GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

LOKACINE, TABBAS KOMAI LOKACINE GASHI LOKACIN YAYI MUN GAMA GIMBIYA HAKIMA SAI KU TARENI A SABON BOOKS ƊIN NA WANDA ZASU ZO INSHA ALLAH NGD????
101&110????
Ruɗewa sosai Gimbiya Zulaha tayi, waya ta ɗauko ta kira Hakim ta gaya mashi Gimbiya haihuwa ta zo, Hakim kiran Aliyu yayi suka zo suka ɗauketa sai asibiti, domin ganin anceto rayuwarta ita da abunda ke cikin cikinta.
Bayan sun kai ta asibitin, shidai Hakim kasa tsaye yayi ya kasa zaune dan yana cikin tashin hankali balle da yaga sun kusa aya babu labarin komai tashi yayi kawai yayi alwallah ya shiga massalacin da ke asibitin ya sallah yana rokan Allah ya tada ƙafadun matarshi lafiya, cikin ikon Allah Hakim yana cikin sallah sai ga Hamad yazo yana sanar dashi haihuwar Hakima, duk farincikin da yake cikin sai da ya gama sallah ya ƙara godema Allah sannnan ya tashi ya bi bayan Hamad suna zuwa suka shiga direct wajen Hakima ya wuce bai tsaya tambayar abunda aka haifa ba shidai so yake yaga Jewel ɗinshi wani hali take ciki, yana zuwa ya kama hannunta yana mata sannu, kallonshi tayi sai tayi murmurshi kawai dan har lokacin bata ida jin ta dai dai ba, tsugun nawa yayi yai mata kiss a goshi sannan yace, “Allah yayi maki albarka Jewel, Allah ya saka maki da mafificin alkhari, Allah nagode maka da ka sauki matata lafiya, tabbas yau ranace ta farinciki a gareni Jewel da ba abunda ya samaiki ina godiya ga Allah(SWT).”
Kallonshi take wani sonshi ke fisgarta tabbas tayi dacen miji da kowace mace take da burin samu a duniya, duk wani qualities da ake so namiji yake to Hakim ɗinta yake har ya wuce wajen, riƙe hannunshi tayi tace, “Mijina abun sona ina alfahari dakai Angle, inasonka ina kaunarka, fatana Allah ya raya mana abun da muka haifa.”….. Sai da tace haka ya tuna ashe ma baiga mai aka haifa ba cewa yayi, “Jewel fatan dai mace kika haifamana mai kama dake ko.”?… Kallonshi tayi tana mamakin tambayar shi sannan tace, “kana nufin bakaga kyautar da Allah ya bamu ba.”?
Shafa fuskarta yayi sannan yace, “hankalina baya jikina, yana wajenki lafiyarki itace lafiyata, kece rayuwata idan na rasaki bansan ina zan sa kaina ba Jewel, na safa’a na wutosu parlour na wuto nan domin naga lafiyarki,amman yanzun zan tafi na gano su.”
“Ba sai ka taso ba gasu nan mun biyoka dasu.”…. Gimbiya Zulaha take cewa haka fuskarta kunshe da farinciki dan ji take kamar Hamad ne aka haifarma yaran, dan yanda take jin Hamad a zuciyarta haka take jin Hakim da Humad suma, taso yayi yana kwantar da kanshi bisa ƙafaɗarta sannan yace, “wallahi Gimbiya na rudene shiyasa ban tambayesu ba.”… “Eh ai dole ka rude, kai mai mata ko? To mu kuma masu jikoki.”… “Wai kike cewa jikoki ni ɗaya na gani kuma gashi nan a hannunki bani na ganshi ma.”… “Wa ya ce maka ɗaya ne? Maryama ku shigo.”Gimbiya Zulaha tace tana dariya nan su Maryama suka shigo da yara guda biyu a hannunsu dan maryama ta ɗauki ɗaya Sadiya ma ta ɗauki ɗaya sai ɗaya a hannun Gimbiya Zulaha, ja da baya Hakim yayi, sujada kawai yayi yana godiya ga Allah da ya bashi wannan kyautar dan yasan ba wayaunshi ko dubararshi ba ta bashi wannan kyautar, hawaye ne sarkar a idanunwanshi Gimbiya Zulaha ta fara goge mashi hawayen tana cewa, “Hakim ba kuka zakayi addu’a zakayi masu kasa masu albarka, Allah rayaiyune masu taimakon al’umma kuma mahaddata quri’ani mai girma.”
Kai kawai ya girza mata sannan ya anshe su ɗaya bayan ɗaya maza biyu sai mace ɗaya, hudiba yayi masu sannan ya sa masu albarka.
Ta haihu da kwana ɗaya suka dawo gida, sheshen Gimbiya Zulaha dai aka sauke ta ita ke mata wanka dan kula ta musanman Gimbiya Hakima take samu wajen Gimbiya Zulaha ita da yaranta, ranar suna yaran suka ci sunan YARIMA JALALUNDEEN shine Hassan sai YARIMA JAMALDEEN shine hussaini sai GIMBIYA JALILA itace Gambonsu ta ukkun kenan.
Bayan suna da sati ɗaya aka fidda Gimbiya Kilishi kasar saudia dan nema mata maganin haukan dake kanta, ita da Gimbiya Fulani Kubrah suka tafi aka bar Gimbiya Zulaha tana kula da gida ta kuma fara shirye shiryen bikin su Maryama.
Tunda su Gimbiya Kilishi suka tafi saudia aka fara shirin biki dan Gimbiya Zulaha zagewa tayi tana gyara amaran nata harda Hakima itama mai wanka dan duk abunda aka basu Maryama sai anba Hakima itama dan danan suka chanza saboda gyaran dasuke sha ba yau ba gobe, Hakima ta chanza ta zama babban mace dan jegon ya ansheta tayi kyau sosai komai nata ya ƙara fitowa kuma bata shan takurar Hakim saboda yana fada bai dawowa sai dare kuma yana zuwa Gimbiya Zulaha taga zai takura mata zata korashi a haka akai tayi har tayi arba’in, kamar yanda al’ada take haka Gimbiya Zulaha ta shirya ma Hakima komai ta sa harda su Maryama suka tafi kano yawon arba’in, taga kokarin Hakima tunda akayi bikinta ba ta sake zuwa gida ba, sai da zata yawon arba’in, aiko Hakima tayi murna sosai dan sai da sukayi faɗa da Hakim wai tana murna zata tafi ta barshi bata ko tausayinshi haka dai suka rabo wai yana fushi da ita, tafiyar su itama Gimbiya Zulaha ta shirya ta tafi Dubai dan haɗo ma su Humad lefe da kuma yin kayan ɗakin su Maryama.
Sai da sukayi sati ɗaya sannan suka dawo, gida kwana ɗaya tayi a shashen Gimbiya Zulaha ta haɗa komai nata aka maidata shashen ta dan Gimbiya Zulaha ta fahimci idan bata maida ma Hakim Hakima ba to ya kusa shima ya haɗo kayanshi ya dawo shashen ta shiyasa ta bashi mnatarshi can su gane tunda daman ta gama komai ya dace ayi ma Hakima, ranar da ta koma Hakim yasa doka a fada ko wani lokaci Sarki yana iya tashi yaje yaga lafiyar iyalanshin, sannan ba kullun zai ringa zuwa fada ba, randa bai samu damar zuwa ba Hamad ko Humad suna iya zama bisa kujerar suyi duk abunda ya dace ba dole sai shi ɗaya ba zai kama hawan kujera ba, kowa yayi na’am da dokar Hakim daman fadawan duk sa’in ninshi ne shiyasa.
Koda ya tashi daga fada yana dawowa gida ya tadda tana ba Jalalundeen nono shi kuma Jamaldeen yana kuka wai shi a dole sai ta dai na ba Jalalundeen ta bashi bayan bata daɗe da bashi ba amman da yake Jamaldeen yana da rigima shine yake yi mata kuka, ita ko Jalila wasanta take dan su duka sun fara rairafe ga wayou dasuke dashi masha Allah, yana shigowa ya ɗauki Jameldeen yana cilawa sama yana yi mai wasa, nan aka samu yayi shiru, Hakim ya tambayeta abunda tayi mashi har yake kuka, “Jewel kinsan bansan kukan Jamal ko.”?… “Angle wallahi bansan ina Jamal ya kwaso wannan halin ba, ace yaro bai san gaskiya komai sai dai ace shi ɗaya za’ayi ma? Yanzun nagama bashi nono, daga yaga na fara ba Deen shine fa ake wanann kukan.”… “Ai ba kyaleshi zakiyi ba Jewel lailashin shi zakiyi ai.”.. “Nace yayi shiru fa.”.. “Ko.”? Abunda yace mata kenan ya cigaba da lailashen Jamal sai dai yayi shiru sanann ya sauke shi ya ɗauki Jalila da take wasanta ba ruwanta da rigima, wasa ya cigaba da yi mata tana dariya, bayan ta gama basu nonon suka shiga ya taya ta yi masu wanka sannan suka yi masu shirin bacci, suna gamawa Gimbiya Zulaha tayi aike a bata yaran dan wajenta zasu ringa kwana haka suka bada yaran aka tafi dasu shashen Gimbiya Zulaha, bayan tafiyar su ya ɗauke ta bai sauke ta ko ina ba sai toilet cikin kwamin wanka nan shima ya shiga zasuyi wanka, kissing ɗin juna suka fara sai da suka gama dan taɓai taɓainsu sanann sukayi wanka suka fito, Hakim da kanshi ya shirya ma Hakima sannan shima ya shirya ya ɗauke ta sau bisa gado yayi mata rumfa ya fara aika mata sakonninshi masuwuyar fassarawa wanda suke sa Hakima ta manta da wacece ita, koda naga abunda ya fi ƙarfina na haɗo yan kafafuna nace su Sarki Hakim asuba ta gari.