ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp

This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️
5️⃣5️⃣

Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.

wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp

This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️

Dawani irin gudu tai kanshi tana kuka sosai, hannunta takai tadaura akan fuskanshi tana bubbugawa ahankali tace “Ya Aliyu dan Allah katashi, Innalillahi mena maka haka, Ya Allah kaduba zuciyata I don’t want wani abu yasami Ya Aliyu” jin baya numfashi yaki farkawa yasa tamike tsaye tashiga kalle kalle adakin kozata ga ruwa amman ko alamun ruwa batagani ba wajen kofa tayi ta murda ina yaki budewa saitasa password kuma batasan mene ba, dawowa tayi hankalinta ya bala’in tashi tazo jijigashi tashigayi tana kuka. “Ya Aliyu katashi dan Allah katashi kaji Ya Aliyu” mikewa tsaye tayi tama rude tana juye juye tarasa maizatayi hannu tasa tazare dan kwalin kanta ta warware dasauri sanan tashigamai fifita dashi da sauri da sauri tanamai addu’a.

Almost 5min tadauka tanamai fifita sanan ahankali taga idanunshi na motsi hakan yasa ta tsayar da fifitan datakemai tana kallon fuskanshi daga tsaye datake akanshi gently yabude jajayen idanunshi yadaurasu akanta all kalaman data gama fadamai suna dawowa kanshi zuciyanshi da kirjinshi namai wani irin ciwo kaman ana kona garwashi acikin kirjinshi wasu zafafan hawaye ne suka fito daga idanunshi suka gangara gefen idanunshi yana kallonta motsi datagani yayi da bakinshi dan yanda kirjin kemai zafi baijin zai iya wani ihu ba dawani irin sauri tai kneeling kusada shi takai kunnenta saitin bakinshi tana sauraron meyake fadi, cikin wata kalan raunanniyan murya yace “I hate you Ummulkhair! Na tsaneki with every bone and flesh na jikina, I regret the day I ever told you ina sanki! Nayi daman saninki arayuwana, I regret knowing you and even spending time with you, Ummulkhair Muhammad I Aliyu Hydar Abdullahi Abdulwahab hate you with every drop of blood na jikina!” wasu kalan hawaye taji sunzo mata amman tadaure ahankali tadago da kanta tajuyo takalleshi gani tayi yadauke kanshi yakalli gefe yana cijan lips dinshi kana ganinshi kasan wani abu kemai ciwo, ahankali yace “the door password is Pickle open and go back home” jitayi jikinta kaman yay kankara takasa ma wani kyakkwaran motsi daga inda take takai hannunta kan bakinta ta taushe sabida kukan datakeji tana kallonshi ganin yanda Aliyu ya tsaneta duk wani soyayya dayake mata ya rikida yakoma kiyayya bamayason yakalli fuskanta kaman ba Aliyun taba. “Leave from here!” Yadaka mata wani irin tsawa yana kama kirjinshi da karfi yana wani irin nishi, ahankali ta tashi jikinta narawa sosai tana kuka mara sauti taje gaban kofan danna keyboard din tayi tasaka pickle tana sakawa kofan yabude fita tayi sanan tajawo kofan tarufe ta tsugunna agaban kofan tana wani irin kuka mai bala’in tsuma rai, kaman tai hauka takeji, ita kanta batasan tanason Aliyu hakaba saida ya furta mata he hates her jitayi her whole world is crippling before her eyes, ahankali tadaga hannayenta sama hawaye na zuba daga idanunta. “Ya Allah na, Ya ubangijin al’arshi ubangijin sammai da kassai, Ya Allah kai kadai na yarda dashi, Ya Allah kaga zuciyana all I am doing is bin umarnin iyayena, Ya Aliyu is suffering” tai maganan tana wani irin fashewa da kuka kafin ahankali tace “Ya Allah yau ina gabanka I am even confuse on what to ask you and what to pray for all I know is addu’a kawai nake amman bansan na miyeba, Ya Allah kaduba lamarina and solve this problem for me domin ko babu abinda yafi karfinka kaine Azza Wajal” tafashe da kuka takasa tashi ta tafi dudda yabata chance din dan bazata iya tafiya tabarshi ba.

Da kyar Aliyu ya iya ciro wayanshi daga aljihun gaban riganshi ya kunna, ko kadan baya gani da kyar shidai baisan ya akayi yama kira number Dad ba kawai daura wayan yayi a kunnenshi ringing daya Dad yadauka arude cikeda tashin hankali Dad yace “Aliyu where are you? Aliyu don’t do anything stupid dazakazo kayi nadama nan gaba, dan Allah kafadamin inda kake”? Murya chan kasa Aliyu yace “security post Dad come and get me” wayan yafadi daga kunnenshi Dad na hello hello amman shiru wani irin gudu Dad yakara amotan babban abokinshi Dr Sani yace “yagaya maka inda yake” gyadamai kai Dad yayi yana tukin cikin minti 10 suka iso wajen, ganin mota yasa Khairy ta tashi tsaye dasauri tana share idanunta dasukai jajir, bude kofa Dad yayi da Dr Sani suka fito yana binta da kallo saukarda kanta kasa yayi yakarasa gabanta anatse yace “Ummulkhairy kiyakuri I apologize on my son’s behalf” kasama cema Dad kala tayi sabida kukan dake zuwan mata Dad da Dr sani suka shiga dakin bayan Dad yasa password din tana tsaye wajen, ko 5min basuyi ba taga sun fito da Aliyu kaman wanda yamutu dawani irin sauri tazo wajensu tana kuka tace “maiya sameshi” sashi amota Dr Sani sukayi suka rufe sanan yabama Dr Sani car key yace “go to hospital with him bari namaida Ummulkhairy gida zan biyoka abaya” gyadamai kai Dr Sani yayi sanan Dad yakalli Ummulkhairy yace “let’s go” wajen motan Aliyu sukayi suka shiga Dad yatada wayan, wani irin kuka tahauyi cikin kuka tace “Abba I am sorry, dan Allah kuyafemin, dan Allah kuyafemin” dan murmushi Dad yayi yana tuki yace “kidena kuka Ummulkhair, non of this is your fault, Aliyu will be okay, muje namaida ke gida hankalin iyayenki ya kwanta stop crying now” umarnin Dad tabi ta share fuskanta, ana kiran sallan magrib sukakai gidan, kowa na tsakar gida dan Dad yariga yakirasu yace musu gashinan zuwa da a Khairy, parking yayi sanan yafito Khairy itama ahankali tafito kowa na binta da kallo barinma Zayn da idanunshi sunyi jazur yana kallonta tundaga kasa har sama, dawani irin gudu tai wajen Baba fadawa jikinshi tayi cikin wani irin murya tace “Baba Ya Aliyu zai mutu, he’s very sick Baba, an wuce dashi asibiti, Baba idan Ya Aliyu yamutu because of me yaya zanyi da rayuwana” alamu Baba yamata datai shiru sanan yakalli Anty Mariya hakan yasa tazo ta karbeta tawuce da ita ciki.

Hannu Dad yahada duka biyun yana kallonsu Baba yace “dan Allah ku yafema d’ana abinda yamuku yayi bala’in kuskure” hannunshi Baffa yakama yana girgizamai kai cikeda kulawa yace “Ya jikin Aliyun”? Dan murmushi yayi yace “he will be fine asibitin zan tafi yanzu saida safen ku” gaggaisawa yayi dasu Baba sanan yawuce motanshi kowa yabishi da kallo haryabar gidan sanan Baba yasauke ijiyan zuciya yace “Alhamdulilah muje muyi salla” wucewa sukayi dukansu Zayn na juyowa yana kallon gidan, suna idar da salla yafito daga masallacin batare daya jira kowaba yataho gidan.

Direct sama yawuce sanan ahankali yay knocking tareda bude kofan yana sallama kasa kasa hada idanu da Anty Mariya dake zaune bakin gado tana juya mata tea data hada mata, ganinshi yasa ta mike tsaye tace “Zayn kaine tana bayi wanka take” Gyadamata kai yayi batare dayace mata komiba, ahankali itama Anty Mariya ta ijiye tea sanan tazo tabi tagefenshi tawuce tafita daga dakin tareda rufomusu kofa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button