BARRISTER IBRAHIM KHALIL 1-END

BARRISTER IBRAHIM KHALIL Page 71 to 80 (The End)

        *CHAPTER Twenty Eight*________????Yana tura ƙofan Halwa tabuɗe idanun ta, dama tun ɗazu bata yi barci ba tunani ya cika mata zuciya

Jin ya nufo wajen gadon sai tasake Rufe idanun ta tana sauraron bugun zuciyar ta dake sake hauhawa

Ajiyan zuciya yasauke lokacin da ya’iso bakin gadon yasami waje yazauna, fuskarta yake kallo kasancewar Facing ɗin sa take yi kuma da hasken lantarki da yakunna shigowar sa, yasan ba barci take yi ba don haka yace

“Tashi zaune muyi magana”.

Runtse idanuwan ta tasake yi, sai kuma ahankali taware su kan bayan sa da yajuya mata, tashi tayi tazauna tana sake jawo bargon jikin ta duk da ba wai ta saka kayan barcin me nuna tsiraici bane, sai dai kasancewar yanda yalafe a jikin ta ana ganin komi, gashi kuma rigan iyakan ƙasan gwiwan ta yatsaya

Shima gyara zaman sa yayi sosai yana fuskantan ta

Kanta a ƙasa tana jiran abinda zai biyo baya, sai dai shiru yaƙi yin magana, ita kuma ta kasa ɗago kai bare ta kalle sa sabida tasan idanun sa na kanta

Zuba mata idanu kawai yayi yana kallon ta, jujjuya maganar da yake son furta mata yake yi a zuciyar sa, sai da ya ɗan ja lokaci kafin yafesar da numfashi yabuɗe baki yasoma magana

“Halwa”. Yakira sunan ta a hankali

“Na’am”. Ta’amsa masa batare da ta ɗago kanta ba

Hannayen sa yahaɗe waje ɗaya kafin yace “Da farko dai ina so in baki haƙuri agame da zamantakewar da mukayi abaya, sabida yanda na nuna miki halin ko in kula a matsayin ki na Matata, duk da ba wai nayi hakan a son Raina bane, har a cikin zuciyata ina jin zafin abubuwan da nayi miki, don Allah idan na ɓata miki ki yafe min yanzu ina so mu gyara zaman auren mu ne shiyasa nake so mu soma fahimtar juna a yanzu ɗin”.

Lumshe idanuwan ta tayi hawayen da suka soma sintiri a fuskarta tun soma maganar sa suka ci gaba da tsiyaya, wani irin sanyi ne yake ratsa ta har cikin zuciyarta, har a yanzu ɗin ma bata ɗago kanta ba tace dashi

“Yaya Khalil wlh baka yi min komi ba, idan ma har kayi min to na yafe maka domin ban taɓa kallon ka matsayin me cuta min ba”.

Tattausan hannayen ta yariƙo cikin nasa wanda sai da yasaka suka ji tsigan jikin su ya tashi, domin hakan ba wai ya taɓa faruwa bane dasu, fatar jikin junan su be taɓa haɗuwa waje ɗaya ba

Sauke ajiyan zuciya yayi yana ƙara damƙe hannayen nata, idanun sa kafe akanta duk da ba wai kallon sa take yi ba, sannan yasoma magana

“Duk da bansan cewa kina sona ko baki sona ba but ina me neman alfarma ki bani dama a cikin zuciyar ki, Ni kuma zan koya miki ƙaunata sannan nayi miki alƙwari zan faranta miki da iyawa ta, sannan duk abinda ke faruwa naji komi wajen Dad”.

Shiru yayi yana jan numfashi sabida jin wani kishi ya turniƙe shi tunawa da wani banza shi yasoma ɓata wa Halwan sa rayuwa, ɗan daidaita muryan sa yayi yace

“Ina so in ƙwato miki haƙƙin ki wajen tsinannen mutumin da yaruguza miki rayuwa”.

Yanda yayi maganar cikin wani irin murya da dole ne kagane tsananin kishin sa, duk da kuwa ya daure sosai wajen dai-dai ta muryan nasa, hakan yasa taɗago kai akaro na farko tazuba masa idanu, bata yi tunanin wai ko wannan maganar yake son faɗa ba koda yace mata yaji komi wajen Dad, cikin sanyin murya tace

“A’a Yaya Khalil abinda yawuce ya rigada ya wuce, duk da ada Ina da burin ɗaukan fansa amma yanzu tuni na cire hakan a raina, Husna yanzu ta zama mallakin Saleema na bata ita har abada..”

Katse ta yayi da faɗin “duk da haka dole ne na ƙwato miki haƙƙin ki, Ni lauya ne ke kuma Matata ce, taya kike tunanin zan iya barin wanda yataɓa yin ma Matata Fyaɗe batare da na ɗau mataki ba? Ba wai mayar masa da Husna za’a yi ba but dole ne Kotu ta yanke masa hukuncin abinda yayi, na rigada na gama bincike a kansa zuwa kwana biyu da yardan Allah zan miƙa Case ɗin kotu”.

Wani irin farin ciki me haɗe da kuka ne suka taho mata, ko kaɗan ta kasa ɗauke idanun ta akansa, sai dai ta matse bakin ta gamm ta hana kukan nata fitowa illa hawayen dake ƙara sintiri saman fuskarta tare da murmushin farin ciki dake gudana

Kazalika shima kallon nata yake yi, yayinda yasauya riƙon da yayi wa hannayen ta yana murza mata su a hankali yana jin ƙaunarta na ƙara shiga zuciyar sa tare da ƙara girma sosai, yana son yafaɗa mata sirrin dake ransa sai dai kuma baya son yasanar da ita da baki illa a aikace, don haka yabata umarnin tamiƙe tasauko su gabatar da Sallah kamar yanda ko wanne ma’aurata suke yi

Hakan kuwa yafaru, ita tasoma yin alwalan tafito tasanya Hijab tazauna zaman jiran sa

Shi kuma sai da yayi wanka sannan yafito da alwalan sa, doguwar riga kawai yazira suka ta da Sallah, har suka idar yayi musu dogon addu’a inda daga nan kuma yafice zuwa kichen yaɗauko Plates da Spoon yasake kazan da Saleema taba shi, sai da yagama dai-dai ta komi sannan yayi wa Halwa magana akan tasauko su ci, don ita tuni ta haye kan gado tana lissafi cikin zuciyarta, tayi mamaki da ganin abinda ke gaban sa wanda hakan yatabbatar mata ya shirya ma daren, duk da ko kaɗan bata ji ƙamshin ba sa’ilin da yake sake wa illa motsin leda da take ta faman ji kuma bata yi tunanin dashi yazo ba

Babu musu tasauko duk da bata jin yunwa, amma kuma zuciyarta bata ba ta shawaran musa masa ba ko dan faranta masa da take son Yi, domin kuwa ta ɗau alƙawari faranta masa sosai a daren nan ta yanda zata nuna masa godiyar ta a duk kan komi da yayi mata kuma yana shirin sake mata wajen ƙwato mata haƙkin ta

Bata wani ci ba, shima haka ɗin, ita ta tattare komi zata kai kichen yadakatar da ita yakwasa yamayar

Kafin yadawo har ta shiga ta wanke bakin ta, yana shigowa tana fitowa sai tanufi kan gado tahaye

Shima ɗin Toilet ɗin yashiga, babu jimawa yafito yanufi gaban mirror, anan yagama shafe-shafen sa tamkar wani mace, sai da yabi ko ina nasa da turaruka kafin yakashe wutan yanufi kan gado ya haye…

A wannan dare Khalil da Halwa sun raya sa ne cike da farin ciki da annashuwa, tare da soyayya me tsayawa a rai ga duk kanin su, wanda tuni ko wannen su ya sanar da ɗan uwansa sirrin dake cikin ransa batare da sun an kare ba, har gabanin asuba kafin suka yi barci manne da juna tamkar zasu maida junan su ciki. ????????‍♀️????

        *****

Washe gari a makare suka tashi dukan su, don lokacin ƙarfe 07:38am. Ne, Sallah suka gabatar a gurguje, suna idarwa Halwa tasake nannaɗe wa akan gadon don barci ne sosai a idanun ta tunda basu samu sun yi ishashshe jiya ba

Khalil kuwa shirin Office yayi a gaugauce Cuz lokaci ya ƙure masa, gashi babu daman zama agida tunda yana tsaka da soma wani Shari’a ne aiki yayi masa yawa sosai

Koda yagama shiryawa wajen gadon yanufa yasakar wa Halwa kiss a kumatu sannan yaƙara mata a goshin ta, yashafa kanta yana murmushi ganin yanda take yamutsa fuska tana gyara kwanciyarta,

Sosai idan tana yamutsa fuska take masa kyau ainun, ya kula hakan ya zame mata ɗabi’a ko da yaushe sai tayi

Gyara mata Bargon yayi yasake rufe ta yafice dasauri riƙe da briafcase ɗin sa, ɗakin Saleema yashiga sai dai babu ita ciki, har Toilet ya leƙa be ganta ba don haka yafito Direct yanufi kichen

Tana ciki kuwa tana haɗa musu Breakfast, daga ita sai doguwar riga iya cinya da gajeren wando baƙaƙe, sai hula me raga-raga shima baƙi tasaka a kanta, kasancewarta fara sai kayan sukai mata kyau suka sake haskata sosai

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button