ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Ko’ina na dakin takebi da kallo idanunta namata gizo daga taga Mama tafito daga bayi tana mata murmushi saita ganta kan dadduma tana mata murmushi, saita ganta kan kujera tana zaune rikeda littafin zikirin ta saikuma chan taganta kan gado kwance tana mata murmushi, hannayenta duka biyun tadaga takai kan idanunta ta murza idanun da kyau sanan taciresu tasake kallon dakin amman babu kowa ciki dawani irin sauri ta shiga dakin tai bayi budewa tayi dasauri tace “Mama kina ina” ganin babu kowa abayin yasa tadawo dakin tana juye juye kalle kalle bakinta na rawa tace “Mama kina ina”? Gadon tayi ta yaye bargon kan gadon, jini jini datagani a zanin gadon wanda na aman jinin da Mama tadingayi ne yasa taji kafafunta sun kara sanyi kawai tayi kneeling awajen takifa kanta akan gado sai kuka kaman ta kwakulo zuciyanta tayar takeji kukanta sa duk wani wanda zaiji tanayi kuka yake, kowa na falon tunda tafara kiran Mama suka farka amman babu wanda ya iya shigowa yacemata wani abu abar Khairy tai kuka dan ita akama Wanan mutuwan.

Da kyar Manaf ya iya tashi yashigo dakin gaban gadon yazo kusada ita yadaura hannunshi akan bayanta murya chan kasa yace “Khairy stop crying and pray for Mama, kinga tun jiya baki magrib ba balle isha’i, muje dakinki kicire rigan nan shower kiyi salla and pray for Mama, Mama tariga tarasu……” wani kalan ihu tayi da saida gidan gabadaya ya amsa. “Mama bata rasu ba, Mama batada lafiya babu wanda yafadamin, mena muku? Ni yarinya ce dazaa boyemin uwata batada lafiya, nama Mama laifi dayawa bansami dama na roketa gafara ba, nabar Mama agida natafi school nadawo kucemin Mama tarasu, babu wanda yagayamin Mama batada lpy saidai kugayamin tarasu, Mama b…….a…” maganan yasoma gagaranta sabida mugun attack na Asma daya taso daukanta chak Manaf yayi yafito da ita daga dakin yana karban inhaler da Maheer kebashi, Mom tace “please ku kulle dakin nan tadena zuwa ciki” kwantar da ita kan gadonta yayi yasa mata inhaler cus nishi take kaman zata mutu da kyar ta shaka, Mom tashigo dakin takalli Manaf dake kanta tace “tafi Manaf” fita yawuce yayi daga dakin.
2️⃣5️⃣

Almost good 10min na silent ne yacika dakin, at this point Baba jiyayi kaman shima yamutum ne dan he could feel yanda hannayenta suka sassandare ajikinshi kasa koda motsi yayi hakan yasa Baffa yay taking over, daga Baba tsaye yayi, ahankali Baba yasauke kanshi kasa yana kallonta in disbelief, yadade ahaka sanan yakai hannunshi ya kulle mata idanu kafin yaja bargon yarufeta saikawai yazauna akasa dabas baimasan mema zaiyi ba dan he’s still in shock idan ya kalli su Manaf daduk suke kuka saiyaji zuciyanshi yakara tsinkewa, kafadanshi Baffa yakama ya matsa hakan yasa ya fuzar da iska kafin ahankali yasa hannunshi yakamo su Manaf daya bayan daya duka yarikesu ajikinshi kam kam, juyawa Baffa yayi yakalli Hafiz dashima yay mutuwan zaune hakama su Hassan ahankali yace “Hafiz jeka dauko Khairy daga makaranta”
Tashi Hafiz yayi ahankali yafice daga dakin tafiya yake but jiyake kaman iska ke kadashi yana tuna all memories dinshi da Mama shikenan daba danta data haifa ba balle kuma yaranta yaya zasuji.

A famfon gaban flower ya tsaya saida ya wanke fuskanshi tass sanan yakarasa wajen mota shiga yayi yatada motan yana kallon yanda mai gadi ke budemai gate he just wish yanada karfin sanar da su, amman ina motarshi yaja yafita daga gidan zuwa school din su Khairy, har gaban department dinsu yaje accounting yay parking yakai kusan good 20min zaune acikin motan baida courage na facing Khairy, da kyar ya iya gyara mood dinshi sanan yakashe motan yafito yamaida yarufe yana kallon ko’ina kafin ya shiga ciki, Khairy nabashi labarin how popular she is a school so yasan ganinta bazai tabamai wahala ba, wasu yammata guda uku dasuka sauko daga bene yatare yace “hello ladies dan Allah kunga Khairy” daya daga cikinsu ce tace “yanzun nan muka rabu da ita ga ajinsu chan wanchan floor din suna lectures” thanks yace musu sanan yawuce sama zuwa gaban class din excuse yay taking hakan yasa lecturer yafito dan yana ganinshi yasan Wanan baimai kala da dalibin makarantan nan ba, dawowa cikin ajin lecturer yayi yace “Ummulkhair” dasauri Khairy dake zaune ta kwantarda kanta kan table takalli lecturer tace “yes sir” waje yanuna mata yace “ana nemanki” tashi tayi ahankali tana daukan jakanta tafito tana tafiya kadan kadan dan sosai kafafunta basuda karfi ganin Ya Hafiz yasa tabude baki cikeda mamaki takarasa gabanshi da sauri tace “Ya Hafiz mekazo yi a school dinmu”? Hararan ko’ina yayi yay gaba abinshi tana binshi da sauri yace “me zanyi a school dinan naku Baffa yace nakawo ki” dasauri tace “Allah sarki Baffa yana ina tare kukazo kenan” “yana gida” yafadi kai tsaye batare daya juyo ya kalleta ba daidai suna karasa sauka kasa tana binshi abaya tace “Ya Hafiz wani laifin nayi ne wanan da dazu dasafen nan nabar Baffa agida mekuma nayi” juyowa yayi yakalleta daidai yabude mota yay murmushi yace “yarinya laifi dayawa” zare idanu tayi cikeda tsoro tace “hala saisa gabana keta faduwa wlh” tada motan yayi tashigo ganin duktai wani irin yasa yace “common babu abinda kikayi so relax” murmushi tayi dasauri tana sauke ijiyan zuciya but dudda haka she’s not just feeling ok hakan yasa tai shiru kaman ba itaba danda tacikashi da surutu shima shiru yamata baice mata komi ba ahaka har suka shigo layinsu, tundaga nesa take hango tulin mutane ata kofar gidansu maza na alwala hakan yasa ta gyara zama tace “Ya Hafiz maiya faru a anguwan mu”? Hango gate din gidansu abude awangale gakuma mutane yasa taji kawai gabanta nafaduwa ba kakkautawa, shiga cikin gidan sukayi daga baki baki Hafiz yay parking dan compund din yacika da mutane wasu tsaitsaye wasu zazzaune hango mai gadinsu da Adamu direbanta na kuka yasa kawai taji wani karfi yazo mata tawani bude kofan taduro juye juye tafara tana juwa juwa tanabin all mazan da idanunta kan sauka akansu tana kallo, kaman daga nesa taji dodon kunenta yaji wani magana. “Itace diyar Hajiyar data rasu” kafafunta da tun dazu sukai sanyi jitayi karfi yazo mata acikinsu kawai tahau gudu tai flat dinsu dataga kofar abude tashiga uwa an jefota tanabi kowa na falon da kallo matan anguwansu ne makotansu sunci mayafai some da charbi a hannu, stairs tayi dawani kalan mahaukacin gudu kawai neman mutum daya take dan gidansu she wants to know what’s happening idanunta ma sun rufe zuciyanta na bugawa batama ganin gabanta bum! Taji sunci karo da mutum da sauri takoma baya sanan tazaro idanunta tadaga kanta takalli wanda ke gabanta kaman yanda shima yake kallonta, batasan wayeshi ba but she could see kamannin shi da Ammi wani kayatyaccen kamshi nafitowa daga jikinshi, ahankali bakinta ke motsi numfashinta na neman gagaranta yi sabida yanda kirjinta ke bugawa ba kakkautawa ahankali tace “I……ina…….ina….”? Idanunta ne suka sauka kan gawar dataga an shimfide anan falon sama da aka suturta, sai yanzu ma talura da mutanen dake falon saman, Baffa, Baba, Ammi, Mom, Ya Manaf, Ya Mu’az, Maheer, Ya Hassan da Hussain Mama ce kadai batagani, still numfashinta na bala’in katsewa tabi idanun kowada kallo barinma Maheer dake kallonta yana wani irin kuka harda majina da she just think that answers her question, gently tadaga kafanta tana wani kalan kyafkyafta idanuwanta tana dambe da numfashinta dake kokarin daukewa tana kokarin tai taking just a step forward kawai tajita blank tai baya straight, wani irin tareta yayi dawani irin sauri Baffa yataso yana kallon Zayn daya tareta yace “Zayn kwantar da ita akasa she’s asmatic, Manaf get me her inhaler” dakinta Manaf yashiga yafito da sabon inhaler dago kanta Baffa yayi yadaura akan kafanshi yakai inhaler bakinta yana bubbuga kumatunta da kyar ta shaka tai wani irin nishi tadawo Baffa takalla tashi tayi zaune kaman bata hayyacinta tace “Baffa ina Mama na”? Ganin Baffa yay shiru yakasa bata amsa yasa takalli Ya Manaf tace “Ya Manaf ina mama ya akayi banganta ba” saukar da kanshi kasa yayi, ahankali Baffa yace “Ummulkhair” wani irin gyadamaikai tayi jikinta ko’ina na ta rirrike Baffa, all this while Baffa has been mai taurin zuciyan but for the first time yaji Khairy kaman itace zata karyashi, dakewa yayi yace “listen to me Khairy, kinaji” gyadamai kai tayi jikinta har kafafunta bari suke ta rirrike Baffa wani irin zufa na keto mata agoshi, anatse yace “dukanmu anan da mazajen dakika gani a waje ke kawai ake jira domin inaso kima mahaifiyarki addu’a, Ummulkhair inaso kizama yarinya mai Imani da kaddara mai kyau ko mara kyau sanan kisani cewa kullu nafsin za’ikatul maut, i want you to calm down don’t shout and don’t cry kinga kinada Asma karkije kima kanki illa, Ummulkhairy Allah yayiwa…..” Baffa yadanyi shiru ganin yanda tazaro ta kwalalo manyan idanunta waje kaman zasu fado kasa yanda jikinta ke rawa zaka dauka ajikin injin markade take, daurewa Baffa yayi ahankali yace “Allah yayiwa mahaifiyar ki, Maman ki rasuwa Ummulkhairy”.
2️⃣8️⃣

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button