SIRRIN ƁOYE COMPLETE

for those who viewed, vote, like and comment i really apprciate, thank so much to you guyz, i love you lodi lodi.
Plss Comment, Share & Vote.
SIRRIN ƁOYE
By Oum Ramadhan✍????
Kuyi Haƙuri Ƙafa dubu sau dubu kunji Mutanen Arziƙi Mutanen Amana.
(43)
3Months Letter.
Qatar University, Doha.
“Maryam Mukhtar”. sautin kiran sunan nawa ya fito ta cikin hall ɗin daga can sama, kuma daga bakin Shamsiyya Sani, sanin cewar kiran nata bana arziƙi bane yasa ban tsaya sauraronta ba, naci gaba da tafiya abina, tafiyar daka kalla yanda nake yinta zaka san nayi matuƙar gajiya.
a hankali nake saukowa daga steps ɗin bakin hall ɗin namu, hannuna na dama riƙe da matsakaiciyar jaka kasancewar yau ban lodo handouts ba. kamin na kai ga ƙarasa sauka daga step na ƙarshe na zare space glass ɗin dake kewaye da rabin fuskata, sannan na zura hannun haguna cikin aljihun pink abayar dake jikina wadda su Shamsiyya sukai ta santinta suna faɗin rigar ta dace da ƙirar jikina.
a bakin ball ɗin na tsaya ina jiran fitowar Shamsiyya da Nusaiba amma shiru shiru basu fito ba, naja ƙaramin tsoki na takaici sannan naci gaba da takuna cikin natsuwa har sanda na taka kan titin cikin makaranta, yanda nake ta faman ɓata fuska zaka ce ko banda lafiya ne, haka ina ji wayata na ringing amma naƙi ɗagawa duk dana san mutumin da kiran nasa ke shigowa cikin wayar me muhimmanci ne a gareni, kamar yanda na banbanta ringing ɗinsa dana saura.
“Ya Ahmad”. angona wanda zaa ɗaura min aure da shi nan da sati biyu masu zuwa. tafiyar da nayi akan titin gaba ɗayar baifi taku 8 ba naja na tsaya, tsayawar tawa kuma tai daidai da tsayawar motar da ta zo ɗaukana a gabana.
acikin yaren larabcin da a yanzu ya maye harshena nace da driver,”me yasa kayi late yau?”. “kiyi haƙuri ranki ya daɗe, na kai Alhassan library ne, bai kammala da wuri ba ne shi yasa, kuma nayita kiran wayanki baki ɗaga ba”. “yana ina?”. na tambaye shi a sa’ilin da nake duban cikin motar ban ganshi ba. “yanzu zai ƙaraso ya tsaya da abokansa ne suna gaisawa, hangoki da yay ne yace na ƙaraso na ɗaukeki…ga ma shinan naga ya taho”. ya ƙarashe zancen yana min nuni da direction ɗin da Alhassan ɗin ke tahowa wanda ke gab da iskomu.
“menene? ba ki da lafiya? wani abun aka maki?”. tambayoyin da Alhassan ke jera min kenan sanda ya ƙaraso yana ɗora hannunsa saman goshina, yana mai tambayar cike da nuna damuwa da kulawa. na kwaɓe fuska ina karayar da kai nace,”na gaji ne”. “to sannu”. ya faɗa yana amsar jakar hannuna, sannan driver ya buɗe mana motar muka shiga, kuma ko da shigarmu ban iya zama ba sai kwantawa da nai na ɗora kaina saman cinyarsa.
“Mami ta tafi?”. na tambayeshi a sanda amon muryata ya fito a hankali. “har ta shirya sai kuma tace ta fasa wai ba yanzu ba”. lokaci guda naji wani abu ya tsarga min a zuciyata, wani abu da ya haddasa jin daɗi a ƙasan ruhina. ko kaɗan bana son nesanta da ita, shi yasa ko da na taho karatu wata ukun nan da nai babu ita kusa da ni sai nake jina tamkar ina rayuwa ne acikin kurkuku, irin kurkukun nan dake da duhun ɗaki da kuma ganiyar azabtar da me laifi.
driver ya tsayar da motar a rumfar wajen da aka tanada dan ajiye motoci, motocin da ake fita da Ammi kaɗai acikinsu, saini dana zo a yanzu, ya fito yazo ya buɗe mana ƙofa, kamin na zuro siraran ƙafafuwana da suke ɗauke da gajiya waje, Alhassan ya kama hannun mukai cikin gida. sanin cewar a irin wannan lokacin Ammi na tare da Abbi ne, yasa bamu biya ta parlon da ta ke zama ba. muka wuce kai tsaye zuwa ciki inda sauran ɗakunan ɓangarenta suke wanda acikinsu ne aka fitar min da babban ɗaki guda aka bani tun zuwana karatu ƙasar, dan lokacin da Ummi tai aure acan saudiya wurinta na koma da zama, saima lokacin da za’a saka ranar biki ne naje can abuja inda Mami ta ke na zauna na tsawon sati biyu daga nan kuma nayo nan, dan ko su Yagana banjewa sallama ba a lokacin.
“Subhanallah, me ya faru da ita?”. muka jiyo muryar Ammi da bamu tsammaci gani ba tana tambayar, na kalleta da gajiyayyun idanuwana ina ƙara kwaɓe fuska nace,”Ammi yau na gaji ne”. sai ta miƙa jakar dake hannunta wa Kuyangar dake bayanta, sannan tai saurin tahowa gareni ta riƙoni zuwa jikinta. Alhassan kuma ya wuce ɗakina kaimin jakata, akan cushion ɗin parlon muka zauna Ammi ta shiga warware min vail ɗin dake kewaye da fuskata tana yi min sannu.
ta kwantar da kaina bisa kafaɗarta tana jera min wata sannun, sannun da bata da adadi tun daga lokacin da ta riƙoni. cushion ɗin da muke zaune akai na fuskantar steps ɗin da sukai sama acikin parlon, ta nan na jiyo takun tafiyar takalmi ƙwaf-ƙwaf na sakkowa daga upstairs ɗin, kamin wucewar sakanni biyu kuma naga ɓulluwar Mamina, tana sanye ne da butter milk ɗin abaya wadda tasha stones a jikinta, ta kuma matuƙar amsar kyawun nata, ta ƙarasa saukowa tana exchaging hannu na riƙe wayar dake kare a kunnenta zuwa ɗayan hannun dake riƙe da ƴar ƙaramar jakarta. kuma ta ƙaraso wajen cushion ta cikin wayar dake kare a kunnen nata ta ke faɗin.
“a’a i just want to stay more for a while”. tai shiru kamin ta ƙara magana,”oak hakanma Yayi Your Excellency. muyi waya letter”. daga haka ta katse wayan a yayinda ta ke zama acikin ɗaya daga cushion din. “sannu da hutawa Ammi”. “yauwa”. lokaci guda idona ya cika da tarin ruwan hawayen da basu kai ga sakkowa ba, muryana na rawa nace da ita,”Mami sannu da gida”. “yauwa sannu”. ta faɗa ba tare d ta nuna halin in kula a gareni ba, wanda hakan ke damuna sosai, kuma da dukkan alamu bata gane ina cutuwa da wannan shariyar tata ba, haka ko time ɗin dana zauna a abuja zaman da mukai da ita tamkar wani zaman kishiyoyin da basa jituwa ko kuma zaman sirikan da, wannan ƙwaƙwƙwarar magana bama yi da ita, sai dai na bito da ido, nayi tunanin kala daban daban ko wani laifin na ma ta amma na gagara gano komai, kuma taƙi bani damar da zan zauna da ita naji laifina na bata haƙuri.
nasa hannu na mayawar da hawayen dake neman sakko min, kamin muryarta ta ƙara fito min da faɗin,”Daddynku na gaidaki, wai bai sameki a waya ba”. tai maganar idonta na kan wayar da ta ke shafawa. “munyi lectures da yawa ne yau shine nasata a silent”. bata ƙara cewa komai ba sai Ammi da ke cewa,”inaga ki kira doctor ya duba Maryam, ban yarda da yanayinta na yau ba, kanta ma naji da zafi”. nai saurin ce da Ammi,”Ammi lafiya fa nake wallah, kawai stress ɗin yau ne”. “eh duk da haka dai yazo ya baki wani maganin kisha…tashi kije kiyi wanka ki ɗan huta kamin ya ƙaraso”.
Alhassan daya ƙaraso wajen yana zama kusa da Mami ya ɗora hannunsa a bayan wuyant aya dafata ya kalleni yana cewa,”zama ki rabu da wannan son jikinne, kwana nawa ya rage”. na turo baki gaba ina hararsa. sai yasa hannu ya ɗago fuskar Mami yana ce ma ta,”kalla yanda ƴarki ke hararata, to ki faɗa ma ta na rigata shaƙar iskar duniya, ta kiyayeni kamin taji ajikinta”. Mami ta murmusa kuncinta ba tare da ta ce masa komai ba ta maida kanta kan wayar. Ammi tave da shi,”shegen son girma kaman gyaute…kai yanzuma akace ka daketa saika taɓata”. ina siririyar dariyar nace,”rabu da shi Ammi, ai yanzu ko Bro Almustapha ba zai ɗaga hannu akaina ba, kasan kenan kuwa na girmi gaban dukanka”. sai ya jijjiga kai baice komai ba, sannan ya sumbaci Mami a kumatunta kamin ya miƙe tsaye yasa hannu acikin aljihun wandon suite ɗin dake jikinsa, ya dubi Ammi yana ce ma ta,”mijinki ne fa yace na kira masa ke, kiyi sauri sauri kije fita zamu yi”. Ammi ta kai masa hannu ya kauce yana dariya. “kai ni wai yaushe ma zaka koma inda kafi wayo ne, na gaji da ganinka ina faɗa maka”. yana nufar hanyar fit ya nunani da baki yace,”sai anyi bikin wannan ƴar zan koma, nima na gaji da ganinta saboda tana shigar min cikin al’amura”.
ko dana shiga wanka na jima acikin bathtub cikin ruwan zafi kamin na fito, dan saida na tabbatar ruwan zafin ya ratsa ilahirin jikina ta yanda gajiyar zata saurin sakata, ina tunawa da karatun test ɗin da nake da ita gobe.
na shirya cikin wata riga armless kamin na zauna a dining ɗin da yake acikin ɗakin nawa na shiga zuba abinci. kuma fara cina kenan wayar Sweety ta shigo cikin tawa, na daɗa kallon sunan Ya Ahmad ɗin dake yawo akan wayar fuskana ɗauke da tarin murmushi na jin daɗi, ban ɗaga ba saida kiran yazo gaba da yankewa tukunna.
ajiyar zuciyarsa na fara juyowa a kunnena kamin kiran sunana ya fito daga bakinsa. “me kyauna”. laɓɓana suka tale da kyakykyawan murmushi kamin na amsa masa da cewar,”na’am Yaya nah”. murnushinsa mai sauti ya fito kamin yace,”me kyauna yau nayi kewanki da yawa, duk kinsa na shiga damuwa da rashin jinki”. cikin sigar lallashi da ban haƙuri nace da shi,”sorry Yaya Nah, wallah yau munyi busy ne da yawa a school, baka kalla ba ma duk na gaji, jikina sai ciwo yake min”. na faɗa ina shagwaɓe murya da fuska kaman ina gabansa ne. muryarsa ta fito cikin tausaya min da faɗin,”ayyah sannu Me Kyau nah, sannu kinji, inama ace munyi aure dana kawar maki da dukkan gajiyan dake tare da ke…kinci abinci?”. na kaɗa kai kaman ina gabansa b atare dana amsa da baki ba, kuma shima kaman yaga hakan sai yace,”to please ki samu kici abinci saiki kwanta ki huta, kiyi bacci mai yawa please”. nace da shi,”tom Swty”. “albishirinki”. nai saurin amsawa da,”goro”. “tomorrow by now insha’Allah ina tare da ke, zanzo na ganki me kyau nah, na gaji da rashinki a kusa da ni, wannan 2weeks ɗin daya rage ji nake kamar shekara biyu ce nan gaba”. na doka wani tsallen murna da jin daɗi ina faɗin,”Allah ya kaimu goben, Allah ya kawo min kai lafiya…Allah nima Yaya kewanka nake sosai, wataran har sai naji kaman nayi kuka”. duk da ba kallonsa nake ba a lokacin amma nasan ya kaɗa kai kamin yace,”a’a karki kuka plss, kinga hawayenki masu tsada ne, bana so ake zubar min dasu any how, duk da cewan akaina ne za’ayi”. na gyaɗa kai kawai, da haka muka ci gaba da hiranmu ta masoya, haka mukai ta hiran ina cin abinci, bai kuma yi min sallama ba sai daya ji nace na ƙoshi, kuma bai bai yarda da hakan ba sai da muka vedio call ya kalleni sosai sannan yace na haska masa cikina tukunna ya gyaɗa kai yace na yarda yanzu, saura bacci kuma, shima kar a tashi saina tashi me kyau da kaina.
acikin baccin dana kwashi mintuna ashirin inayi na jiyo daddaɗan ƙamshin turaren Mamina ya karaɗe min cikin hanci da cikin kaina, na buɗe murfin idona a hankali ina dubanta, tana tsaye bakin dressing mirrow ɗina tana maƙala sarƙata a wuyanta, sai nai murmushi kamin na tashi zaune na dubeta ta cikin madubin da ƙwayar idonta ke kallona ta cikinsa. sai nai ƙasa da kaina ina wasa da yatsuna nace,”Ummi ce ta saya min”. murmushinta me ƙarfin sauti ya fito kafin tace,”na sa ni ƴar gidan Mami, aro za’a bani please”. saina ɗago kaina ina dubanta ta cikin madubin kamar yanda ta ke dubana nace,”duk yawan sarƙoƙinki sai kin ɓige ata aro Mamin Alhassan, wannan fa me ƙaramin kuɗi ce ba dai-dain sawarki bace”. ƙwayar idonta ƙyam akaina, talewar da leɓenta yay da murmushi tun ɗazu har yanzu, tace,”na sa ni ƴar gidan Ummi, yau ɗin banjin saka nawanne, na aro na keso, na aronma wannan, ko ba za’a bani bane?”. na ɗauke idona daga ƙwayar idonta na kaishi ƙasa sannan nace,”karki taɓa min abina, ki aje min ban baki izini ba”. ba kallonta nake ba, amma ina jin sanda ta zare sarƙan daga wuyan nata ta buɗe akwatunta ta saka, sannan tace,”kiyi haƙuri na taɓa maki kaya ba tare da neman izininki ba, ba zan ƙara ba insha’Allahu”. na ɗago fuskata da tai shaɓe-shaɓe da hawaye cikin ƙanƙanin lokaci, na kalla har ta kai bakin ƙofa zata buɗe ta fice daga ɗakin, saina maida kaina ƙasa nasa tafukan hannuna na rufe fuskata, kuka ya kuma ƙwace min.
sai naji tausassun hannunta akan nawan suna ƙoƙarin buɗe fuskar dana rufe, daga nan kuma ta janyoni jikinta gaba ɗaya ta rungumeni tsam wanda har ina iya jiyo bugun zuciyar dake harbawa a ƙirjinta, a hankali ta ke shafa gyararriyar sumar kaina da ta sha gyara, bata hanani kukan da nake ba har sai da na gaji dan kaina na tsaya, na tsayar da kukan a sa’ilin da na shiga ma ta magana cikin shashsheƙar kuka.
“Mamina…”. ban iya cewa komai ba wani sabon kukan ya kuma zuwar min. sai naji ta sauke ajiyar zuciya a hankali kamin ta fara magana. “na sa ni Maryam, Na san dalilin hawayenki. baki min laifin komai ba, Maryam kunyarki nake ji shine dalilin daya sa nake kasa sakewa dake”. na ɗago kaina daga jikinta ina dubanta nace,”Mami wacce iriyar macuciyar kunya ce wannan da za ki bari ta kassarar da ƴarki? Mami ba zan yarda da wannan furucin naki ba, saboda haka karki yaudareni da batun cewar wai kunyata kike ji shi yasa kike yakice kanki daga gareni, ba don mu biyun da kika haifa duk ta dattin hanya kika samar damu ba, da saina ce ba kya ƙaunata ne saboda kin haifeni a shegiya, amma tsakani da Allah meye banbancina da Alhassan da ni ba zaki iya bani soyayyarki da kulawarki ba, ko kuma dan shi ya taso acikin gata da daula ne, ni kuma na rayu cikin karkara, na rayu a ƙazantaccen wurin da kike ganin ba za ki iya tarayya dani ba saboda shi, to bari kiji, wallahi summa tallahi ƙauyen bichi ya fiye min wannan daular masarautar taku sau dubu miliyan, ina ƙaunar bichi fiye da wannan ƙasar taku, nafi ganin kyanta akan wannan wajen da rashin rayuwata acikinsa ya hanani samun soyayyar uwata…ba komai Mami, na gode da iya amsawar ma da kikai na cewar kike haifeni, Allah sarki Gwaggona, Allah ya jiƙanki da rahma ya haskaka ƙabarinki, na tabbata ko babu soyayyar wata uwa a gareni a duniyar nan, tunawa da iyaka tata dana samu ma kaɗai ta isheni nai farin ciki muddin rayuwata, ballantana ina da Ummi, wacce ta sadaukar da jin daɗin rayuwarta dan ganin na rayu, ta hana kanta jin daɗi da walwalar duniya duk saboda kada na shig damuwa ko na sakan ɗaya”.
sai kawai itama naga na shiga zubar da hawaye daga idonta, kuma ta ke hankalina ya kai ƙololuwar tashi, hakan yasa na tsayar da maganganuna, na shiga kaɗa ma ta kaina da sauri ina kama fuskarta ina goge hawayen, saita kuma rungumeni muka shiga kukan tare, kukan da bana komai bane saina huce takaicin da zuciyoyinmu ke ciki.
“ki yafe min Maryam”. muryan Mamin ta fito a hankali, a hankalin daya haifar da tsargawar jin wani tsananin tausayi da jinƙai na mahaifiyata. “ni ba ki min komai ba Mami, dan haka ki daina neman yafita, nice dai zan nemi yafiyarki, na kuma roƙeki da Allah nima ki samman soyayyarki da kulawarki, ko da ace bai kai kwatankwacin yanda kike nunawa Alhassan ba”. “Maryam kenan, ba ki san cewar nafi ƙaunarki akansa ba. ba za ki gane bane, you are still a baby, shi yasa gaba ɗaya kika kasa fahimtata, Maryam ina kunyarki ne idan na tuna ta irin hanyar dana samar dake, amma kiyi haƙuri ki yafe min, nima bana jin daɗin yanda nake mu’amalantrki, kuma daga yau na daina, insha’Allahu, zan nuna miki dukkan so da ƙauna da kulawa muddin rayuwata, ƙila ma har kice Mami wannan soyayyar ta fara isata, domin za ki dinga ganinki ne kamar jaririyar dake shan nono…kin yafe min ɗin?”.
ban san lokacin da wani murmushi ya suɓuce min ba, na kaɗa ma ta kawai, saita ɗago da fuskata sama ta sumabace ni a goshina da kumatuna, kamin ta furta,”ina sonki Maryam, ina tsananin sonki”. nima nace da ita,”nima ina sonki Mamina”. ta kamo hannuna ta riƙe acikin nata, sannan murya a hankali tace,”idan kina cikin fushi ki daina magana kinji, ki dinga bari sai kin sauko, dan na lura ba kyau iya controlling harshenki a duk sanda kike cikin yanayi na ɓacin rai, kinga aure za kiyi, idan ni na ɗauka ba lallai mijin rufin asirinki ya ɗauka ba”. sai na. kaɗa kai nace,”zan kula insha’Allah”. “yauwa Allah yay maki albarka”.
shiru ya gimla a tsakaninmu na wasu ƴan sakanni, kamin tai min tambayar dana iya amsa ma ta da ƙyar saboda kunya. “ba muyi maganar da Umminki ba, aina Ahmad ɗin yace zaku zauna?, lagos ɗin ko kuma a kano?”. “Lagos ɗin yace, idan ya sami hutu kuma sai muke zuwa kano”. “hakanma yayi, to ya batun tsarin gidan ya faɗa miki?”. na ƙara yin ƙasa da kaina cike da kunya nace,”ehh hoton yana wayata”. “to saiki turawa Daddynki, ɗazu yace yanata kiran wayarki zai tambayeki. duk da Umminki tace ita zata sayayyar komai. kin san Mai Martaba ya baku gida ma anan?”. sai nai saurin ɗago da kaina ina kallonta, kafin na girgiza kai nace,”a’a Mami”. “ɗazu ya bawa Yayanki Almustapha key ɗin gidan, yace ya bawa Ahmad ɗin idan sun haɗu”. na shafa gefen fuskata a hankali kamin nace,”Allah sarki Abi an gode Allah saka da alkhairi, Mami ki masa godiya”. ta ɗan harareni da wasa kan tace,”tunda ni ce bakinki ko”. sai kuma ta ƙara cewa,”me za kiyi yanzu?”. na ɗaga kaina sama na kalla agogo sannan na sauke nace ma ta,”muna da test har uku gobe, zan duba littafaina”. ta gyaɗa kai,”to yayi, ai karatu da yawa. bari na ƙyaleki idan kin gama saiki sameni a ɗakina, dama saboda ke na fasa komawa gida, dan haka daga yau har zuwa ranar da Umminki zata miƙaki ɗakinki lokacina gaba ɗaya naki ne”. murmushi kawai nake yi, na sakko akan gadon na dakatar da ita taga fitar da zatai. “Mami baki sa sarƙar ba”. da murmushin da bai bar fuskarta ba tace,”yanzun kuma zaa ara min?”. nasa hannu a fuskata cike da kunya sannan na kamo hannunta ta tsaya a gaban madubin, na ɗaura ma ta sarƙar sannan na ɗora haɓata saman kafaɗarta muna kallon juna ta cikin madubin, kuma muna sakarwa juna ƙayataccen murmushi, tare da haskawar tsantsar soyayyar da muke yiwa juna acikin ƙwayar idonmu. “kinyi kyau Mamina, kin haska sarƙar”.
Alhassan ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, ya tsaya daga bakin ƙofar yana kallonmu cike da burgewa, kuma ba mu juya gareshi ba, shima kuma baiyi magana ba sai daya gama kallon namu sannan yace,”gwara dai ma kiyi auren ki tafi ki ƙyalemin Uwa”. baki kawai na murguɗa masa bance komai ba, ya ƙwalo min biron dake hannunsa na kauce ya sauka akan wuya Mami, Mami tace da shi,”ya maka kyau Alhassan”. “yi haƙuri Mami”. tace,”ai ba wani abu bane, indai ƙwalowa mutum abune karka daina kaci gaba, zanyi maganinka wataran tunda kai baka san alkunya ba”. yay dariya yana cewa,”yi haƙuri Hajiya Mami”. “ka dai ci gaba kaji, garin jifan mutum da abu ka jefa ka sami Ubana, to nima kuwa da izinin Allah zan rama akan ubanka Major, ko da yake Allah ba azzalumin bawansa bane gashi yau da kanka ka rama min akaina, amma duk da haka ka sa ni sai dai idan ban sami abin jifa ba, saina jefi goshin Major da shi yayi ƙwalele”. ya rufe bakinsa yana dariya yana faɗin,”wa yaga goshin Dad yayi tsini”. ta girgiza kai tana faɗin,”Allah ya gyara min kai, yanzu ya akai? me kawoka takura mana?”. sai ya dubeni yana faɗin,”waike me ya sami wayarki?”. nace,”me ka gani hala?”. “Dad ne yace yanata kiranki tun ɗazu a kashe”. saina sa hannu na rufe baki na nufi wayar ina faɗin,”laaa wallah na manta na kashe sim ɗin, Na Yaya ne kawai a kunne”. yaja tsaki kamin ya taɓe baki ya haɗa da faɗin,”to dai yace ki kira Ya Ahmad ɗin ki faɗa masa ya kawo masa result ɗin genotype ɗinsa”. ban san dalili ba haka kawai naji allon ƙirjina ya girgiza, na ɗago na dube shi da sauyin yanayin da fuskata ya samu nace,”me za’ai da shi?”. yace,”ki kira Dad ɗin ki tambaye shi tunda bani nake nema ba”. daga haka yasa kai ya fita a ɗakin. Mami kuma tace,”dama tuntuni ba’ai wannan gwajin ba?”. nai shiru ban iya cewa komai ba, dan yanda naji jikina yay sanyi a lokaci ɗaya. sai tai fita tana faɗin,”to ki kira shi da sauri ki sanar masa kinsan halin Daddynki sarai baya son delay”. na ɗauke idona daga bayan ficewarta, na haɗiye wani abu a maƙogorona da ban san mene shi ba, kamin na iya neman wuri na zauna.
nasa finger print na buɗe wayar, kuma ta ke fuskata ta washe da annuri sakamakon cin karo da saƙon Ya Ahmad da nai, wani taraddadi dan aji yana neman mazauni acikin zuciyata ya washe, na shiga karanta text ɗin nasa da haskawar hoton fuskarsa acikin idona.
“I am in you and you in me, mutual in divine love. Saying it a thousand times won’t be enough to express my feelings towards you, but I’m going to keep saying it nevertheless- I love you! I will keep loving you till the end of my days, no matter what lays ahead of us Cutie nah, waiting and eager of the day, wannan ranar, a wannan daren da Ummi zata damƙa hannunki a nawa tace Diman Da’iman Ahmad…”.
sai na rungume wayar a saman ƙirjina na kifa kan gadon, na haɗe murfayen idona waje guda na lumshe, sannan naja leɓena na ƙasa na shigar da shi cikin bakina ina tsotsa da tarin murmushin daya ƙi barin fuskata, ji nake ajikina tamkar Yaya nah na rungume ba wayar dake ɗauke da saƙonsa ba. kuma ta ke hoton wannan ranar ya shiga haska min acikin idona, wannan daren ranar da Ya Ahmad ya buɗe min zuciyarsa, ya tona min sirrin dake shimfiɗe acikinta a ga me dani da soyayyata.
wannan daren daya sameni da Al’ameen a parlo muna hira, saurayina da ya min proving soyayyansa a computer school ɗin dana shiga, kuma a wannan daren ne zuwansa na farko gida da izinin Baba da Yagana, amma zuwan Ya Ahmad ya wurin ya tarwatsa zaman fahimtar junan da muke shirin yi ni da Al’ameen.
a gaban Yagana, gaban Ya Kabir, gaban Basma da Inna Zulai, gaban Ya Aminu da Baba, gaban Ummina, gaban kusan kowa na gidan. ya jawoni daga kan kujerar da nake zaune gefen Al’ameen, ya tsayar da duga-dugaina a gabansa, dab da shi sosai, ya kama dukkan hannayena biyu ya ɗora saman ƙirjinsa, saitin zuciyarsa, wani abu daya haifar da tasirin dana ji kamar zanyi fiffike na tashi sama.
wannan lokacin da nake a dab da gabansa, hannayena saman ƙirjinsa, sai nake jin zuciyata a lokacin kamar fayau ta ke babu komai acikinta, na kasa haɗa ido da kowa na kuma kasa kallon gefen da kowa yake, sai haɗiyar wani yawu nake a maƙogarona dake wucewa da ƙyar, kamin daga bisani naji ƙafafuna na neman gaza ci gaba da ɗaukata, dalilin wannan harufa huɗun da Ya Ahmad ya furta min.
“Maryam zaki Aure ni?.”