SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Nasan Tambayoyinku duka suna kan taya akai hakan zai kasance bayan Almustapha ya shaidawa Maryam Ahmad AA ne kamarta, kuma taya akai ya faɗi result ba tare da sanin Ahmad ba?…findout in the next chapter????…
Plss Vote and Comment…God Bless You as you do????.
SIRRIN ƁOYE
By Oum Ramadhan✍????
Not Edited.⚠️
am quite beat up, a bit stressed…so ban iya yin editing you should manage with the errors da zaku ci karo.
(51)
washegari
02:00pm.
akan ƙafafuna nake acikin turakar mai martaba, kaina a ƙasa cikin hular alkyabbar da aka saka min white colour, tunda aka wayi garin yau naji cewar za’a kaini gidana, zanje inda zan fara wata sabuwar rayuwar da ta ke daban da irin wacce nai a baya, gidana, gidan aurena, shikenan jikina ya mutu gaba ɗaya, wani irin yanayi nake ji da bazan iya kimanta shi ba. a yanzu da nake a tsakiyar turakar mai martaba ina fuskantarsa shi da mahaifina, da Kakana na wajen Uwa daya sauka a daren jiya, sai Ammi da Bella da Ummina da Mamina, da Hajjah Nashwa da Shamsiyya duk suna zaune, kuka nake amma mara sauti, hawaye wani na bin wani saman fuskata, yana ɓata ƙwalliyar da aka ɗauki tsawon lokaci a safiyar yau ana min ita, kwalliyar da Ummina ta kasa rufe baki tana ta aukin yabawa, faɗa ta ke wai ai Kwalliyar Kabirunta ce, Kabirunta za’ayiwa dan haka Mai Kwalliyar ta baje duka basirarta yau, tayi kwalliyar irin yanda nake sheƙi kaman dafaffan ƙwan da aka ɓare, ni dai ko a lokacin murmushi ma ban iya ba, saboda acikin fargaba nake, faɗuwar gaban data riskeni tun a jiya dana fito daga wannan jikin daya rungumeni, na buɗe ido nai tozali da mutumin da tun a ƙamshinsa na gama shaida ko waye.
a yanzu da Mai Martaba sarkin bichi yay shiru, Bella ta kada baki itama ta kira sunana, nai shiru na kasa amsawa saboda ƙullutun dake maƙale a throat ɗina, cikin wannan muryartata dake fita da zallar izza ta ƙara kiran sunana. “Maryam amsa min za kiyi”. na buɗe baki na amsa kiran da muryata da ta gama disashewa da kuka. “Maryam Haƙuri, Haƙuri, zaman aure gaba ɗayansa haƙuri ne, Maryam haƙuri shine jigon zaman aure, sai da haƙuri aurenki zaiyi lasting Maryam. dan haka Maryam idan ba ki sanshi ba to ki nemo shi duk inda yake ki kamo shi, ki ƙanƙame shi, irin ƙanƙamar da ba zai taɓa suɓuce miki ba…haƙuri ba wani abu ne mai wahala ba, mutanene kawai ke ɗaukansa a matsayin kaya, amma muddin mutum ya riƙe haƙuri to tabbas darajarsa hauhawa za ta dinga yi, domin shi haƙuri arziƙi ne babba Allah ya nufe ka da samunsa, dan ba kowa Allah ke bawa ba sai kaɗan daga cikin bayinsa, da haƙuri da tawakkali haka suke”. Hajjah Nashwa ta shiga maganar Bella da cewa,”to ai rayuwarma ita kanta haƙuri ce”. Bella ta gyaɗa kai,”to dai…dan haka ni iyaka abinda zan daɗa jaddada maki kenan, dan tun jiya kike shan nasihohi a gidan nan”. Ammi da naji shigowarta babu jima tace,”Maryam tun jiya nake ce miki ki zama mace ta gari, kuma ko kullu yaumin zanke zuwa gidanki ba zan daina faɗa miki wannan kalmar ba…Mace ta gari Maryam bata fallasa sirrin rayuwar aurenta ga kowa ba, ki zama mai riƙe sirrin gidanki, ina kuma tunasar dake akan yin biyayya ga mijinki dan samun rahamar Allah acikin rayuwar duniya da Lahira, ki zama mai gaggawa wajen cika umarnin mijinki, ki zama mai kiyaye dukkan abinda zai ɓatawa mijinki, ki zama mace ta garin da idan mijinki ya kalleki zaiji farinciki ya lulluɓe shi…tun jiya na gama faɗa miki macen da ake kira da mace ta gari, Allah ya baku zaman lapia”. Ummina ma ta fara magana da irin muryar dake shaida rauni na zuciya tana cewa da ni,”Daughter nah dan Allah karki zama mace mai halin maza a gidanki kinji, namiji baya son wannan, abunda nake nufi kar ya zamana baki iya kisisina ba, ya zamana kin iya dabara, da kuma shagwaɓa ba, da kwalliya, da soyayya mai rikita kwanya, Daughter da iyaka waɗannan ma za ki mallake zuciyar mijinki…Allah yay miki albarka kinji”. sauraronsu nake tare da saƙa abubuwa da yawa araina, tun jiya zuwa yau komai sai dai ace Maryam ki zamarwa mijinki kaza ko kiyi masa kaza, to shin ni bani da hakki akansa ne da ba zaace yay min duk abubuwan da nake so? ko kuma ni banda abubuwan da nake so? ko kuma shima za’a faɗa masa nasa kamar yanda ake faɗa min?…nai shiru ina ci gaba da sauraron faɗan Dad daya amshe shima, faɗa yake min sosai tare da wasu nasihohin da suka sanya ƙafafuna wani irin sanyi, ni dai wannan aure ji nake kaman nace na fasa, dan har yanzu ma ni ban gama sanin me zuciyata ke ciki ba ga me da Kabirun da aka laliƙa min. nayi mamakin kaina ajiya, nayi mamakin kaina sose dana kasa fesar masa da kalaman rashin kunya da masifar dana tattaro zanyi masa a lokacin dana buɗi ido na gansa…abunda ya faru a lokacin na iya ƙarfin halin saka ƙwayar idona a tasa tarr babu ko ƙifce, sai dai abubuwa biyu dana hasko acikin idanun nasa suka hanani aiwatar da abunda nai niyya, wannan kwarjinin nasa, da kuma ƙyallin wani abu dana kasa tantance menene, kawai dai nasan ya zama silar mutuwar jikina gaba ɗaya. da ƙyar na iya kai hannuna dana dunƙule na kai masa duka a kafaɗa, sai kuma na fashe da wani irin kuka da ban taɓa yin irinsa ba, sai ya saki murmushi yana riƙe ɗaya hannun dana kuma kai masa duka dalilin ganin yana wani munafikin murmushi…yasa hannunsa a haɓata yana tambayata menene, saina ture shi ina ƙara sautin kukana, ina ƙara kumbura sai aukin huci nake, na kuma buɗi baki zan amayar masa da abunda ke dunƙule a ƙirjina cikin ƙarajin bala’i, amma sai naji muryata na fitowa cikin sanyi kuma a hankali. “da wacce manufar ka aureni Kabir, wanne irin shiri kai na ganin ka ƙuntatawa rayuwata da har kasan yanda kayi ka rabani da masoyina na gaskiya…to wallah bari ma kaji ta kowacce tsiya da bala’i sai ka rabu dani, sai ka sakeni yanzu bada jimawa ba dan ba zan taɓa zama da kai ba, bana sonka kuma ba zan taɓa sonka ba, dan Allah ka faɗa musu ka sakeni naje na Auri Ya Ahmad ɗina me so na da ƙauna tsakani da Allah bada wata manufa ta cutarwa ba”. na ɗago da ƙwayar idona da tun fara maganata ta ke akan cinyoyinsa, na kalle shi hawaye naci gaba da sauko min, a wannan lokacin ƙwayar idonsa ta kaɗa tayi jajir, haka kuma ya sauya zuwa wani launin halitta na daban. saina ƙara saka kuka ina kaiwa duk ilahirin jikinsa duka ina faɗin,”Kabir ka sakeni, ka sakeni dan Allah, ba zan iya zama da igiyoyin aurenka a kaina ba, duk abunda kaje ka faɗawa Ummina ƙarya kake yi, kalamai ne na zallar yaudara…”. muguwar matsar da yaywa tsintsiyar hannuna ita tasa nai shiru, sai shashsheƙar kuka da nake ina son ƙwacewa, cikin wani amon sauti yace da ni. “ni ne nake ƙarya Maryam? nine mayaudarin?”. na jijjiga masa da ƙara tabbatar masa sannan nace,”ai zancena gaskiya, saboda baka so na…”. kuma ban iya ƙarasa faɗin abinda zance ba wani sabon kukan yaci ƙarfina, nai shiru ina jin wani ƙunci da suya a ƙasan zuciyata. sai ya janyoni jikinsa y haɗe fuskarmu wuri guda, iskar bakinsa ta sauka ajikina a lokacin da furucinsa ya fito da faɗin,”waya ce maki bana sonki Maryam, waya faɗa miki hakan? menene hujjarki na gasgata cewar bana sonki? me zan miki da ki tabbar da duk zancen dana faɗawa Ummi babu ƙarya acikinsu?”. “ai baka so na da gaske”. “shine ai nake so ki amsa min waɗancan tambayoyin”. “ba kana ƙyamatata bane saboda ni shegiya ce, shi yasa ka tsaneni baka ko son yi min magana, bayan bani nace a haifeni ta hanyar zina ba”. sai kawai naji ya galla min wani mintsini a gadon bayana da yasa na miƙe zaune a gigice ina shafa wurin, kuma kan nai yunƙurin furta wani abun yace. “naji fiye da wannan zafin a zuciyata, a waccan ranar da kika baɗawa idonki toka, kika yi watsi da tarbiyar da Gwaggo tai miki, ki ɗauki huɗubar shaiɗan kika dinga faɗawa Ummi son ranki, da gaske tun a wannan ranar na fara jin haushinki, irin haushi sosai ɗin nan da yafi ƙarfin a musalta shi, shine dalilin ɗauke miki wutar da nai Maryam…amma ko kusa ba saboda wannan negative tunanin naki ba ne”. saina saka hannu akan idona ina cewa,”to bana nemi yafiyarta ba kuma ta yafe min…ashe kai ba mutumin da zai iya yin afuwa ne ga wanda yay masa laifi ba, bacin ko Allah ma muna masa laifi kuma mu roƙe shi ya yafe mana”. “ba haka bane Mairo tah, Mairoro wannan sauya mikin da nai ya haɗe ne da tsananin kishinki da nake”. Kuma kukan da nake sai naji ya ɗauke kamar ɗaukewar ruwan sama, na tsaya cak ina kallonsa, ina kallon yanda yake murza tafin hannuna a hankali. kamin na ɗago da ƙwayar idona ina kallon Kabir ɗin da idanuwansa ke ɗauke da full of love, kamar ba wannan Ya Kabir ɗin dana sa ni ba. sai naji wani sanyi na mamaye min ilahirin jikina, ba zan iya cewa ga halin da nake ciki ba a wannan lokacin, amma dai kalamai sunyi ƙaranci a bakina da zan iya jefa masa tambayar dake raina. “Mairoro duk maganganun dana faɗawa Ummi gaskiya ne, kuma duk abunda Ummi ta faɗa miki gaskiya ne…Mairon Gwaggo Allah da gaske nake miki, ni ɗan Adam ne ina yin kuskure amma Allah bana ƙarya kuma kema kanki shida ce”. ya faɗa a sanda ya saka hannu ya sake kwanto dani jikinsa, yaja hancina yana faɗin,”Mairo tah kin san kuwa tun yaushe zuciyar ɗan Kabiruwa ke ɗawainiya dake”. ba tambayata yay ba amma sai naji na girgiza masa kai. “ba sai na tsaya ina miki dogon bayani ba, amma what i want you to know shine na fara sonki tun ba ki san kanki ba, kuma ƙaunar da nake miki mai zafi ce Mairon Kabiru, Allah ma yasan da wannan…kuma na jingine hakan a rainane saboda babu damar na furta miki hakan ke kin san dalili…kuma lokacin daya kamata na furta miki cewar kece zaɓin raina cikin rashin tsammani sai na tsinci soyayyarki a tare da Ahmad, kin san irin halin dana shiga a wannan time ɗin? ba ki sa ni ba, amma ke na ɗorawa laifin, dan gani nake kamar ke kika bashi damar hakan…Allah ya sa ni a wannan lokacin da ban janye miki ba wallahi i might loose control zafin kishinki yasa na aikata abunda ba shikenan, abunda zanzo ina dana sani… lokacin da kika amince masa Allah ɗaya yasan da irin ciwon da kika haifarwa zuciyata, kin gani kin kuma lura da hakan amma tunaninki ya hanaki gane mawuyacin halin da kike neman jefa bawan Allah…ba zan iya ganin kina soyayya da wani ba, ba zan iya ganin kina soyayya da ɗan’uwana ba, shi yasa na bar muku ƙasar kuci karanku babu babbaka…Abdurrahim ne kaɗai zai iya baki labarin mawuyacin halin dana shiga a sanda naji an tsaida ranar aurenku, shi da Ummi ne kaɗai zasu iya ba ki labarin yanda soyayyarki ke nuƙurƙusar zuciyata, duk wannan farin ciki da kuma walwalar dana daina duk akan sonki ne…kuma sai dana gama cire rai da samun ki, nayi giving up da komai na rayuwa ta, sai Allah ya dubeni, ya dubi haƙurina, alokacin da banyi zato ba banyi tsammani ba Allah ya bani ke, ya bani ke matsayin matata…Alhamdulillahi Rabil Alamin, amma babu ƙarya wannan me bakin tsiwar ta wahalar da ni, kuma nima saina rama, Allah ya kaimu akai min ke ɗakina, zaki sha mamaki, za ki sha mamakin sonki daya shekara goma sha daskare a zuciyar Kabir”. Allah ma ya sa ni a lokacin ba zan iya cewa komai ba, kuma ba zan iya aiwatar da komai ba, illa bige hannunsa da nai dake neman shiga cikin rigata. murmushinsa mai sauti ya fito haɗe da cewar,”wai duk wannan dogon bayanin da na maki ba ki yarda da ni ba?”. cikin sauri na ɗaga masa kai. sai ya lakuce min kumatu da faɗin,”to karki yarda ɗin, ni dai ai nasan haka ne, kuma tunda Ummi ma shaida ce karki taɓa yarda ɗin…ni ai ba yaronki ba ne da zan tsaya kina min yanda kika so, dan ki yarda da ni ma har saina miki kalar tausayi, to sannu Yagana”. nace da shi,”in ka iya tsara Ummina ni dai ba zaka tsarani ba…dama ai nasan duk ƙarya ne kake gillawa…”. sai ya ɗalle min baki yana cewa,”wai ni sa’anki ne da kike faɗin ina miki ƙarya? ko kin manta wane ni, nine fa wannan Ya Kabir ɗin naki”. sai naja hancina a lokacin da nake jin wani mixed feeling nace,”kai ɗin, ina ruwana da kai”. “zanyi maganinki ne soon, ranar da aka kai min ke ba za ki samu damar faɗa min haka ba”. sai kawai nasa kukan shagwaɓar da ban san lokacin daya zo ba ina faɗin. “ai dama nasan kasheni za kai shi yasa ka aureni, kuma ni ka sakeni ko kuma duk abinda nai maka a gidan kai ka siya da kuɗinka, ai na faɗa maka bana sonka, dan haka ka rabu da ni tunda kaima ba sona kake ba”. na lura wannan kalmar tawa na saka shi a wani yanayin, a jikina kawai na tsinci ɓacin ransa, a irin matse hannuna da yay na tsinci irin ɗacin da yake ji idan nace baya so na, so kawai sai na shiga raira kukana a hankali, shi kuma ya miƙe ƙafafunsa yana jingina da gadon, sannan ya sakani tsakiyar ƙafafunsa ya lafar dani a ƙirjinsa, kuma lokaci kaɗan naji bacci ya fara fizgata, kamin baccin ya ɗaukeni gaba ɗaya ina jin time ɗin da yake waya da wanda ya kira da suna Abdurrahim yana faɗa masa shi dama ai ba ma’abocin yin abunda mutane suka raja’a akai bane, indai dinner ce zai yi gagarumar dinner amma a gidansa, cikin ɗakinsa, kan gadonsa, a cikin wannan daren. kuma baccin da nai ban san da lokacin daya tafi ba, na farka naga babu shi, kuma naji na farka da mararin son ganinsa a lokacin, har nake tambayar Shamsiyya wama ya maidani kan gado, ta harareni tace sai na kira shi wanda nai baccin ajikinsa na tambaye shi. tana ƙara ce min wai wallah wannan Ya Kabir ɗin bashi da kunya, in banyi hankali da shi ba sai ya dinga bada ni a gaban mutane, nace me yayi tace wai na tambayi Ummi ta ban labarin a yanda tazo ta samemu, kuma ganin nata baisa ya daina abunda yake ba, tayi magana kuma yace wai ai Maryam ɗinsa ce. tsaki kawai nayi a lokacin na sakko daga kan gadon na shiga banɗaki da tunani kala kala acikin ƙoƙon kaina.
Anty Iftihal da ta shigo yanzu bayan ta gaida su Abi da Daddy tace,”zamu iya tafiya?”. Bella tace,”babu damuwa”. Daddy ya miƙe yana faɗin,”dawa zamu tafi?”. Ummi ta miƙe tana cewa,”ai ƙafata ƙafar ƴata”. Ummi ta duƙo ta ɗagoni na tsaya akan dugadugaina, sandararriyar ƙafata na neman ta watsar dani na zube. na hangi Mamina na goge ƙwalla sai kawai na ƙwace daga hannu Ummi na faɗa jikinta ina fashewa da wani irin matsanancin kuka mai taɓa zuciyar duk mai saurare.
Mami ta rungumeni tsam ajikinta itama tana kukan. muryarta na fita da amon kuka tana faɗin. “Allah ya sani bana son rabuwa dake, amma babu yanda zanyi aure ibada ne kuma sunnar ma’aiki wadda ta zamar mana dole mu rayata…Auta Allah yayi miki albarka kinji, Allah ya albarkaci dukkan rayuwarki, Allah ya haskaka rayuwarki, Allah ya tsare gaba da bayanki, Allah ya rabaki da sharrin maƙiya mahassada, Allah ya ɗoraki akansu, yasa ki zama mai rinjaye akansu…Ya Rahmanu yasa ki zama haske a cikin gidan aurenki, Ya Maliku yayi riƙo da hannayenki wajen kyautata zaman ibadarki, Allah yasa ki zama sanyin idaniyar mijinki, Ya Hayyu ya qayyum yasa masa tausayinki a zuciyar mijinki, ya ƙara ninka soyayyarki a zuciyarsa, Allah kuma ya bashi ikon sauke nauyin duk wani hakki naki, ubangiji yasa ku zamewa junanku inuwar salama har ranar alƙiyama, Allah ya baku zuri’a ɗayyiba, Allah yasawa zuri’ar da zaku samar albarka, Allah ya tashi rayukanku cikin rahamar ibadarku a lokacin da zaku koma gare shi…Dan Allah Auta ina roƙonki kiyi riƙo da dukkan tarin nasihohin da aka miki, karki watsi dasu dan bana so ki koka ko kaɗan, yin watsi dssu dsi-dai yake da yin bankwanan farin ciki a rayuwar aurenki…ina sonki, ina sonki sosai ƴata…duk wani abu da kike so ki kirani ki sanar dani kinji ɗiyar albarka, zanyi kewarki sosai”. tai maganar ƙarshe tana sa hannu ta goge min hawayena alhalin nata basu tsaya daga zuba ba. cikin kuka nace,”Mamina na fasa auren kinji”. sai kawai ta kauda kai gefe dan kar naga sabon hawayenta da zai zuba. da ƙyar da siɗin goshi aka rabani da jikinta. Daddy ya kama hannuna na dama, Ummi ta riƙe na hagu suka fita dani daga ɗakin, kuma muna isowa haraba busar algaitu ta fara tashi, ana kwararo adu’a da kirari wa ni dasu Daddy.
gidansu Ya Kabir aka kaini, sai da aka kaini wurin Baba Daddy ya damƙa masa amanata, shima yay min kalar nasa nasihohin da faɗan sannan aka tafi dani ɓangaren Yagana, suka ƙara damƙa ni a hannunta, Yagana tana ƙwallar nuna farinciki take cewa ta amsa, fatanta Allah ya tayasu ruƙo…daga nan kuma su Daddy suka mana sallama suka wuce gida inda suka barni da sharɓar kuka.
bayan tafiyarsu babu jimawa Mama Siddiqa wacce ta ke ƙanwa wurin Mamansu Ya Kabir ta shigo ɗakin, ta umarceni dana tashi nayi sallar la’asar, na miƙe jiki a sanyaye da tarin kunya na shiga bayi nai alwala sannan na fito na gabatar da sallah.
dasu Adawiyya muka zauna a ɗakin munata hira, duk dana kasa sakewa jina nake kamar ban taɓa rayuwar cikin gidan ba, kamar baƙuwa nake, Sadiya ma sai tsokanata take wai duk gulma ce ni dai bancewa kowa acikinsu ƙala ba. so nake ma duk su tashi su fita na samu sakewa da Basma tah.
har magriba muna tare dasu, kuma kowa da kalar tsiyarsa da yake min, Yagana ta kawo min wayarta da Shamsiyya ta kira. na amsa ina sallama, ban san lokacin da kukan da nake ta riƙewa tun ɗazu ba ya sauko min. tace dani,”ke dilla ni ba kuka na kira ki min ba”. nace da ita,”Shamsiyya dan Allah kizo mu zauna tare kamin gobe mu tafi”. sai ta saki wata munafukar dariya tana tambayata wai aina zan kwana yau ɗin da nake cewa tazo. kamar ina gabanta na saki harara nace,”ban sa ni ba, banza ƴar iska kawai”. ta kuma ƙyalƙyalewa da dariya tana cewa,”naji dai…ke dama Ummi ce tace na faɗa miki ɗazu tai mantuwa da humrarki a jakarta, amma Ya Kabir ɗin yazo ɗazu ta bashi ya taho maki da ita, idan yazo saiki amsa”. na turo baki nace,”amma dai ba cewa zanyi ya ban ba ko?”. tace,”oho ke kika sa ni”. duk sai naji ta ɗebe min kewar dake damuna, mun jima muna hira tana ta zuba min iskancinta dake cinta, wanda na rasa aina Shamsiyya ta san irin waɗannan abubuwan, kuma da nayi magana sai tace,”oho ni dai faɗa miki nake in baki iya abu kaza da kaza ba kina ji kina gani wata can zatai miki wuff da shi kuma babu yanda kika iya”.