NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Dan Allah dan Annabi kuci gaba da haƙuri da ni, insha’Allahu komi ya kusa zama dai-dai, zaku sami lokacina kaman yanda kuke samu a farkon farawarmu…Allah dai ya bamu tsawon rai da lafiya…ina miƙo saƙon gaisuwata gareku, i love you all????.

Vote,Comment and Share plss????.

SIRRIN ƁOYE

By Oum Ramadhan✍????

Ina Mana Barka Da Juma’a.

(45)
Ethiopia.
Addis Ababa Bole International Airport

NOTHING GONNA CHANGE MY LOVE FOR YOU.
“if i had to live my life without you near me the days would all be empty, the nights will seem so long with you i see forever, oh, so clearly. i might have been in love before but it never felt this strong, our dreams are young and we both know they will take us where we want to go, hold me now, touch me now, i don’t want to live without you…nothing gonna change my love for you, you ought to know by now how much i love you…”.
Abdurrahim daya shigo motan ya kai hannu yay reducing volume ɗin waƙar dake tashi acikin motar, Kabir dake kwance ajikin kujerar motar ya buɗe idanuwansa dake a lumshe ya saukesu akansa, kallon Abdurrahim ɗin yake da irin kallon dalilinsa na rage masa volume tunda bashi yake jin waƙar ba, haka kuma motar ba tasa bace balle yay masa iko da abinda ke cikinta.
Abdurrahim ya shafo sumar kansa tunda ga ƙasan ƙeyarsa zuwa sama sannan shima ya jinginar da kansa jikin kujerar motar, kamin kuma ya kai hannu ya kwantar da kujerar shima yana sauke ajiyar zuciya.
“gashi, in the next 25mints jirgin zai tashi”. ya faɗa yana miƙawa Kabir wata farar takarda. Kabir ɗin ya amsa ya aje sannan muryarsa ta fito a hankali da cewan,”ka sami damar maida min da volume yanda yake ko kuwa?”. idanuwan Abdurrahim na kulle yace da shi,”kana da damu Kabir, wai mene amfanin earport ɗin dake kunnenka?, ka maida waƙan kaji kayarka kai ɗaya mana tunda ta zame maka waƙi’a farilla. ni wannan waƙoƙin soyayyan ciwon kai suke samin kasan da hakan amma sai kai ta shiga da hakkina, muji a gida muji a mota haba abin ai yay yawa. ni wannan Maryam ɗin ma ai jaraba ce agareka”. Kabir ya gyaɗa kai sau biyu ba tare daya ce masa komai ba, sannan ya ɗago daga kan kujerar gaba ɗaya ya kai hannu ya kashe waƙan duka, a zafefe yay kan Abdurrahim da cewa,”duk ranar daka ƙara min zancen Maryam, duk ranar daka ƙara alaƙantani da Maryam, duk ranar daka ƙara haɗa special mood ɗin da nake ciki da Maryam, na rantse maka Abdurrhim sai na sassaɓa maka kamanni, sai na bar maka mummunan tabon da ba zaka iya shaida kanka ba…i told you, don’t stop talking to me about someone’s wife kaga yanda zan faffasa maka baki”. a fusace yake maganar kamar zai kaiwa Abdurrahim ɗin duka, kuma shirunsa yay daidai da buɗe idon Abdurrahim ɗin ya kallesa sau ɗaya yana mai sauke guntuwar dariya a saman fuskarsa, kan yaja tsaki yace,”in ka fasa fasan baki Kabir”. gaba ɗayansu kuma sai suka saki ƙwafa a tare, shiru ya gimla tsakaninsu na wasu ƴan daƙiƙu, sai sanyin acn dake dukan jikinsu, kuma a wannan shirun na shuɗewar daƙiƙu biyu Kabir ya jera guntayen tsaki sunfi biyar, Abdurrahim daya gaji ya ɗago a harzuƙe yana cewa,”dilla Malam ni ka isheni da wannan tsokin naka. ai bani na kar zomon ba dan haka sai ka bari idan ka hau jirgi ka ƙaraci yin abinka acan, amma ni ka dameni”. sai kuma yaja gajeran tsaki yace,”you know i totally forgot”. yay maganar yana mai zira hannunsa a aljihu ya zaro wayarsa. “what do you forget?”. Kabir ya tambaye shi yana kallonsa a sa’ilin daya buɗe baki da zummar sauke masa bala’in dake cinsa.
“I was at the reception Yagana called me on whatsapp she wanted to talk to you. tana ta kiran naka wayan a kashe”.
“swithh off?” ya tambaya in surprise trying to pick up his phone from his pocket. “to ni dai haka tace min”. Abdurrahim ɗin ya ce a sanda ya shiga whatsapp yana serching numbern Mu’azzam ya danna voice call daga nan ya miƙawa Kabir.
wayan bai jima yana ƙara ba Mu’azzam ya ɗaga, daga can ɓangaren Mu’azzam ya gaida shi sannan Kabir yace ya miƙawa Yagana wayar idan yana gida. kuma abinda ya ɗaga hankalin Kabir a sanda Yagana ta karɓa kukan da ta fashe da shi, ƙirjinsa ya buga, fargaba kuma ta dirar masa. ya sauke gajeriyar ajiyar zuciya kan yace da ita,”Yagana lafiya? me ya faru?”. maimakon amsar daya zata daga bakinta sai yaji ta kuma rushewa da wani kukan, dan haka yay saurin katse kiran ya ɗauko tasa wayar ya kira Ahmad hankalinsa a tashe. “Kana gida?”. daga can ɓangaren Ahmad yace masa,”ehh ina gida amma ina shirin fita yanzu. i heard your voice full of anxiety, what happened?”. Kabir yay ɗan jimm baice komai ba, dan ko a iyaka muryar Ahmad ɗin ya tabbata ba wata matsala bace a gidan, rigima ce ta Yagana kawai, and now he can undertand the reason for her crying.
“Kabir kayi shiru, meke faruwa dama?”. tambayar Ahmad ta katse masa shirunsa, ya fitar da numfashi sannan yace da shi,”ba komai, ka kaiwa yagana wayar zanyi magana da ita. vedio call zan kira so on your data”. Ahmad ɗin yace da shi “to” ba dan ya yarda da cewan ba komai ɗinsa ba, duba da yanayin yanda yake maganar very cool.
A bedroom Ahmad ya tadda Yagana zaune a gefen gado ta duƙar da kai sai kuka ta ke, Inna Zulai da jikokinta sun zagayeta, da kuma ƴan’uwanta waɗanda suka fara zuwa biki tun a shekaranjiya da biki ya rage saura kwanaki huɗu.
“mene ya faru?”. ya tambaya yana ƙarasawa bakin gadon gefen da mahaifiyarsa ke tsaye. “uhmm waya san me aka ma ta, tun ɗazu dai ta ke kuka, kai tunda ta tashi ma zance maka. kuma anyi tambayar duniya taƙi cewa komai”. ya daɗa maida dubansa ga Yagana yana cewa,”Hajiya Yaganata menene? ko dai nine ba ki son rabuwa da ni kawai na haƙura na tare acikin gidan?”. sai a yanzu taji maganarsa dan haka ta ɗago kai da ta dube shi da cewar,”Yauwa ɗan aljannah zo zauna nan”. ta faɗa tana masa nuni da kusa da ita. “kukan na menene? ko duk saboda zan miki kishiya ne?”. sai kawai tai murmushin da za’a iya kiransa dana dole kuma na yaƙe sannan tace,”yo ni meye ruwana da amaryarka, me zai ɗagan hankali akan wata kishiya bayan nasan naci gida na kuma gama siye zuciyar mai gida, mtswww ni Allah sauƙenma nai kishi da wannan abar”. yay guntun murnushi shima yana cewa,”faɗi gaskiya dai”. tace, “kaga bar batun wannan sillan karan amaryar taka, kira min Kabiru a wayanka, na kira shi da ta Mu’azzam yaja min tsaki ya kashe”. tai maganar with serious face. yana kunna data kuwa sai ga kiran Kabir ɗin, ya ɗaga ya miƙa ma ta, a kallo ɗaya da taiwa idanuwansa ta kuma rushewa da kuka tare da zabga salati kaman wadda akayowa aiken mutuwa. Kabir ya matse idonsa yana cewa,”dan Allah dan Annabi ki bar ɗaga min hankali da wannan kukan naki”. “to Allah ya jiƙan rai Ubana Manniru nayi shiru”. ta faɗa tana sa gefen ɗankwali ta sha re hanci. yaso yin dariya amma kuma sai ya gimtse yana cewa,”kin san abinda hawayenki yake haifar min ai”. “ina kuwa zan sa ni Kabiru tunda nasan ba ba ƙaunata kake ba, Kabiru idan so ka ke na mutu ka aiko kawai a kashe ni ka huta da jin numfashina a duniyar nan, tunda ka tsaneni baka ƙaunata. wallah Kabiru a yau ko gobe ko jibi ko wani watan na mutu to kaine ajalina, na faɗa maka wannan sabuwar halayyar taka ita zata zama ajalina saboda zuciyata ba zata ɗauketa ba, duba fa tanda ka idanuwanka sukai loko, ga fa yanda ka rame, ka zuge ka zaftare kaman ragowar yaƙi”. ganin yana motsa baki zai magana ta dakatar da shi da faɗin,”kaga karka jama min musiba riƙe salatinka da kake ƙoƙarin jaa tunda ni dai Rakiya ba annoba bace….wai Kabiru ko sai ansa dalma an zana sunanka a goshina sannan zaka tabbatar ka kuma yarda da cewar kafatanin jikokina kai nafi so, to banma sa ni ba ko sanin hakan yasa kake galabaitar da sauran numfashin daya rage min, to matuƙar na mutu Ubanka Adamu kayiwa ba wani ba”. sai kuma tai shiru taci gaba da kukan. ya sauke ajiyar zuciya a hankali yace,”kiyi haƙuri Yagana”. “yo haƙurinka ko cuta Kabiru, tsakani da Allah watanka nawa baka gidan nan? ka ɗauki ɗabi’ar banza ta miskilanci ka ɗorawa kanka kana neman katange kanka ga kowa, yanzu abinda ban gane maka ba nake so naji shine bikin ma ba zaka zo ba kenan? kuma sai yaushe zan kuma ganinka a zahirance ba’a wannan hoton gajimaran ba, dan na gaji da ganinka a wannan iskar nasaran, ka yiwa Allah da ma’aikinsa ka dawo naji ka a kusa dani na sami natsuwa da kwanciyar hankali”.
“Yagana yanzu haka ma fa tahowa zanyi me zai hanani zuwa biki. kiyi haƙuri dan Allah nan da mintina kaɗan jirgin namu zai taso”. kawai sai fuskarta ta washe da fara’a ta shiga saka masa albarka da masa adu’ar isowa lafiya, kamin nan suka yi sallama ta bawa Ahmad wayar tana juyawa ga Inna Zulai tace ma ta ai maza a daddafa duk abinda aka san Kabiru naso kamin ya dawo.
“ka bawa Basma wayar please”. abinda Kabir yace da shi kenan sanda yake fitowa parlo. Ahmad ya kira Basma ya miƙa ma ta wayar da cewan idan ta gama ta kawo masa ɗaki. “Ya Kabir ina kwana”. “lafiya lau Basma, ya kike ya shirin biki?”. “muna tayi Yaya, yaushe zaka dawo? ko ba zaka zo bikin ba?”. “anjima zan sauka insha’Allahu”. “tom Allah ya dawo da kai lafiya. Ya Kabir karka manta da kit ɗin makeup ɗin dana ce maka”. “insha’Allahu Basma ba zan manta ba. ina Nawwara?”. “tana kitchen tana aiki”. sai kawai ya ɗan rumtse idonsa for a while kamin ya buɗe yace,”je ki kai ma ta wayar”. tai knooding masa kanta sannan ta nufi hanyar kitchen ɗin, ko da taje kitchen bata sameta ba dan haka ta nufa ɗakinta, zaune ta sameta kan carpet tana yanke farce, gashin kanta a barbaje wanda ta gama tsifarsa babu jimawa. Nawwara ta tsaya da yankan farcen tana kallonta har Basma ta ƙaraso ta miƙa ma ta wayar ta juya ba tare da tace ma ta komai ba, ita kuma ko da ta amsa wayar saita ajiye wayar a gefenta taci gaba da yankan farcen, har a sannan Kabir baiyi magana ba, kallonta kawai yake yana mai hango irin tarin gajiyar dake tattare da ita.
ta gama yankan farcen ta ɗago hannun tana dubawa ta gefen idonta sai ta kalla kaman mutum, hakan yasa tai saurin juyowa ta kai idonta kan wayar gaba ɗaya. sai tai saurin waro idanuwa waje tana dubansa da mamaki, sannan tasa tafukan hannunta ta rufe bakinta tana faɗin,”kaii”. tai maganar a irin wadda ta gama cika da mamaki.
“Ya Kabir ai ban shina ba wallah, bata faɗi mani kaine a waya ba kawai bani tai ta juya, ni kuma nai zaton ajiya ta ban”. bai magana ba sai ƙare ma ta kallo da yake for some seconds sannan yace,”me ya sami gefen bakinki?”. ta kai yatsa tana taɓa wurin kamin tace,”huciyan zazzaɓi ce”. “when kika yi ciwon?”. “an kwana biyu”. irin yanda yake ma ta maganar da kuma kallon da ya tsareta da shi duk saita ji ta kasa sakewa. ta miƙa hannu ta janyo ɗankwali zata rufe kanta taji yace,”karki saka”. hakan yasa ta dakata tana mai ƙara saukar da kanta ƙasa cike da kunyarsa na yanayin da ta ke na rashin ɗan kwali.
“wanne magani kika sha?”. “suna da yawa harda allurai ma. Yagana ce ta kaini asibiti”. tai maganar still idonta na ƙasa tana wasa da yatsunta, sai taji yace,”bada gashinki nake magana ba da kika wani hasko min shi gaba ɗaya, ki ɗago min fuskarki ki min magana ko na kashe wayata”. bata san mene ba amma haka kawai sai taji wani abu ya harba ta zuciyarta, ta ɗago da fuskarta gaba ɗaya ta ɗan dube shi sannan ta ɗauke idonta. “an gama alluran?”. “ehh an gama”. “magungunan fa?”. “suma sun ƙare na gama sha”. “amma me yasa ita huciyan zazzaɓin bai warke ba?”. “ai zai warke gaba ɗaya sai a hankali”. kaman a tsoroce ta ke da shi a yanda ya lura, ya sauke numfashi da sake tambayarta,”tun yaushe kike aiki da kika tara gajiya haka?”. sai tayi saurin ɗago manyan idonta tana dubansa da tsananin mamaki, ƙwarai da gaske ta gaji, gajiya ma iya gajiya amma taya akai yaga hakan shi?. ya katse tunaninta da faɗin,”why din’t you go to school today?”. taji me yace amma ba zata iya mayar masa acikin harshen ba, dan kamar yanda ya faɗa ma ta ne in yay ma ta magana da hausa to da hausan zata mayar masa, hakana inda english ne ma. sai tai shiru bata ce komai ba. “am asking you, you kept quite?”. sai taji wucewar wani abu ta maƙoshinta kafin nan ta kalle shi da cewan,”aiki ne yay yawa a gidan shi yasa”. “ke ɗaya kike aikin dama? ita iya ina ta ke? dan me aka ɗaukota? ba dan saboda ta karɓeki ba a time ɗin makarantarki. ko kuma dama can asarar kuɗina nake ba zuwa makarantar kike ba?, da kika san ba kya son makaranta why can’t you tell me eyeee?”. muryarsa a ɗage yake maganan kuma cikin faɗa, tuni idonta ya ciko da ruwan hawaye ta shiga girgiza masa kai, ta kuma kasa cewa da shi komai. “karki sa ke wannan hawayen su zubo”. ya ƙara faɗa very loadly, hakan yasa tai saurin sa hannu ta maida hawayen. “idan na dawo zan maki exams, idan kika kasa zan sami amsar tambayoyina anan, kuma za ki kalla mai zan maki”. “dan Allah Ya Kabir kayi haƙuri, wallah yau ne kawai banje ba”. “comon shut your mouth up”. sai tai shiru kaman yanda shima yay shirun, can kuma yay nisa yace,”ke me yasa ba’a maki ƙunshin ba?”. “mutane sunyi ma ta yawa, tace na bari zuwa gobe idan ta gama yiwa kowa saita yi min”. sai ya sa ki guntun tsaki na haushi da cewa,”ita ɗaya ce me yin lalle dama?”. tana girgiza kai tace,”a’a, Yagana ce dai tace ita zata yi mana”. “kuma da aka ɗaukota sai akace idan ta gama yiwa kowa na gidan ta tsallakeki ta gama yiwa baƙin da suka zo kamin ke ɗin ko?”. bata bashi amsa da baki ba ta girgiza masa kai kawai. ta ɓangarensa yay shiru yana janyo leɓensa na ƙasa cikin bakinsa, ya tsotsa for 1minutes sannan a hankali muryarsa ta fito da cewa,”karki wanke gashin, ƙunshinma ko da an sauya ra’ayi kar ayi. ki jirani na dawo, am on my way, in the next 5hours zan iso insha’Allah, be ready dana dawo zamu fita”. “to Allah ya dawo da kai lafiya”. sai taji yace,”tsorona kike ji ne?”. tai saurin kaɗa masa kai alaman a’a. “to ɗago ido ki kalleni kiyi adu’an”. ta ɗago tana kallonsa tace,”Allah ya tsare hanya, ya dawo mana da kai lafiya, ya kareka da kariyarsa”. “ameen ya Rahman…thanks to you. ki nemi abinci kici kinji ko, idan hidiman bikin yasa baku tanadarwa cikinku komai ba ki jira a parlo zanyi taking maki order yanzu”. “ai zuwa anjima za’ai girkin”. bai bi ta kan maganar tata ba yace, “me kike son ci?”. “Yaya ba sai ka kashe kuɗin wurin saya ba. aiki ne ma ya min yawa shi yasa ban samu naci ba, yanzu dana gama yankan farcen zanci”. a lokacin da ta ke maganar ji yay kaman ya zura hannu ta cikin wayar ya fizgota zuwa gabansa, yay ma ta kashedin muhimmancin cikinta a wurinsa da kakkausar murya ko ta samu ta shiga hankalinta, tai masa shiru da wannan surutun wofin. kuma a yanda itama ta ke kallon idonsa tana iya hangowa da kusa da ita yake zai iya make bakinta.
ta cikin shirunsa da yay yana jifanta da wani hargitsatstsan kallo maganarta ta kutsa ciki. “zanci abincin”. “me za ki ci?”. “komai aka samu Yaya”. sai ya gyaɗa kawai, ba tare da yace komai ya kashe wayan, kuma kashewan nasa yay dai-dai da shigowan Basma ɗakin.
“ba sai ki faɗi mani Ya Kabir ne a waya ba kuma kawai sai ki bani ki wuce”. Basman ta cuno bata baki tana miƙa ma ta hannu da cewar,”oho ni nai zaton kin gane nufina”. Nawwara ta ɗau wayan ta miƙa ma ta jikinta a sanyaye. Basma ta kuma cewa,”Yarinya kuma yanzu Yaya tazo”. wannan fargabar da Nawwara keji tun a ɗazu ta gushe, ta miƙe cikin jin daɗi tana faɗin,”tana ina?”. “see you kika wani miƙe, to ai har ta tafi”. Basma ta faɗa tana dariya. “are you serious?” “wallah, ita da Ummi ne fa, kin san sai yau ta dawo daga Qatar ɗin, kamin su wuce Abujan Ummi tace bari tazo ta gaida Baba”. Nawwara na murmushi tace,”Allah sarki Yaya naso na ganta wallah. anyway sai gobe ma haɗe a wurin dinner, Allah yasa dai aje dani”. “karma ki saka ran zuwa ma, saboda gidan duka za’a daɗe Yagana ma tace sai tace”. sai kawai Nawwaran ta gyaɗa da rashin jin daɗi a ranta, ta fita domin ci gaba da aiki.
tunda ƴan biki suka fara zuwa bata zauna ba, duk da cewar akwai iya yanzu da suke aiki tare wadda Kabir yasa aka kawo ta ke tayata aikin, ba damar ta zauna waccan zata bijiro ma ta aikinta, tunma masu ƴaƴan nan, itace wankin kashi, wankin kayan yara, ga ƙawayen Adawiyya ma motsi kaɗan sa ƙwala ma ta kira. hakanne yasa duk jikinta ke ciwo babu abinda ta ke a wannan lokacin irin tai wanka ta ɗan miƙe ko yane ta huta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button