SIRRIN ƁOYE COMPLETE

Anyi auren Abdurrahim da Nawwara inda suma suka tare nan kusa damu babu nisa, dan abotarsu da Yaya da gaske ne, kusan kullum kuma Nihla na wurin Nawwara acewata ni kam nafi son Ramadhan me sunan Babana, yaron da na ɗora dukkan so da ƙaunata akansa, ɗaukansa ma ban fiya so ayi ba, har faɗa mu kanyi da Jay wani lokacin dan idan na tattara hankalinta akan Ramadhan bana fuskantar kowa da komai. shima kuma duk sanda yaso ya rama idan ya ɗauki Nihla sai na kusan kuka sannan yake saurarona, dan shima yafi son mai sunan Mamansa.
Ya Ahmad yayi aure shima, ya auri wata ma’aikaciyarsu me suna Ngozi ada, dan lokacin da ta zo wurinsa ta faɗa masa tana so ta shiga addininsu yaji duk duniyarsa babu macen da yake so sama da ita, kuma ta amsa kalmar shahada ta tashi daga Ngozi ta koma Nusaiba, suna nan zaune a lagos.
Adawiyya ma tayi aure, ta auri tsohon saurayinta na farko da ta wulaƙanta shi akan Suhail.
Inna Amarya kuwa ta kamu da paralize, inda aka maida ita gidansu taci gaba da jinyarta acan, ni dai tun ranar farko da muka je dubata ban ƙara sanin a halin da take ciki ba yanzu, ta zama bar tausayi maganarta sam bata fita, kamar me gwaranci, duk tabi ta ƙare ta lalace, ranar da mukaje tana ta miƙo hannu wai zata taɓa su Nihla na doka ma ta tsawa nace “kull ɗinki, har yanzu ban mata da ke kikai ajalin Gwaggona ba, ganina ma da kika yi anan darajar Mijina kika ci, amma ni ko a lahira ban fatan haɗuwa da ke, kuma har ki mutu ban yafe miki da abubuwan da kika mana ba”.
da zamu taho kuwa sai kuka ta ke, Allah masanin abunda ta ke son cewa damu, ni kuwa a raina cewa nake dama ta mutu bata nemi yafiyar waɗanda ta cuta ba taji daɗin cin ubanta a ƙabari. shi kuwa sai wani jimami yake yana tausaya ma ta, haushi ma yasa har muka isa gida ban ƙara kula shi ba.
Bross Almustapha ma yay aurensa, yana zaune da matarsa acan London.
bayan tsawon wani lokaci, ina ɗauke da cikin wata tara Allah yayiwa Yagana rasuwa, bayan tayi fama da rashin lafiya, jinyar da ta zama ajalinta. mutuwar da ta kusa zautar da ni da mijina, ba mutane kaɗai da suka kasa gane kanmu ba, hatta mu ɗin mun kasa gane kanmu, dan har akai adu’ar bakwai bamu dawo hayyacinmu ba, haka kuma tun zuwanmu washe garin rasuwar bamu ƙara haɗuwa da juna ba sai ranar da zamu tafi, shima kuma dan Baba ya takura ne akan mu shirya mu bi su Mami abuja washegari sai mu wuce gida, tunda dai zaman namu ba shi zai dawo da Yaganan ba.
kuma daren ranar da muka a abuja na haihu, na haifi yarinyata mai kama da Yagana sak, kuma tana dirowa duniya nida babanta muka kirata da suna Ruƙayya, kuma bamu ɓoye ma ta suna ba kaman yanda Yaganan ta roƙa.
Matar Ya Ahmad ma ta haihu, kuma ita sunan Yagana ɗin ya saka, ƴarsa t biyu kuma ya saka ma ta Maryam wai mai sunana.
yanzu haka anata shirin bikin Basma da Alhassan nan da kwanaki ƙalilan da suka rage, abu ya zama tuwona maina, auren Yayana da Ƙanwata, sai shiri nake kamar wadda zata aurar da ƴar fari.
TAMMAT BIHAMDULILLAH!
Alhamdulillah, Alhamdulillah.
ina roƙon Allah ya haɗamu a alkhairin dake cikin wannan littafi, sannan yayi mana gafara a kuskuren dake cikinsa…amin y Rahman
Finally zan tsaya anan????…and its time to say good bye to you my people????????. thank you very very much for your love and support????…thanks to all of you that took your time to read, comment, and vote for each and every chapter????….and most crucial; thank you very much for all the prayers and well wishes that you guyz have sent my way since the starting point to the ending point????❤…i will forever be grateful to all my wattpad family and Oum Ramadhan Palace, i feel loved and i love you to the moon and back????….kuna da yawan da ba zan iya lissafo ku one by one ba, akwai sunayen da idan ban lissafo su ba zan iya cewa SIRRIN ƁOYE bai kammala ba, to amma a kaɗan ɗinsu idan nace zan jero waɗannan sunayen zamu ƙara ɗaukan wasu chapters enne????, amma dai kowanne makarancin littafin nan ya sa ni wannan page ɗin nasa ne sukutum guda na bahi????.
My headech, matar Awwaluuu, jikar Yagana and my pracetamol nace ba????????…bari dai nai quite kafin na fara ɓallo sunaye????….ina yi mana fatan alkhairi
Start:-15 October 2021.
End:-25 february 2022.
Please for those following youtube channel kindly search for my Channel SAHAZ MULTIMEDIA, do subscribe and press the bell icon for vedio update.