GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan Sarki Abdulsamad yayi murabus ya maida mulki a hannun Yarima Abdulhadi da shekara hudu, sarki Abdulhadi ya auri yar’sarkin Adamawa Gimbiya Aisha ana kiranta da Gimbiya Fulani…
Gimbiya Fulani ita ta haifi Gimbiya Hakima Abdulhadi Abdulsamad..
Gimbiya Hakima ta taso cikin gata da kulawa a wajen Yakumbo, dan Gimbiya Hakima bata san Fulani ce mahaifiyarta ba sai da ta girma sanann ta san ita ce mahaifiyarta.
Fulani da Gimbiya Hakima ba wani shiri suke yi sosai ba, duk da mahaifiyarta ce, amman Fulani tace mundun bata chanza halinta ba, to basu taba zama inuwa daya.
Gimbiya Hakima ta tashi da wani kallar hali wanda ya girgiza iyayenta, domin Gimbiya Hakima bata san tallakawa ko kadan, tun tana yarinya indan su Inna Lantana suka dauke ta, to suna ajiyeta sai anyi mata wanka inba haka ba bata iya bacci a ranar..
Tun Yakumbo na ganin kamar Gimbiya Hakima tana da kyamane, sai daga baya ta lura baki daya Gimbiya Hakima bata san tallakawa ko kadan…
Sunyi mata fadi amman bataji saboda ita acewarta bai dace sun hundanya da tallakawa ba, domin su masu mulki da kudi ne, wannan shine dalilin da yasa Gimbiya Hakima bata san tallakawa ko kadan..
Bata jin komai ta wulakanta tallaka, ko waye duk tsufanshi kuma duk yarintarshi, haka suke ta hakuri da halin Gimbiya Hakima tun tana karama take haka har yanzun gashi ta girma ta mallaki hankalinta..
Gimbiya Hakima, tana bala’in san taje kasar turkey karatu, wannan yana daya daga cikin burinta na taje kasar turkey..
Tun da sarki Abdulhadi ya fahimci Gimbiya Hakima, tana san zuwa turkey karatu shi kuma yace indai tana san ya kai ta turkey to sai ta chanza hali domin baya san halinta baki daya..
Gimbiya Hakima, tayi iyakar kokarinta na ganin ta rake abunda take amman ta kasa, duk da a haka tayi sanyi sosai akan da..
Ba yanda batayi ba sarki ya fahimta shida Fulani ta chanza hali, amman sunce su dai basuga wani change ba, shiyasa Maimartaba Abdulhadi ya samar ma Gimbiya Hakima addimission a A. B. U zaria yanzun haka yasa ana yi mata registration jira yake ayi resume ya hada mata kayan ta ta wuce makaranta dan so yake ta san maiye rayuwa..
Shi kuma yarima Annas yanzun haka yana turkey karatu yana karata engineer..
Wannan kenan kunji wacece Gimbiya Hakima in Summary dan bani san mu bata time wajen bata labarin da gwara kawai muyi mai anfani.. ????
Back to story ????????♀️????????♀️
“Lantana!
“Naam, Allah ya taimakeki Gimbiya Hakima uwar marayun masarautar Kano..
“Yau bani san fita parlour cin abincin rana, dan haka Ina san keda Bilkisu ku kwaso man abincin dasu ka dafa Yau a shigo man da shi ciki..
“To, angama yar’sarki jikar sarki, nan Inna Lantana ta tashi ta fita..
“Tashi bacci bai ganki ba, “na shiga uku ni Bilkisu wani abu muka sake yi ma Gimbiya Hakima, tunda naji ta kiraki hankali na yake a tashe?
“Kwantar da hankalinki, ba abunda mukayi sai dai yanzun muke san janyo ma kanmu bala’i, kin san dai Gimbiya Hakima bata san jira indan ta sa aiki, dan haka tashi mu shigar mata da abinci cikin uwar’daki, Yau bata san cin abincin a parlour sai cikin uwar’daki..
“Alhmdulh, wallahi Lantana har hankalina ya kwanta, bansan abunda zai hadani da Gimbiya Hakima dan ita bata gani tsufanka zata ci maka mutunci ba ruwanta…
“Yanzun zaki tashi mu kaimata ko har sai ta ne maimu? “To na tashi Allah ya fiddo mu lafiya, “Amin ya Allah Bilkisu..
Nan su Ba’ba Bilkisu suka kama kwasar abinci suna kaima Gimbiya Hakima a bedroom dinta sai da suka gama kai mata komai sanann suka zuba mata..
“Bilkisu! “Naam Allah ya taimakeki, “maza kije ki Kira man A’bu da Murya suzo ina bukatar ganinsu..
“Angama uwar marayu, Allah ya huci zuciyarki, nan Ba’ba Bilkisu ta wuce kiran su A’bu..
“Lantana! “Naam Gimbiya Allah ya da tsawancin kwana..
“Yau wa zai wanke wannan bayin?
“Allah ya taimakeki, ai mun wanke shi da kika tafi shashen su Gimbiya..
“A haka kuke nufin kun wanka bayin? “Muna neman Sausaucin Gimbiya Hakima mai farar Aniya..
“Tashi ki sake wanke shi, har sai nace ki barshi haka, “to Gimbiya angama, haka Lantana ta shiga toilet ta fara wanke shi, toilet din da sai ka kwanta kayi bacci cikinshi saboda wankuwa da yayi Amman Gimbiya Hakima tace bata ga wanki a nan ba????..
“Sannunku! Madafa, “Aa Ba’ba Bilkisu kece da kanki da kafafunki, kice har yanzun Gimbiya Hakima bata fito waje ba?
“Waya gaya maku Murja? To Gimbiya Hakima ke san ganinku yanzun tace komai kuke ku ajiyeshi ku zo tana bukatar ganinku..
“Inalillahi wa’inna’alaihirajiun! Allah yasa dai lafiya Ba’ba Bilkisu Gimbiya Hakima ke neman mu?
“To nima wallahi ban sani ba A’bu kawai dai tace tana san ganinku, dan haka ni kunga tafiya sai kun iso…
“Tashi mu tafi Murja karda laifin ya kara nunkuwa, dan nasan Gimbiya Hakima bata kiran arziki, in dai Gimbiya Hakima ta kiraka to rashi mutunci da cin mutunci zata yi ma mutun..
“Hakane A’bu, Allah yasa dai Gimbiya Hakima ba wulakantamu zatayi kamar dazun da safe ba, kinga dai yanda taci mana zarafi gaban shashenta Yau din nan da safen nan..
Haka suka taho duk hankalinsu tashe, jiki duk a sanyaye dan sun san kiran Gimbiya Hakima ba alheri bane..
“Ranki ya dade, na isar da sakonki, ga sunan zuwa, “Bilkisu zo ki tausaman kafar naji ta ba yanda nike san ta..
“To Gimbiya, nan Ba’ba Bilkisu ta fara yin ma Gimbiya Hakima tausa..
Lantana sai wanke kewaye take, ta gaji sosai ga daman abunka da jikin tsufa, ga dukuwa ba dadi, ta wanke yafi sau goma sha hudu, amman Gimbiya Hakima tayi burus da ita, ta nuna bama ta san da ita cikin toilet din ba..
“Ranki ya dade, ga mutanan madafa nan sun iso, “je Bilkisu ki shigo da su, “to ranki yadade..
“Har kun iso Kenyan? “Wallahi ko Ba’ba Bilkisu mun iso, “to bissimilla ku shigo cikin, “har ciki zamu shiga? “Eh ko insha Allah, ku taho..
“Ranki ya dade gamu mun ansa kiranki cikin gaugaugawa..
“Bilkisu! “Naam Gimbiya Hakima, “sake zubo man sabon abinci ki kawo man..
“To Gimbiya, Nan ta sake zuba mata wani sabon abinci ta bata..
“Gashi Uwargijiyata, “ajiye shi nan, sake zubo wani, “to Yanzun ko Gimbiya, nan ta sake zuba mata wani sabon abinci, “gashi ranki yadade…
“Mika masu, “to angama Gimbiya yar’sarki jikar sarki, Nan ta mike masu abinci tana kallon ikon Allah..
“A’bu! Murja! “Naam ranki yadade, “kuci abincin nan yanzun gabana, “to..
Nan suka fara cin abinci, su dai basu ji abunda abincin yayi ba..
“Allah ya taimakeki munci, “ai na gani, ko kinga ana yi man jagora?
“Allah ya huci zuciyarki..
Nan itama Gimbiya Hakima ta fara cin abinci, tana ci ta ya mitse fuska ta furzar da abincin bakinta akan fuskar A’bu, sanann ji kake…
Tas!!! Ta wanke Murja da wani lafiyayen mari sannan ta fara magana.
“Ni zaku kashe?
“Ranki yadade muna neman agaji da Sausauci wajen Gimbiya Hakima uwar marayu.
“Bana maku bana san yaji yayi yawa a cikin abinci ba? Sannan kuma kun cika man mai cikin abinci, wato na mutu ko?
“Allah ya taimakeki, ai mu yau muka dawo madafa da girki, wallahi su Ladi basu gaya mana ba..
“Ku baku da hankalin da zakuyi aiki da kwakalwarku ehye? Maiyasa ku wasu kallar dabbobine ku baku aiki da hankali..
“Ayi hakuri ba zamu sake ba..
“Dallah can kuyi man shiru, wawayen banza wawayen wofi, ku tashi ku kwashi tsiyarku ku barman waje salan in kun tashi yin na dare ku juye buhun barkono a ciki..