NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE


Habib dake daga kishingiɗe akan 3seater ɗin ɗakin Ahmad, ya ɗan waiwayo kaɗan ya kalli Ahmad ɗin dake shafa oil akan askin da yay a ɗazu. Yace,”Ahmad tela ya kawo sauran kayan nan kuwa?”.
“kai bama dolensa ba. kayan fa da zan saka ne gobe a wajen dinner”. Mubarak dake gefe ya fashe da dariya sannan ya ce,”Daren farko mai sanya zumuɗin angwaye. Ahmad na lura gaba ɗaya a ƙagauce kake da zuwan jibi, gaba ɗaya tunda akace an wayi garin yau ka kasa sukuni”. Habib ma na dariya yace,”kai baka jishi bane da muka dawo daga masallaci, ya dokawa Maryam ɗin kira da sanyin asuba wai Mai Kyau 2days remaning fa ki zama mallakina”. Ahmad yay dariya da cewa,”Kai dai Habib anyi munafuki. shi yasa banso kazo ka tare a gindina ba, ba dama nayi waya da matata kunnenka na wajen”. Habib yace,”ni wane sa’ido ne baka min ba a lokacina”. Shuru ya ratsa ɗakin na tsawon wani ɗan lokaci, hakan ya bawa sautin tv’n dake kunne damar fitowa sosai. Jim kaɗan Mubarak ya yunƙuro zaune yana cewa,”Yauwa! ya maganar zuwan Umar M. Shariff wurin dinner?”. Habib ya kalle shi yana bashi hankalinsa da cewan. “naso jiya mun sake komawa da Saifullahi office ɗin Umar M Shariff ɗin, amma yau Mai Shadda yace muje around 4 mu same shi sai muje can office ɗin nasa tare, tunda akwai fuskar sani ai bayayi denying zuwan ba”. “Yauwa hakan ma is oak, dan ina son zuwan gayen nan wajen nan wallah, ina matuƙar ƙaunar waƙoƙinsa over”. Ahmad ya ɗan muskuta kaɗan a inda ya zauna yanzu sannan yace,”kuna ta batun M Sharif banji kuna maganan zuwan Moh-bad ba, after all kun san da cewan shi Mai Kyau tafi buƙatan zuwansa wurin”. Mubarak yace,”sha kuruminka angon ƙarni, wannan ai su Jemiron sun gama magana da shi ba, har kuɗin buking nasa duk sunyi payment run last week”.
Ahmad ya ƙara cewa,” ƙwamma hakan dai kam. a burge Matata da Ƙawayenta shi yafi, ba wai taku buƙatar ba”. ya numfasa sannan yaci gaba da cewa,”ni inata jibi, ita tana ta gobe dinner, ai na faɗa ma ta ta shiryawa jibin nan a jarumarta”. Habib ya kai hannu ya doki kafaɗar Ahmad yana cewa,”Ango sarkin zumuɗi, me kana ci na baka na zuba ne. kaman yaune fa, kuma wannan daren dai daka ƙwallafa rai akansa kaman yanzu ne”. dukansu kuma sai sukai ƴar dariya, kuma a wannan lokacinne Nawwara ta turo ƙofar ɗakin bakinta ɗauke da sallama ta shigo. daga bakin ƙofar ta duƙa ta gaida su sannan ta wuce kan ƙaramin table ɗin dake daga can gefe ta aje tray ɗin flask ɗin abincin da ta shigo da shi.
sannan ta ƙarasa ta bawa Ahmad wayarsa tukunna ta fita ta bar ɗakin. tana shiga parlo taji landline na ƙara, ta ƙarasa da sauri ta ɗauka dan bata manta da maganar Kabir ba. kuma tana ɗagawa deliver Man ke sanar ma ta yana bakin gate, tace ya bawa mai gadi sannan ta shiga ɗaki ta ɗako hijab ɗinta ta fita taje ta amso.
tabbas a duniyarta bata taɓa ganin mutum mai nutumci, karamci, tausayi, mutuntawa irin Ya Kabir ba, hakan yasa mutumin ke daɗa shiga ranta a kullum, kuma har abada ba zata manta da shi da alkhairansa ba, kamar yanda a kowacce sallah ta kewa kanta adu’a haka shima ta ke masa, kuma kaman yanda ta kewa kanta adu’ar samun miji na gari haka shima ta ke masa adu’ar samun mata ta gari. tasa fork ɗin dake hannunta ta datsi naman gandar dake cikin takeaway tare da yin bismilla ta kai bakinta…tana fara tauna ta ƙumshe ido saboda daɗin ɗanɗanon daya ratsa harshenta da bakinta, taci green banana salad ɗin kaɗan, kuma sai bayan ta gama tama sha ruwan swan ɗin dake haɗe sannan ta lura da maganin dake wata farar lleda ta daban, ta ɗauko shi tana duba sunansa da akasa provigil, sai kawai tayi murmushi ta ɓalla ta sha guda ɗaya kaman yanda taga an rubuta ba tare da tasan ko maganin menene ba.
kuma tasha ɗin bayan ta fito daga wanka sai ta ɓingle akan katifarta bacci ya ɗauketa, haka iya ta shigo ta dinga tashinta amma bata tashi ba.
ƙarshe Yagana tace a ƙyale ta huta dama ta gaji ai da yawa.

Please Comment, Share & Vote.

SIRRIN ƁOYE

By Oum Ramadhan✍????

(46)
8:30am
“ina Nawwara?”. Kabir dake tsaye a bakin entrance na parlon Inna Zulai ya jefa tambayar ga Jamila. “Yaya ba zata wuce part ɗin Yagana ba”. sai ya zare hannunsa na dama dake zube cikin aljihun wandon suite ɗin dake jikinsa, ya sose gemunsa a sanda yake kallon sashin Yagana, ya ɗauki kusan daƙiƙa uku yana kallon sashin kaman baƙonsa, nazari da tunani yake akan ta yanda zai iya shiga part ɗin Yaganan da yake ɗinke da jama’a ƴan taron biki da suka zo, ya kuma ratsa su ya wuce zuwa inda zai sami Nawwara ya kamo hannunta ya fito da ita, yay ɗakinsa da ita ta shirya acan sannan ya ɗauki mota ya fita da ita zuwa inda ya gama tsara zai kaita a gyarata kaman kowa, abinda ya tsara a jiya kenan da zarar ya dawo. kuma abinda ya hana faruwar hakan tun a jiya baccin da tai, lokacin daya dawo tana bacci bata tashi ba, kuma ko daya shiga ɗakinta ya taɓa jikinta sai yaji da ɗumi da alama ma akwai zazzaɓi jikin nata, wanda ya lura da hakan tun a lokacin nan da yake waya da ita. idanuwansa sun kalleta tar kuma sun fallasa masa yanayi ne na ƙarfin hali takeyi saboda babu yanda ta iya, matsayin ƴar aiki ta ke a gidan bata da batun cewar zata huta kaman yanda ta ke so, hakanne yasa ya haɗo ma ta da wannan maganin saboda bacci me nauyi ya ɗauketa, ya kuma saukar ma ta duk wata tarin gajiye dake tare da ita dama sauran ciwukan dake jikinta.
kuma abinda zai iya cewa shine tun a daren jiyan zuwa yanzu da yake tsaye anan hankalinsa da tunaninsa na kanta, yana kan son sanin a wanne hali ta ke ciki, taci abinci?, ta samu damar yin wanka?, ciwon dake damunta ya warke?, gajiyar jikinta ta barta?, sannan kuma ya tambayeta me ta ke so?. kwanaki da kwanaki kenan yana jin wani abu na wuce har zuciyarsa akan yarinyar, ya kuma rasa menene shi, abunda kawai ya sa ni yana so ya zamana yana kasancewa tare da ita, kuma yana so ta sake dashi ta dinƙa faɗa masa wannan ɓoyayyun sirrikan damuwar daya lura tana tare da ita tun farkon zuwanta gidan, ya sa ni ba zai magance ma ta komai ba, amma zai yi duk mai wuyar da zaiyi dan ganin ya rabata da damuwar da mutum zai ke iya tsinta a tare da itan.
sai kawai ya kulle idonsa ya buɗe tare da fuzgar da iska daga bakinsa, shi kansa ya san ya sauya 100%, baya da walwala a yanzu, baya da sukuni, baya iya sakewa da mutane, yanayin fara’arsa ma ta sauya, kullum zuciyarsa matsewa ta ke, foresure yasan ya canja daga Kabir ɗin shekaru baya da yawa, kuma kullum ƙaryata zuciyarsa da Abdulrrahim yake akan cewar Soyayya ce ta maida shi hakan, shi ai ba ragon namiji bane, dan haka mace da soyayyarta basu isa su lugwigwita shi ba, basu isa kuma su sauya shi daga Kabir ɗinsa ba, abu ɗaya ne yanzu dunƙule a zuciyarsa, kuma ya kusa kora shi ya wuce da abinda yake ganin shine mafitarsa, nan kusa ba sai an kai ga nisa ba, a gobe ba jibi ba. abunda ya sani shine aure ya ƙunshi abubuwa guda uku; abota, aminci ko yarda, sannan so da ƙauna. tabbas waɗannan sune ginshiƙin aure, in har dasu aure zai yi inganci da ƙarko, anya ba zaiyi kuskure ba akan abinda ya gama yanke tabbatuwar faruwarsa a gobe?, idan shi akwai waɗannan abubuwa ukun to ita fa?. ya sa ni baya tsoron komai goben kawai yake jira, babban fatansa shine Allah ya kai kowa lokacin.
ya kai hannu ya ciro wayarsa dake ringing a aljihunsa, bai ɗaga ba saida ta kusa tsinkewa kana ya kai kunnensa yana yin sallama. Akila ta amsa masa yanayinta babu yabo babu fallasa. “are you coming to Abuja?”. “no Ummi”. “but why?”. “just like that”. “but you will attend the dinner party ok?”. bata jira cewarsa ba ta ƙara cewa,”Kabir i want to you to go to the dinner party please, don’t say you will not go”. to dama me ta ke tunanin zai hana shi zuwa?, zaije foresure, wata ƙila ma Dinner ɗin ta tashi ata mutane biyu, mutane ɗayan da aka shirya da mutane ɗayan da ba’a shiryawa ba.
Ya rufe murfin idonsa sannan yace da ita,”zamu zo insha’Allah Ummi”. “kai da wa?”. “mu biyu”. Akila na miƙawa maid wasu kaya tace,”are you sure Kabir?”. kaman yana gabanta ya gyaɗa ma ta kai,”ehh Ummi indai ba zai wuce nan kano ba zamu zo”. Akila ta sauke numfashi daga inda ta ke kafin tace masa,”ananne mana za ai, komai ai a masarautar bichi zamu yi tarukan bikinmu”.
baice da ita komai ba yay shiru yana sauraron bugun zuciyarsa dake harbawa da sauri-sauri. ta katse shirun nasa da faɗin,”Kabir jikina sai yake bani kaman zaren wata ƙaddarar zai gifta kamin ɗaurin auren nan”. nan ma baice komai ba yay shiru. ta ƙara cewa,”na kasa yardarwa kaina ba zaka mallaki Maryam ba. Kabir mai yasa ba zaka fito ka faɗawa su Baba abinda ke ranka ba?”. yay wani gajeren murmushi a saman leɓensa sannan yace,”zan iya faɗa musu hakanne kaɗai a sanda Ahmad yace ya fasa kuma baya son Maryam. amma muddin Ahmad na sonta ba zan taɓa iya buɗewa kowa zuciyata ba yaga abinda ke dangane da Maryam ba. Ummi hatta raina zan iya sadaukar da shi akan ƙannena balle kuma wata aba soyayyar mace. dan Allah ina so ki manta da na so ƴarki, haka kuma ki daina kawo faruwar wani abu a ranki da zai hana auren nan domin ina son farin cikin ɗan’uwana, ni na cire soyayyar Maryam a raina tuni, zan kuma tabbatar miki da hakan wata ƙila a gobe”.
Tai murmushi mai sauti sannan tace,”kaima kasan ba zan taɓa yarda da batunka na cewan ka daina son Maryam, duk wannan fiffizgewar da kake ƙarfin hali kawai kake, dakiya ce irin taka ta jaruman maza, amma yanayin maganarka kaɗai ya isa ya ƙaryata kalamanka, kuma kaman yanda na faɗa maka sam sam bana farin ciki da auren nan kamar yanda kaima baka farin ciki da shi”. “Ummi ya za’ai ki faɗi hakan. taya zanƙi farin ciki da auren ɗan’uwana, gaba ɗayanmu fa alkhairin auren nan muka nema, kullum cewa kike Allah ya bani ita idan har itace alkhairina, to tunda kika ga hakan ta kasance Allah ne zai mana sauyi mafi alkhairi tsakanin ni da ita”.
kuma yana gama maganar ɗiff yaji ta katse wayar. sai kawai ya girgiza kai, sannan kuma ya fara tafiya sannu a hankali har ya kai ga parlon Yagana, kuma yana shiga hayaniyar mutanen dake zazzaune a parlon anata hira ta shiga kansa, ta ke yaji wani ɗan ƙaramin ciwon kai na neman kama shi, saboda haka ko tsayawa cire takalmansa bai yi ba ya gaidasu a tsaitsaye, da yake duk ƴan’uwana sai suke ta masa tsiyar ƙaninsa zai yi aure ya barshi, shi dai murmushi kawai yay baice musu ƙala ba, har wata Yayar Malam ƴar wan Babansu tace da shi,”Allah Kabiru kaji mun faɗa maka tazarar aurenku ba zata wuce wuta guda ba, wannan ai sai ya zama hauka, so kake ka zama tuzuru…ni shi yasa sam ban so wannan karatun nasaran ba, gashi nan kun ɗauki aƙidarsu kuna amfani da ita, tsakani da Allah a tsarinmu mutanen ƙauye Ƴaƴanka nawa yanzu? kai ko kunya baka ji, Aminu yayi, ga Amadu zaiyi amma kai wai Yagana ma ce min ta ke ta karatunka kake bata aure ba, to naci uban bokon”. kansa a ƙasa yace da ita,”za’ayi Umma, ai lokaci ne”. daga faɗin haka ya wuce kai tsaye zuwa ɗakin Nawwaran, yana zuwa kuma ya tarar bata nan sai ƴan ƙunshin kayanta da jakar kayan a tsakiyar ɗakin, da alama tayi wanki ne tana haɗa kan kayan ko kuma ta fito dasu dan zaɓan wanda zata saka. jin baiji motsinta ba a ɗakin ya fito ya koma bedroom ɗin Yagana. tana ganinsa kuwa ta taso tana faɗin,”ɗan albarka ya akai?”. yana kanne idanu yace,”ranki ya daɗe babu komai, ganinki kawai nazo yi”. sai ta kaɗa kai kawai tana cewa,”ni kuwa kaga jiya gaba ɗaya banyi bacci me daɗi ba. ramar nan taka na bani tsoro Kabiru, duk yanda akai akwai abinda kasa a ranka yake damunka, dan Allah ka taimaka ka faɗa min, nasan ban isa na rabaka da ita ba amma zan maka adu’a Allah ya yaye maka koma menene”. ya wadata fuskarsa da murmushi a sanda idanuwansa suka hango masa Nawwara ta fito daga toilet ɗin Yagana riƙe da wani yaro, alama kuma ta nuna masa wanka taiwa yaron tunda gashi nan naɗe cikin zane, ita kuma hannunta da ƙafarta duka da ruwa, ya shafa fuskar Yagana yana faɗin,”Yagana ki kwantar da hankalinki babu abinda ke damuna, idan ma akwai to komai yazo ƙarshe insha’Allah”. ba hakan taso ba sai dai bata da yanda ta iya da shi, bata so ta takura masa sam. “to kaci abinci?”. yasa hannu yana shafo bayan wuyansa yayinda idanuwansa ke kan ƙafar Nawwara yana bin yatsun ƙafarta da kallo, yace da Yagana. “banci komai ba tukunna. na ɗan fita ne sai yanzu na dawo”. cikin dabara kuma sai yace da ita,”waccan yarinyar sam bata son tsafta, ana biki kowa na gyara jikinsa amma ita kalleta wani curkuɗe-curkuɗe”. ya ƙarasa maganar yana haɗawa da ƙaramin tsoki.
Yagana ta waiga ta dubi Nawwaran da yake magana akai sannan ta dawo gare shi da cewan,”wallah ba laifinta bane…aiki ne ya ma ta yawa bata zama, kaga ɗazu ma harta zauna za’a ma ta ƙunshin kuma wannan yaron sai yasa kuka, shi kuma uwar tazo ba lafiya shi yasa dole ta tashi”. a lokacin ji yay kaman ya haɗa uwar yaron da yaron ya yarfa masu zagi, sannan yaywa Uwar yaron kashedin karta ƙarasata rainon ɗanta tunda ba ita ta haife shi ba, kuma acikin kuɗin aikinta babu na raino, ba kuma raino aka ɗaukota yi ba.
lokaci guda ɓacin ransa ya ƙaru yana me cewa da Yagana. “jiya ma bata je makaranta ba yauma haka. ɗazu Principal ɗin nasu ya kirani ai…tazo ta sameni a ɗaki suyi magana da shi”. Yagana tace,”to Allah yasa su karɓi uzurinta, ni ban san hakan zai zama da matsala ba da ban hanata zuwa ba”. shi dai juyawa kawai yay yana daɗa faɗawa Yagana,”ta taho min da kayan abincina”.
Kwata-kwata Nawwara bata lura da shigowarsa ɗakin ba, sai lokacin da furucinsa na,”bata je makaranta ba”. ya shiga kunnenta. A lokacin ne ta ɗago kai ta gansa, idonta ya shiga cikin nasa, kuma haka kawai ƙwayar idonta ta haska da wani irin tsoro da fargabar da bata taɓa ji ba, bata san ya dawo ba sai cikin dare da ta farka taga kwalaben madarar waken suya acikin leda har guda uku, da kuma tufa guda shida, da bunch na ayaba, kuma a wannan lokacin yunwa ce ta tasheta, dan haka ta tashi Iya dan neman izininta akan taci, tunda babu damar ta fita yanzu neman abinci, tama san ba zata samu ba dan yanzu abinci baya saura a gidan.
kuma da Iyan ta tashi ta ke shaida ma ta tsarabar Kabir ce daya dawo, ta tsorata sosai da irin baccin da tai dan tun sha biyu na rana itace sai 11 da rabi na dare ta farka, baccin da zata ce bata taɓa yinsa ba tun girmanta, sai dai taji dadin yanayin jikinta sosai, wannan ciwon kan ya ɗauke gaba ɗaya, haka duk inda ke ma ta ciwo ajikinta ma ya saki, amma tayi mamakin baccinta sosai. kuma murɗawar da cikinta keyi yasa ta aje mamakin a gefe ta shiga cin tufar tana korawa da madarar waken suyan, tana sha kuma tana lumshe ido daɗinsa na ratswa har cikin kanta.
fatanta ɗaya ne a yanzu Allah yasa bai ganta ba, dan a yanda ta tsara sai lokacin dawowa daga makaranta yayi zata je ta gaishe shi, kuma jin yace ta kai masa abinci taji wani abu me kama da tsoro shi kaɗai ya dira a ƙirjinta. kallonsa ta ke har ya ɓace daga bakin ƙofar ɗakin sannan ta ɗauke kanta da sauri ta shiga shafawa Abbas mai ajiki, jikinta sai rawa yake kamar wacce taiwa sarki laifi, yanayin fuskarsa ta ke tunawa da yanayin furucinsa, da kuma kalmarsa na cewar zaiyi ma ta exams idan ya dawo, me zai faru idan ransa ya kai ga ɓaci yace ya zare hannunsa daga ɗawainiyar makarantarta?, zata iya ɗaukan wannan ɗanyen hukuncin?, tana ganin kamar ƙwallafa ran da tai akan karatun bokon zai iya ma ta illa a duk sanda akace yau karatun ya datse ma ta?, ya zama dole ma taje ta bashi haƙuri tun kamin zuciyarsa ta gama yanke hukunci.
dan haka da sauri ta ƙarasa shirya Abbas ta saɓe shi ta goya shi, daga yanda ta ke nishi zaka gane goyon yaron yaywa ƙirjinta nauyi, ta fita a ɗakin cikin hanzari tana jijjiga Abbas dan yay bacci. ba ta kai ga tsakiyar parlon ba kiran sunanta da Yagana tai ya tsayar da ƙafafunta a lokaci guda. “ga kayan abincin Kabiru can na haɗa, ki ɗauka ki kai masa ɗakinsa”. “tom Yagana”. sai kuma Yagana ta bita da kallo tare da jefa ma ta tambayar,”lafiyarki kuwa na ganki kamar a firgice?”. tai saurin girgiza kai da cewan,”a’a babu komai Yagana”. Yagana ta kaɗa kai kawai ta wuce ta barta, ita kuma ta nufi kitchen ɗin har tana tuntuɓe.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button