ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Har suka shigo anguwan su badaidai takeba yau sau uku kenan tana ganin mutumin nan, saida suka shigo gida tukunna sanan taji wani kalan dadi, parking sukayi sanan tafito dasauri tana kwaso kayayyakin ta tana kwalama Mama kira. “Mamaaaa! Mama nadawo” daga Mama, Baba, Baffa da yayyinta da Hafiz duk suna zaune a falo dan basu dade da dawowa daga asibiti ba babu wanda yama iya wani kwakkwaran motsi, ita tsabagen murna batama lura da Karin mota kan tagidansu ba tai hanyar flat dinsu tana shouting Mama. “Mama nayomiki tsaraba yau nasayo miki ice cream kuma best flavor naki mint ban miki adding any thing ba ayanda kike sonshi plane” tai maganan tana bude kofan falo tana shiga tana kiran Mama. “Maaaam……” kasa karasa kiran Mama tayi ganin mutane a falon ga Mama zaune kusada Baba tana kallonta tana murmushi, hararanta Hafiz yayi yayi yace “inda ace ke kadai keda Mama aduniyan nan Khairy da munsha takaici” cikeda wasa Baffa yace “kagamin d’a kai kanama namiji ka more taka Maman balle ita mace kuma auta, ina tsaraban dakika kawoma Maman bazaki zo kibata ba kin wani tsaya awajen” akunyace takaraso cikin dakin wani irin rungume Mama tayi tana murmushi akunyace ganin duk ana kallonta yasa tadaurama Mama paper bag na ice cream din akan jikinta akunyace ta sauko dagakan jikinta tace “Baffa ina wuni” murmushi yayi yace “diyar Mamanta ya makaranta” ahankali tace “fine” sanan takalli Hafiz tace “Ya Hafiz ina yini ya baby kuma, dan Allah ya Hafiz kasa mata sunana” dasauri yazaro idanu yace “waaaa niii rufamin asiri Khairy sokike y’ata tazama fitinanna irinki” dariya aka hauyi adakin ahankali Khairy tace “Baffa kaga Ya Hafiz ko” kafin Baffa yay magana Baba yace “karya yayi to Khairiya” turo baki tayi kaman zatai kuka Baffa yace “sharesu Yar albarka, sun lashe basusan baiwan dake tattare da sunan ki bane saisa suke magana ahaka” wani kalan murmushi tayi tace “yauwa Baffa” sanan tajuyo takalli Mama tace “Mama kin sha maganin kan yadena miki ciwo muji” takai hannunta tana taba goshin Mama with so much care, gyadamata kai Mama tayi tace “yadena, cikani maza tashi kai ice cream din kisa a fridge kije kiyi wanka kiyi salla idan bakiyi a school ba saiki sauko kici abinshi” gyadama Mama kai tayi sanan ta tashi tana kallon yayyinta dataga sunyi wani iri harzata wuce tace “Ya Manaf kungaji ne haka naga kunyi wani iri, Ya Maheer idanunka sunyi ja kaman kayi kuka” hararanta yayi hakan yasa ta murgudamai baki tawuce abinta sama itama, dayake yana takanshi dayaji ciwon Mama yatashi yau baima biyemata ba.
???? ALKAWARIN ZUCIYA ????

    ✍????M SHAKUR

1️⃣4️⃣

Free page
Wuraren 8:50Am sukakai school. Adamu na parking wajen parking tafito da saurinta bama ta tsaya mai sai anjima ba tashiga sauri cus 9 dot mutumin nan ke shiga aji gashi baya wasa da attendance, tana cikin tafiya zuwa class saiga wasu yammata su hudu sun taho tunda suka ganta sukahau ihun murnan ganinta Khairy nada wani irin farin jini naban mamaki wajen mata, tareta sukayi. “Khairy how far”? Murmushi tayi dake karamata bala’in kyau tace “lpy lau wlh, yanaga zaku waje daban ba class garemu ba yanzu” yatsine fuska sukayi, daya daga cikinsu tace “wlh dabaki wani wahalar da kanki ba wajen class din Mr Okeme ba ba’a taba ganewa ba, ke saurayinki Ahmad celebrity yazo nemanki fa” hararanta Khairy tayi tace “Malama niba saurayina bane kidena hadani dashi, na wuce class nidai” tai gaba abinta ranta abace, daya daga cikinsu ne ta daga murya tace “idan yakadoki meet us a garden chan mukayi” daga murya itama tayi tace “that’s not gonna happen Ladies” tana tafiya wasu another set na yammata na tareta bamata tsaya sauraransu ba tace “I will see u later ladies inada class now” tahau tafiya gudu gudu sauri sauri, duk inda tabi ana kwalamata kira Khairy Khairy waving mutane kawai take tawuce benen dazai kaita ajinsu tana kaiwa yana shiga tana tsaye yana kallonta yaja kofanshi yarufe, ahankali ta yatsine fuska murya chan ciki tace “this wicked man cannot make heaven” sanan tajuya tana kallon kasa daganan bene yanda student kowa na takanshi sanan ta fuzar da iska ita dai ko itace allazi boko bazata taba tsayuwa jikin window har agama 2hrs class ba, tashi tayi abinta tafara tafiya tawuce tana sauka daga staircase abinta tanadan turo baki ita kadai tana kunkunai.
Sabida yanda ranta yake abace taji bamatason tabi normal hanya friends nata suyita tareta da magana hakan yasa tabi ta parking space dan taje garden daga wajen, ahankali take tafiya ita kadai a parking space din tana cikin tafiya a parking space din taji an kwala mata kira. “Khairy” dan tsayawa tayi jim batare data juyoba jin muryan namiji ne ke kiranta, tunani tafara acikin kanta muryan waye wanan sai chan taja wani kalan annoying tsaki tacigaba da tafiya abinta gani kawai tayi ansha gabanta wasu maza guda biyu sunshamata gaba suna sanye da kananun kaya sun bubbude hannuwa irin suna tareta dinan, wani kalan daure fuska tayi babu ko alamun wasa akai tace “me haka” dan dariya sukayi daya daga cikinsu yace “listen to Ahmed mana Khairy yasan bazaki tsayaba saisa yace mutareki” yay maganan suna nuna mata bayanta, juyawa tayi cikeda masifa wani black skin guy ne da dududu bazai wuce mate nata ba in age maybe 20 ko 22yrs haka yake, yana sanye cikin rugget kayan yan iska dinan, crazy baggy jeans da wata babbar baggy riga yayi dying gemunshi zuwa blond color kana ganinshi kaga irin yan iskan yaran nan gashinan very popular aciki school nasu, wani kalan mugun kallo tamai da manya manyan idanunta tace “kai da boys dinka Ahmad should get out of my way” wani kalan murmushi yamata tareda daura hannunshi akan kirjinshi yana shafawa yace “auuch! I love it when you look at me like that Khairy with those ur big big lulu white eyes, Baby my heart only beat for you” spitting miyau tayi agefenta sanan tajuyo takalleshi tace “you disgust me Ahmad, nagayamaka time without numbers stop wasting ur time on me, you are not my type of guy, idan maza irinkane suka cika duniyan nan I rather die banyi aure ba dana aureka, I don’t like you an taba soyayya dole ne” dan takowa sahu daya yayi zuwa gabanta, tsayawa chak tayi tareda kama waist dinta kirjinta na bugawa fat fat, wani mayen kallo yabita dashi barima kirjinta dayaga yacikamai idanu tunba yauba tunda ya lurada yanda Khairy keda boobs yaji yakara haukacewa akanta, dan hucin zafi Ahmad yayi yana kallonta still sanan yanuna kanshi yana bude kafafunshi da tsabagen effizy sun koma kaman boleg yace “look at me kinsan how many babes anan School namu ke kiyamun laili because of me eh? Look at me Khairy, I have money, I was born in wealth, banda haka I am a hip hop rapper number 1 a arewa, yaro mai zamani, har rap nayi da sunanki natura miki a watsapp u don’t even open my chat balle kiji how much I love you, Khairy tell me mezan miki dazaki soni eh, kinga we are the only ones here, just tell me babu kowa don’t be shy Khairy, baki sona don’t u wish to be mine, don’t u wanna make matan makarantan nan jealous ace Kece tawa, I want you to be my Choima while I become your Davido, lemme make you famous, lemme make u a star gurl, what will I do to make you mine baby na? Don’t u want all of this” all maganganun dayake mata jitake kaman tai amai bala’in kyaman Ahmad take bawai he’s dirty bane, kawai dai yanayinshi yanda yake dressing yana shiga kaman wani su wizkid yayi coloring gemunshi da halinshi na waka ita kawai he’s not her spec, yana mata magana yana wani wawware fingers kaman yana rapping yana kama tsakiyan baggy wandonshi, ko kiranshi amatsayin boyfriend nata ma bataso ta tsani taji anyi, bakin ciki da haushin shi yamasa tama kasamai reply kawai tajuya ta gefenshi zata wuce dan sometimes idan abu is really annoying agareki rasama abinda zakace kake, kawai ji tayi yariko hannunta “don’t go baby wait” wani irin juyowa tayi batai wata wata ba kawai ta daukeshi da mari jikake tass! Wani irin ihu abokanenshi sukayi suna waige waige ko there’s anyone there dayaga Marin datama Ahmad dan zai zama abin kunya ance wata tamari hiphop rapper. “Ke celebrity kika mara” fizge hannunta tayi tana kallon yanda yadaura hannunshi kan kuncinshi yana wani irin kallonta da idanunshi dasukai jajir dan marin ya shigeshi, rawa jikinta yafara da sauri tajuya Ahmad daya bala’in zuciya yace “ku bita” jin haka yasa ta kwasa da bala’in gudu acikin parking space din dababu kowa tana kalle kalle, kaman ance takalli right side dinta, hango wani dogon mutum tayi yabata baya Awani lane na motoci yana tsaye jikin wata suv waya a kunenshi da alamu waya yake, wani irin kwana tayi tana gudu tai lane din dayake batai wata wataba tana kaiwa daidai inda yake batai wata wataba tawani zaga ta gabanshi ta shige kirjinshi at once tana boye fuskanta akirjinshi jikinta ko’ina narawa sosai sabida tsoro yanda maza har biyu komatace uku suka biyota, cikin Yar siririyan muryanta that is trembling sosai tace “please save me…..plss…….I’m sca…….” tana maganan tana nishi da sauri da sauri dayake jinshi harcikin fatan kirjinshi don fuskanta gabaki daya na wajen ne, daidai lokacin daga boys din Ahmad din har Ahmad din dukansu sunzo wajen sun tsaya agabansu suna maida ijiyan zuciya sabida gudun dasukayi, One by one mutumin ke binsu da kallo batare daya furta ko a word ba har lokacin wayan nakan kunneshi bai cireba, faduwa gaban Ahmad yayi ganin fuskan mutumin dake kallonsu, ahankali yajuya sadaf sadaf daso samune ko takalmin shi da kasan wajen karma suyi motsin nuna alamun yana moving sanan ya yafito abokananshi da hannu yace “let’s go guys” dasauri sukace “marinka fa tayi Boss” da saurinshi kaman ana hankadashi yawuce yace “shikenan nidai natafi ku ku tsaya” ganin yanda yake tafiya da saurin bala’i tun bayan yaga fuskan mutumin yasa suma sukasha jinin jikinsu suka juyada sauri suka wuce.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button