SIRRIN ƁOYE COMPLETE

AFTER 1 YEAR…MK
“Hellowww Daddyn Urnborn”. nayi whispering softly acikin kunnensa. “It looks like someone will be late for work today”. na ƙara faɗa ina bashi kiss a kowanne eyes nasa, that made him open his eyes lazily yana kallona da murmushin dake talewa a leɓensa.
“Morning to you Baby Doll”. ya faɗa yana janyoni jikinsa. “morning sarkin bacci”. na faɗa ina kama tsinin hancinsa. “Doll wannan ɗumin jikinne bana gajiya da shi shi yasa kullum nake kusan yin late a work”. sai na ƙara sakin wani murmushin na kwanta lamo ajikinsa ina jin yanda zuciyarsa ke bugawa. ya kai hannu kan ƙaton cikina yana faɗin,”1 week remaining ko?”. na gyaɗa masa kai kawai ina tura hannuna cikin singlet nasa na shiga wasa da nimple ɗinsa. “i have to be at the office by now shine za ki tsokanoni ko”. shiru nayi masa, dole ce take sawa nake barinsa fita office, amma ba dan son raina ba, ina son mijina, ina matuƙar sonsa, kuma ina godiya ga Allah daya mallaka mani shi, haka ina godiya ga wannan ƙaddarar da ta sauya komai.
duk sanda nake tare da shi, sai naji inama akwai wata hanya da zan sanya lokaci ya tsaya cak, so i could cherished our moment together forever, or if my life was a dream zanyi fatan naita baccin ba tare dana farka ba. ya bani kiss a saman kumatuna da forehead ena, duk da cikin jikina ya tokareshi amma haka ya san yanda yay ya haɗe hancinmu wuri guda yana gogawa, shaƙar numfashin juna kawai muke, kuma tuni na gama kashe masa jiki da shafa hannuna da nake a saman mararsa, sai ya ƙanƙameni yana lumshe idanu, sai na saki murmushin daya haɗe da dariya ina janyewa daga jikinsa. sai yay saurin buɗe shanyayyun idanuwansa yana ƙara janyoni yace,”Allah ba ki isa ba”. kuma ba tare da ɓata wani lokaci ba muka fara nunawa junanmu soyayya har zuwa lokacin da muka gama samun natsuwa sannan mukai wanka…na shirya shi muka fita mukai break fast tukunna ya wuce office ina cewa da shi,”Jay plss be home in time for dinner”.
ko da na dawo ɗakin Nawwara na wuce, na sameta tana shafa icing a jikin cake ɗin munafurcin da ta gama haɗawa. yawuna ya tsinke na zauna kusa da ita, tsabar walaƙanci tana jina amma saboda abinda ta ke yafini bata kula dani ba. bata ankara ba kuwa na kaiwa cake ɗin damƙa nai ƙatuwar gutsira na kai baki, tsananin baƙin ciki da takaici ya hanata cewa dani komai sai sakin baki da tai tana kallona, kaman ta kurma ihu ta rufeni da duka. haka na janyo cake ɗin gabana naci iya cina bata ce dani ƙala ba, sai da nai hani’an tukunna na dubeta ina dariya nace. “sorry ba laifina ba ne”. “dama ai haka za ki ce”. ta faɗa kaman tasa kuka. na shafe ma ta icing ɗin a fuska har lokacin ban bar dariya ba saboda yanda ta cukule. “dilla can Allah na tuba dan dai cake, me akai akayi shi…sai a tura driver ya sayo masa wani”. “ai nasan dana sayarwa naƙi saya na zauna nayi da kaina saboda bana so hubbina yake cin kayan waje”. na taɓe baki nace,”oho dai, tun jiya nake cewa ki rakani kawai ai min operation a ciro waɗannan yaran kika ƙi, da yanzu ai cake ɗinki na nan lafiya”. ta buɗi baki za tai magana wayarta tayi ƙara da ringtone ɗin i love you my baby boy. tana ɗagawa sai cewa tayi da Abdurrahim “Habibi kaga Yaya ko?”. ta faɗa masa da kukan shagwaɓa, ina jiyo shi ta cikin speakern wayan yana tambayanta me nai mata, tace da shi. “na gama haɗa maka birthday cake ɗinka tazo ta cinye tana wani ƙalawa unborn”. ina jinsa ya saki ƙwafa yana faɗin,”yanzu duk wahalan da kika shiga bata tausaya maki ba ta zauna ta cinye, ina ce ma ko sannu bata maki ba ko?”. tace da shi,”ina tace min sannu kuwa tana can ɗaki liƙe da miji bata ma san nayi aikin ba, sai iya zuwa ta cinye”. “rabu da ita, zan rama ne akan mijinta…kuma zanzo na ɗaukeki ai sai naga yanda zata yi da zaman wannan ƙaton gidan”. na ƙyalƙyale da dariya na warci wayar ina cewa da shi,”ka ɗauketa ka kaita ina ƙaton gwauro?”. “ina ruwanki, ke da mijinki ya ɗaukoki daga gidanku ina ya kaiki, Allah kina shigar mana hanci da ƙundundune…sa’arki ɗaya ma ɗanmu ne yaci da sai dai kiji sammaci yanzun nan”. “oho dai cake ne na cinye kuma ko yanzu akai wani naji ina so sai naci ehe…kuma wallah Abdurrahim kar na sake naji kaima Jay wani abun in ba haka saina shiga na fita na lalata wannan auren naku”. sai ya bushe da dariya yana cewa,”yasin munfi ƙarfinki, munsha li’ilafi da tabbatyada, dan haka munfi ƙarfin muguntar mutum”. kashe wayar nai na jefa ma ta kayarta ajiki, na dafata na miƙe ina roƙonta akan taiwa Allah tazo muje asibiti ai min operation ai yanzu ya isa acire twins ɗin dake cikina duk da Edd ɗina sai nan da 7days, danni nace ban haihuwa da kaina sai dai a yankani.
kuma dan walaƙancin Nawwara sai ce min tai bata ƙi ganin ma na fara naƙuda yanzu ba ta miƙe ta bar min gidan bama ɗakin ba. ta fice ta barni tana jarabar ɓata ma ta cake ɗin da nai, sauranma sai mage ta bawa ta cinye akan ta ban na ƙarasa shi…kuma nace zan haɗa ma ta sharri wurin Jay tace na manta itama tana da Habibi, yarinyar nan tunda Ya Kabir ya haɗasu da Abdurrahim ta fitsare kamar shi. ashe dalilin tahowarmu da ita kenan, yace tausayin yarinyar da yake ji ne yasa shi ganin babu wanda ya dace daya aureta kamar Abdurrahim, kuma kasancewar munbi duk da wata hanya da Nawwara zata ja hankalinsa nan da nan kuwa Abdurrahim ya amince da ita. yanzu haka bikinsu wata uku ya rage dan zuwanmu da wata bakwai muka je can inda har iyayen Abdurrahim ɗin muka tafi suka nema masa aurenta.
After 2days.
“ina kika maida wannan kayan?* yana tsaye daga bakin closet ya kama ƙugu yake tambayana. nace da shi,”yanzu dan Allah kaya nawa gareka da zaka ce min ina na kai maka wannan kayan”. sai yay murmushi ya wurgo min singlet ɗin hannunsa yana cewa,”to sarkin dalla dalla…kayan da Ishaq ke ɗinka min nake nufi”. har yanzu hankalina na kan kayan Babies ena da nake ninkewa ina zubawa a riyo ɗinsu, haka nake kullum banda aikinyi sai na fito dasu na ƙara ninkewa, takaici ya ƙume Nawwara dalilin daya sa ma kenan idan taga ban fito parlo ba zata kira wayana tace wai ina fama da rashin aikinyi.
“ka manta kai kace na tattarasu gaba ɗaya na bawa Abubakar…kai Jay wai me yasa kake da mantuwa tun baka tsufa ba”. yasa hannu yana shafo bayan wuyansa, ba tare daya ce komai ba ya ƙaraso inda nake shima ya zauna a ƙasa kusa da ni, sai kallon cikina yake kamin nace da shi. “lafiya? kafa daina kallan mun yara dan kyauna nake so suyi ba naka ba”. “ni dama ai nafi so suyi kyanki, kawai dai ina mamaki ne idan na tuna yanda da cikin nan ke a shamule”. sai kuma ya tankwashe ƙafa ya kuma matsowa kusa da ni yana faɗin,”Preety wai nayi ƙoƙari kuwa ransr first night enmu?, har yanzu ji nake kaman a maido shi baya”. na sauke masa ɓawon ayaban da na gama ci a fuska, ina cewa,”idan kwaɗayin ayaba ne ya kawoka ba baka zanba…gwara ka tashi kaje ka haɗa kayan wankinka dan ni daga nan har na haihu kayan ƴaƴana kawai zanke taɓawa”. sai kawai naji hannunsa cikin rigana y fito da breast ena yana faɗin,”ni ai ba mayen ayaba bane…kema kin san da wannan”. na taɓe baki nace,”kasha iya shanka, twins na zuwa ya zama ƙwalelenka, tsakaninka da shi kallo daga nesa”.
Fashin Baƙi.
Na haifi kyawawan ƴaƴanna twins Mace dana miji, ranar suna kuma da aka sha shagalin da ko biki albarka suka ci sunayensu masu albarka, Namijin akasa masa Adam(sunan Baba) muke kiransa da Ramadhan, macen kuma Hajara wadda muke kiranta da Nihla. aiko munsha sababi wurin Yagana akan ba’a saka sunanta ba, wai dama ba son tsakani da Allah muke ma ta ba, da muna sonta har zuciyarmu sai muyi ma ta kara. Jay yace tasha kuruminta haihuwa ai yanzu aka fara, ta rubuta ta aje haihuwa ta gaba sunanta ne, tace daga baya kenan nan da shekara uku ko biyu ai tana gidanta na gaskiya.