shiga na fita na kauda it cikin ƙanƙanen lokaci, buƙatata ta biya, kuma burina ya cika, domin a yanzu dukkan wata daraja tata da matsayi zai dawo kaina”.
sai kuma tai wani murmushin nasara daya tsaya iyakar leɓenta taci gaba da cewa,”ƴarta kuwa Mairo, ko kuma nace ƴar zinar da ta riƙe Mairo na zanata a cikin lissafina ne tun bayan shekaruna biyar da zuwa gidan, dalilin daya sa naso na kassara rayuwarta tun farko kenan amma sai Malam yay gangancin shigar min cikin al’amarina har aka samu aka ceci ranta”. sai tai wani tsaki dake bayyana tsantsar takaici kamin tace,”ban san dalilin daya sa Malam ya fifita yarinyar nan akan duka ƴaƴansa ba, Khadija Malam ya shayar dani ruwan mamaki a sanda gaskiyar cewar Mairo ba ƴarsa bace ta bayyana…Malam ya so yarinyar fiye da yanda alƙalami zai rubuta, ke zan iya ƙaryata duk wanda ya nemi ya kwatanta irin yacca Malam ke sonta, saboda ba abu ne da zai ƙiyastu ba dan ko mizani yay kaɗan ya auna irin soyayyar da yakewa yarinyar nan, shi yasa tun kamin na kamu da kishin Uwar riƙonta na kamu da nata, ni da Mairo na fara kishi a gidan aurena, ƴaƴan Malam sama da goma sha uku amma kyace ita kaɗai ya haifa, shi yasa da sirrin ɓoye ya fito fili na ɗora alƙalamin zargina akansa, zuciyata bani ta ke shi yaywa Uwarta cikin nan dan ruwa baya tsami banza”. Khadija dake dubanta da tsantsar mamaki tace,”kina nufin Yaya Mairo ma kinsa hannu acikin rayuwarta?”. “ƙwarai kuwa, aini da ita na fara kishi kamin matan gidan…nai amfani da kissata ne wajen karɓarta a matsayin ƴa ta yanda zan kauda ita cikin sauƙi kuma ba tare da wani abu ya taɓa farina ba, ni na dinga ɗirka ma ta wasu ƙwayoyi da nasa aka min safararsu waɗanda zasu illata ƙodarta, kuma sunyi ɗin, amma sai Malam ya sadaukar da ƙodarsa ɗaya gareta, haka kuma ni na ɗauki kwangilar ɗauketa da akai…hmmm cikin hikima nake gudanar da aikina ta yanda hankali ba zai taɓa gasgata zargi akaina ba, a yanzu idan na dafa ƙur’ani nace ni na zuba ma ta maganin ɓera a tsiren da taci babu wanda zai gasgata ni, illama kallon mahaukaciya da za’a min”. sai kuma ta bushe da dariya sannan ta ƙara cewa,”ban taɓa aikin asiri ba sai a sanda nasa aka tura ma ta miji, kuma nayi dana sanin wannan lokacin saboda ban sami buyan buƙatar haukacewarta ba kamar yanda na tsara, Mtsssww Yasira ce ta bani wannan banzar shawara, dama tun farko na faɗa ma ta ni ban yarda da wani aikin asiri ba, shi yasa na barta akan komai, dalilin haukar Yasira da kike ganin shine wannan…Khadija a da Mairo da Uwarta ne kawai acikin lissafina amma daga baya sai Yasira ta nusar dani zuwa hanyar dani ban taɓa ganowa kaina ita ba saboda kishin waɗancan abubuwan da suka rufe min ido, Gado! tsawon shekarun dana ɗauka babu haihuwa a gidan Malam banza a wofi zan tashi a sanda ya mutu, ban mallaki komai daga gare shi ba balle na sami gadon wani abu me tsoka, ni na shigo gidan na ɗauki tsawon shekaru ita rayuwa tre da shi amma ban shuka bishiyar da rassanta zasu min amfani ba a sanda baya raye…dalilin shigar lissafi na uku kenan cikin tsarina, da Mairo da Suwaiba ne kawai, amma sai tunanina ya lissafa min cewar ya kamata sauran ƴaƴansa ma su shigo cikin lissafin, ta inda na ɗauki aniyar kaudasu 1 by 1, kinga duk sanda akace bashi da ɗa ko guda kasona zai zama dai-dai dana Zulai, kamar hakanne yasa zan fara ta kan Amadu sai kuma aka sami akasi a jiyan…amma shi Kabir da kike gani sam ban sanya shi acikin lissafin waɗanda zan rabasu da duniyar nan ba, saboda ina sonsa”. sai da ta dubi Khadija da ta zuba ma ta ido sannan ta murmusa kamin tace,”So dai da kika sa ni, ina son sosai irin soyayyar da ko ubansa bai sami gurbi a zuciyata ba kamar yanda shi ya samu yay bake-bake acikinta, dana lura cewar ba zan sami biyan buƙatata a tare da shi ba, sai zuciyar ta karkata akalarta akan dukiyarsa, kuɗinsa kawai nake buƙata a yanzu shi yasa zan kauda shi amma ba don son raina ba saboda still wannan soyayyar tasa na raina, sai dai nasan shi ba zai min amfanin da kuɗi zasu min ba”.
tai shiru a sanda ta miƙa hannu a gefenta ta ɗauko wasu takardu tana murmusawa,”kinga waɗan nan taksrdun da kika kalls ina kaffa kaffa da su kamar ran mahaifiyata, ba komai bane fa ce takardun gonakin Malam…ni ce na shirya faruwa komai da tsaruwar yanda abin zai kasance ace Gwamnati ce ta ƙwace masa su…wannan itace babbar Kadarar Malam kuma da ace nai haƙuri da Gonakin nan kaɗai dana mallaka ta ƙarfi ƴaƴansa ma basu isa su gaji kwatan abinda na samu ba…Ya kika kalla kwanyar tawa?”.
Khadijan ta jinjina kanta, bayan ta sauke numfashi tace,”kin wuce tunani da kuma dukkan hasashe…amma kuma Yaya acikin maganganunki kin faɗi da ace da yawa, kinga kenan cikin tsarin naki ma ba a ko da yaushe nasara ke tare da ke ba”. sai Amarya ta kama ya karan hancinta ta murza, buɗar bakinta za tai magana wayr dake kusa da ita tayi ƙara, dan haka tai saurin ɗagawa ganin sunan Musbahu akai tare da karawa a kunne.
“Ya akai?”. daga can ɓangaren yace da ita,”sn sami mishkila”. tai saurin rumtse idanuwanta,”karka ce min har zuwa wannan lokacin Kabir bai mutu ba kuma baka sami abubuwan da muke buƙata daga jikinsa ba?”. “ehh Hajajju duka babu ɗaya daya faru, ai na taƙaice miki ma gaba ɗaya jikin Kabiru babu wallet a tare da shi, duk na caje shi wallahi babu kuma har wurin da accident ɗin ya faru babu irin duban da banyi ba amma babu…”. “Dakata Musbahu, zan samo mafita akan wannan wuyarta na zurfafa tunanina…mene abu na gaba?”. “Amadu ya kuɓucewa shirinmu”. “fahimtar da ni”. “Ranki ya daɗe Amadu tare da motar jami’an tsaro suka zo, shi kansa Kabirun an sauya masa asibiti zuwa wani babban asibiti…Hajajju tare suke da wata Mata me babban matsayi dan baki kalla yanda jami’an tsaro ke nan da ita ba, ance ƴar sarkin Qatar ce tazo nan ƙasar ziyara…Hajjaju babbar matsalar itace…”. ɗif ta katse wayar kamin ya kai ga faɗa ma ta abunda ba ta shiryawa jinsa ba, a hankali ta furta kalmar,”zanga bayanta itama”. “zanga bayan itama idan har ban sami biyan buƙatata ba, yacca na gama lissafin adadin kuɗaɗen da naji Kabiru na ƙiyastawa a matsayin mallakinsa idan har suka kuɓuce min lallai wannan Matar zata shigo cikin lissafina tabbas kuwa”.
Kuma sai muryrta ta katse tare da katsewar numfashinta, da tsayar da idanunta akan mutanen dake tsaye a bakin ƙofa, mutanen da bata san da zuwansu ba, sai dai dukkan wata alama ta nuna ma ta sun ɗauki mintina sama da goma a wajen, hakan ya bata tabbacin sun shafci jin wasu daga cikin maganganun da ta ɓarin faɗawa Khadija a ɗazu. bata san lokacin da taja wata doguwar ajiyar zuciya ba kuma ta kasa sauketa, a yayinda lokaci guda maƙogoronta ya bushe, haɗiyar yawu ya gagareta. me zuwan waɗan nan mutanen ke nufi? Me ke shirin faruwa da ita ne? Wa ya shirya girgiza teburun da ta ke lissafi akansa ne dan komai ya tarwatse?.
ƙwayar idonta ta sauka akan Khadija da ita ta ruɗe saboda ganin abinda bata tsammace shi ba a kurkusa haka. “You are under arrest”. kalmomi huɗun da suka fito daga bakin police ɗin daya ƙarasa shigowa cikin parlon kenan, wasu ƴan sanda biyu kuma suka mara masa baya, lokacin da Amarya ta buɗe baki dan yin magana, lokacin kuma ta girgiza da mamakin ganin Malam na shigowa shima.
“idan har ba mafarki nake ba, kuma abinda kunnuwana suka ɗauki tsawon lokaci a wurin nan suna ji haka suke, to yallaɓai na baku damar ku kamata ku tafi da ita…Aisha daga yau kuma yanzu ina so yatsanki guda ɗaya da kike amfani da shi wajen zanen tsarinki, to a wannan lokacin ina so ya zana miki rabuwata dake, rabuwa ta har a bada”. Malam na faɗar hakan ya dubi Amadu da cewar,”kwaso min waɗancan takardun”.
daga haka kuma akasa ma ta ankwa aka fita da ita, da rufaffen bakin daya kasa furta komai.
Bichi
“Inna kin san dai turancin nan ba sosai nake jinsa ba, dan Allah ki rabu da ni idan suka gaji da tsayuwa zasu tafi ne”. Zulai dake wanke roba ta ƙwalowa Adawiyya robar akanta,”shashar banza ana sonki da arziƙi kina miƙa kanki da talauci, dan ubanki kin san adadin kuɗaɗen da za ki samo mana idan kin fita ɗin”. Adawiyya ta miƙe ta yafa mayafi tana turo baki ta fita, a ƙofar gidan daga gefen dakalin gidan tai arba da wata dakakkiyar mota fake a wurin, sai Almustaphaa dake tsaye jingine a jikin motar ya harɗe hannunsa a ƙirjinsa, ɗaya hannun kuma yana kare da waya a kunne kuma yanda ya tattara hankalinsa akan wayar gaba ɗaya zaka san waya ce me muhimmanci yake yi.
sai kawai taji wani abu ya zarce ta maƙogoronta da bata san ko menene shi ba, tabbas da ta san da akwai surar halittar da ta fi ta Suhail, wannan tsarin halittar dake gabanta, Allah ya sani da basu wahalar da kansu akan Suhail ba, abin tambayar shine, me yasa ne ita Mairo ke sa’ar samun irin waɗan nan tsadaddun mazanne?, sam ta kasa ganewa ita kam. shin da me Mairon ta fita?, har yanzu fa da ta sauya bata fita dirarran jiki ba, wannan sangalallun siraran ƙafafun nata kamar sillan kara sune dai suke yawa a cikin zane, to kuwa namiji me rai da lafiya ina shi ina kwasarwa kansa mace me sikila, dan ita a ganinta wannan sirantar da Mairo ba zata rasa nasaba da sikila ba…amma bari shima zata kora shi ne, zata shaida masa yarinyar da za’a laƙaba masa ba komai bace fa ce illigemate child, ai idan ta ɗanɗana masa wannan kalmar ta illigitimacy dole ya haƙura da ita, wai tun yaushe ne ma taiwa kanta alƙawarin Mairo ba zata auri mijin kerewa sa’a ba ne?, to kuma na mene zata damu kanta akan abinda ta ke da yaƙinin tabbatuwarsa, a wannnan lokacin daya bayyana cewar ita ƴar zina ce waa zai ɗauka?, sai tai guntun murmushi cikin ranta tana ƙara cewa ai ta koma gefe kawai tai dariya son ranta.
“Is Father at home?”. tambayarsa da ta shiga cikin kunnenta ita ta katse shirmamman tunanin da ta ke, dan haka ta ɗago na saci kallonsa kamin ta bashi amsa da cewar,”baya nan sun tafi asibiti”. kums kamin Almustapha ɗin ya ƙara cewa wani abu, Dad dake cikin mota ya fito ya jefo ma ta tasa tambayar,”what about Ahmad, is he around?”. sai ta girgiza kanta alamar a’a. shiru ya ratsa tsakaninsu na ƴan mintuna kamin Almustapha ya jefa ma ta tambayar,”wane bashi da lafiya?”. “Maman Mairo ce”. sai ya waro ido waje da mamaki,”Maman Mairo kuma?, ita bata mutu ba”. anzo wurin da ta ke so, dan haka ta gyara tsayuwarta ta shiga koro masa bayanan da ke buga ma ta sarewar daɗi a ranta, kuma bata kai ga furta cewar,”amma ba’a san wane Babanta ba”. Dad yay saurin cewa da Almustapha ya kira Ahmad yaji suna ina, hankalin Dad a matuƙar tashe ya shiga mota suka bar wajen bayan Amadu ya shaida musu asibitin da suke, a gefe guda kuma sai kiran wayarsa ake akan bikin mutuwar su Granny da tuni aka kai gawar tasu can chapel ɗin ana jiransa shi da Emanuel.
Apex Consultant Hospital, Kano.
a cikin harabar asibitin, Aaliya na zaune kan plastic farar kujera, yayin da Amadu da Alhassan ke tsaye daga gefen damanta, a gabanta kuma ƴan sanda ne guda biyu sai guda ɗaya da uniform ɗinsa ya banbanta dana sauran yana zaune shima a plastic kujera yana fuskantarta, yayin da ta ke sauraren duk bayanin dake fita daga bakinsa.
“mun kama shi yaron da yay causing accident ɗin, bayan an kai shi mara lafiyar asibiti so a time ɗin ya shiga yana laluben aljihunsa time ɗinne wata nurse ta gansa sai tai gaggawar sanar damu. so kamar yanda ita Akila ta bamu waɗancan bayanan akan ita wadda kuke suspecting, mun sami dukkan ƙarin bayani a wayar shi Kabir ɗin, ofcourse kaman yanda Akila ta faɗa akwai record ɗin maganar ita waccan matar mun same shi a wayar Kabir, to mun sami bayanin inda ta ke daga bakin shi yaron nata, dan farko munje can gidan shi Malam ɗin bata nan, kuma lokacin da muka je gida sai muka je a daidai gaɓar da ta ke bada labarin abinda ta shuka, duk da cewar ba duka muka tsinta ba amma mun tsinci muhimman abinda zarginmu yake akanta, kuma yanzu haka tana can a cell suna karɓar hukunci ita da yaron nata”.
Aaliya tayi ajiyar zuciyar dake shaida tsananin damuwarta kafin tace, “wannan mata anyi sheɗaniya, DPO idan kaji labarin ainihin fuskar da kowa yasanta da ita zaka sha mamaki, zaka rantse kace ƙazafi ne aka ma ta akan wannan abin da ta aikata…yanzu kenan mene ƙarshen hukuncinta?”.
“ehh to ranki daɗe for now dai zamu yita horasu ne zuwa lokaci zai nuna mana halin da Kabir zai kasance a ciki, yanzu dai nauyin kashe duk wasu kuɗi da za ai akansa ya rataya ne akan wuyanta…”. Aaliya ta tari numfashinsa da cewar,”ka bar wannan batun matsiyaciya ce ba zata iya ba, ko ka taɓa ganin faƙiri ya tallafi wani?, tukunna ma ba kalla duk akan kuɗi ta aikata hakan ba, so just go stregth to the point ɗin da nake son ji”. ya jinjina kai,”right! to abunda dai hukunci zai tanadar akanta shine, idan Kabir yaji sauƙi case ɗin mutuwa akanta ya zama guda ɗaya kenan, amma idan Allah baisa ya rayu ba case ɗin mutuwa akanta ya zama biyu kenan, so a wannan lokacin zamu danganata ga kotu domin ta yanke ma ta hukunci akan abubuwan da ta aikata”.
Aaliyan ta ƙara cewa,”DPO matar nan ta shiga rayuwata da yawa, bima’ana ta shiga rayuwar ƴata tun tana ƙanƙanuwarta, dan haka kamar yanda ta ɗau lokaci tana saka firgici a rayuwar ƴata, haka nake so daga yau ta shiga fara ƙidayar mutuwarta da kanta ta hanyar irin gana ma ta wahalar da zaku dinƙayi, DPO da gaske nake maka daga yau Amarya karta kuma rufe idanuwanta da sunan yin bacci, kuyita galabaitar da ita acikin bugawar kowanne sakan na agogo…idan kayi min haka zan biyaka da kaso mafi tsoka”. DPO ya jinjina kai alamar za’ai yanda ta buƙata ɗin.
sai ayanzu Amadu yay magana a sanda DPO ɗin ya miƙe yana yiwa Aaliya sallama. “DPO nace me yasa itama ba za’a ɗanɗana ma ta irin allurar da taiwa Gwaggo ba kamin zuwan lokacin da ake jira ɗin”. “karka damu, duk wani nauin wahalar da me laifi acikin aikinmu yake”.
daga haka yay musu sallama ya wuce, yayin da Aaliya ta miƙe suna nufar hanyar wani dogon corrido, da zai sada su zuwa ga room ɗin da aka kwantar da Kabir, zuciyar Amadu na raya masa cewar ko ya sanar ma ta da zuwan su Major da suke kan hanyarsu, kwatsam kuma saiga kiran Almustapha ya shigo wayarsa, saboda haka ya ɗan dakata da tafiyarsa ya ɗauki wayar, Almustapha ke shaida masa gasu a compound ɗin asibitin, kuma wucewar daƙiƙa ɗaya sai gasu sun iso inda yake.
“Alhassan”. Alhassan ɗin ya juyo daga tafiyar da yake a sanda yaji kiran Amadu, “ka tsaida Mami”. dan haka sai ya juya ya kira sunan nata, juyowarta tai dai-dai da ɗago da idon Major ya kai kanta da Amadu ke masa nuni da ita, itama kuma daga tazarar dake tsakaninsu ta ganshi, ga mamakin Major sai idonsa ya ƙyallo masa saɓanin tunanin da zuciyarsa tai a sanda ya kai ƙwaya idonsa cikin nata lokacin daya iso inda ta ke.
ayanzu daya ƙaraso gabanta tana amsa wayar da Ammi ta kirata ne, dama tun a ɗazun ta kirasu ta shaida musu halin komai da ake ciki a yanzu da na baya ma daya wuce, sanda ta sauke wayar daga kunnenta taiwa Major kallon sama da ƙasa tamkar bata ma taɓa ganinsa ba, ko kuma wacce ta sanshi amma ta manta inda ta san shi ɗin tana dai ƙoƙarin recalling, kafin a hankali muryarta ta fito da faɗin,”why now?”. kuma kan yace wani abu ta juya ga Alhassan tace,”ga Ubanku…”. sai dai abinda ta gani ne baisa ta ƙarasa sauran maganarta ba, kamar yanda Alhassan da Almustapha ke kallon junan su da mamakin kamanninsu haka itama ta ke kallon Almustaphan da mamakin kamar dake tsakaninsu.
“Major ban lissafa ganinka a yanzu ba, me zuwanka ke nufi?, kuma da wacce tsiyar kazo naji ko kaina zai iya ɗauka?”. bai iya cewa komai ba, shi dai yay shiru kawai yana kallonta da wani irin kallo da shi kaɗai yasan me zuciyarsa ke ji a ga me da hakan. kuma gaisuwar da Alhassan yay masa ita ta datse igiyar tunanin da yake, dan haka ya juyo gare shi cike da wata iriyar kunya ya amsa masa. sai Aaliyan ta dubi Alhassan ɗin da cewa,”binsa zaka yi ne?”. sai yay saurin girgiza kansa,”no Mami, na gaishe shi ne saboda sunan mahaifi daya amsa a gareni”. sai tai guntun murmushi,”to kaji, so saika jira zuwa time ɗin da zan kammala activities ɗin da suka kawoni ƙasar taku, idan na koma ka iya zuwa da ƙafar rashin kunyar naka ka karɓesu”. ta faɗin hakan ta juya dan ci gaba tafiya. sai a sannan taji yace,”where is Merry?”. ba tare da tsaya daga tafiyartata ba ko kuma ta juyo ba tace da shi,”ni ƴata sunanta Maryam, kar ka ƙara kiranta da wannan ɗan iskan sunan tunda ba rainonka bace…kuma abinda ma zan sanar maka shine ka cire lissafin karɓarta dan ba abu ne da zai yiwu ba in har Aaliya na numfashi, kaji da kyau bada wai ba, wannan dai me zubin naka kana iya jansa ko daga yanzu domin shi na rayu da shi, ita kuwa yanzu ne zamu soma rayuwa tare”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button