GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️
*M. W. A*
Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
STORY AND WRITING BY
_Jameelah jameey ????_
*(Yar mutan kankia????????)*
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI
Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.
NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????
????????????????Wallahi ko yau kun bani dariya sosai TEAM HAKIMA, haka kuke da kishi daman????
89&90
Shigowa yayi ya samu waje ya zauna, kallonsu kawai yake ɗaya bayan ɗaya dan bai san ta ina zai fara ba, dakewa yayi sannan ya fara magana yana cewa, “fatan kowa yana lafiya.”?…. “Lafiya lau, Alhmdulillah.” ….. Sukace gaba ɗayansu, dan kowa mamaki yake wannan taron gaugawar da Maimartaba ya tara, numfasawa yayi sai da yayi kusan 6min sannan kuma ya fara magana,”kamar yanda kuka sani ni na bukaci ganinku wajen nan.”
Ba wanda yace komai sai dai kallonshi da wasun su suke wasu kuma ƙansu ɗuke yake suna sauraran Sarki Abdulmalak, numfasa yayi sannan ya kira sunan Hakim, “Hakim.”… Ɗago kanshi yayi yana kallonshi, gabanshi faɗuwa yake sosai dakal ya samu bakinshi ya buɗe yace, “Naam Allah ya taimakeka.”… Cigaba da cewa yayi, “Hakim nasan waye kai, bance kafi kowa cikin yaran da na haifaba, Aa amman ina da yaƙinin ko bayan raina yazaka kula da yan’uwanka, kaine babba kunsan Hausawa sunce Babban wa uba, haka ne.”?..
Yayi tambayar yana kallon Gimbiya Zulaha, ɗaga mashi kai tayi tana murmurshi, amman ji take kamar tayi kuka dan yace Hakim shine babba, shidai Hakim baice komai ba,dan tunda yaji Abbanshi ya kira sunanshi yake addu’ar Allah yasa ba wani laifi yayi ba , yana cikin tunanin yaji yana cewa, “to saboda Haka, kai Hakim yau ma ga wani umirnin zan baka kamar yanda na baka umirnin auren Hakima kuma kayi man biyaiya naji dadin haka, kuma su Hamad ina fatan haka daga gareku.”
“Insha Allah Abba zamu zama mai biyaiya a gareka, zamuyi koyi da abunda Yaya Hakim yake da yarda Allah zamu zamo masu bin umirnin iyayenmu.”…. Humad yace haka kanshi ɗuge, shi dai Hamad baice komai ba, kallon Humad Sarki Abdulmalak yake dan ba tun yau ba yake yaba hankalin Humad dan kusan halinsu ɗaya da Hakim, Hamad ne kawai yasha banban,cigaba da cewa yayi, “Alhmdulillah, Allah yayi maku albarka gaba ɗayanku, to dalilin kiran da nayi maku ba komai bane ila kai Hakim na sake shidamaka da nan da wata ɗaya zani ɗaura maka Aure da Gimbiya Hikimatu yar’ sarkin Katsina.”
Wani kallar faduwar gaba ya ziyarci Hakim da Hakima lokaci guda, dan Hakima ji take bata gani sosai ma dakewa tayi, Gimbiya Fulani Kubrah lura da yanayin da Hakima ta shiga yasa ta riƙe hannunta tana shafawa ba tare da kowa ya gani ba, amman kash sai dai Hakim yana ganinsu duk da tashin hankalin da yake ciki dan bai da niyar yi ma Hakima kishiya dan son da yake ma Hakima ya wuce ya haɗashi dana wata mace, amman bashi da zaɓi dole ya bi umirnin mahaifinshi dan faɗar Allah(SWT) ce duk wanda yayi ma mahaifinshi biyaiya yana tare da Allah, sannan kuma wanda ya bujirewa iyayenshi yana tare da fushin Allah, dan haka shi ko dole ya bi umirnin mahaifinshi mudun bai saɓama shara’ir musulunci ba, yana cikin wanann tunanin yace Gimbiya Zulaha na cewa, “ina wallahi sun wannan abun ba zai saɓuba, na gaji da rashin gaskiyar da kake nunawa cikin gidan, komai dai kace Hakim, mu bamu da ya’yan ne? Ko kuwa namu basu isa su zauna da mata ba? Ko kuma basu da kwain haihuwa? Shiyasa komai ka samo sai ka kaishi wajen ɗ’an so to wallahi wanann karan ba zan yarda ba , haka kazo kace zaka ɗaura ma Hakim auren Hakima, kuma yanzun kadawo kace zaka ɗaura ma Hakim wata Hikimatu to wallahi ban yarda sai dai maida auren a kan Hamad ko kuma yanzun Hakim ya saki Hakima, a ɗaura ma Hamad ku kuma a ba Hamad auren Hikimatu ba dai Hakim ba, ehe.”
“Kingama.”? Sarki Abdulmalak ya faɗa cikin ɓacin rai dan sai yau ya ƙara yarda da Zulaha bata da hankali… “Eh nagama, kuma dole ayi yanda nike bukata, dan shima Hamad ɗ’ane kamar kowa, idan shi Humad ka nuna bai isa ba to ai shi Hamad ya isa tunda duka duka wata biyar Hakim ya ba Hamad.”
“Ashe ke Zulaha baki da hankali?, “ai ba rashin hankal… “Yi man shiru mutuniyar banza, kinci darajar ya’yan nan suna cikin wajen nan kikayi wannan maganar, da mu kaɗaine ni ɗaya nasan abunda zan maki dan haka ku duka ku tashi ku ban waje, kuma kai Hakim kasani aure na nan ba fashi nan da wata ɗaya insha Allah, sai ku fara shiryawa idan kuna bukatar kudi kuyi man magana, ai shi aure lokacine, to lokacin auren su Hamad ne baiyi ina nasan kin san da haka.”
Zubewa Hakim yayi yana godiya da babbar kyauta da Sarki Abdulmalak yayi mashi sannan suka taso suka taho ko wane ya wuce shashen shi da abunda ke cikin zuciyarshi.
Tafiya kawai take amman ita batasan ya akayi ba sai dai kawai ta ganta a shashen Gimbiya Kilishi, Kilishi tana shafa mata ruwa, tashi tayi zauna tana cewa, “wallahi sai inda ƙarfina ya ƙare, dan ba zan zuba ibo na naga anayi man kallar wannan cin kashin cikin gidan nan ina ido to yau tazo karshe.”
“Haba Gimbiya maiyasa kike haka wai? Ko kin manta sauran wata hudu Hakim ya matu.”?…. “Duk da haka Kilishi ba zan bari Hakim ya auri Gimbiya Hikimatu ba, bayan ga Hamad yana numfashi, shima fa Hamad mutun ne kamar Hakim yana bukatar mace kusa dashi.”
“Nasan da haka, amman ni kibarsu suyi auren su sai itama aje wajen Turmurturs ya bamu maganin da ya bada aka sama Hakima cikin abinci kinga shi kenan ba ita ba haihuwa idan Hakim ya mutun sai ta gama gabanta kinga daman bata haihu balle muga bakin ciki,amman kiyi tunani Gimbiya.”?
“Shikenan Kilishi zan hakura na bi shawararki anayin auren zan je na anso maganin dan yanda na hana Hakima ɗaukar ciki cikin gidan nan haka zan hana Hikimatu ɗaukar ciki,ba dai sunga auren Hakim ba, to har su mutu basu ganin jinin Hakim.”
Ohi nace Gimbiya Zulaha sudai suna mantawa da Allah, basu tunanin kafin wata hudun su su mutu????.
“Hakima Fulani nasan ganinki yanzun, “Maryama yanzun da safen nan.”?
“Eh haka tace dai kizo yanzun, “to shikenan, amman ban dafa mana komai ba dan wallahi dan daɗe da tashi ba wanka kawai nayi, “karki damu Yaya Hakim ma yana shashen mu wajen Fulani tun safe daman yace baki tashi bacci ba da tuni nazo na kiraki, “to mu tafi Maryama.”
Haka suka tafi tare shashen Gimbiya Fulani, amman da kaga Hakima kasan tana cikin damuwa ko bata faɗa ba , amman Hakima ta ɗaure dan tunda akace Hakim zaiyi aure bata yi ma kowa maganar ba sai Gimbiya Yakumbo kuma Gimbiya Yakumbo ta kwantar mata da hankali sosai tayi mata wa’azi mai shiga jiki, haka suka isa shashen Gimbiya Fulani, tunda ta shigo Hakim yake kallon ta dan damuwar ta sama kanta har tasa tayi rama dan ta faɗa ba laifi, samun waje tayi kusa da Fulani ta zauna sannan tace, “Fulani ina kwana.”?
“Lafiya lau, Ɗiyata kin tashi lafiya.”?… “Lafiya lau Alhmdulillah, gani kince kina san gani na.”
“Eh Daughter inasan ganinki, tunda Abbanku yayi maganar ƙarin auren da Hakim zaiyi ban sake ganinki ba, Hakima nasan abunda kike ji gamai da wannan auren da Hakim zaiyi ko wace mace dole taji kishi idan za’ayi mata kishiya ko ya take balle ke da kika tashi baki san yanda ake zaman kishi ba tunda Alhmdulillah gidansu iyayanki sun zauna lafiya basu kishi irin na masarautar nan ba zamansu, gaskiya ina san kallar wannnan zaman.”