NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

My apologizing will just be annoying ko baku faɗa ba na sa ni, becouse these days am just apologizing for not updating yanda aka saba, but karku damu it will change insha’Allah tunda har na kusa making up abinda ke gabana…but even though am still gonna say sorry to you guyz, wlh am just managing fa????, saboda am a busy human being wallahi, ku yarda da ni????.

Plss Comment,Vote&Share.

SIRRIN ƁOYE

By Oum Ramadhan✍????

(39)
idan har zai iya bada rabin jininsa ga Ahmad saboda kawai son da yakewa ɗan’uwansa, to baya ganin akwai wani abu da Ahmad zai biɗa a rayuwarsa yaƙi bashi damar samu matsawar hanyar samar masa bata fi ƙarfinsa ba.
hoton wani lokaci can baya ya shiga haska masa a cikin idonsa, lokacin da yake shekara 22 a duniya, Ahmad kuma na 21, wannan lokacin da sukai accident kan hanyarsu ta dawowa daga makaranta, Ahmad ya sami rauni sose da har saida aka buƙaci jini, a wannan lokacin kuma Malam bashi da kuɗin da za’a saya ledar jini har guda uku, aka kuma gwada duk wanda ya dace a gwada acikin siblings nasu amma babu jinin wanda yay daidai da na shi sai shi da Malam, shi kuma Malam a lokacin babu damar a ɗebi nasa kasancewar ba shi da cikakkiyar lafiya, dan haka ya zagaya ba tare da sanin kowa ba, ya fasa bankin ƙasarsa ya bada 20k sannan ya roƙi likita aka ɗebi nasa har leda biyu aka sakawa Ahmad, duk da cewar likita ya gargaɗe shi akan zai iya samun matsala idan aka ɗibi jininsa da yawa haka tunda shima jinin ba isarsa yay ba, yace ba shi da damuwa idan har ɗan’uwansa zai sami lafiya, shi zai iya sadaukar da rayuwarsa ma akan Ahmad.
kuma tunda aka ɗebi jininsa ikon Allah ne kawai ya rayar da shi, amma yasha baƙar wuya, dan da taimakon Allah da taimakon Gwaggo da tai ta sayar da abubuwanta ana siya masa abincin da zai dinƙa ci na ƙarin jini, tukunna lafiya ta sami gareshi, kuma har yau, har kwanan gobe babu wanda ya san da cewar akwai jininsa a jikin Ahmad…to idan har zai bashi jini a lokacin da shima ba isarsa yay ba, mene a rayuwarsa zai kasa sadaukar da shi gare shi? babu! babu shi ba’a halicce shi ba, ya sa ni babu wanda ya san da cewar Ahmad na son Maryam, kamar yanda itama Maryam ɗin bata san da hakan ba, haka kuma shima Ahmad ɗin bai san da cewar ya fahimci soyayyar Maryam a tare da shi ba, kamar yanda hakan ta kasance, kamar hakanne zaisa ya zame kansa dag zuciyarta da tasa, ba tare daya bari kowa yasan dalilin hakan ba, ai dama shi bai taɓa furtawa kowa cewar yana sonta ba illa Akila balle har hakan ya zam masa wani babban ƙalubale, Allah ya sa ni yana sonta, amma akan ɗan’uwansa tabbas zai iya haƙuri ya zama me juriya akan rashinta, zai bar masa ita, wannan alƙawarinsa ne matuƙar yana nunfashi, sai dai idan shi Ahmad ɗinne yace ya fasa, zai ta ɓoyewa Ahmad wannan Son da bai san ya naiwa Maryam ba kamar yanda shima ya ɓoye masa nasa sai shine ya fahimta.
ɗigar ruwan hawayen daya sauka bisa cinyarsa ne ya katse dogon tunaninsa, ya juyo da ƙwayar idonsa gareta yana mai kallon fuskarta da laɓɓanta dake magana cikin muryar kuka, mai shaida wani rauni daga ƙasan zuciya.
“Ya Kabir dan darajan Allah kai min afuwa akan laifin dana maka bisa kuskure, wallahi tallahi banyi da gangan ba, ko me nayi banyi da sanina ba, dan Allah kayi haƙuri na tuba ba zan ƙara ba, amma ka daina fushi da ni haka…Yaya wallahi zuciyata har zafi ta ke min akan hakan, ka kalla fa yanda ta ke motsawa a irin kumburin da tai.” na ƙarasa maganar ina masa nuni da ƙirjina daidai saitin zuciyata, sai kawai ya tsurawa saitin zuciyar tawa ido da nai masa nuni, daga can ƙasan ƙwayar idonsa yana hango irin yanda zuciyarta ke harbawa da irin yanda salon tasa ke harbawa.
ita ya kamata ta bashi haƙuri ko shi ya kamata ya bata haƙuri?, shi daya saba ma ta da sonsa, kulawarsa, damuwarsa tun bata san kanta ba, ƙwarai ya san zata shiga damuwa, damuwar da ko kaɗan baya jin daɗinta, yana ƙoƙarin danniya ne kawai da kauda kai gefe.
“Ya Kabir dan Allah”. na ƙara faɗa ina kama kunnuwana da karayar da kai gefe, gami da yin narai-narai da idanuwa ina ƙoƙarin fashewa da kuka. sai kawai ya rufe ido for a while kamin ya buɗe ya saukesu a saman fuskata dana kwaɓe baki irin na shagwaɓaɓɓu, wanda hakan ba ƙaramin burgeshi yay ba, dan saura kaɗan ya saki murmushi amma sai ya danne hakan, ya sake kauda kai kamar bai ji me ta ke cewa ba koma bai san da zuwata wurin ba.
ganin bashi da niyyar saurarena kawai sai na yunƙura zan miƙe cikin rashin ƙwarin jiki da jin daɗi, ga mamakina kamin na kai ga miƙewa sai naji ya riƙo hannuna, na waigo a hankali ina dubansa, still idonsa naga inda yake kallo, yatsunsa ne kawai acikin nawa yatsun, ban san ya akai ba, sai na tsinci wani guntun murmushi a gefen leɓena.
ta yanda yake janyoni a hankali na fahimci me yake nufi, dan haka na koma na kuma duƙawa a gabansa, kaina a ƙasa nace,”Ya ka haƙura?”. kai ya gyaɗa min alamar a’a. “Ya me yasa to?.” nanma kafaɗarsa ya ɗaga ba tare da yay magana ba. sai kai nai tafi zuwa jikinsa na kwantar da kaina saman ƙirjinsa ina faɗin,”please Yayana, kaifa baka fushi, balle fushi da Maryam ɗinka…Yaya idan ma ba zaka min afuwa cikin ruwan sanyi ba to na yarda dan Allah ka hukunta ni ta wata hanyar amma bata wannan hanyar ba, fushi da ni! hakan na min ciwo a zuciya matuƙa.” inda ace da dutse a kusa dani zan iya cewa maganar da nai da shi nake ba da Ya Kabir ba, dan duk sammakal, ni da zaace zai buɗe baki yace da wani abu ko da da faɗa ne wallahi zanji daɗi fiye da wannan shirun da yake min.
abinka da mai ruwan ido akan Ya Kabir ɗina, sai kawai naji wasu hawayen da ban san dasu ba sun shiga sauka, maimakon na tashi saina ƙara lafar da kaina a ƙirjinsa, yayinda kunnuwana ke juyowa yanda heart ɗinsa ke beating very fast. duk da ba ganinsa nake ba, amma a yanda naji hannunsa me ɗan lafiyar ya ɗago zuwa bayana, na fahimci wannan kewayenin daya saba zaiyi, amma sai naji ya dakatar da hannunsa ga kaiwa hakan a sanda Ya Ahmad ya shigo ɗakin bakinsa ɗauke da sallama.
abu guda ɗaya kawai na sa ni a wannan sallamar tasa, shigowarsa ta haɗe ne a lokaci ɗaya da saukar ajiyar zuciyoyinmu. kuma ta yanda naji Ya Kabir ya doki ƙasan carpet ɗin a hankali nasan hannunsa a dunƙule yay hakan, kuma tabbacin alamar ƙorafin cimma abinda yaso yi ne.
“No Sir, i don’t think that is all planned.” yay shiru na ƴan sakanni kamin ya ƙara cewa,”Yes Sir, actually abinda ya faru a lokacin na fita, so i don’t know ko after fita ne Joshua ya duba su, saboda tunda nace musu kace they should bering refference before you sign on the pappers suka ce sun haƙura da contract ɗin”. ya kuma yin shiru na tsawon daƙiƙa guda kan ya ƙara cewa,”oak Sir i will see on it by tomorrow insha’Allah”. “thank you too Sir, bye”.
cewar Ahmad kenan a sanda ya kai ƙarshen wayar daya shigo ɗakin yana yi, ya zura wayarsa a aljihu yana mai neman kujera ya zauna tare da cire hular dake kansa ya ajiyeta a gefensa, sannan ya dubi Kabir dake kallonsa tun bayan gama wayar tasa yace da shi,”Sannu, ya sauƙin jikin?”. “da sauƙi, wannan hannunma naji ya daina tsamin kamar da”. Kabir ɗin ya faɗa yana nuna masa hannunsa na dama da yatsunsa ke tsarƙe dana Maryam, wacce tun shigowar Ahmad yake cikiniyar ya zare yatsun amma taƙi bari.
“Dr Yusuf ɗinma ya kirani yanzu ba jimawa, yace zuwa dare zai shigo wai ayyuka ne sun masa yawa a office ne yau amma kayi haƙuri.” “babu komai tunda dai lafiya, ni dama harga Allah na gaji da zuwansa…ba son allurar nan nake ba wallahi”. fuskar Ahmad ta washe da gajiyar dariya kamin yace,”kai dai ka shiga uku, wai dan Allah sai yaushe zaka daina tsoron allura ne, haba sai kace ba Gentle Man ba”. “to ai ba’a bar so bace Malami balle kace min ragon namiji”. “kaima gashi nan ka faɗa da kanka ai”. Kabir ya ɗan harareshi da cewar. “wai meke faruwa a office ɗin naku?”. “ka bari kawai, wani company ne yake neman yasha damu, suna so mu haɗa partnership dasu sai MD yay bincike akansu aka gano cewar kuɗaɗen bogi suke turawa, to bamu san wa yay musu signing ajikin takardar ba kuma exactly irin na CEO fa nake faɗa maka, alhalin shi bama ya ƙasar”. Kabir yace,”tsananta bincike zaku yi, munafikin na cikin staff en…yauwa next week zamu fara exams kuma kasan na faɗa maka”. “ehh ban manta ba ai, jiya ma munyi chart da Abdurrahim ɗin, amma insha’Allahu ma kamin time ɗin hannun naka zaiyi normal ka sami damar yi, Allah ma ya taimakeka online ce”.
shiru ya ratsa tsakaninsu, kuma a wannan shirunne Kabir ya lura da irin kallon da Ahmad ke bin Maryam da shi ta wutsiyar idonsa, Maryam ɗin da tai bacci a yanda ta ke ajikinsa tun shigowar Ahmad, bai san wacce iriyar yarinya bace ita, son jikinta yy ma ta yawa sai kace mage, haka bacci sai dai in bata kishingiɗa a jikin mutum ba, tun da can ma haka suke da shi, da ta ɗan kwantar da kai a kafaɗarsa zata fara lumshe ido, kuma yana ganin hakan zaice ta miƙe akan cinyarsa dan yasan ƙarshen zancen bacci ne, amma Gwaggo kam ɗaleta ta ke tace ita bata son wannan lalacin.
“ita kuma wannan fa?”. tambayar Ahmad ɗin ta shigo ta cikin shirun daya ratsa ɗakin yana mai masa nuni da Maryam.
“rigima mana”. “me aka ma ta?”. “shopping ta ke so akaisu ita da Basma, Yagana kuma tace a’a sai an kwan biyu saboda kashe kuɗinsu yay yawa, to kuma tazo nan tana ƙorafi nace taje ta sameka wai kaima haka zaka ce a’a, kuma kasan hali ai ba saina ƙarasa maka ba”. Ahmad ya sauke numfashi, bayan ya sosa gashin girarsa yace,”kai kake biye ma ta, ya kamata zuwa yanzu kasan yarinyar nan ta girma amma sai kai ta ƙara biye ma ta tana jin kanta kamar ƴar shekara 2 ko 3. kalla fa wata ƙatuwa da ita ajikinka wai sunan baccin kuka tai, ba saika maketa ba ta shiga taitayinta”. Kabir ya motsa leɓensa yace,”da kake magana cikin ɗaga murya wani ya hukuntata kaima ai ba iyawa za kai ba…yanzu dai kawai idan zaka fita ka fita da su, kasan dai daga ita har Basma ɗin ƴan auta ne ƴan alallaɓa, dan kowacce ita ɗaya ce a wurin Mamanta”.
Ahmad na ɗan ɓata fuska yace,”ni ba ruwana da wani ɗan Auta…fita dama zanyi in sun fito mu tafi tare, in sunyi delay kuma nai tafiyata”. ya faɗa yana miƙewa tsaye, ba dan yaso tashin ba, dan da niyyar ya huta ya shigo ɗakin Kabir ɗin, haka kuma ba dan ya shiryawa fitar ba, ba kuma dan yay niyyar kaisu shopping ɗin ba, sai dan wannan kwanciyar, kwanciyarta ajikin Kabir, kuma dama yana so ya faɗawa Kabir ɗin, yana so ya tuna masa cewar Maryam ba muharramarsa bace, ya kamata ya gyara kusancinsu.
“ni nama manta, ɗazu Yayan Inna yazo ya shigo dubaka kana bacci, yana maka sannu”. Ya faɗi hakan kamin ya ƙarasa fita daga ɗakin, kuma ba tare daya ji amsawar Kabir ba, kuma a yanda ya fita ɗin fushi da ɓacin rai na haskawa a saman fuskarsa, wanda a ganin farko ga mai saurin fahimta zai gane cewar kishi ne tsagwaronsa ba komai ba, kuma Kabir daya gane hakan sai ya murmusa kuncinsa kawai yana girgiza kai.
Allah ya sa ni, tun a doguwar ajiyar zuciyar farko da ta sauke, da kuma numfashin da ta shiga saukewa daga baya, yaji ba zai iya tashinta daga baccin ba, dan daga yanda ta ke yinsa yasan baccin yay ma ta daɗi, kuma shi kansa ya sa ni, ba wani baccin daɗi ta ke ba within these days, dan waccan ranar yana jinta da Alhassan tana faɗa masa cewar ita nutsuwar a tare da mutum biyu ta ke, Maminta da Ya Kabir ɗinta, kuma a yanzu duk basa kusa da ita, saboda haka ne baccin bata yinsa a daɗin rai sai dai ɓarawo ya ɗauketa.
sai ya lumshe ido ya jinginar da kansa ga pillow da akasa masa ta baya, kamin wucewar awa guda Maryam ɗin ta farka, farkawar tata kuma tazo daidai da shigowar Zulai ɗakin, inda ta nufi wajen da room heater ke ajiye ta kunna bayan ta ajiye flask ɗin abincin da ta shigo da shi.
“Ba sai ka kira waya kace azo a kunna maka heater ɗin ba, ɗakin duk ya ɗau sanyi”. “ai Inna sanyin bai wani ratsani ne shi yasa”. “lallai lafiya ta isheka, to da Ahmad ya shigo yay maka gashin ko ya?”. “a’a Innah”. “to ka shirya dan lokacin gashin naka ma ya wuce”. ta faɗa tana buɗe toilet ɗin ɗakin ta shiga. kuma da shigarta na shiga magana a hankali ina cewa,”lokacin da Inna da Ƴaƴanta ke neman yafiyarmu akan laifukan da suka aikata mana wanda bamu sa ni ba, kai da kanka kace na yafe musu, rayuwar nan ba komai bace, ubangiji ma muna masa laifi yay mana afuwa, balle kuma a tsakaninmu ƴan Adam…to dan me ni ba zaka yafe min ba Yaya?”. kuma abinda ƙwayar idonsa ta nuna min a lokacin shi ne, na tashi na basa wuri.
ina miƙewa Inna na fitowa daga toilet ɗin, ta ƙaraso da robar ruwan zafi a hannunta ta ajiye, sannan ta umarce ni da shiga toilet na ɗauko ma ta towel.
bayan na kawo ne ta ke cewa dani,”ke ni ai na manta ma Yayanku Ahmad na kiranki”. murya a ƙasa na amsa ta da cewan,”to Inna”. sannan na juya na fita daga ɗakin, dama ko babu kiran Ya Ahmad ba zama zan ƙara yi ba bisa dalilai biyu, bana iya zama a sanda ake masa gashin karayarsa, kuma ba zanci gaba da zama ba alhalin ya nuna bai son ganina, kuma ba zai ƙara ganina ba a part ɗinsa ba insha’Allahu.
a compound na tarar da Ya Ahmad ya fito daga part ɗinsa, ya bini da wani mugun kallon da yasa nai saurin ɗauke idona daga barin kallonsa.
“saƙon dana aika miki ne bai isa gareki ba?, Maryam kin koyi wata rashin kunya ko, me kike nufi da hakan?”. ya faɗa cikin muryar faɗa, ni dai baki kawai na tura gaba nai part ɗinmu, ni faɗansa na cin marai, ya fiya jarabar masifa, idan yana so ya daki mutum kawai sai ya takali laifi ya ɗora maka, shi yasa ranar nan da Jamila ta kai ƙararsa wurin naji daɗi, ta ko’ina Ya Kabir ɗina yafi shi daɗin sha’ani.
ina shiga kuma na gamu da sababin Yagana wadda ke tsaye bakin ƙofar ɗakina tana jiran dawowata, ta riƙe ƙugu sai karkaɗe karkaden ƙugu ta ke.
“yauwa Uwar masu Sharri barka da dawowa, dama dawowarki nake jira ai kowacce wacce…kamin na juye miki masifar tawa, ina da ina kika je kika yanka min mugun sharrinki me hawa kai, kamin gurin shi Uban nawa da kikai ƙarata wurinsa”. da shirunta da dariyata suka haɗu a lokaci ɗaya, ban kuma ankara ba ta ƙwala min ludayin hannun Nawwara da ta amsa, na sa ki ƙara inaja da baya ina sosa wurin.
“ni dai Rakiya iyakar tsayin rayuwata ba’a taɓa min sharrin daya kai naki ba, ban san haka kika girmama a wajen yiwa mutum sharri ba Maryam Guntsi, ai da kin faɗa min kina da wannan mugun halin da tuntuni na raba hanya dake yasin”.
ni dai dariyar ma da nake ta hanani jin ba’asin wannan bambamin da takeyi, da ta kai maƙura da dariyar tawa saita wawuri takalmin Basma tayo kaina da shi, ni kuwa na arta zan fice da gudu sai karaf mukai karo da Ya Amadu na ƙumu da ƙirjinsa. ta ke yaja wani dogon tsaki ya hauni da faɗan rashin nutsuwa, da kuma cewar na wuce na ɗakko mayafina ko yay tafiyata ya barni, na ɗago na kalle shi da son jin inda zamuje sai dai banzan kallon daya wurga min yasa ni gimtse maganata nai ɗakina.
na bar Yagana da faɗin,”Allah yaji ya gani ba zan iya ba, ina dalili haka kawai ina zaman lafiya Yarinya zakije ki ƙunduma min sharrin wai na hanaki fita shufin, kai jama’a kuji wani mugun ƙulli…yanzu tsakani da Allah idan wannan maganar ta kai kunnan Uwarta ai sai tace min butulu, saboda naga ta gina mu shine zan azabtar ma ta da ƴa ta hanyar hanata shaƙatawa, to ai akwai Allah yana ji kuma yana gani, shi zai saka min…ke Basma tsakaninki da Allah yaushe waccan abar tazo tace min zakuje Shufin?, dan Allah ma yau ni na haɗu da ita ne banda ɗazu da zata fita, to amma kinji yarinya saboda baƙin sharri taje tacewa Kabiru wai na hana akaita shufin, kiji zancen nema min masifa a wajen Uwarta da bata barin ta kwana…to ba zan iya ba gaskiya, ni dai Amadu idan kun fita da ita ka kaita can gidan ƴan’uwansu suci gaba da riƙonta acan kamin ita Akilar ta dawo, ba zai yiwu ta jazamin bala’i ba da mugun sharrinta tasa a ɗaureni, dama yanda ta ke da gata nan ta ko’ina wannan uban nata da ba fuskar imani gare shi ba, ba zai duba tsufana ba, Mairo dai yanzu ta zama annoba kam dan tafi ƙarfina, gwara ki tafi na samu salama…kuma sharrin da kika min kije da halinki na rashin kyautawa”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button