NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE


76 Kafe District, Asokoro, Abuja.
“i will definetly teach her a lesson, ni ba shashashar matan nan bace da zan bar ƙawa ta ƙulla alaƙar gaisawa da mijina ko saurayina. ni kika sa ni dan haka dani za ki zumunci, so Aisha Tayo tell your that stupid friend karta ƙara kiran Yaya ko da sunan menene ma, in ba haka ba kuma wallah zata ga ɗanyen hauka”. Shamsiyya Sani dake daga kan gadona a kwance ta bushe da dariya tana yunƙurawa zaune.
“wallah ke dai Maryam anyi masifaffiya, wannan wanne irin kishin jaraba ne. ance miki kiransa fa kawai tayi ta tambayeshi ke saboda tana ta kiran wayarki bata samu, amma kinzo kin ishi mutane da bambami”. naja tsaki na miƙe daga kan kujerar da na ke, na kalli Shamsiyya Sani na banka ma ta uwar harara kamin nasa kai na fice daga bedroom ɗin, ina jinta ta rakoni da dariyar da ta ƙara ƙular dani, dan dana dawo ciki sai munyi faɗa sosai da ita, to matsalar ina son Shamsiyya.
kai tsaye ɗakin Mami na nufa sai huci na ke, su huɗu na samu a ɗakin suna arraging gift ɗin da za’a bada a wurin dinner, baka jin komai sai ƙarar acn dake hurawa a ɗakin, dan da alama yanda suke magana a hankali lissafin kayan suke ba kuma sa so ya kubce masu. na nemi bakin gadon Mami na zauna ina aikin ɓata fuska kamar zan fashe. Mami ta waiwayo tana dubana tace,”Auta waya taɓan ke?”. na ƙara kumbura fuska ina bata amsar,”ba Yaya bane”. “to shi kuma Yayan da kansa yau. me ya maki hala?”. kuma tambayar tasa kawai na fashe da kuka. Ummi tai saurin aje kayan dake hannunta ta iso gareni. “ke da wa wai? sanin kanki ne bana ƙaunar kukanki”. nasa hannu na goge hawayena nace,”to Ummi ki yiwa Yaya magana kar ya ƙara picking call en kowacce shegiyar ƙawata da zata kira shi. kawai yaje ya biyewa wannan banzar Mabrukan sunata waya for morethan 3mints wai da sunan kwatance yake ma ta. ni nace ma ta dole sai tazo bikin nawa ne?, banma san a gidan uban da ta sami nunbernsa ba, dama waccan banzar Shamsiyyar ce ta jajuɓo min ita kuma Allah itama kiyi ma ta magana Ummi”. “to yanzu mene abin ɗaga hankali akai. address fa kawai ta tambaye shi ba wani abu ba”. sai na ƙara kumbura ina cewa,”bada address ne Ummi for more than 2minutes?, duniyar yake ma ta kwatance gaba ɗaya ko me?, to ni dai bana son ake jiye min muryan miji, just call him and talk to him in ba haka ba Allah ni mai iya zuwa wurin Daddy ne yanzu nace na fasa auren”. Mami tai guntun tsoki tace da Ummi,”du Allah leave this girl, go and meet Ibrahim outside naji kaman tsayawan motansa”. kuma sai na shiga shashsheƙar kuka ina faɗin,”ni nama fasa auren, dan ba zan auri me sauran maganar wata ba”. Anty Samiha(cousin ɗin su Mami) ta wurgo min harara da faɗin,”kin tashi kinje kin shirya ko saina jefo maki wannan plate ɗin…ki wuce kije ki shirya tun kamin azo tafiya kizo kina ɓatawa mutane rai, akanki Maryam ba zan ɗauki faɗan Bella ba kinji na faɗa maki”. ina ƙunƙuni nace,”ita wannan Bella ta cika iko, dole ne sai anje inda ta ke sannan zaai bikin, nima baga gidanmu ba ta bari ayi gidan ubana mana. mene haɗina da wani masarautar bichi, kaje ma duk wannan Jawad ɗin ya ɓata maka rai”. ina rufe baki Anty Iftihal ta wawuro pillow ta jefo min, nai saurin miƙewa ina dariya na kaucewa jifan. “yar ƙaniya mara kunya, Mahaifiyar tamu kike faɗawa haka saboda kin rainamu baki da ta ido a gabanmu”. Mami tace,”to ba Kakarta bace, haka zaku yi haƙuri, ni kar a takurawa Ƴata”. ina wata dariyar nace,”Allah kam wannan tsohuwan ta isheni, ko da yake kwana nawa ne ma ya rage ma ta Allah na tuba, ta tafi kowa ya huta da mulkinta”. Anty Samiha tayo inda nake da plate ɗin hannunta nai tsalle akan gadon nai wurin Mami na ruƙunƙumeta. Mami kuma ta kareni ta hanata dukana.
Anty iftihal tace,”Maryam kici gaba, rabon kisa nai adua ne a ɗaura aurenku ku biyu gobe”. na waro ido waje ina cewa,”ni da wa?”. tace,”ke da kishiyarki”. na taɓe baki nace,”Anty Iftihal baki da labarin nayi zarra a zuciyar Yaya ne ko”. kuma dan ta ƙunsa min saita taso da maganar ɗazu, nai saurin tashi na bar ɗakin ina faman zumɓure zumɓure na koma ɗakina.
“ke kuma gorilla you know very well bana ƙawance, da ma ke kika naye min, ƙawata ɗaya ce Basma my sister, so dan haka daga yau na yanke ƙawancen dake, ki tarkata komatsanki ki koma gidanku, bikina ko babu ke za’a yi shi ai dama bani na gayyatoki ba, gayyar soɗi kika zo kuma manzon Allah ma ya hanata”. abinda nace da Shamsiyya kenan a sanda na shiga ɗakin, amma da yake Shamsiyya ƴar iska ce saita ci gaba da dariya ƙasa-ƙasa sannan ta sauko akan gadon tazo ta rungumeni tana bani peck a kumatu.
“easy mana my sister, maida wuƙar kinji”. na ƙara ɓata rai fiye da ɗazu dan ma tasan da gaske nake maganata, kuma abinda ta raɗa min a kunne yasa na ƙyalƙyale da dariya na juyo ina wartar wayar hannunta nai kan gado. muka haɗe kai muna karanta posting ɗin dake cikin group en Matan Sirri dake whatsapp, Aisha Tayo tazo zata gani muka korata da cewar ita yarinya ce da sauranta tukunna, abin na manya ne bana yara irinsu ba. hakan kuma ya ƙular da Aisha ta bar mana wurin.
wayata ce ta shiga ƙara, kuma sanin mamallakin ringtone ɗin yasa na bar iya shegen da muke ni da Shamsiyya na maida hankalina kan wayar, na ɗaga da zummar caccake Yaya nai masa ruwan masifa, amma furucin farko da yay akaina yasa na sauko daga wannan saman mai nisan ta bala’in kishin dana hau, nima na shiga kwantar da murya kaman yanda tasa ta ke, muka shiga zuba zantukan love ɗinmu ni da shi, kuma a wannan lokacin gaba ɗayanmu ji muke kaman muyi fiffike mu tashi zuwa wata sama mai nisa, mu zauna a duniyar da zamu kasance mu biyu ne kacal acikinta.

Double Today, God’s Promise????…thanks for your patience, thanks for your time and support, keep voting and commenting please, love you all????????.

SIRRIN ƁOYE

By Oum Ramadhan✍????

haba! Kabiro ba Kabir ba????duk kun damemu da wani Kabir sai kace gwal???? yana fama da wani ƙaton kansa anan, mu muka ce yay dakon soyayyartata ko mu muka ce yay nauyin baki????….#teamAhmad whre are guyz kuzo mu raƙashe a filin dinner????????Maryam da Ahmad zasu tabbata abu guda, our dream has come true????????…
the whole page is dedicated to Ahmad’s team.

(47)
“me Kyauna kina irin zumuɗin da nake ne?”. na juya ƙwayar idona sama kamin na dawo na saukesu kan hannuna ina kallon ƙunshin da yayta santinsu ajiya, muryata tayi ƙasa kafin ta fito a sirance nace da shi,”me ka gani Yaya?”. daga inda yake naji saukar sautin murmushinsa, kuma na tabbatar kamin murmushin nasa sai daya shafo saman sumarsa wanda hakan ke ɗabi’arsa. “i heard that emotions in your voice, so tell me wanne irin shirin tarba kika min a daren gobe?”. ban iya bawa Yaya amsa ba nai saurin saka tafukan hannuna na rufe fuskata saboda kunya kaman ina gabansa. daga inda Ahmad yake ya saki wani ƙayataccen murmushi sannan yace,”hmm indai wannan kunyar ce daga gobe dai ne zan cire ta”. ban dai ce komai ɗin ba ya ɗora da,”ɗazun da safe before i hurt you who made you sad that you cried?”. tambayar ta ɗauke nishaɗin da nake ciki na turɓune fuska, murya a kumbure nace da shi,”ba Jawad ba ne”. na faɗa ina aikin harare kaman Jawad ɗin na gabana.
“me Kyauna wai Jawad sa’anki ne? please ban sanki da raina na gaba dake ba wannan ba halin autar Mami bane, ki bar kiransa da Jawad kai tsaye kinji…me yay maki dama?”. “ni to ina ruwana da shi, ai shine yake fara takalata dan haka ba zance masa Yaya ba Jawad sunansa”. nai maganar har ina dukan ƙafa kaman ƙanƙanuwan yarinya. “barni da shi zan faɗa masa karya ƙara taɓa min Matata, her tears are very expensive ya daina zama silar zubarsu, if not kuma zan mance mu inlaws ne na rama maki ko Swty nah?”. nai murmushin daya bayyanar da fararan haƙorana nace,”ai Yaya ko zakai inlaw da kowa karka yi da wannan, kirkinsa ragagge ne. ɗazun fa breakfast ena ya cinye kuma ya kama gashina yaja min da ƙarfi kawai dan nayi magana”. kuma a inda Ahmad ɗin ke zaune sai ya ɓata rai,”ki faɗa masa ke matar aure ce, kar ya ƙara taɓa maki gashi mijinki baya son wannan wasan cousins ɗin kinji ni ko…ko after aurenmu ban yarda idan kinje gida kun haɗu da wani ba ki biye masa da wannan shashancin banzan, ni i don’t take such kind of things as a joke, kin jini ko?”. nai saurin ɗaga masa kai,”naji Yaya and i will keep it insha’Allah”. sai kuma naji voice ɗinsa yayi low a sanda yake cewa,”me kyauna ko dai Jawad bai haƙura dake ba ne?, karfa ya zamana nayi shuka na gama ban ruwa someone else kuma yazo yaci amfanin gonar”. maganar tasa kuma ta haska min hoton abinda ya faru jiya a masarautar bichi da muka je. mahaifiyar Jawad Hajjah Nashwa, ana zazzaune a turakar Bella ta ke cewa,”ni fa har yanzu banga ta inda Maryam ta dace da auren wani bare ba, shi yasa har da ya rage saura kwana biyu ɗaurin aurenta ni da ɗana bamu cire rai da ita ba”. Anty Zaina tace,”hmm ai duk mai martaba ne da rashin yin dogon nazari har ya yanke wannan hukuncin, harma dasu Akilan ai. wai suna duba irin halaccin da mutanen sukai masu, ina wani batun tuna halacci for God sake a inda ake son yarinya ta tsira da mutuncinta…duk wannan rawar jikin da suka ga yaron nayi akanta wallah wataran sai sunyi dakacan inama basu bashi ita ba. domin wuyarta ta ɓata masa rai zai fanshe ta hanyar tuna ma ta wacece ita, wallahi wataran sai ya tuna ma ta da wannan tabon da yake manne ajikinta, amma tsakani da Allah idan ɗan’uwanta ta aura fa, akwai wanda zai fishi ganin ƙimarta da mutuncinta ne?, aiko wani yaji ya goranta ma ta sai iyaka inda ƙarfinsa ya ƙare”. kuma maganartata sai ta zama kamar ta fito da allura ne ta ɗinke bakunan kowa, dan babu wanda ya sake wata maganar. ni kuwa a wannan lokacin banda hawaye babu abinda nake, dakacen inama ba’a haifeni ba nake, fata nake dama ace mutuwa tazo ta ɗaukeni a yanzu ba sai anjima ba, tunda maganar auren nan ta kama babu abinda nake facing sai ƙalubalen daya shafi maganar asalina, hatta a dangin su Ya Ahmad ɗin ma akwai wadda tace min,”Maryam ki bar ganin zuri’arku kuna da dukiya da sarauta, kuma kema naji ance mahaifiyarki da mahaifinki sun mallaka maki kadarori da dukiyar da za’a iya saka ki a sahun farko na masu kuɗin ƙasarku, to ki sani da waɗannan kaɗai baki isa kifi Amadu ba, dan na lura kun siye mana shi ne da kuɗi ko kuma barazanar Yayanki zai iya korarshi daga aiki, banda haka babu ta inda kika dace da shi domin shi yafi ki da abu ɗayan da zai shafe duk wani abu da kuke gadara da shi, Maryam Ahmad ya fiki tsarkakken asali ki tuna da wannan, da tsarkakken asalinsa kaɗai duniya ma zata fi ganin nasa girma da komai ɗin da kuke tutiya da shi”.
a lokacin da Umma Sahura ta ke faɗa min waɗannan maganganun ji nai kaman naje na sami Ummi nace ma ta na fasa wannan auren, to amma kuma saina tuna farin cikin Ummina, ko ba komai ina so na sakawa Ummina da irin sadaukar da farin cikinta da tai akan ganin na rayu. na kai hannu na toshe kunnena dake min amsa kuwar wasu ƙananun maganganu da naji a sanda nasa ƙafata zan shiga ɗakin su Jamila naji ƴan’uwan Inna Zulai nayi, hawaye ne kawai ke sauko min, kuma a lokacin kawai sai zuciyata dani kaina muka tsinci kanmu a matuƙar son ganin Ya Kabir, a wannan yanayin da nake ciki wanda kaina ke daf da tarwatsewa babu hannun wanda nake so na jini, babu kusa da wanda nake so na jini sai Ya Kabir. to me yasa shima nake nemansa a wannan lokacin?, idan na gansa me zaiyi min?, ko dan dai na sami labarin cewar wata a dangin su Baba ta shegantani yasa ƙafarsa yay fatali da ita ya tattaketa?, na tambayi kaina yafi sau cikin masaki dalilin da yasa Kabir zai yiwa wadda ta ke ƙanwace wurin mahaifinsa haka? ya manta girman mace ne?, ban ankare ba kawai naji ƙafafuna na ɗauka suna tafiyar dani zuwa sashensa, kuma sai dana ɗora ƙafata akan steps na entrance shiga parlonsa sannan tunanina ya ankar dani inda nake neman kai kaina, wurin Kabir, wannan Kabir ɗin da a duniyarsa ta yanzu babu wadda yaƙi jini sama dani, karfa na manta ya tsaneni, shi da kansa ya furta min na rabu da shi, kenan da nazo nan ƙara na kawo masa ko me?, after all nasan da cewan a yanzu shi yafi kowa ƙyamatata, illegitimate ta ɓata kyakykyawar alaƙar dake tsakaninmu, shin na manta ne da cewar naiwa kaina alƙawarin ko a lahira ni da Kabir?, to ayanzu da nazo wurinsa dan huce takaici ai babu abinda zan samu fa ce wani baƙin cikin daya fi wanda kowa ke sani aciki, dan na tabbata Kabir zai iya wankeni da muggan kalamai akan ciwon shegantani dasu Mami sukai. “Yaya kin manta Ya Kabir ɗin baya nan”. maganar da Basma tayi kenan a bayana, kuma ba tare dana bari ta fuskanci halin da nake ciki ba na bar wurin da sassarfa, na fita daga gidan na hau motar haya na nufi airpot, wanda sai bayan naje can ɗin tukunna na kira Ummi nake faɗa ma ta.
tabbas zuciyata ta karanta min yafi sau adadin lissafi cewar Maryam ba za ki taɓa auren soyayya ba, balle har ki zama cikin farin ciki, saboda wannan ciwon har abada ba zai bar zuciyarki ba, dan haka asirinki alaikum ki auri Jawad kawai, shine wanda ko da ya goranta maki kansa ya gorantawa. bana son Jawad dan haka me yasa zan aure shi?, ai har gwara ma wannan mutumin da Ummi ta ban labari, shi naji ɗarsuwar sonsa a raina, kuma shi ko daya walaƙantani rantsuwar Allah ce zata ci shi, tunda ya rantsewa Ummi da Allah zai tsaya min, kuma zai gusar da dattin baƙin cikin shegiya daga zuciyata, haka zai goge tabon ciwon shegiya dake tare da ni, duk da nasan cewar wannan soki burutsin soyayya ne kawai, amma shima ba zai so samawa Ƴaƴansa uwa marar asali ba.
“zuwa yaushe zaku taho?”. maganar Ya Ahmad ta katse tunanina, cikin sanyin muryata nace da shi,”Daddy ake jira ya dawo, mu mun gama shiryawa”. “a jirgi ɗaya zaku taho?”. na ɗaga kai da faɗin,”ehh”. “to ki kula min da kanki kinji”. na amsa da,”insha’Allah, kaima ka kula min da kanka”. daga haka wayar tamu ta ƙare. kuma wayar da ban iya saukewa ba daga kunnena ba kenan, haka kawai hoton Jawad ke haskawa acikin kaina da idanuwana. sanda Mai Martaba(kakansu Mami) yace na bashi zoben azurfar hannuna, na maƙe kafaɗa nace da shi,”a’a wannan ba naka ba ne”. da ya tambayeni na wane saina kalla Jawad dake hakimce akan kujerar Mai martaban, fuskarsa da tsananin damuwa, kallonmu kawai yake ba tare daya saki fuskarsa ba, ina murmushi nace da Me Martaba,”wannan zoben daga hannuna sai hannun My Jawad”. nai maganar da sigar zolaya, kuma furucin nawa ya haifar da tasirin tsoro a gareni, dan cikin sauri ya waro ƙwayar idonsa da suka ƙanƙance ya saukesu akaina, kuma kamin ƙiftwar idona sai tsintarsa nayi agabana, ya damƙo hannuna yana matsawa yace,”dan Allah Maryam ƙara faɗa”. na cuno baki nace da shi,”me?”. ya rumtse ido ya juyar da kai sannan ya dawo da kallonsa kaina yace,”sunan da kika faɗawa Me Martaba kamin ya fita”. na karyar da kai na ɗan harare shi sannan nace,”au wai My Jawad?”. sai kawai naga ya ɗaga kansa sama ya cije leɓensa na ƙasa yana wani irin smiling, sannan ya sauke kan nasa yana cewa,”ashe duk pretending kike dama kina sona?”. na kanne ido nace da shi,”kawai dan nace My Jawad sai ka fassara shi da abinda yake zuciyarka. to dama ai dole na so ka tunda kai ɗan’uwana ne, kuma dan nace My Jawad har wani abune dama?”. “Jawad ɗinki fa kika ce”. na sake cewa,”to a matsayinka na Yayana kai ba nawa bane…kaga tsaya! na fahimci dai jingina kalmar My ga sunan mutum ta ƙunshi tarin ma’anonin da yawa, dan haka zan kiyaye gaba”. kuma irin kallon da yake min acikin ƙwayar idanuwansa yasa sauran maganata ta maƙale a maƙogwarona, cikin wani irin mood mai wuyar a fassara shi. sai kawai nai ƙasa da kaina na taka zan wuce ta kusa da shi sai naji ya riƙo hannuna ya dawo dani gabansa, cikin wata iriyar murya da ban taɓa jinsa da ita ba yace,”ina sonki Maryam, wallahi ina sonki, kuma burina ki zama abokiyar rayuwata na har abada, Maryam Jawad mai ƙaunarki ne, ya fara sonki tun a ranar daya fara ɗora idanunsa akanki cikin wannan tsiwar rashin kunyar ta ki, kawai nayi shiru ne a lokacin saboda kinyi yarinta da yawa, kin min ƙanƙanta, idan nace zanyi soyayya dake za ki dinƙa cin karo da abubuwan da suka fi ƙarfin kanki, please Baby doll kice ni za ki aura ba wancan Ahmad ɗin ba da bai ko iya soyayyar ba, kizo gareni na nuna maki soyayya da…”. ban bari ya ƙarasa ba kawai na ture shi daga matsoni jikinsa da yay na fice daga turakar mai martaban, ina jiyo shi yana fitar da wani makirin murmushi mai ƙarfin sauti. kuma ban ƙara ganinsa ba sai yau da safe a dining, wai saukarsa kenan daga ƙasar moroco ya biyo ta nan saboda yasan idan ya wuce ethiopia ba lallai ya sami damar zuwa bikin ba, shine kuma ya shigo a yunwace yana zuwa ya afkawa abincina da muke ci a plate ɗaya ni da Bro Almustapha. na kama ƙunƙuni ya fizgoni gabansa ya damƙe gashina wai bari ya yanke gashin da wani gaja can ya gani ya liƙewa, ai yasan komai, Ahmad ba sona yake ba haskena da gashina yake so, Bro Almustapha ya ƙawaceni na bishi da harara ina murguɗa masa baki nace,”oho dai ba zan dai ce ina sonka ba”.
nasa hannu na sha re hawayen dake sauko min cikin azama, tunawa da maganar Mami da nai a ranar da ta tsuguna min tana roƙon da girman Allah kar na kuma zubar da hawaye akan asalina, in har da gaske ne na yafe ma ta to karna ƙara kuka akan yanda aka haifeni, kuma na ɗaukar ma ta wannan alƙawarin. na zuro ƙafafuna ƙasa daga kan gadon, dai-dai shigowar Shamsiyya da suka fita tun a ɗazu, nai turus daga inda ta ke tana cewa,”kambu wai sai yanzu kuka gama wayar?”. ban amsata ba, nai ma ta harar wasa ina ɗaura towel ajikina. ta taɓe baki tana cewa,”in yayi haƙuri dai gobe za’a kai masa…kuma ke Allah kiyi sauri ki shirya dan ga Daddy can ya dawo, naga ma har driver ya fita kai kaya airpot”. na nufi hanyar toilet ina cewa da ita,”dan Allah ki ɗauko min underwear a ɗakin Mami”. “to”. sai kuma ta ƙara cewa,”dama baki taho da allon saukarki da certificate ba?”. (da yake cikin wata ukun da nai a qatar bayan larabcin da na koya har da alqur’ani muka sauke). “Mantawa nai Shamsiyya, kaina duk ya cunkushe amma zan kira Alhassan in zasu taho ya ɗauko min”. “to wannan gift ɗin da Madam Deborah ta baki na haɗa da shi acikin wannan ƙaramar trolly ɗin ko da za ki nema. tunda nasan kai tsaye gidanki za’a kai kayan, kuma zan iya mantawa ban maki bayanin inda na saka maki wasu abubuwan ba”. “to Shamsiyya sannu da ƙoƙari. kiyi sauri kema ki shirya kar Anty Samiha ta haɗa faɗan har dake…ina Aisha Tayo?”. tana saka wasu kaya cikin trolly ɗinta tace,”to ai kayan fa su Anty Iftihal ne suka tafi dasu, Aisha ta bisu. dagani sai ke sai Mami da Ummi muka rage. dan Daddy ma naga kaman tafiyarmu ba tare ba”. na buɗe ƙofar toilet ɗin ina cewa,”ƙila ko sai ya jira su Uncle Lucas sunzo, wannan bataliyar christian ɗin ba son zuwansu nake ba…ke nifa gaba ɗaya mantawa nake a danginmu akwai arna”. na faɗa da sigar mita da jin haushi, na bar Shamsiyya da dariya tana faɗin,”kuma kin san Ummi tace rigar da Granny Chioma ta baki za ki saka a dinner ba”. nako ce,”tabɗijam Allah tsaren dasa kayan arna wallah, ko mai zasu ce sai dai su faɗa”. daga haka na faɗa toilet na barta da ƙyalƙyala ƴar iskar dariyarta mai cin rai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button