ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Bayan sallan isha tana zaune gaban madubi tana kallon gashinta yanda yawani kwanta kaman tasa shamfo taji Baba ya kwalamata kira wanda tuntuni take jiran kiran, tashi tayi tadau hulanta tasaka sanan tawuce ahankali take saukowa kowa na falon, gaban baba tazo kaman ta Allah ahankali tace “Baba gani” wayanta yadauka yamika mata sanan yace “ki shirya gobe kije school in Allah yakaimu” kallon fuskan Baba tayi cikeda farin ciki sanan tasa hannunta ta karba tana murmushi sosai tama kasa magana tsabagen murna, hararanta Mama tayi tace “kagamin yarinya bazaki godiya ba ko saini na kwace” dasauri tace “Baba nagode thank u, world best Baba” sanan tajuya takalli Maheer gwalo tamai tareda nunamai wayan zaiyi magana Mama tamai alamu daya shareta Manaf da wayanshi yahau kara ganin Aisha akan screen din yasa Mu’az yace “uhum’uhm” amugun kunyace yatashi yadauki wayan su Baba sukai kaman basusan meke faruwa ba yawuce yafita.
???? ALKAWARIN ZUCIYA ????

   ✍???? M SHAKUR

1️⃣3️⃣

WARAKA TEMPLE gidan maganin kowacce irin cuta da izinin Allah
Karin niima da dadi
Karin dandanonki da duminki
Matsewarki ki dawo yar Sha shida
Gyaran nono
Sa megida sambatu
Sa kyauta
Maganin Sanyi
Da sauran magungunan damuwar da ke addabar mata zaku samu a waraka temple ku tuntubemu a no waya ko Instagram. Don magana dasu directly click on this link

wa.me/+2347042419516

Yau dayake Monday sunada lectures 9:00 wuraren 8:00 tasauko ta sanya wata Dubai gown sky blue dayama skin nata bala’in, sai uban sheki fuskanta yake ka kalleta saika juyo kabata second look, yau flat shoe tasaka baki sanan tadauki black bag shima, tana tafiya tana duba jakanta taga ko tasaka komi dan lecturer su na safen nan shege ne ajinshi you must jot inba hakaba yakadaka waje yace “you are not ready for school” Tundaga stairs take kallon Mama dataga tana zaune dinning takife kanta a table which is not like normal Mama, dasauri takarasa wajen dinning din takai hannunta ta taba bayanta tace “Mama” dasauri Mama ta tashi zaune idanunta sunyi ja irin name mugun zazzabin nan kafinma tai magana Khairy tarigata tace “Mama bakida lafiya ne jikinki zafi” dan zaro idanu tayi takai hannunta tana taba jikinta tace “bawani zafi daga AC kika fito Niko dana gama da kitchen ba dole kiji jikina yay zafiba, zo zauna kiyi break kitafi school” kujeran kusada Mama tazauna ahankali tana kallon fuskanta dan bata yardaba, Mama ta tashi tareda daukan plate tace “kici masa sabida yarikeki” tai maganan tana zubamata sanan ta tura gabanta tace “Oya Oya eat” fara ci tayi tana kallon fuskan Mama data daure iya daurewa, ahankali ta hadiye masan bakinta tace “Mama nakawo miki paracetamol kisha kinga kar zazzabin ya kwantar dake” dan shiru Mama tayi tana kallonta ganin dukta damu yasa ahankali tace “to naji zansha amman dakaina zan dauka Nasha ke yanzu kici abinci kitafi school yi maza ina kallonki” murmushi tayi sosai har ranta tace “yauwa Mama, world best Mama, har hankalina yatashi, wlh Mama ko tari banso naji kinayi balle ciwo sai inji komi bayamin dadi” dan dariya Mama tayi tanaji kaman zatai kuka amman ta daure tace “Malama eat bance kitasani agaba da surutu ba, Ummulkhairy aku” dariya tayi bata kara cewa komibaharta cinye kafinma tai motsi Mama tamikamata ruwa a cup, kallon fuskan Mama tayi sanan tai wani kalan murmushin dadi tace “Mama ya akayi ki kasan ruwa zan dauka” bata kofin Mama tayi tace “sabida ni Maman kine, angayamiki just like that naci wanan sunan world best nabakin ki” wani kalan washe hakori Khairi tayi sanan ta shanye rawan ta tashi tazo kujeran Mama rungumeta tayi tabaya tace “Mama natafi, I love you kinji, Mama karki je ko’ina please, koma zaki fita ki jirani nadawo saina rakaki mutafi tare” murmushi Mama tayi tadaga hannunta tashafa kanta tace “naji, a dawo lpy, banda rashinji, banda kula maza Umma, banda rashin kunya” sakin Mama tayi batare data amsaba tafice daga falon da sauri ganin 8:30, Mama na zaune inda take tana kallonta ta window harta shiga mota mai gadi yabude gate driver yafice da ita.

Ajiyan zuciya tasauke ita kadai tasan metakeji ajikinta, jin tafiyan Baba datun bayan yay breakfast yatafi sama shiryawa dan yau ba aiki zashiba asibiti zaikaita yasa tadaga idanunta takalleshi, hada idanu sukayi dawani kalan sauri ya shiga saukowa daga stairs din yace “wife, ur……Han…..hancinki” yay maganan yana karasowa gabanta ganin jini na gangarowa daga hancinta, dasauri tace “hanci na” takai hannunta ta taba jin abu na gangarowa kafin tadawo da hannun gabanta ganin jini yasa tace “laaa banma saniba” cikeda karfin hali tamike tsaye wani irin mahaukacin jiri yadibeta tai baya dawani irin sauri Baba yatarota tafado jikinshi a sume, daidai lokacin Manaf da Mu’az na shigowa falon cikin shirin zuwa office, ganin Mahaifiyarsu yasa dasauri sukai wajen kafin ma suyi magana Bana yace “Manaf daukomin mayafinta afalo mutafi asibiti, Mu’az get the car” dasauri Mu’az haryana bigewa da centre table yafice waje shikuma Manaf yay sama, har gaban flat din Mu’az yakawo motan sanan yadawo ciki atare dukansu suka dauki Mama sukai mota da ita bata Baba yashiga da ita, Mu’az da Manaf suka shiga gaba sanan suka fita gida.

Wani Babban private hospital sukaje, suna shiga aka karbe Mama sanan akasasu tsayawa awaje, zama Baba yayi da kusan yamafi yaran nashi damuwa, ahankali su Manaf suka zazzauna kusada shi babu iyacema wani kala idanunsu sunyi jajir, suna zaune awajen na kusan 2hrs sanan saiga Dr wanda yake abokin Baba yafito, Baba dagashi harsu Manaf na ganinshi duk suka tashi, kallonsu Dr yayi sanan yace “Alhaji follow me” binshi Baba yayi yay tafiya kusan biyu sanan yajuyo yakalli su Manaf dasukai zuru zuru yace “let’s go” dasauri suka biyoshi abaya har zuwa office na Dr, zama Dr yayi sanan yanunama Baba sit ya zauna sukuma su Manaf duk suka taaitsaya kowa kallon Dr yake with hope koma yayane abasu goodnews, lumshe ido yayi ahankali sanan yabude yace “Alhaji ayanda kuke kallona dagaku har yaranka I wish zan iya gayamuku abinda nasan har cikin ranku shi kukeso kuji, I am sorry I don’t have that sai akasin haka, condition din matarka has become worse da ayanzu riketa a asibiti yama kamata muyi muna bata yan taimakon dazamu i……” kasa jiranshi Baba yayi yakarasa sabida yasan menene zai fadi, cikin wata kalan tsinkakkiyar murya dake cikeda sanyi jiki dakuma lack of hope yace “how long does my wife have?” Kallonshi Dr yayi dan baiji Baba nason yaji Wanan amsan tambayan ba amman ganin kalan kallon dayakemai na ya shirya ji yasa ahankali yace “less than a month” hawaye Manaf yaji yazomai dasauri yajuya yafita daga office din, bayanshi Mu’az yabi da sauri yana goge hawayen dayazubomai, shiru Baba yayi kafin ahankali cikin wata kalan karyayyiyar murya yace “kasan dai kai ba Allah bane ba ko likita dazaka gayamin matata nada less than a month to leave” shi kanshi Dr ya bala’in tausayama Baba cus idanunshi sunyi jajir, cikeda lallashi yace “Alhaji listen to me, niba Allah bane, Allah shine masanin gaibu, kawai ina maka discribing lokutan datake dashine base on science, cells dinta sun soma shutting down daya bayan daya, I am just preparing you ne for the worst, you have to be strong ma yaranka, sabida ayanzu they’re looking up to you, ka dake sanan ka koyamusu sudake, kanunama matarka so da kauna sama da da, karku dinga kuka agabanta koku dinga nunamata damuwa, hakan zai saukaka mata abubuwa da dama, ganinku cikin damuwa da rashin walwala shi zai karamata damuwa da zafin ciwo, dan haka Alhaji I am giving you Wanan chance din cry as much as u want now, after yanzu baka kara kuka ko nuna rashin kwazo sabida yaranka” kaman jira Baba yake ahankali hawaye suka shiga kwararowa daga idanunshi, tissue Dr yadauka yabashi karba yayi dasauri yakai kan idanunshi yana sharewa cikin wata kalan murya dake sosarai yace “I don’t want Maryam to leave me, naso mu tsufa tare sanan mu mutu tare, why are you doing this to me now Eh Maryama diyar albarka” saukan da kanshi las Dr yayi yana sauraron Baba yakai kusan minti 15 ahaka sanan ya share fuskanshi tass da tissue Dr yanunamai bathroom yashiga ya wanko fuskanshi yafito yama Dr sallama yafice zuwa dakin Mama ganin su Manaf tareda ita tana bacci ana mata Karin wani abu kaman yellow madara yasa yafito, zama yayi a kujeran gaban dakin sanan yaciro wayanshi number dayay saving da Amini yay dialing, ringing daya aka daga cikeda barkwanci irin na manya yace “badai kahanamin yarinya zuwa makaranta ba” dan murmushi kadan yayi sanan yace “jikin Maryam yatashi muna asibiti Baffa” anatse daga dayan bangaren akace “Subhanallahi, turn d car Bala muje asibiti” kawai aka katse wayan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button