SIRRIN ƁOYE COMPLETE

8:30pm.
more event center.
daga irin yanda kake ganin zuƙa-zuƙan motocin dake cike da harabar events ɗin har zuwa waje zaka san ehh fa lallai bikin na manya ne masu lokacinsu. sojoji da ƴan jarida zagaye da wurin, da yawa nada ga cikin hall ɗin zaune yayinda wasu kuma ke yanzu ne motocinsu ke parking wanda yawancinsu dangin amarya ne, alagaitar da ake busawa na shaida bikin na masu sarauta ne.
kuma a wannan lokacinne jiniya ta ƙaraɗe ko’ina, acikin wurin har daga can waje kan titi sakamakon motar Mahaifin amarya dake shigowa. a yayin da motar amarya ke shigowa daga baya, Major ya fito daga cikin motar cikin dakakkiyar shaddar magic milk colour me cijawa, sannan matarsa Aaliya ma ta fito cikin wani haɗaɗɗan less ɗinta itama milk colour, ta zagayo inda mijinta yake suka jera suka nufa cikin hall ɗin sojoji uku na ta ke masu baya. sai bayan shigarsu sannan Almustapha, Imam, Joseph da Alhassan wato yayyan amarya suma suka fito cikin shaddarsu irinta mahaifinsu da sukai anko gaba ɗayansu, suma sannu a hankali suka rankaya zuwa cikin hall ɗin.
Sauran Page ɗin zaizo anjima, inda nai typing ɗinne yayi yawan da baizo kai tsaye ta whatsapp ba.
Vote, Comment & Share.
SIRRIN ƁOYE
By Oum Ramadhan✍????
Happy Marriage Life Maryam Mukhtar Afafa.
(49)
a motar amarya da ango kuwa a kallo ɗaya za kaiwa jigwayen taron zaka san lallai ranar aure ta musamman ce ga kowa. shigar shadda ɗabi’ar Ahmad ce tun kan su zama wasu, kuma ƙoƙarinsa ne ɗinka babbar riga a duk lokacin da wani biki na abokinsa ya kama, amma a yau yanda kayan suka amshe shi yafi na kullum. kuma daga kallo ɗaya zaka gane cewa kuɗaɗe masu nauyi aka zuba wajen ɗinkin dake jikinsa, duba da ɗinkin ma baiyi kama da namu na ƙasar nigeria ba. askin kansa sai walƙiya da sheƙi yake ta ƙasan hular dake kafe a kansa, fuskarsa sai washewa ta ke da murmushi, Hakan ya saka kyawunsa ƙara fito da ɓoyayyan kyansa.
Amarya Maryam tayi bala’in kyau da haɗuwa sai ɗaukar ido takeyi. net less ɗin dake jikinta kalar shaddar angon nata ash, an ƙawata ɗinkinsa da wasu flowers da suka ƙara fito da kyan ɗinkin, sarƙa da ɗan ƙunnenta silver colour masu shegen tsada, haka pos da takalmin dake ƙafarta duk silver, lamarin dai ba’a cewa komai, dan tun lokacin da aka shirya Maryam ita da kanta tasan ta haɗu, sai dai bata san me yasa a wannan lokacin ba zuciyarta ke a raunane, zuciyarta da ruhinta na faɗa mata kamar wani abu zai gifta wanda ba lallai ta iya ɗaukarsa ba, sai Shamsiyya ce ma ta ƙarfafa ma ta gwiwarta da ada ta mutu tun dirarsu a bichi da sukai ido huɗu da Jawad yay ma ta wannan murmushin nasa da ƙarya ne tace baida kyau.
suka haɗa ido ita da angon nata suka sakarma junansu ƙayataccen murmushi sannan Ahmad ya fito ya zagayo zuwa tata ƙofar, ya miƙa ma ta hannu ta riƙe shi ta fito daga motar, A haka suka shiga cikin hall ɗin daya gaji da haɗuwa, anyi decoration ɗin wajen da silver colour, komai na wurin silver ne da kwalliyar ash ajiki, kuma komai a tsare babu wani hayaniya ko shirme, haske ta ko’ina tamkar rana, fitilu sai walwali suke suna ƙara ɗaukan ido da hankali, Kowa yana zaune a inda ya dace da shi. dan ɓangaren dangin mahaifinta daban kasancewar suke christians, kanta na ƙasa ta ke tana kallon wasu wuraren ta wutsiyar ido, zuciyarta da fuskarta na washewa da tarin farin cikin da ba zata iya musaltawa ba. wannan waƙar dake tashi a hankali na bin jijiyoyin jikinta suna motsata, har ta ƙara tsamke yatsunsu dake cikin na juna. abokan ango da ƙawayen amarya ne suka masu rakiya har mazauninsu inda ya dace kuma aka tanada domin su. bayan daidaituwar zamansu MC ya bada umarnin ai welcoming nasu nan wuri ya ɗauka da tafi rau-rau, daga nan kuma Bella ta fito cikin takun ƙasaita zuwa waje na musamman da aka aje royal chair saboda ita ta zauna ta shiga kwaroro adu’a, daga bisani kuma Granny Chioma wadda ta ke ƙanwar Granny ta fito tazo itama tayi kalar tasu adu’ar ta kiristan sannan ta koma ta zauna.
Shamsiyya Sani ita ta fito ta bada biography na amarya, kuma tunda ta fara gaban Maryam ɗin ke faɗuwa dan sai ta ke ganin kamar zata fito fili ta daɗa faɗawa duniya ita shegiya ce, sai dai har Shamsiyya ta gama wannan bayanin bata ji makamncin maganar hakan ba, da zamanta kuma Habib da yake aminin ango shima yazo yay biograph na ango. Ummi(Akila) itama tazo ta bayyanawa irin jin daɗi da farin cikin da take ciki da kuma muhimmancin wannan rana a gareta. sai bayan ta koma ta zauna ne sannan MC ya umarci amarya da ango su yanka cake ɗin da aka aje akan wani table, kuma dan rashin kunya ko da Ahmad ya yanko cake ɗin a bakinsa yasa shi sannan ya nufi bakin Maryam ɗin da shi, kunya kuma ta hanata amsa ayayin da ihu ya karaɗe wurin aka ɗauki tafi, sai da ƙyar ta iya buɗe baki ta amsa sannan itama ta ciro nata ta miƙa masa, sai dai maimakon tasa masa a baki kaman yanda ya buɗe saita shafe masa icing ɗin a kumatukansa gefe da gefe da kuma kan hancinsa, nan ma ihu ya kuma karaɗe wurin, ta miƙa hannu ta ranƙwafo da fuskarsa ta haɗe goshinsu da hancinsu, kuma kamar MC Rahineena tasan me zata yi ta ƙaraso ta saita speaker nan muryar Maryam ɗin ta fito a hankali cikin wani amon sauti me motsa zuciyar ɗa namiji tace,”i love you”.
aiko nan ta ke aka ƙara sakin ihu ana tafi, MC ma tai ihu tai ihu sannan ta sauya taken waƙar dake tashi zuwa wata waƙar me taken ‘Baby i Love You’ ta Tiffany Alvord, waƙar da ta kuma tashi da wurin, masoyan biyu suka ƙara shiga shauƙi, Ahmad yasa hannu a weast ɗinta ya janyota jikinsa suka shiga rawa a hankali. kuma a wannan lokacinne Daddy da Mami suka fito suna yi musu liƙi, Dad na watsa musu Doller Mami na watsa masu Qatari Riyal, kafin nan ma Ummi ta shigo cikin mutuwar jiki ta shiga watsa nata kuɗin itama, nan da nan kuma hasken camera ya fara shigarsu sound ɗin ƙyas ƙyas kawai kake ji na tashi. duk abinda Akila keyi tana yinsa ne kawai acikin rashin kuzari, tunda aka shigo wurin nan idanuwanta na kan taga ta ina Kabir zai ɓullo, kuma tana ta kiran wayarsa amma bai ɗaga ba, tasan dai yanzu aka fara dinner amma tana ganin kmar har a gama ba lallai ne yazo ba kaman yanda ya tabbatar ma ta da zaizo ɗin.
10:00am
a wannan dare wannan lokaci da kowa ke wurin dinner.
ƴan tsirarrun mutanene sukai saura a gidan, hakan yasa hayaniyar gidan ta ragu sosai ba kaman a ɗazu ba kamin su fita. basu dawo gidan ba sai bayan magrib, zaune ta ke a gabansa a yayinda shi kuma ke kan kujera, hannunsa riƙe yake da nata yay masa wata iriyar matsa, zafin dake ratsata har cikin kanta, kuma duk yanda ta kai ga mutsu-mutsu dan zare hannun yaƙi bata dama.
ba kuma sau ɗaya ba ko sau biyu ta faɗa masa,”Ya Kabir riƙon da zafi”. amma sam baima nuna yajita ba, sai dai a yanda ta lura so yake ya sauke zafin takaicin wani abu da yake ji a wannan riƙon, hakan yasa ta haƙura kawai tana jiran har sanda zai buɗe idanuwansa ya sauke akanta sannan ya fahimci irin nata zafin da taji a sanda yay ma ta wannan riƙon nasa, tukunna cikin tsawa ya umarceta da ta tashi ta bar masa ɗaki. a tsorace ta ke da shi sosai tunda suka dawo, koma tace tunda suka taho, dan lokacin daya je ɗaukota ba haka yake ba, tana iya tunawa sunyi waya shi da Ya Ahmad lafiya, yake masa zancen ya shigo kano ne amma yanzu zai dawo sai ya ƙaraso wurin dinner ɗin, kuma bayan gama wayar tasu ya kalleta da wannan ƙwayar idon tasa da wani yanayi da ta kasa fassarawa, yace da ita, “na ga gyaran gashin”. tana iyawa tunawa da yanda tasa hannunta akanta ta zame ɗankwalin duka, tana iya hango yanda ƙwayar idonsa ke kallon gashin daya sha gyara tarr babu ko ƙifce, a lokacin abinda yace ma ta shine,”Nawwara zan iya taɓawa?”. kuma kanta kawai tasan ta gyaɗa masa amma sai ya girgiza nasa yace,”ba yanzu ba”. sannan ya umarceta da ta mayar da ɗan kwali kafin nan yace ta nuna masa ƙunshin, ananne bai iya hana kansa ba saida ya kamo hannun ya shafa sannan ya faɗa ma ta irin kyan da yay, har yace “amma jan yafi kyau, sai ya ƙara fito da kyawun siraran yatsunki”. a wannan lokacin inda zata danganta yanayin da ta ke ciki da kalmar ruɗani, to tabbas ita kanta tasan da tayiwa kalmar rashin adalci, shi yasa ko kusa bata alaƙanta shi da hakan ba, laɓɓan bakinta dai sun furta masa kalmar,”na gode, na gode sose da kulawanka Ya Kabir, Allah ya biyaka da mafificin alkhairi”. kuma har furucin da tai ya haɗe da wani furucin da bata san sanda ta faɗe shi ba. “Ya Kabir dan Allah nima zanje wurin partyn”. tana kallon sanda ya gyaɗa kansa har sau biyu a lokacin, kafin ya buɗe baki yace da ita,”Za ki je”. daga wannan maganar kuma har suka dawo gida wata maganar bata ƙara haɗasu ba. saima da suka dawo ne ya sata a gaba taci abinci, sannan ya fita ya barta a ɗakin kamar ɗazu da safe yace tai wanka ta shirya cikin kayan daya bata a kwali, kuma sai bayan tasa kayanne wannan matar daya kira tayi ma ta kwalliya tai ma ta ta tafi, kwalliyar da bata san ta mecece ba, haka abubuwa dake ta wakana ta rasa da wanne irin tunani zata masa kuma ta rasa da me zata kira shi. abu ɗaya ta sa ni tunda aka gama kwalliyar ta kalli kanta a madubi, taga ta fita daga siffar waccan Nawwaran ta zama wata Nawwaran ta daban, shikenan tai azamar miƙewa daga kan kujerar da take zaune a gaban madubi, ta sandare a tsaye, irin sandarewa da duk wanda ya shigo ya ganta a wannan tsayuwar kawai zai hankaɗata ne ta ƙarasa faɗuwa, sannan idan gawar tata ta cancanci ai ma ta kuka ya kurma ihu mutane su shigo ya sanar musu ta mutu.
tunanin ya bar kanta a lokacin da Kabir ya shigo ɗakin ya ƙaraso gabanta sosai ya tsaya ya kamo hannunta a nasa, tasan wani tunanin ta tafi amma bata san ko tunanin mene ba, hakan yasa hatta riƙon da yay ma ta da tsayuwarsa bata san dasu ba. maganarsa kawai taji, wannan furucin daya haifarwa zuciyarta yin rawa hatta da gangar jikinta, kuma lokaci ɗaya komai na cikin kanta ya ɗauke, ta ɗauke ƙwayar idonta daga kallonsa ta tsaida su akansa, ba kallo ɗaya kawai tayi masa ba, sai data buɗe ido ta rufe sau uku tukunna ta gama shaida kayan dake jikinsa.
Shadda ce arniya ƴar ubanta aqua colour, taji wani azababban ɗinki da zaisa mai kallonsa kusan zaucewa, kalar shaddar kalar kayan dake jikinta ne, duk da bata san da wanna suna zata kira kayan ba, ta san ba les bane kuma ba material bane, doguwar riga ce itama kuma kamar ba ɗinkata akai ba.
kawai saita tsayar da tunanin dake neman shiga kanta ta natsu akan maganar da yay mata daya shigo, maganar da sai data gama shawagi a iska sannan ta shigo kunnenta da girgiza ƙafafuwanta kaman zata faɗi sai kuma maganar amsar da zata bayar ta riƙe ƙafafun nata.
“Nawwara idan naje gidanku nemawa wani aurenki a yanzu Babanki zai bayar? zai iya damƙa min aurenki Nawwara? ko kuma dole sai mun tura wanda yake uba agaremu tukunna?”. kuma kaman matsar bakinta yay a lokacin ta bashi amsarsa kai tsaye sanda hawaye ke biyo kuncinta. “Ya Kabir ai tuntuni Baba ya bada ni, ba wannan Baban da yake riƙona ba. Babana kamin ya mutu, kuma itama Mama kamin ta rasu ta ƙara shaidawa wannan Umman dake riƙona sun bada ni”. zata iya rantsewa taga ƙyallin wata wuta acikin ƙwayar idonsa a lokacin daya kalleta, kafin ya jefa mata tambayar,”banbance min Baban yanzu da wancan Baban, da kuma Umma da Mama”. a lokacin hannu tasa ta goge hawayen fuskarta da gudunsa ya ƙara yawa, sannan tace da shi,”iyayena sun rasu, inda nake zaune Ƙanwar Mamana ce ke riƙona”. a lokacin da yake kallonta taga tsananin tausayinta acikin ƙwayar idonsa ya haska, kuma shirunta yay daidai da saka hannunsa ya goge ma ta hawayen, sannan ya buɗi baki yay maganar da zata ce da ƙyar ta iya jinta. “waye suka baki?”. “wani ne Kabiru”. “aina yake?”. “nima ban sa ni ba, banma sanshi ba. Baba dai yace min saina shekara 18 tukunna zasu neme shi, hakan Babana ya bada wasiyya”.
zata iya cewa wannan furucin nata shine silar wannan muguwar damƙar da yay ma ta, dan shirunta ya haɗe ne da matse hannunta cikin nasa sosai, sannan ya janyota suka ƙarasa bakin kujera, shi ya zauna akan kujerar ita kuma ta duƙa a gabansa. kuma ayanzu in zata iya lissafi sama da wucewar minti ashirin kenan idonsa a rufe yake, haka wayarsa dake kan ƙafarsa tayi ringingin yafi sau goma bai ɗauka ba.
har tsawon wucewar yawan wasu daƙiƙu tukunna ta fara jin hannunsa ya saki daga riƙon nata, ta leƙa fuskarsa kamar yayi bacci ne, saboda haka ta zame hannun a hankali sannan ta fice daga ɗakin da sauri, burin kawai ta isa ɗakinta ba tare da kowa ya ganta ba, har ta wanke wannan kwalliyar ta cire kayan ta maida nata ta dawo asalin Nawwaranta ƴar ƙauye.
sannan ta samu wuri ta zauna ta hana ƙafafunta da hannunta rawa, tukunna ta saita kanta ga natsuwarta, bayan nan saita tashi ta hau aikin gida kamin a dawo daga wurin partyn.