SIRRIN ƁOYE COMPLETE

****ɓangaren Kabir kuwa yana fita direct ya zagaya ta ƙofar baya, inda ɗakinsu Nawwara yake, dama ƙofa biyu ce, ko ka shiga ta kitchen ɗin Yagana ko kabi ta baya wajen flowers ɗin gidan. da farko daya shiga ɗakin bai lura da kowa ba dan ko sallama baiyi ba bare a amsa yasan da wani a ɗakin, sai iya ce da ta kula da shi ta yunƙura ta miƙe daga kwancen da ta ke tana gaishe shi. ya shafi bayan wuyansa ya amsa sannan ya tambayeta ina Nawwara. tace da shi ta shiga wanka ne da yake yau ta wuni da zazzaɓi sai yanzu taji daɗin jikinta. sai ya juya ya fice bayan yace da ita,”iya idan ta fito kice ta sameni a ɗakina”. ta amsa mishi da “to” tana ƙara yi masa Allah sanya alkhairi dan jiya gaba ɗaya ma bata ganshi a gidan ba.
bai yi minti goma sha biyar da shiga ɗakinsa ba yaji knocking ƙofa. ya ƙarasa saka button na rigarsa sannan ya bata izinin shigowa ɗakin. ta sanyo siraran ƙafafunta ciki bakinta ɗauke da sallama kanta a masa tana wasa da yatsunta. “Ya Kabir gani”. ba tare daya dubeta ba yace,”na ganki, idan kin gaji da tsayuwar kya iya hawa kaina ki tsaya”. daga yanda yay maganar tasan ransa babu daɗi, dan da sauri ta ɗago ta dube shi, kamin nan ta durƙushe a wurin tana fuskantarsa. “ɗauki wannan abincin ki cinye”. ta buɗi baki zata yi magana ya dakatr da ita da cewa,”bana son musu”. saboda haka ba dan taso ba ta shiga cin abincin, bata wani ci da yawa ba tace da shi ta ƙoshi. sannan ya ƙara cewa da ita,”ɓalli wannan maganin kisha”. ta kalli inda wani ƙaramin box yake ta ɗauki maganin daya ma ta nuni da shi ta ɓalla tasha, ya kuma taso yace ta miƙe yay ma ta allura, lokaci guda ta shiga matse hawayen dake shirin sakko ma ta, tana cewa da shi. “Ya Kabir na warke wallah”. baibi ta kanta ba ya janyota jikinsa ya tsira ma ta allurar a sanda ta ke ruƙunƙume shi tana sakin ɗan ƙaramin kuka. sanin cewar ba iya lailayawa zatai ba ya lailaya ma ta sosai kan muryarsa ta fito a sanyaye yana cewa. “kin gama haɗa kayan naki?”. ta ɗaga masa kai alamar ehhh. ya sauke numfashi sannan yace,”ɗazu naje wurin Baba”. sai tai saurin zamewa daga jikinsa tana ɗago kai da ido ta kalle shi. shima ya kalli ƙwayar idonta da ta ciko da hawaye tukunna yace,”bana son kuka”. ya faɗa yana saka hannu ya goge ma ta su da suka sami damar sakkowa.
“munyi magamar Kabirun da kika ce an ba ki, yace sun neme shi tunda jimawa kuma an tabbatar musu daya rasu, basu faɗa miki ba ne kawai…ashe almajirin Ummanki ne da yay musu halacci, kuma shi ya nuna yana biɗar aurenki tun kina tsumma…na faɗawa Baba cewar zan tafi dake can ƙasar da nake zaune za ki ci gaba da karatunki acan…na basu haƙuri na ƙurewar lokaci da aka samu wurin sanar dasu, amma nayi musu alƙawarin ko shekara ba zakiyi ba zan kawo ki kona sa akawoki ki gaida su…hakan yayi miki?”. ta ɗaga kai tana cewa,”na gode da kulawanka gareni”. sai taji yasa yatsunsa ya ɗago haɓarta yana cewa. “idan waɗan nan ƙafafun basu daina rawa ba idan suka ganni next time ɓallasu zanyi, kin san dai ba zasu yi wuyar ɓallewa ba yanda suke kamar sillan karan nan”. bata san lokacin da murmushi ya suɓuce ma ta ba. “kin dai gama shirya komai ko?”. “ehh na gama”. “karki haɗa da tsaffin kayanki, na saya maki wasu suna wurin tailor sai zamu wuce zamu tsaya a amsa”. “tom na gode, Allah ya ƙara arziƙi”. “amin amin..kije ki kwanta Allah ya ƙara sauƙi…amma ki tabbata ban fito ina cewa Nawwara fito ba, ko kuma ki fito kina ce min kinyi mantuwa”. “insha’Allahu”. daga haka tayi masa sallama ta fita yana bin bayan da kallo, zuciyarsa na lissafa masa wani abu da yake ganin da wuya ya yiwu…amma yana roƙon Allah yasa hakan ta kasance.
Plsss Comment and vote.
SIRRIN ƁOYE
By Oum Ramadhan✍????
Abbas Haruna, Hassan ATK, Muhammad Kareem, Hussain ATK, N Yareema, Mu’az, Sdeen, Mukhtar, Muhammad Kamji…Ina maku fatan nasara a rayuwaku tare da adu’an alkhairin Allah da kariyarsa su isa gareku a duk inda kuke.
(53)
6:00am.
akan dining muke, ina fuskantar Ya Kabir shima yana fuskantata, sai Nawwara dake daga ɗayan kujeran ta gefensa. na cika nayi fam da abunda ban san menene ba, wannan ƙullutun abun daya tsaya min a wuya na rasa na menene, dan ta ƙarfi da yaji nake kora shi da abincin da nake ci amma yaƙi wucewa.
“wai ke ba ki gama ci ba ne?”. bakina ya furta maganar da ban shirya ma ta ba ga Nawwaran da idona ke kanta tun ɗazu ina banka ma ta wata uwar harara, ban san dalilin daya sa nake jin mugun haushinta ba haka kawai babu gaira babu dalili, kuma jin haushin daga jiya ne zuwa yau amma lokacin da nake gidan kaman Basma na ɗauketa. kuma sai naga ta tsorata da maganar da nai ma ta har cokalin hannunta yana neman ya faɗi. “dilla Malama dake fa nake kina wani muzurai kaman baƙar munafuka”. na ƙara yin maganar a tsawace, sai kawai Ya Kabir ya tsaya yana kallona kamin ya maida kallonsa gareta. sannan saboda wani rainin wayo nasa daya kusa sawa na kaiwa bakinsa duka yake tambayana wai dawa nake. naja dogon tsaki na miƙe ina tura kujera baya zan wuce ɗaki ya riƙo hannuna. “wai ke meke damunki ne…na faɗa miki fa ba zamu tafi haka ba ki ci abinci ba…kin san tafiyan awa nawa zamuyi? ko bana ce miki mun fasa zuwa abujan ba ne direct Ethiopia zamu wuce”. na warce hannuna a nasa ina binsa da harara kamin nace,”idan damuwa kayi da cina ka biyoni da abincin ɗaki…amma ba zan zauna da mijina muna cin abinci tare da ƴar aiki ba, for what reason?…kuma ma indai da gaske da ita zamu tafi sai dai ku tafi tare amma ba zan bika ba, ai na faɗa maka bana son ƴar aiki”.
“to dama waya ce miki aiki zata je miki? itama nata personal zaman ne zai kaita”. ban tanka masa ba nai wucewata ɗakin Yagana ina sakin kuka mara dalili, kawai dai nasan idan nayi zan huce takaicin wani abu dake ƙasan raina.
bayan kusan minti ashirin sai gashi ya shigo ɗakin Yagana, ya zauna bakin gadon kusa dani, na juyar da kaina daga kusa da shi na koma fuskantar Yagana dake juye min wani rubutu a jarka da Baba ya bayar ɗazu da asuba. “to gashi nan Babanku yace karta yi wasa da sha…har kaima zaku ke sha tare kaji ko”. y amsata da cewan,”tom Yagana an gode Allah bada lada”. bayan ta kamalla komai ta taso ta kamo hannunsa da nawa ta haɗe wuri guda tana cewa da ni,”Mairo kike ko Maryam, ni dai dan girman Allah ki kula da marayan nan, bashi da uwa dan haka na roƙeki ki zama uwa a gare shi, tun yana ƙarami ya rasa mahaifiyarsa dan haka dan Allah ki zame masa farinciki uwa ga ɗanta…tun bayan mutuwar mahaifiyarsa ni na zame masa uwa, ban taɓa bari yayi wani nisa da ni ba sai da karatunsa ya riske shi, yanzu gashi yayi aure kuma ba lallai wannan tafiyar me nisan zsmani da zaiyi ba mu ƙara samun damar ganawa ido da ido”. sai kawai naji wani mugu mugun tausayinsa ya kamani, na kalle shi ta gefen ido naga yana goge ƙwallar idonsa. sannan na kalla Yagana da itama ke goge hawaye, sai naji nima hawayen na sakko min, muryana a hankali nace da ita. “insha’Allahu Yagana”. sai tai murmushi tana ƙara damƙe hannunwanmu anata tana cewa,”kin min alƙawari”. na ɗaga ma ta kai da cewan,”ehh Yagana nayi miki, haƙiƙa babu abinda za ki nema daga gareni na kasa yi miki shi, dn kinyi min komai a rayuwata… kuma insha’Allahu duk tsayin lokacin da zamu ɗauka acan zamu dawo mu sameki da rai da lafiyarki, da yardar Allah sai kin ɗauki ɗan jikanki da hannunki”. a tare suka kalle ni, tana shafo fuskata da cewan,”Allah ya amsa min Mairo…au ashe fa Baba Kabiru ya hanani faɗin wannan sunan”. sai na ɗan cukule fuska a sanda muka haɗa ido da shi nace ma ta.”to amma Yagana shima kiyi masa faɗa kar yake min ƙiriniyansa, dan baya jin maganata”. nai maganar a kumbure. tace da shi,”Baba Kabiru kaji dai…ka rage ƙiriniyanka tunda Mama Mairo tace bata so, in ba haka ba kuma duk hukuncin da tayi maka babu ruwana ko ƙara karka kawo min”. yana murmushi yace,”za’ai yanda kika ce Hajiya Yagana”. ta gyaɗa kai sau biyu sannan tace,”Maryam amanar Allah ce tsakaninmu Kabir, na ba ka amanarta, dan darajan Allah ka kula da ita, Kabiru idan ka cutar da ita kai da Allah”. “insha’Allahu Yagana ba zan ba ki kunya ba”. ta saki hannunmu tana miƙewa da cewar,”bari naga iya ko ta gama dakan waccen daddawar da kace a haɗa maku da ita…sai daren jiya Zannira ta aiko da ita”. ta ƙarasa ficewa a sanda ta ke ƙara cewa,”ita Nawwaran ta gama shiryawa to?”. shi kuma yana bata amsa da ehh.
ya jinginar da gefen fuskarsa atawa yana cewa da ni,”Ya ya dai?”. bance masa komai ba sai ɗan murguɗa baki da nai. sannan ya miƙar dani tsaye, ya ɗauko vail ɗin abayata ya min rolling, sannan ya kama hannuna muka fice daga ɗakin, inata cewa ya cikani amma yaƙi har sanda muka ƙarasa bakin mota, kuny kuma duk ta dabaibayeni ganin Baba a tsaye a wurin, amma shi ko a jikinsa, ganin Ya Ahmad ma yasa sai ƙara wani janyoni jikinsa yake.
munsha adu’a daga ƴan gidanmu, har sai da suka sakani kuka sosai, musamman Inna Zulai da duk ta kashe min jiki a sanda ta ke ƙara roƙata yafiyar abunda tayi min. babu kowa a gidan sai Ya Ahmad, kuma shi ya kaimu airpot, muna tafe suna hirarsu da Ya Kabir ni dai da Nawwara munyi tsit. sai da muka hau jirgi tukunna shima ya bar airpot ɗin, sanda zamu hau jirgi kuwa raina ya washe da dariyar Nawwara dana ci, wadda ta kasa hawa jirgin saida Yaya ya riƙeta tukunna.
kuma tunda muka hau jirgin haka kawai sai nake jin wani mixed feeling da duk ya ɗauke wani ɓacin rai nawa, naji na wanzu a wani sabon yanayi da jin daɗi, dan haka kawai naji zuciyata na washewa, Ya Kabir na min hira wadda duk akan company ɗin da yake son buɗewa ne, wata maganar na tsoma baki wata kuma nabi zanen ginin company ɗin da kallo ba tare da nace komai ba…tashinmu da awa biyu naji idona ya fara rufewa, dan jiya ban wani samu nai bacci sosai ba saboda miskilanci, na zura hannuna ana Yaya na kwantar da kaina a kafaɗarsa daga nan kuma bacci ya ɗaukeni, ban farka ba sai buɗe ido nai na ganni akan gado, wai ashe time ɗin da muka sauka baya so ya tasheni sai kawai ya ɗaukoni a hannu.
time ɗin dana tashi baya gidan, sai Nawwara ce ke faɗa min wai sun fita shi da wani abokinsa, inaji kuma nasan Abdurrahim ne…da yamma muna zaune ni da Nawwara a living room muna kallo muka ji ƙaran bell, Nawwara ta tashi taje ta amsa abincin da Yaya yay taking mana order…kallo nake amma gaba ɗaya hankalina na kan Mamina, tun jiya rabona da jin muryarta, gashi wayana na hannun Ummi inaga mantawa tai bata bani ba.
na shiga bedroom ɗin da yake mallakinsa ne wanda na tashi a bacci ɗazu. akan dressing mirrow na kalla ƙaraman wayansa a ijje, nasan kuma baya aje dan ya manta bane sai dan saboda yasan zan buƙatata. fuskatata ta washe da murmushin jin daɗi a lokaci ɗaya, na ɗauko wayan na zauna bakin gado tare da danna kiran wayan Mamina.
“Autana”. na amsa a sanda ta kira sunan nawa, ina jin kaman na shiga ta cikin wayan na rungumeta. “ya akai? kun sauka?”. kaman ina gabanta na ɗaga kaina alaman ehh tare da cewan,”ehh Mamina tun ɗazu ma”. “to masha’Allahu…babu dai wata matsala ko?”. “ehh Mami babu…sai dai Mamina ina kewanki”. tai murmushi mai sautin daya motsa min zuciya sannan tace,”tun yanzu Autana, jiya ne fa kawai”. na turo baki a shagwaɓe ina cewa,”Mami kawai fa kike cewa, to Allah Mami jina nake kaman na shekara dubu bana tare dake”. mun ɗau tsawon lokaci muna waya da ita kamin muyi sallama. daga nan kuma na kira Ummi, ita kuma ta maida ni kaman wata ƙawarta sai tsiya ta ke min, har nake ce ma ta aini na daina kulata, tace ai dama tuni tasan da cewan na daina yinta, itama mun daɗe muna waya daga ƙarshe take ce min,”Maryam nasha gaya miki Kabir na matuƙar sonki, dan haka yau sai kinyi haƙuri da yanda zaizo miki, ta salon da za ki sameshi…dan haka kiyi dauriya da juriya, dan wannan ruɓaɓɓan son daya ɗauki tsawon shekaru masu yawa yana yi miki yau zai nuna miki shi, kuma kema ki zage ki zama mace ta gari Maryam, a wannn daren ki faranta masa rai, kuma dan Allah a daren yau ba sai an kai da nisa ba ina so ki ɗauko min jika, tunda ni dai ba zan yarda ƴata na haihuwa nima ina haihuwa ba, zan dai ta rainon jikokina…yauwa sannan idan kin shirya wannan humrar dana bashi ya kawo miki, ki tabbata kin shafe duk ilahirin jikinki da ita, dan so nake kiyi zarra a zuciyar Kabiruna, ya zamana babu mace mai iya kamoki a zuciyarsa da idanuwansa”. Maganartata ta saka naji kunya, mukai sallama da ita cike da kewarta ina daɗa jin ƙaunarta acikin raina. na kira Alhassan ma muka sha hira da shi, yana ce min wai idan zaizo nai masa girki sama da kala goma dan so yake ya tabbatar da ingancin girkina, nai dariya nace da shi aikuwa sai dai kar yaci. Shamsiyya Sani ma mukai waya da ita, tana ta tsokanata da wannan iskancin nata, ƙarshe dai ba dan mun gama hiran ba na kashe wayan, dan idan na biye ma ta saita lalata min kunnena. na kira Yagana na sanar ma ta mun sauka, sai da zamuyi sallama nake tsokanarta yace ko ta fara lissafin, tai dariya sosai tana ce min shaƙiya tare da cewar zatai kewarmu.
bayan sallar isha’i nayi shirina cikin wasu riga da skirt na english wears da Yaya ya lodasu akwatu huɗu, kaman me shirin buɗe kanti. kayan sun min kyau sosai dan har saida na bawa Nawwara tayi min hotuna, na duƙa ina rufe drowern dana maida humra sai jin mutum nai ya kwantar da kansa a bayana ya kuma ziro hannayensa saman cikina, cikin wata iriyar muryar da ban taɓa jinsa da ita ba yace,”i love you Maryam”. sai naji ƙafafuna sun shiga ruwa, na ɗago ina juyowa gare shi tare da dafa kafaɗunsa gudun karna faɗi, sai ya rungumeni tsam irin rungumar da ta banbanta da sauran da yake min, dan har ƙashin bayana sai daya amsa. a hankali naji yana shinshinar wuyana kamin muryarsa ta fito can ƙasa yayin da yake murza hannuna cikin nasa,”Maryam wannan ƙamshin fa?…wane irin turare ne kika saka haka?, wayyooo Maryam kinji yanda yake motsa min jikina kuwa”. kaɗan ya rage yawun dake zarcewa zuwa maƙogorona ya haɗo tare da zuciyata su fito, na motsa jikina ina so na zame daga jikinsa sai ya kuma ƙanƙameni, fuskarsa kwance kan kafaɗata yay shiru kaman wanda yay bacci, sai numfashinsa dake fita a hankali a hankali…shirun da naji yay yawa yasa nace,”Yaya”. har ga Allah a irin yanda yay shirun nan da yanayin yanda yake sauke nunfashi zaka rantse kace ko bacci yake, amma da mamakina sai naji ya amsa da,”ummm”. sai nai shiru ban ƙara cewa komai, kafin na ƙara jinsa ya kira sunana.”Maryam”. a hankali na amsa da,”na’am”. “ina sonki, ina sonki da yawa, dan Allah kinji…”. kamar wani ƙaramin yaro me neman wani abu a yanda yay roƙon, naga kaman yana neman faɗuwa saina ruƙo shi ina tambayansa,”dan Allah me?”. baice komai ba har tsawon sakanni uku, kamin nan ya ɗago da kansa ya haɗani da jikin bango, sannan ya duƙo da kansa saitin bakina a ƙoƙarinsa na ya haɗe bakinmu wuri ɗaya, haɗuwar leɓensa da nawa yay daidai da bugawar wayarsa, sai kawai yaja wani dogon tsaki na ƙorafi ya saki ƙuguna da yake riƙe da shi sannan ya ɗaga wayan yana magana murya a ɗage. “Abdurrahim kana da matsala”. ban san me Abdurrahim ɗin yace da shi ba naji ya ƙara jan dogon tsaki kamin yace,”su jirani ina zuwa”. ya kashe wayan yana zurawa a aljihu, ya tsareni da idanuwansa da suka fara ƙanƙacewa tare da ce min kiyi alwala ki jirani yanzu zan dawo, just some minutes kinji. gyaɗa masa kai kawai nayi, kuma sai dana ɗauki tsawon wasu sakanni tsaye a wurin kamin na iya jan ƙafafuna cikin mutuwar jiki na shiga toilet nai alwala na dawo bakin gado ina zaman jiran dawowarsa.
inata jera hamma ya dawo ɗakin yana aje leda a bakin drower, tukunna ya shiga yayo alwala ya dawo yace na tashi muyi sallah, munyi sallah raka’a biyu kaman yanda sunnah ta koyar, sai kuma naji ya shiga koro adu’oi wanda zan iya cewa adu’ace dake cikin kansa gaba ɗaya yake yinta, yayinda ni kuma nake binsa da amin har lokacin da shima yace amin muka shafa tare. ya juyo ya fuskanceni ya dafa kaina yay min adu’ar da sunnah ta koyar sannan ya matso kusa da ni, yasa duka hannayensa ya tallafo gefen fuskata yace. “doll”. da wannan muryar tasa mai zurfi ya kirani da sunan da shi yasani saurin ɗago ido na dube shi, ƙwayar idonmu ta sarƙe wuri guda. “kina jin yunwa?”. na girgiza kaina acikin tafukan hannunsa alamar a’a, bai janye hannunsa ba ya ƙara cewa. “amma ai yought zai iya shiga wannan shamulallan cikin ko?”. ya faɗa with full of smile on his face. shiru nai bance komai ba, dan ni gaba ɗaya gani nake kaman ba Ya Kabir ba, kuma komai ganinsa nake kaman a mafarki. sai ya ƙara cewa,”wannan yought din ba irin sauran bane, kisha ko kaɗanne kinji”. ya faɗa a sanda yake buɗe roban yought ɗin yana kawowa bakina, na buɗe baki na sha ba wani da yawa can ba. sai naji ya matso da fuskarsa jikin tawa sose sannan ya haɗe bakina da nasa, na saurin runtse a sanda naji yana zuba min yought ɗin dake bakinsa cikin nawa, wanda sai bayan da ɗanɗanonsa ya hau kan harshena tukunna na tantance yought ɗinne amma da farko nai zaton ko yawunsa ne. lokaci ɗaya naji wani abu ya tsarga tun daga tafin ƙafata har tsakiyar kaina, wani abu dake neman hargitsa min ƙwaƙwalwa…kuma take duk wata jijiya ta jikina ta shiga juyawa, a sanda naji tafukan hannunsa masu sanyi a saman cikina, yatsansa ɗaya cikin cibiyata, sai nai saurin riƙe yatsan na sa zuciyata na wani irin bugu acikin kunnena.
a zaune nake amma jina nake kamar zan faɗi, kuma kawai sai naji kansa a saman ƙirjina, muryarsa na fitowa da wani irin sauti da yasa idanuwana rufewa lokaci guda, muryarsa ta fito a hankali kaman mai jin bacci da cewan, “Doll ba zan miki komai ba sai da yardarki”. sai nai ƙarfin halin ɗago da kansa da ɗan saurin kuzarin da nake da shi, a wannan lokaci idanuwansa sun ƙanƙance sun sauya launi, yanayinsa na komawa kaman wanda yay maye. sai naga yay wani irin murmushi yana cewa, “Doll ko na haƙura mu wuce wannan part ɗin?”. sai kawai na tsinci kaina da saurin girgiza masa akai alaman a’a ina mai miƙa hannayena na riƙo kansa sosai na haɗa goshinmu wuri ɗaya. sannan muryata ta fito a hankali da kiran sunansa wanda zan iya cewa ya amsa minne da ƙyar, kafin nai shiru na gaza cewa komai dan ban san me zance da shi ba, ni dai na kira sunan nasa ne kawai, sai naji yana cewa da ni.
“Doll ba ki bani amsa ba, mu tsallake wannan part ɗinne? ba zan miki dole ba, ba zan miki komai ba har sai kin yarda da ni, zan iya haƙuri insha’Allah”. yay maganar da yanayi na ban tausayi, sai na ƙara kamo kansa muryata a hankali nace,”a’a Yaya, karmu wuce, indai wannan part ɗinne kar mu tsallake shi…na yarda da kai, Allah Yaya na gama yarda da kai thousand percent”. sai kawai naji ya saki wata nauyayyar ajiyar zuciya yana motsa yatsansa babba acikin kunnena tare da yin hamdala ga Allah.
“Yaya nima wannan jaririyar zuciyar dake dashe a ƙijina tana sonka tana ƙaunarka, Yaya zan zauna da kai muddin rayuwata…zan zame maka baiwa a komai, dan kaine muradina, kaine walwalata, kaine farin cikina, kaine annashuwata…Yaya duniya kanta shaida ce da cewar kai kafi cancanta da ka zama abokin rayuwata, kayi min halacci, kana da ƙima da daraja a wajena fiye da tunaninka….Yaya kaine, only you, only you nake so ka zama uban ƴaƴana”. yaja wani numfashi a sanda nai shiru yace,”nima haka Doll”. kuma daga hakan bai jira komai ba ya haɗe laɓɓana da nasa a hankali, kuma a hankali cikin wani salo nasa na daban shi kaɗai, salon daya sakani damƙe hannayensa saboda yanda nake jina tamkar ana jana zuwa sama, kuma a wannan lokacin ji nake dama mu tashi zuwa wata duniyar da ta ke tamu mu biyu kacal…tsawon wasu daƙiƙu muna haka kamin ya janye daga jikina ya kamoni mu miƙe tsaye a tare, har wannan lokacin ban buɗe idanuna ba, a rufe suke tun sanda ya haɗe laɓɓanmu, bakinsa a kunnena naji ya zura harshensa ciki, yay wani irin zuƙa aciki daya sa numfashina ya shiga kakkatsewa sannan dukkan jikina kuma ya ɗauki rawa. akan ƙafafunsa nake tafiya har sanda muka iso bakin gado yasa hannu ya kashe light, ɗakin ya gauraye da wani irin duhu da acikinsa babu abinda nake ji sai numfashinsa.
jikina kuma ya hau ɓari a sanda naji yana ɓalle min buttons ɗin rigata, kuma sannu a hankali bakinsa ya sauka akan ƙirjina tsakiyar breast ɗina, a hankali yake kissing wurin tasirinsa na bin kowacce jijiya ta jikina, kuma kawai sai naji yana bin kunnena da wasu irin kalamai, wasu kalamai da saƙonni da a lokaci guda sukai kacakaca da dukkan lissafina da tunanina.
duk wani rawar jikinsa da kakkarwarsa sai naga ina nema na fishi, nema nake na fishi zaƙuwa da zalama, ban san lokacin da muka hau gado ba, ban lokacin daya rufemu da bargo mai ɗumi ba, ban san lokacin da duhun ɗakin ya daɗa bayyana ba, haka ban lokacin da labule ya ɗaga wata lumsashshiyar iska ta shigo ɗakin ta gauraye shi ba. abunda kawai na sa ni, a wannan gadon, cikin wannan ɗumin bargon, cikin wannan duhun mai haɗe da ni’imtacciyar iska, da ƙyar Yaya ya iya gamsar dani, shikenan tushen wata sabuwar rayuwa ta wanzu a tsakaninmu, muka tabbata abu guda, sunanmu na MK ya tabbata.
sanyin iskar dake shiga hancina ne ya farkar dani, na buɗe idanuwana a hankali cikin hasken alfijir ɗin daya ratso ta labulen windon ɗakin, asuba ce a wannan lokacin a yanda na fahimta, saina lumshe idona a hankali kamin na sake buɗe shi a hankali, cikin sakan ɗaya, biyu sannan idona ya sauka akan fuskar Yaya dake kwance akan ƙirjina, kamin na fahimci kuma hannayensa na kewaye dani ne. murmushi ya ɓalle min, na kai hannu na ƙara rufemu da bargon ina mai tusa hancina acikin sumar kansa da wani sanyayyan ƙamshi ke tashi.