ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Wuraren 10 yau taga kiranshi wayan na gabda katsewa tadauka ahankali tace “Ya Aliyu” ahankali shima yace “Ya muran? Jikinki yadena zafi” gyadamai kai tayi tace “eh yadena naji sauki” dan ijiyan zuciya yasauke kafin ahankali yace “I am sorry for hurting you Pickle, will you forgive me” gyadamai kai tayi tace “bakomi yawuce” dan ijiyan zuciya yakara saukewa ahankali yace “kinada paper ranan Monday” gyadamai kai tayi tace “yes but in the morning” ahankali yace “good, I want to invite you to my promotion stuff zakizo” wani irin murmushi tayi tace “za’ayi promoting naka awajen aiki”? Dan yatsine fuska yayi yace “kind of and I want you to be there for me, ina stage ina ganinki ina murmushi” dan murmushi tayi sosai tace “to baranzo ba” Dasauri kaman dan yaro yace “pleaseeee Khairirin Baba” dan dariya tayi ganin yanda yake tsokanta ahankali tace “okay shikenan zanzo but kaizaka daukamin jakana” dasauri yace “zanma goyaki like my baby idan kinas..…..” katse wayan yayi dasauri jin alamun mutum tsaye adakinshi, dago kanshi yayi ganin Abba tsaye yana sanye da jallabiya ya rungume hannunshi yana murmushi yasa yaji wani kalan kunya, daman abinda yasa baije wajen Abba ba sabida yay wasu manyan baki ne, patient dinshi saisa baije ba.

Ahankali Aliyu yatashi zaune daga gadon kasa kallon Abba yayi dan murmushin da Abba keyi kadai ya tabbatarmai da yaji all maganan dayake da Ummulkhair, akunyace yace “Abba bakin sun tafi” dan murmushi Abba yayi yamaida kofan yarufe sanan yashigo dakin har zuwa inda Aliyu yake zaunen sanan yazauna agefenshi, ahankali yace “Aliyu so kanada yarinyar dakakeso haka baka sanar dani ba” kunya yasakeji ganin yakasa magana yasa cikeda kulawa Abba yace “what’s her name”? Ahankali murya chan kasa Aliyu yace “Ummulkhair” dan murmushi Abba yayi yadade yanaso yaga Aliyu yayi aure amman ko budurwa Aliyu baidashi, daurewa yayi yay hiding farin cikin shi karya nunamai yace “yaushe zamuje mu nemamaka aurenta”? Dan murmushi yayi dashi kanshi Abba saida yaga murmushi hakan yakara tabbatarmai da yanda Aliyu ke sonta sanan yace “inaso dama takarasa gama school ne Abba” ahankali Abba yace “nan da kaman yaushe kenan” ”sauran mata just one semester, Accounting takeyi” gyadamai kai Abba yayi saikuma yatashi tsaye yana kallonshi ganin yanda har yanzu yakasa hada idanu dashi, cikeda tsokana yace “bari natafi nabarku kucigaba da soyayyan ku, anyway greet my daughter in law for me” dan dariya yayi Abba yawuce yafita ranshi fess. Kiran Khairy yakarayi sai after 1 sanan sukai sallama.

Yau Monday wuraren 12 tadawo gida dan 11 tagama paper ta na yau, tanacin abinci tai bacci dan 4 zata wajen ceremony na karin girman Aliyu.

4 ta tashi agurguje tashiga bayi wanka tayo tana fitowa tai salla sanan tashiga shiryawa cikin wani embroidery exclusive atampa, gold and red, an mata dinkin doguwan riga A-shape dayay mata kyau, dan kwalinshi ta daura dayay kyau akanta sanan tadauki wani simple red veil tasa kafin tadauki wani warwaron zinare ta tasaka da dankunnen zinare mai kyau sanan takalli kanta a madubi kwalli tadauka tasaka ma manyan idanunta kafin tashafa man baki, wani takalmi mai tudu tasaka red, sanan tadauki gold jaka tahada sake kallon kanta tayi amadubi tai wani irin kyau kaman amarya, dan murmushi tayi sanan tafito tana kallon agogo 4:40, sallama tama Mom da sunan zata gidansu sanan tawuce Adamu yadauketa she wants to get a gift for him is his promotion and banda hakama bata taba bashi anything ba, hakan yasa tacema Adamu yakaita wani Men’s boutique.

Shigatayi ciki tana kalle kalle kayan maza ne awajen babu abinda babu gaban wani Jaguar special edition watch tana kallo, yanda take kallonshi yasa mai shagon yadauko yabata murmushi tayi tace “how much is it”? 359k, gyadamai kai tayi sanan tazabi wani bakin sunglasses dayamata kyau shima designers product na police shikuma 156k sanan taciro ATM card dinta tabiya, indai kudi ne tanada shi, every month tun suna yara Baba nabasu monthly allowance, yayyinta nabata kudi just like that, Mama ma nabata kudi, Baffa shima every month saiya bata kudin break dan haka yake kiran kudin, banda random kudin datake samu every now and then bata kashe kudi tanada komi, wrapping everything aka mata sanan tasa aka rubutamata congratulations a paper tag aka makala jikin cute bag din sanan tafito tashiga mota suka tafi wuraren 5:15 sukakai wajen, tana rikeda abin tashiga wajen bayan tanuna IV dinta daya turamata awaya, wajen yacika makil baya tasamu tazauna tana kallon stage lokacin ana decorating Aliyu ana karamai stars a uniform nashi murmushi tayi tahau tafi, yayi wani irin kyau kaman bashiba, bata wani dade da zama ba aka gama abin Dj yasa waka, gani tayi Aliyu ya sauko daga stage din yafara tafiya dudda ana tareshi ana gaisawa dashi but idanunshi nakanta chass, ita bama tasan yaganta ba sai yanzu dataga yana kallonta dauke kai tayi daga kallonshi ganin yanda mutane ke kallon inda yake kallo tahau wasa da yatsunta chan kuma taciro wayan ta daga jaka tana daddannawa. “U look beautiful Pickle Anya zan iya jira kigama school kuwa”? Taji muryanshi akanta, dan turobaki kadan tayi sanan takalleshi ganin yanda yake kallonta yasa akunyace tadau bag dinshi tamikamai murya chan kasa tace “congratulations” wani irin kallon cute bag din yayi sanan yay murmushi yasa hannu yakarba yace “Pickle got me gift, I promise dazaran nakoma gida shi zan fara budewa thank yo….” Bai karasa maganan ba jin wayanshi na ringing zaro wayan daga aljihu yayi yakalli screen din sanan yamaida kafin yakalleta yace “come muje lemme introduce u to some people” makemai kafada tayi ahankali tace “ni kunya nakeji kabari natafi” dan hararanta yayi yace “kokizo muje Kona daukeki wlh” dasauri ta tashi daga kan kujeran tana turomai baki, murmushi yayi yace “muje gimbiyar Aliyu” jerawa sukayi atare yana kallonta ganin yanda take bin wajen da kallo tayi kyau ba kadan ba kaman amarya, wajen dasu Gwaggo ke zaune yakaita, Gwaggo da Mami sai Meena da Khadija da Amal ke zaune Abba ne kadai bashi awajen shima bai dade da tafiya ba sabida emergency da aka kirashi for a hospital, ita binshi kawai take har gabansu Gwaggo dabatasan suwaye ba, dukansu kallonsu suke sanan yadan juyo yakalleta ahankali yace “meet my family Pickle” Innalillahi! Tafadi dasauri jitayi zata nitse akasa dawani irin sauri tajuya zata gudu dan bama tasan mema zatayi ba, hannunta ya chapke yanadan dariya cikeda wani irin mugun sonta yace “come back here” wani rin boyewa abayanshi tayi tana jan gyalenta trying to cover her face, sanan Aliyun yakalle su Gwaggo kafin ma yay magana Meena tace “Ya Hydar Anty Khairy ce”?Gyadamata kai yayi sanan yakalli Gwaggo hararanta yayi yace “ga Ummulkhairy nakawo miki kiganta” wani irin washe baki Gwaggo tayi itakuma Meena tashi tayi tazo har bayan Aliyu tawani irin rungume Khairy tace “Anty Khairy oyoyooo please kibari inga fuskanki dan Allah” kafinma Khairy tai magana tashi Gwaggo tayi ta dakama Meena duka abaya tace “ke dalla tashi kibama mutane waje da rawan kai zakija yarinya tafadi bakiga kunya takeji ba, angayamiki irinku ce ita fitsararru muna kallonku kuna kallonmu kuri, Khairiya ta yaki kinji” Gwaggo tai maganan tana kamo hannun Khairy, sakin hannunta Aliyu yayi yana binta da kallo ahankali Khairy tabita still tana rikeda hannun Aliyu dake murmushi dudda shi yasaketa, sosai Mami tabi tundaga hannun nata data rike Aliyu dashi da kallo harzuwa fuskan Aliyu dazata iya cewa bata taba sanin yanama murmushi hakaba sai yau, wani irin kallon yarinyar yakema yarinyar kaman zai hadiyeta, zama Gwaggo tayi akan kujera Khairy kuma tadan tsugunna agabanta sanan ahankali taja gyalen Khairy baya sunnar da kai Khairy tayi kasa murya chan kasa tace “ina yini Gwaggo” wani irin washe baki Gwaggo tayi tace “Allah nagode maka Aliyu wayyo Allah na, yarinya ga ladabi ga biyayya gakuma kunya kagama biyana Hydar, Allah ya tabbatar da Alkhairi, inane gidanku gobe zanzo na nemama jikana aurenki” dagota Aliyu yayi dasauri yana hararan Gwaggo yace “ni bazakije neman mini aure ba hakanan kisa ahanani” Mami yadan kalla sanan yadauke kai yace “ga Mami Pickle” ahankali batare data dagakai takalli Mami ba tace “ina yini Mami” kan Mami nakan waya batare data kalleta ba tace “lpy sannu” Khadija da Amal ne duk suka gaidata suna murmushi sanan yakalli Gwaggo yace “bari narakata sai indawo mutafi” dasauri Gwaggo takara tashi tana warware kullin zaninta tace “bari nabata kudin mota” dariya Aliyu yayi yace “direbanta na waje Gwaggo” “kai wlh makirin yaro ne Aliyu bakin ciki kake zan bata kudi kai bani baka, katon banza kawai andaiji kunya” dariya Khairy tayi kanta akasa, sanan Gwaggo takawo dubu daya tasamata a hannu tace “gashi asaiwa kanne tsaraba ki gaidamin da mamanki kinji” Gyadamata kai Khairy tayi tace “nagode Gwaggo” Aliyu ya harareta irin hararan makwaduwa dinan yace “muje” Meena tace “bye Anty Khairy” bye tamata sanan suka wuce Mami tabi Khairy da kallo tundaga kasa har sama daya tabbatar mata da Yar masu kudi ce, ga zinare a hannunta da kunne atampan jikinta kadai is worth 260k gashi kuma taji Aliyu nacewa direban ta na jiranta awaje, a ina Aliyu yasamo Yar masu kudi haka, iska tadan fuzar ahankali takara kallonsu yanda Aliyu ke kappa kappa da ita kaman Yar Kwai, jitayi zuciyanta namata zafi, “kinga Zainabu kiramin mijinki awayanki bani da kati atawa in gayamai danshi yasami mata ohhh ashedai zanga Auren Aliyu kafin na mutu iyye, kai Allah nagode maka Allah, kiramin imaza” akufule tace “nima banda katin” dasauri Meena tazo wajen tace “Gwaggo inada shi bari nakira” wai Gwaggo kaman zata zare, sabida murDna.
3️⃣9️⃣

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button