ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Baba bai bari sun tafi ba sai bayan sallan isha’i sabida su Manaf sun dawo suma duk aka taru a falo anata hira, rakosu duk sukayi Matan Baba nama Khairy tsiyan tasaba alkawari tana bata hakuri sanan tabude mata motan tashiga, Baba sai murmushi yake bude musu gate akayi sanan suka fice Khairy nama yan uwanta bye bye.

Kaman ba itane tagama surutu agidansu ba kaman aku shiru tayi tai lamo akan kujera tana kallon hanya, agaban wani babban waje dataga an rubuta Variety Pot Zayn yay parking, kallonta yayi daidai itama ta kalleshi dan batasan mesukazo yi ananba, ganin sun hada idanu yasa dasauri tadauke kanta, ahankali yace “stay in the car I am coming” maida motan yayi yarufe yashiga cikin wajen bayan yabar motan a kunne dan yabar mata AC akunne, wajen tabi da kallo bata iya ganin komi naciki tadaiga maza daban daban na shiga ciki harma da mata, tabe baki tayi ta gyara zamanta abinta babu abinda kemata dadi data fito da wayanta da yanzu takira Aliyu tamasan ya kikkirata yanzu Mtsww.

Tana zaune shiru almost 30min tacika tai fam sabida yanda ranta yabaci bacci ma harya soma kwasheta sama sama taji anyi knocking kofan motan tareda bude motan gabaki daya dan Zayn bai rufe motan ba dama sabida AC daya barimata a kunne, bude idanunta tayi takalli mazaunin direban dan tama zaci shine yadawo, ganin wani saurayi yashigo ciki kaman an wurgoshi yana sanye da Riga da wando irin rugget dinan yadaura handkerchief a goshi yazauna gakuma wani ta kofan inda take tsaye yana kallonta hannunshi daya rikeda sigari yana busamata a fuska, saikuma taji an bubbude kofofin bayan motan guda biyun wasu maza biyu suma sun shigo sun zazzauna suna rufe kofan back yasa taji kirjinta yabuga da mugun karfi, wanda yazauna mazaunin direban ne yakalleta yace “Madam rufin asirinki shine ki sauka daga motan nan batare dakince ko uppan ba” dudda gabanta nafadi dan tagane barayi ne saida tadaure tace “akanme zan sauka daga motan gidanmu saidai ku ku sauka” hannu wanda yake gaban kofan motan kusada ita yasa zai jawota dasauri tawani irin kwala ihu tareda saka hannunta ta tureshi yay baya tangal tangal zai fadi dan ya kwale sosai, sanan tajuyo na bangaren direban bakinta takai kan shoulder shi tawani irin gantsaramai cizo dayasa ya kwala ihu yana tureta su amman ko gezau mazan bayan suka shiga kaimata duka suna kokarin finciketa ganin tana neman cire ma Oga fata amman taki sakin fatanshi da hakoranta.

Yana zaune yanashan shisha shikadai akujeranshi yanadan lumkunshe idanu dan sosai yasoma bugarda shi kawai jiyayi heart dinshi yabuga at the same time yaji kaman Khairy ta kwalamai kira, tashi yayi dasauri yana kallon agogon shi this is almost 30 minutes daya barta a car shi wlh yama manta da ita, mikewa tsaye yayi dasaurin shi yawuce yafita.

Fincike bakinta nabayan sukayi da kyar daga jikinshi saigata kwaaaa daga namanshi har yadin riganshi abakinta kaman vampire ta tofarmai a fuska sanan suka wani irin jefata kasa kara tayi saida tabugu sosai dan motarshi jeep ce tanada tsayi daidai Zayn nakarasowa wajen dawani irin gudu dayan dake waje yazo zai shiga motan kafin yay one step Zayn ya damkoshi hakan yasa Khairy tamike tsaye da kyar tana ihun security barayi, ganin haka yasa sauran sukaja motan da gudu suka tafi suka bar dayan da Zayn kecin ubanshi ganin karfinshi baikai na Zayn ba ga Khairy na ihun security jama’a barayi gang dinshi sun tafi aka kama shi kuma ya shiga uku yasa yaciro wata yar wukanshi daga bayan wandonshi kaman ance Khairy ta kalloshi dawani irin sauri tazo wajen ko tunani batayi ba wani irin kwalama Zayn kira tayi. “Ya Zayn wuk” juyowa yayi zai kalleta dawani irin gudu ta taho ta tureshi yafadi akasa dan ita azatonta idan ta tureshi barawon zai hakura tunda babu wanda zai chakamawan tana wani murmushi ita adole hero tana kallon fuskan Zayn din gani tayi Zayn yataso dagudu amman ina yachaka mata wukan aciki daidai security da jama’a na zuwa wurin yaron yatafi dagudu security suka bishi itakuma tazaro idanunta atsaye tana kallon Ya Zayn jin wani sharp pain har brain nata jikinta nawani irin bari, ahankali takai hannunta saman cikinta dataji kaman ruwa nabulbulowa nabin jikinta ta shafa sanan tadago hannunta takalla taga jini wani irin baya tayi zata fadi dasauri Zayn yatareta shikanshi jikinshi rawa yakeyi zuciyanshi nawani irin tsinkewa, mutane dasuka taru akansu sukace. “Any Dr anan idan babu akaita asiDbiti”.
4️⃣0️⃣

Dakin Ammin shi yawuce, tana zaune as usual cikin shiga na alfarma kaman matan shugaban kasan Nigeria waya a kunnenta tana waya, kan stool na gabanta kuma fruits ne yankakku da spoon aciki da alamu sha take sai wayan ya tsayar da ita, zama yayi kusada ita sanan yadauki bowl na fruit din nata yafara sha abinshi wayanshi yaciro yana dubawa miss calls yagani like 9 daga number daya shiru yayi yanaji ranshi na baci baisan ya akayi Faisal yabama that Aisha girl number shi ba, bayan yabar Abuja lokacin da Mama tarasu daya koma baima sauka agidan ba hotel yakoma da zama dan he’s tired of yanda yarinyar keep stalking him school gida kaman zata haukace akanshi, he just had sex with once which he paid which infact ma bashi yama nemeta ba, Wanan halin datakeyi yasa kwata kwata bayama neman yaran naija, all babes dinshi achan turawa ne cus sunsan menene sex for fun not sex for attachment, dan tsaki yaja ganin tasake kiranshi ya ijiye wayan Ammi datagama call tace “kai lafiya kana neman fasa wayanka” ahankali yace “Ammi damuna wata mayyan yarinya take ne wlh” dan murmushi Ammi tayi tace “kai haka kakema yammata wulakanci ahaka zaka sami matan kayi aure, danni wlh tasaka zanyi agaba Kwanan nan zakai aure dan bazan barka hakama yaro kanada 36 kana neman 37 ace ba mata ina, akwai ma wata yarinyar kawata danakeso kaje kadubo bakaga yarinyar ba kaman baturiya” ijiye bowl na fruits din yayi yace “Ammi please don’t start niba yaro bane dazaki dinga nemomin mata ba I will get married but lemme take my time baaa rushing ayi aure, I still young bawai tsufa nayiba” tunda yake maganan Ammi ke kallonshi tace “wai kai Son na lura bamaka son Auren nan gabaki daya” murmushi yayi ya kwanta akan kujeran yana daura kanshi kan cinyanta ashagwabe yace “Ammi kaina kaikayi sosamin” hannu tasa cikin soft gashin nashi tana sosamai scalp tace “daga ina kake dan na aika dakinka bakanan” ahankali yana lumshe idanu yace “dakin Mom” tsayarda susan tayi tace “akanme zakaje gaida matan nan ita yaran datake zama dasu bata taba turosu sun shigo sun gaidani ba barinma Wanan mai idanun mujiyan Khairy” shiru yayi yana jinta baice komiba yace “ita tanaso yarana sudinga girmamata ita batasa nata sunyi hakaba” murya chan kasa yace “common Ammi nowww, yaran gidan nan waye baya tsoronki masifanki yasa babu wanda keso yashigo side dinki ya gaidake” ture kanshi tayi dagakan cinyanta tace “ni uwarka kake kira masifaffiya eh” maida kanshi yayi kan cinyanta yace “Ammi ok bazan kara zuwa ba cigaba damin bacci nakeji wlh” yanda takeson Zayn yasa shi kadaine bata iyawa masifa da wanine yau daya shiga uku, cigaba da sosamai kan tayi baidauki cikakken 4min ba yay bacci ahaka, ta tasashi gaba tana kallo ahaka Baffa yashigo side din yana kallonsu murmushi yayi yace “kin sangarta yaron nan dayawa wife” murmushi tayi tace “wai nan lallabashi nake yaje yadubo yar kawata idan tamai mu musu aure koya kagani dan wlh Alhaji na lura Zayn bayason yau aure at all” tunda tafara maganan Baffa yay gim yana kallonta, ganin yanda yayi yasa Ammi tace “tunanin me kake bakace komi ba” dan murmushi yayi yawuce sama sanan yace “idan bayaso karki takuramai” binshi da kallo tayi dan reply din Baffa seems strange, dan tabe baki tayi tace “zaimaje kuma zai sota atoh”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button