BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

Kasancewar da Mom da Aunty Amarya sai wata ƙanwar Momy da yayarta za’aje yasa Anam maƙalema Mom sai taje. Mom bata hanata ba, dan ita tanada sauƙin kai sosai shiyyasa suke zaune lafiya da Mommy tsahon shekaru, duk da dai itama Mommy ɗin bawai tanada faɗa bane ko rikici, kawai dai ta tsani Mamie ne saboda tun farko akan hakan Gwaggo ta ginata, ta riga ta nuna mata shi Abie ɗan uba ne a cikin su Daddy duk da kuwa ba itace ta haifesu ba. Sai kuma ta kasance mace mai son komai ace itace sama da kowa, sannan a wajenta ake neman komai, a ganinta bazai yiyu ita matar farko a gidan ba, sannan mijinta shine babba ace wata a matan ta fita. Fin da Mamie ta mata kuma ya ƙara ƙiyayyar, itako Mom Abbah bai kai Daddy ba gaskiya, sai dai na waje bazai taɓa fahimtaba kasancewar ana ganinsu kansu a haɗe a koda yaushe kuma suna gida ɗaya ne.
Kasancewar matar da Shareff ɗin zai aura ɗiyace ga gwaggo halima (ƙanwar daddy), kuma mahaifinta yaya a wajen mommy gawurtaccen ɗan siyasa mai muƙamin babba a jihar ta kano gidane katafare suka iso. Komai yaji na more rayuwa. Fadwa shine sunanta, ɗiya ga Alhaji Sadiq Dakata. Mahaifinta kamar Yayane ga Mommy. Dan da mahaifiyarsa, da Mahaifiyar Mommy da gwaggo duk uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Zumincine mai ƙarfi a tsakaninsu, dan haka ita da Gwaggo suka zaɓama Shareff Fadwa matsayin mata tunkan ya dawo gida Nigeria. Sunyi hakane a cewarsu dan kar Abie yay tunanin basa auren Anam. Da farko dai Shareff bai maida hankali ba duk da baice baya sonta ba. Sai da Mommy ta masa jan ido sannan ya ɗan ke kula Fadwa ɗin. Fadwa ƙyaƙyƙyawar yarinya ce gwargwado kuma ƴar gata, sannan kuma sele (celebritie) a social media, musamman tictok da istagram harma da twitter. Idan zan zauna fayyace muku wacece Fadwa zamu cinye labarinne a kanta. Kuje zuwa dai lokaci zai nuna muku ainahin Fadwa Sadiq Dakata.
Sun sami tarba ta girma da girmamawa. Inda babu kunya Fadwa ta fito tare da tarin ƙawayenta da suka cika gidan kallon kaya tun a gaban su Mom. Yayinda su Abie ke can suna tattaunawa da su Alhaji Sadiq domin tsaida rana. Dama dai shine yace baya son aita jeka ka dawo, su haɗo komai rana ɗaya su kawo har sadaki sai kawai a tsaida ranar ɗaurin aure.
Su dai su Mom wannan abu ya sakasu jin lallai akwai gyara a lamarin wannan amarya, duk da kuwa ƴar gida ce dan sun san wasu a cikin halayenta saboda kowa yasan ƴaƴan gwaggo Halima basu da ƙwaɓa. har cikin rai suna jin tausayin Shareff ɗin kasancewarsa bai wani cika zafi da yawan magana ba a mafi yawan lokuta. Amma sauran ƴan uwan Mommy da yake ƴan uwansune suma sai basuji komaiba a lamari, dan kuwa dai basu nuna a fuska ba sai dai in sun barma ransune suna nuna normal ne a zahiri.
Fadwa tasan labarin Anam a wajen Mommy da Gwaggo da mahaifiyarta. Sai dai bata santa a zahiri ba sosai saboda gwaggo halima ba shiga duk abinda ya shafi su Abie take ba, tasha jin sunzo ƙasar tabi duk hanyar datai mata ta toshe haɗuwarsu sai idan wata fitinar suka shirya da su gwaggo shima ita kaɗai take zuwa babu ƴaƴanta. Hakan yasa yaranta basu wani san Abie ɗin bama balle ƴarsa, shima kuma bawani gama sanin ƴaƴanta yay ba tunda bata bari su raɓesa. Hakan yasa Fadwa bata nuna damuwarta da ganin Anam tare da su Mom ba. Amma dai yanda Anam ɗin ta zama miskila a wajen tana kallon komai ya ɗan ja hankalin su Fadwa da ƙawayenta gareta. Har takai babu kunya Fadwa na tambayar su Mom ina suka samo Anam ɗin?. Murmushi kawai Mom tai da faɗin “Itama ƙanwarki ce”. Daga haka ta tsuke bakinta duk da tambayar bin ƙoƙwanto da ƙawayen Fadwa ke cigaba da jefamasu Mom ɗin. Aunty Amarya dama bata tanka ba dan ita bata da farin jini a garesu kasancewarta kishiyar Mommy.
Har dai suka baro gidan Fadwa da ƙawayenta basu san matsayin Anam ba. Ita kuma ta miskile ko ruwa bata sha ba a gidan har suka taho. Gwaggo halima ma duk da taga kamanin Abie a jikin ta kuma tasan sun zo bata tanka ba bata nuna komaiba.
Anam ma sai da suka ɗakko hanyar gida ta fara yima su Mom mitar Fadwa da ƙawayenta masu shegen rawar kan tsiya da nuna wayewa. Murmushi kawai Mom da Aunty sukeyi dan mota ɗaya suke su uku, ƴan uwan Mom ma na nasu su biyu.
Bayan sun iso gida kowa yaji ainahin watan bikin a bakin su Abie. Nan da watanni biyu. Sauran yaran gidan nata murna duk da wannan ba shine karon farko da za’ai biki ba. Anyi bikin Rahma dake bima Khaleel, da Binta ƙanwar su Shareff dake bima Maheer. Yanzu Aysha ce a layi kuma sa’ar Anam ce dan watanni ta bama Anam ɗin kawai, itace ɗiyar Mommy ta biyar daga ita sai autoci su twins. Ga Anam kam babu dalili ta wani tsume sai kallonsu take da taɓe baki, har bayan magrib babu fara’a a tare da ita. Rashin walwalar tata yasa koda Aysha ta tambayeta. Sai tace ba komai.
Sai bayan magrib suna hira duk kusan yaran gidan a falon aunty Amarya, gaba ɗaya hirar tasu ta ta’allaƙa ne akan shirin biki. Sai dai Anam taƙi tako tanka sai faman game take bugawa a waya. Sai dai kuma kunenta duk yana a garesu ne. Jin sun cigaba da damunta ta tashi zaune tana wani taɓe baki da harar Nusaiba mai gwada rehearsal na rawan da zasuyi wai a wajen dinner….
“Kun wani dage sai tsara events kuke bayan amaryar ma ko aji bata da shi mtsoww!!”.
Lokaci ɗaya falon yay tsit duk suka juyo suna kallonta. Hussaina ta ɗan waro ido da ƴar tsiwa tace, “Aiko dai aunty Fadwa nada aji gata ƙyaƙyƙyawa ƴar babban gida bama son jealous”.
“Jealous!!. K! Hussaina dani kikeyi wai! kowa ma? Ni Juwairiyya ce zanyi jealous ɗin wancan farin ƙasan mai kama da ƴar tallan kasuwa. Baki da hankali”.
A yanda take maganar a fusace yasa Hussaina tsorata, dan in tsiwa takeji Anam kakartace a iyawa. Amma shirun nata badan tsoron bane kawai, harda wanda idonta ya hango ya shigo falon ne yasa tai shiru. Anam kam da sam bataji ko sallamarsa ba sai faman faɗa take da sule Fadwa iya gaskiyarta. Tsaki ta doka da fisgar tab ɗinta dake hanun Hashim da nufin barin wajen, karaf idonta ya sauka a kansa. Yana tsaye tamkar an dasashi ya kafeta da manyan idanunsa masu razana wanda ya shiga gonarsa. Sosai gabanta ya faɗi, amma da yake ƴar gagiyar bata yarda aga gazawarta a fuska ba sai ta ɗaukesu cike da wani irin sallo da kaɗasu kamar mai harara ta nufi hanyar kitchen domin bi ta baya, dan tana shakkar bi ta gabansa tunda a ƙofar falo yake tsaye. Duk da bai nuna yama ji abinda tace ɗin ba hakan bai hana su Aysha ƙara nutsuwa ba.
Washe gari Abie yay shirin komawa. Anam ta zauna taita kuka itafa sai dai su koma tare. Yasan halinta akan kafiya, baiyi da wasa ba yay mata fata-fata, sai su Abba ne da aunty Amarya keta lallashinta da Ya Khalel. Shareff kam duk da yana wajen ko tari baiyiba. Yamaƙi nuna yasan abinda akeyi. Sai da zai buɗema Abie baya zai shiga ne ya harareta. Ƙasa tai da kanta ta sake fashewa da kuka.
Daddy da yaga hararar Shareff na ƙoƙarin shiga mazaunin driver ya dakatar da shi. “Kaga ku wuce da Mamana tai rakkiyar itama”. Kansa ya duƙar ƙasa fuskarsa na sake tsukewa da satar kallon Mommy. Murya a rissine yace, “Daddy zanje wani wajene fa bayan airport ɗin”.
“Sai ku tafi tare da ita tama huce kafin ku dawo gida”.
Sosai takaici ya sake lulluɓesa. Sai dai baice komaiba. Daddy da kansa ya buɗe gefensa ya sakata dan Abie baya ya shiga. Koda suka bar gidan shi da Abie ne kawai keta hirarsu. Itako tai tsit kamar bata a motar, sai ajiyar zuciya take faman saukewa idanunta a lumshe sanyin ac na ratsata. A airport ɗin ma Abie shareta yay har sai da aka fara shelar masu tafiya a jirgin da zaibi sannan yaɗan fara lallashinta da ƙara mata nasiha. Daurewa kawai takeyi, amma ita dai bata ƙaunar zama a ƙasar batare da iyayenta ba. Da ƙyar ya ɓanɓareta a jikinsa domin amsa kira, tana ganin ya shige ta dirƙushe a wajen. Takaici ya saka Shareff buɗe motarsa yay shigewarsa. Jin ya mata key ya sata miƙewa da sauri dan ta tabbatar kaɗan daga aikinsa ya wuce ya barta a wajen.