SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Qatar, cikin masarauta.
zaune ta ke daga gefen wani ƙaton dutse dake acikin ɓangaren masu yiwa gidan hidima, ta haɗa kai da gwiwa jikinta kuma sanye da uniform na bayin gidan, wannan uniform ɗinma aji aji ne kuma nata yana ajin ƙarshe na ƙasƙantattun bayin masarautar.
gaba ɗayanta ta sauya tamkar ba ita ba, a halin da ta ke ayanzu ita kaɗai tasan me ta ke ji, wannan wahalar ta kullum ta gaji da ita, gashi dai babu duka babu zagi amma bautar da ta keyi kaɗai yafi ace dukan nata ake kullum. tasa hannu ta goge guntuwar ƙwallar da ta cika idonta.
bata taɓa tunanin ƙaddara zata wanzar da ita acikin wannan yanayin ƙasƙancin da ta ke ciki ba, domin bata lissafa hakan acikin tsarinta ba ko kuma hasashen hakan, amma sai gashi tunda alƙalami ya riga ya bushe komai ya sauya ma ta, bata da ikon dawo da baya ta gyara lissafin tsarinta, balle labari yasha banba da wanda ake kai ayanzu.
dama Larai ta faɗa ma ta, watarana zaren labarin shirinta zai sauya ayayinda akazo kan wata gaɓa da bata taɓa haskowa kanta ba, ashe kuwa hakan zata faru, za kuma ta kasance. wataƙila da ace tayi haƙuri ta barwa lokaci komai, da ta tsinci abinda sauyin mummunar ƙaddara zai kawo ma ta, wannan lokacin na ganiyar da Malam da iyalansa suke kai ayanzu, kuma wataƙila inda tayi haƙurin ta tsinci ribar haƙurin, tunda Allah na tare da ita ba mantawa yay da ita ba, haihuwar dai! wannan haihuwar tabbas da tai haƙurin taci gaba da adu’a wataran Allah zai bata in har tana da rabo, to yanzu gashi tayi biyu babu, ba wan ba ƙanen.
lokaci guda wani abu yay tsalle ya harba allon ƙirjinta, ta sa ni, ba zata taɓa dawwama a haka ba dole wataran zata fita, duk da bata hango hakan amma tasan rayuwa zata iya rubuta hakan. zuciyarta taji ta matse, tai saurin matse idnuwanta gam zuciyarta na harbawa da wannan sunan, wannan mutumin, wannan bawan da tunaninsa ke hanata sakewa a kowanne bugawar sakan na agogo tun kamin zuwan wannan lokacin.
Kabir! Kabiru dai ɗan mijinta, bata san taya ba, bata san ya akai ba, ita dai kawai ta tsinci kanta cikin matsanancin son yaron a duniyarta, wanda ta ke jin kishi da baƙin cikin duk wanda ya raɓe shi ko da kuwa ace ƴan’uwansa ne, ta kuma sha alwashin haramtawa duk wata ƴa mace shi da sunan mallaka. kuma ko ayanzu bata janye ƙudurinta ba, in har akwai boka, Malam da bori a duniya tabbas saita mallaki Kabir, sai dai in bata raye, ba’acikin nan ba, ko inda yafi nan matsi ne saita samarwa kanta Kabir, wannan alƙawarinta ne.
“Mami karku kaita kotu, dan Allah ta zama ƙasƙantacciyar baiwar masarautarmu, zuwa cikar wasu wa’adin lokuta dana shirya ta dawo ƙarshin ikona, ta zama mai min bauta”. maganar Maryam a waccan ranar, wannan lokacin da ake ikirarin za’a yanke ma ta hukuncin zaman gida yari ɗaurin rai dalilin allurar gubar da taiwa Gwaggo, furucin ya shiga tariya acikin kanta, sautinsa acikin kunnenta. baƙin ciki da takaicin halin ko’in kula ɗin da Maryam ta nuna akanta ya doki ƙirjinta, ko babu komai, duk da cewar ta ƙaunace ta ne ba don Allah ba sai dan biyan buƙatar kanta, amma ya kamata ace ta tuna da kulawarta da hidimtawarta gareta.
ruwan da aka watso ma ta ajiki yasata yin firgigit ta dawo duniyar zahiri. a tsawace shugabarsu ta shiga ma ta magana. “dilla Malama miƙe kije kici gaba da aikinki”. ta faɗi hakan tana jin tamkar ta kai ma ta duka saboda tsananin haushinta. “Amarya kike ne kowa?, ke wacce iriyar shashar mata ce ne wai, kullum sai anzo ance miki yi kaza yi kaza, gaba ɗaya ƙwaƙwalwan kifi yafi naki jaa…to wuce ga Sadauki can na jiranki, za’a kaiki aikin nome gonaki”.
“dan Allah ai min afuwa, bana jin daɗi, inata fama da zazzaɓi tun jiya kuma bansha magani ba”. Matar ta banka ma ta harara da faɗin,”ko ba zazzaɓi ba, to faɗawa wani ba ni ba…mtswww, karki ɓatan lokaci”. tai gaba ta barta anan tsaye tana cije fuska saboda yana dukkan gaɓɓan jikinta ke ma ta ciwo.
a harabar wajen gate ta tarar da sauran bayin da za’a tafi da su, ta tsaya daga gefe tana matsa kwankwasonta dake ma ta ciwo matuƙa, idanuwanta na daɗa ƙarewa kyawu da girman masarautar, ƙwarai rayuwa test and trial ce, yanzu duk wanda zai kalli wanda ke cikin wannan masarautar zaice ba shi da wata matsala da zata kaishi ga damuwa a rayuwarsa, daular da suke ciki tafi gaban ta haifar musu da rashin jin daɗi, to amma sai dai ba anan abin yake ba, sun ɗanɗani ɗaci da baƙin ciki, sun gogi wani tabo da ba zai taɓa goguwa agaresu ba, indai har da rai da kuma lafiya a kowacce rana da bugawar agogo sai sun tuna wannan ƙaddarar, wannan jarabawar ta ubangiji, haihuwar ɗan gaba da fatiha acikin zuri’arsu.
ta karkata hankalinta ga motar sojojin dake shigowa jiniya na tashi, fadawa da securities na kewaye motar har zuwa lokacin da ta sami waje ta faka, bata ɗauke kai a motar ba da mutanen ciki da ta ke jiran fitowarsu, duk da tasan cewar ba zai wuce Major bane, dan yawanci motarsa ce kaɗai ke shigowa jiniya ta karaɗe ko’ina. to amma duba da yanda mafi yawa dakarun gidan sukai kan motar zaka san akwai wani mai ƙafa na gidan nan acikin motar. sanda ta sosa kanta saboda ƙaiƙayi lokacin idonta ya sauka akan farar ƙafar dake fitowa zuwa waje, ta ke gabanta ya faɗi, tai saurin ɗauke kai zuwa gefe, dan Allah ya sa ni Aaliya na ma ta kwarjinin da numfashinta ke katsewa a duk sanda ta ganta.
ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana kallonta ta gefen ido lokacin da ta fito daga motar gaba ɗaya ita da ɗanta da kuma Major ɗin da taji jiya su Sakina na raɗe-raɗin cewar sati na gaba za’a ɗaura auren Aaliya da Major, ita kuma Akila zata auri wani ministan health dake saudia. kallonsu ta ke cike da burgewa da sha’awa, da ace tai haƙuri tabbas da a yanzu da duniyar Maryam ta sauya dole itama tata ta sauya zuwa cikar burinta, inda ace ta bar wannan soyayyar da ta kewa Maryam a matsayinta ta gaskiya babu sirkin yaudara da a farar fuskarta da aka santa da ita, saɓanin baƙinta.
lokacin da Aaliyan tazo wucewa saita tsinci kanta da saurin zube gwiwoyinta a ƙasa ta shiga roƙon alfarma da magiya akan sassaucin irin wahaltuwar da ta keyi wajen bauta.
Aaliya ta dubeta kaɗan tace,”bani da hurumi da matsalarki, ki nemi Maryam”. daga hakan suka wuceta, Alhassan na jin tausayinta a ransa, domin a kallo ɗaya zaka ma ta ka gane tana garuwa.
“hankalina yayi can gaba ɗaya, na kasa samun natsuwa…ban san me yasa Akila ta hanani zuwa ba”. Aaliya ke maganar da Major Mukhtar fuskarta na nuni da tsananin damuwar da ta ke ciki akan lalurar ƴarta da aka sanar ma ta tun a daren jiya.
cikin taushin muryar dake kwantar da hankali Major ke lallashinta akan haƙuri da tafiyar da ta dage saita yi a yau zuwa nigeria. “kuma ki kwantar da hankali, kinma fa ji muryar Daughter, kinga kuwa ai ta sami lafiya”. tai shiru for some seconds kamin ta ɗago raunannun ƙwayar idonta ta kalle shi tace,”but Major me ya kawo asthma a tare da Maryam?, bayan ni da kai babu wanda yake da wannan cutar”. “your Excellency wata cutar ai ba gadonta akeyi ba, jarabawa ce kawai daga ubangiji”. ta sauke numfashi da faɗin,”haka ne, Allah ya bata da sauƙi. amma Major ina so Maryam ta kasance a wurina sai dai ina jin nauyin Akila”. yay murmushi kamin yace,”itama zata ji nauyinki ai, hakan zaisa ta bar mana ita mu tafi da ita gidanmu”. Aaliya tasa hannu ta ɗan rufe fuskarta, yana murmushi ya saita camerar wayarsa ya ɗauketa saboda kyawun da tai masa a hakan.
“idan an ɗaura aure, ko Alhassan ya zauna anan, ko kuma na kaishi wata ƙasar”. tai saurin ɗagowa tana dubansa da son jin dalilin hakan. ya kai ƙaramin kofin shayi bakinsa, bayan ya kurɓa yace,”saboda na lura idan yana tare damu ba zai barni na sake dake yanda nake so ba…ki kalla a hakanma yanda yabi sawa dukkan wani motsi namu ido”. siririyar dariya kawai tai bata ce komai ba.
“Almustapha zai wuce italy gobe ƙaro karatu”. ya faɗa yana dubanta ta cikin reflection glass na cup ɗin. tana datsa naman da fork ɗin hannunta tace,”Imam fa?”. ya murmusa leɓensa sannan yace,”burin Imam shine football, shima next tomorrow zai wuce england”. ta ƙara tambayarsa,”ehen what about Ibrahim”. sai daya ɗaga gira sama sannan yace,”kin manta yace ba zai baro saudia ba sai ya sauke alƙur’ani”. ta tsayar da ƙwayar idonta cikin nasa da cewar, “zamu je can fa honeymoon, dan haka shima kamata yay ka tura shi da nisa…tunda na lura 1by1 so ake a nisantani da yarana”. ta faɗa tana ɗan ɓata fuska kaɗan, yay dariyar da ta bayyanar da haƙoransa tare da kai hannu zai shafo fuskarta maganar Alhassan ta dakatar da shi. “Dad…”. tsayuwarsa a gaban dining ɗin ta haɗe da dunƙulewar hannun Major yana cije leɓensa na ƙasa da kallon Aaliya ta ƙasan ido, a hankali ya furta.”u see bah…ai dole ma na luluƙa wannan yaron da nisa”. Alhassan yaja ɗaya daga cikin kujeran dining ɗin ya zauna, yana naɗe hannun jallabiyarsa yana faɗin,”be a little more patient…next week ne fa kawai”. ya faɗa kamar bada mahaifin nasa yake ba, yana mai janyo plate ɗin chicken burger gabansa. “kuma Mami shikenan haka ake fisabilillah, dan kin sami Dad sai kike mantawa da ni a duk time ɗin cin abincinki da kika san tare muke ci. duk da Dad ɗina ne am little bit jealous”. yay maganar yana kai fork bakinsa, ya kuma haɗe da ranƙwashin da Major ya bashi. Aaliya dai kallonsu kawai ta ke tana murmushi.