NOVELSSIRRIN ƁOYE COMPLETE

SIRRIN ƁOYE COMPLETE

washe gari, ƙarfe tara da rabi na safe, cikin masarautar bichi, turakar Sarauniya Hauwa’u.
Net ɗin dake jikina wani farin net ne daya ji adon flowers pich clour ajiki, doguwar riga ce irin tamu ta larabawa da suke sawa ranar biki, an yafa min wani farin mayafi irin namu daga saman kaina, shima kamar rigar adon jikinsa da pich colour. bangles da zoben dake hannuna suma farare ne hakama yari da sarƙar. kwalliyar yau ta ɗauki fuskata fiye da ta jiya, sai dai yau ɗin fuskata fayau ta ke.
tunda na farka yau sam bana son yin magana, dan idan nai maganar muryar na fita ne kaman nayi kuka, tunda na wayi garin yau na tuna cewa yau ɗinne za’a ɗaura aurena shikenan wani kuka ya shimfiɗe a zuciyarta, jikina duk yay sanyi na zama kamar mara lapia. ina zaunene akan ƙasaitaccen gadon Ammi gefen haguna da damana an saka tum-tum kamar wata basarakiya, duka Ammi ce tai min wannan shirin, kuma sai bayan ta gama shiryani ne Hajjah Nashwa ta shigo tai min feshi da wani turare da ban taɓa jin ƙamshinsa ba, zan iya cewa dai naji irin yanayin ƙamshinsa a jikin mutum guda, wannan ƙwayan mutum ɗin da na cire shi a lissafin rayuwata.
na rasa faɗuwar gaban na menene duk da Shamsiyya Sani ta faɗa min haka amare ke tsintar kansu a wannan rana da ta ke me albarka da muhimmanci a wurinsu…amma ni nawa sai nake ganin kaman mummunan abune zai faru, ina zaune ne kawai dan babu yanda na iya, domin Hajjah Nashwa tace kar na motsa a wurin har sai an ɗaura aure tukunna, idan ango ya shigo shine za’a zo a fito dani. a yanzu da nake zaune muryar Yaya kawai nake sonji, so nake na kira shi ko sunana ne ya ambata wannan taraddadin dake liƙe dani ya samu ya barni.
na kulle idona sakamakon wani abu da naji ya daki allon ƙirjina ya girgiza a lokaci ɗaya, nai saurin saka hannu hannu na dafe ƙirjina ina jin wani irin baƙon yanayi a tare dani, irin yanayin da ban taɓa tsintar kaina aciki ba. daga waje na jiyo tashin algaitu da busar sarewa na tashi, saina ƙurawa ƙofar shigowa ido kaman ina jiran shigowar wani, kuma ɗora idon nawa akai yay daidai da shigowar Jakadiyar Ammi tana cewa,”Alhamdulillahi, Allah kasa albarka”. sai naga ta zube a gabana tana ci gaba da faɗin,”gaisheki ranki ya daɗe, a yau kuma daidai wannan lokaci kin shiga cikin sahun matan nan masu girma da darajara, martabarki ta ɗaga sama, Allah ya sanya alkhairi, ina tayaki murna”. kawai sai naji harbawar wani abu a zuciyata ya kuma wuce. sai na karkato kaɗan na kai dubana ga wayata ina duban agogo, lokaci bai ba, lokacin da akasa na ɗaurin auren bai cika ba, ɗaurin auren ƙarfe goma da rabi ne amma me ya dawo da shi ƙarfe tara da arba’in?. a yanzu dana gama kallon lokacin ba shi lokacin nake jiran gama lissafawa ba, ƙwayar idona na kansa ne da jiran shigowar kiran Yaya.
“Maryam an ɗaura”. na jiyo muryar Shamsiyya na cewa dani. na juyo na dubeta daga inda ta ke tsaye jikinta a sanyaye. ni da ita duk sai muka tsaya kallon juna, muka kasa yiwa juna magana, kowannenmu idonsa da gangar jikinsa na bayyanar da fargaba dake ɗauke da ita, sai itace naga tasa hannu ta goge ƙwallar dake shirin sakko ma ta, kamin ta ƙaraso ta rungumeni tana fashewa da kuka.
muryata na shaking nace,”kukan na menene?”. “ina tayaki murna”. “wai da gaske an ɗaura?”. ta ɗaga min kai alaman ehh kafin kuma nace,”amma…”. nai saurin tureta daga jikina nace,”amma me?”. “naji Ummi na cewa bada Ya…”. ban bari ta ƙarasa faɗin abinda take son cewa ba na tureta daga jikina a zafafe, na diro a saman gadon ina damƙe kafaɗunta, na shiga girgizata da ƙarfi ba tare da bakina ya iya furta wata kalma ba.
kuma shigowar Mamina ɗakin na sami amsar tambayata dana gagara yiwa Shamsiyya, abu ɗaya na sani shine, naji sanda Mami tace,”ina Jawad ɗin?”. amma bayan nan ban kuma sanin komai ba da kuma inda kaina ya tafi.

09:40.
a parlon ɗakin Ahmad ne da abokansa anata shirin tafiya wurin ɗaurin aure.
ango wanda tuni ya shirya yana karya hularsa yake cewa da Mubaraq,”ko ka shirya ko kuma wallah muka gama muyi tafiyarmu”. “kai dai angon zumuɗi ci gaba da shirinka kawai. ni ka ganni lokaci nayi miƙewa zanyi na bula Babbar rigata”. Habib yace da Ahmad,”duk kabi ka ishi mutane bayan da sauran lokaci”. bai tanka masu ba ya nemi wuri ya zauna tare da ɗaukan wayarsa, inda yaci karo da message ɗin Maryam wanda ya shigo tun ƙarfe shida, sam bai lura da saƙon ba sai yanzu, kuma kalaman dake ƙunshe acikin saƙon shi ya saukar da wani annuri da murmushi mai ƙarfin sauti lokaci ɗaya a saman fuskarsa, kuma a lokaci ɗayan daya fito ɗin sai ya ɗauke sakamakon furucin daya ji ta bayansa da muryar Baba Mujibu.
maganar da tasa shi hanzarin miƙewa ya juyo gare shi yana kallonsa da kyau, da irin tsananin tashin hankali da ruɗanin da ba zai musalta shi ba, haka zalika idan ya kira ysnayin da yake ciki yanzu da tashin hankali kaɗai to ya yaudari kansa.
ya sani Baba Mujibu uba yake a gare shi, kuma Baba Mujiba ba sa’ansa ba ne, kuma ba sa’an wasansa bane, hasalima basa wasa da shi, dan ba haka babu ta yanda za’ai ya kira wannan furucin nasa da zancen wasa, balle ya kira yanayin fuskarsa da wasa.
“Ahmad an ɗaura auren Maryam amma ba da kai ba, sakamakon genotype ɗinka da mahaifinta yaƙi yarda da shi”. maganar ta shiga kunnensa tarr kuma ya fahimci me Baba Mijibun ke cewa, amma kafin a warware masa komai abunda yake so ya sani dawa aka ɗaura auren?
“Jawad”. yaji kiran sunan ya fito daga bakin Kabir dake zaune kan kujera, amma sai dai sunan bai fito da amsar tambayar da yaywa kansa ba, shi magana yake yi a waya, kuma da alama da Jawad ɗin yake wayar.
sai ya maida kallonsa ga Baba Mujibu yace da shi,”Baba babu mahaluƙin daya isa ya hanani auren Maryam, babu shi. tabbas ko dawa aka ɗaura sai ya warware shi yanzun nan…batun irin Ƴaƴan da zamu haifa babu ruwan kowa da wannan”. sai ya zube akan kujera yana dafe kansa. “genotype”. wannan kalmar da ta haɗu da furucin Baba Mujibu ita ta haska akansa, me yasa tuntuni ba’ai zancen genotype ɗin ba sai a yanzu, sai da akazo kan gaɓar da ba’a isa ai masa abinda ake ganin mafita ce aka samu ba, abinda akasan ba zai ɗauka ba. abunda ya sani kawai bai san genotype ɗinsa ba, ya san dai lokacin da suka je seminer ibadan shi da Md da Almustapha dukansu anyi musu genotype, sai dai bai san sakamakon da result ɗin ya bayar ba kasancewar a jirgi akace zaa sako a biyo su da shi, kuma yasan Almustapha yace masa result ɗinka yazo hannuna amma bai bashi ba, to shin menene genotype ɗin nasa kenan?
“SS kai carrier ne Amadu”. maganar ta fito daga bakin Baba Mujibu kamar yasan tambayar dake ransa kenan, kamin yaji Baba Mujibun yaci gaba da cewa,”wannan dalilin yasa mahaifinta yace ba zai iya baka ƴarsa ba domin ƴaƴan da zaku haifa duka zasu zama carriers. shi kuma bai san yanda ƙaddara ta ke ba amma ba zaiso a jininsa a sami wani kuskure irin hakan ba, familynsu baa aure sai result ya zaman cikin biyun ɗaya, imma AA da AA, imma kuma AA da AS. wannan dalilin ne yasa aka maye gurbinka da ɗan’uwanka Kabir kasancewar shi da ita genotype ɗinsu ɗaya ne AA+AA”. ba shi kaɗai ba, hatta Kabir ɗin da bai san meke faruwa ba kawai yaji saukar maganar ne a yanzu, duka su biyun suka miƙe a zabure.
“Kabir”. Ahmad ɗin ya tambayi Baba Mujibun da tsantsar mamakin dake haskawa a fuskarsa. “Ni kuma Baba?”. shima Kabir ɗin ya sake tambaya da mamaki. “ƙwarai da kai aka ɗaura…kuma bance wani acikinku ya sake yi min wata tambayar ba, abinda Babanku yace da ni kawai shine kai Ahmad na sanar maka yanzu aure ba naka bane, kai kuma Kabir kayo shirin angwaye ku taho”.
Kabir ya ɗauke idonsa daga kan Baba Mujibu ya maida kan screen ɗin wayarsa dake ringing yana kallon sunan Ummi dake yawo akai. ya kai hannu ya ɗaga, ya ɗaga ne ba don komai sai dai ta cire shi daga wannan ruɗanin da Baba Mujibu yasa su. kuma furucin daya fito daga bakinta zuwa kunnensa kai tsaye shine,”Congratulations Dear, You are now the groom of Maryam, i mean you are now Maryam’s Husband”. bai sani ba ko ta kashe wayar, shi dai sauke wayar yay daga kunnensa kawai ya nufi bakin ƙofa, a wuri ɗaya kawai ƙafafunsa suke so su gansu, gaban Maryam, riƙe da ita a jikinsa, ya hana wannan hawayen da yasan dole zasu zuba daga idonta fitowa daga idon nata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button