ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Saukowa tayi shima Aliyu yasauko sanan yakama hannunta suka wuce ciki daidai zasu bude kofan falo aka rigasu budewa Zayn ne da Ya Manaf suka fito atare, ido da ido sukayi da Aliyu Zayn yawani irin dauke kai batare daya basu second look ba yawuce, shikuma Manaf yay murmushi yabama Aliyu hannu suka gaisa cikin mutuci Khairy tarikemai hannu tana mai shagwaba kan baikawo nata Aisha ba yabisu suka koma falon, Baba na falo zaune da Anty Mariya da Baffa suna ganin su Aliyu aka shiga gaisawa while mai gadi na shigo da abubuwan dasuka kawo.

Sunyi hira agidan kaman nothing has ever happened sai wuraren 11 Baba yashiga kwalama Khairy da Anty Mariya tajata sukaje sama tana hadamata wasu hadaddun kayan mata kan suzo sutafi dare yayi.
Saida Anty Mariya tagama hadamata sanan tazaunar da ita abakin gado anatse tace “Khairy nasan niba mahaifiyar ki bace amman yanzu nine ke matsayin mahaifiya a rayuwanki, kinriga kinyi aure yanzu iya zama da miji da dabarun ki na mata sune zasu zaunar dake, kinga maza all of them are thesame, Ummulkhairy biyayya shine abu na farko dazaisa ki siye mijinki completely, kinga Aliyu mijinki yarone mai natsuwa ma gaske, ga kunya gashinan very very calm kinga maza irinsu dinan dako abokanai basuda shi matayensu sune komi nasu, dole zaki daura damnaran zama dashi, kinga shiru shirun nan masu sanyi sanyi sunfi kowani namiji jaraba da yawan bukata, Khairy dole zaki daure ki biyamai kinaganin Aliyu ke kadaice mace dakuma namijin rayuwanshi, u are his mom his everything kika iya tafiya dashi za’adauka kin magance shi ne sabida yanda kome kikace shizaiyi, ki rike sirrin mijinki komene ne bayaso ki kiyayi abin, kinga maza masu suna Aliyu akwai zuciya barin ma wanan nakin dani naga zuciyanshi da idanuna ranan da yazo ya saceki” dan murmushi kadan Khairy tayi tunawa da ranan, Anty Mariya tace “kidage da shan magungunan nan naki kinji karkiyi wasu dasu, sanan karkice kesaikun tare menene menene yakiraki shimfidan shi ki amsa kinajina” Gyadamata kai tayi jin Baba yasake kwalamata kira yasa Anty Mariya ta tashi tace “muje kinga Babban ki chan yana kiranki” tai maganan tana bude kofan suka fice, falo suka sauka babu kowa a falon hakan yasa sukai waje, dukansu na tsakar gida harda Zayn dataga Baba namai magana tareda Aliyun dabata san na meye ba, ganinta yasa Baba yajuyo ya kalleta yace “tahonan ku tafi Khairy dare yayi” gyadama Baba kai tayi takaraso tanaso ta gaida Ya Zayn but sanin halin mijinta yasa ko inda yake bata kalla ba agaban kowa Aliyu yakama hannunta sanan yakalli su Baba da Baffa yace “goodnight Baba saida safen ku” saida safe duk suka musu sanan Baffa yace “muje kaga Zayn, saida safe Amini” suma suka wuce motansu Zayn yaRshiga mazaunin direba yajasu suka fice daga gidan.
7️⃣3️⃣

Gagarumin biki ake shiryawa agidaje uku, gidansu Aliyu gidansu Baffa da gidan su Aysha.

Baba yama Khairy lafiyayyen kayan daki da aka kai babban gidan Aliyu an jeramata komi, akwatinan da Aliyu dakuma Dad da Gwaggo sukama Khairy kusan 40 dan set daban daban designers, fir daga Dad har Gwaggo sun hanashi ganin Khairy da akema lafiyayyen gyara sai yanzu Khairy takeji aure take tasa Batool tamata inviting all her friends ranan Friday da Saturday ne za’ayi biki asabar da night akaita gyara akema Amarya na ban mamaki.

Ranan Friday wajen kamu aka bari Aliyu yaganta bayan yabiya kudi dayaga Khairy saida yadan kusan zarewa akahau nai dariya Dan rudewa yayi su Meena sai dariya suke dan tunda Aliyu yakirata yanunamai shiya yafema Khairy komi yawuce between them kuma yanaso tabata hakuri sudawo kaman sisters taje tabama Khairy hakuri da ita da Batool sune manyan kawayen amarya akai shagali har dare ko kadan ba’a bari Aliyu yakebe da Khairy ba Aiko yacika yay fam yace zata ganene sai dariya take.

Yau babban ranane wajen both Aliyu da Khairy wato babu abinda yakai soyayya dadi sunma kosa dare yayi tabar gidan nan ta tafi gidanta wajen Aliyun ta dan tayi kewan shi sosai kwana nawa bata ganshi ba.

Karfe 8 nadare aka tafi da Ummulkhairy gidan mijinta gidan Aliyu Hydar.
Karfe 8 nadare aka kai Ayshu gidan mijinta Zayn.

VIP kunason amarcin this two angwaye konasu KhairRy kadai???
7️⃣4️⃣

Dagaske Aliyu one single friend bayida shi saidai yaran aiki, hakan yasa Dad yadaukeshi amota sai uban kunya yakeji har zuwa Babban gidanshi, cikin gidan Dad yashiga gidan yahadu bana wasaba kaman wani gidan gwamna, kallonshi Dad yayi yace “Oya get down and go kasayi baki kasan yanda zakayi da kawayen amarya sutafi nidai saida safe” awani irin kunyace yace “Daddd plssss” hararanshi Dad yayi yana murmushi yace “don’t Dady me, Allah baku zaman lpy gud night son” ahankali yabude motan yasauka yabude baya ya kwashi manya manyan ledojin dasuke nan aciki sanan yamaida kofan yarufe Dad yaja mota abinshi yawuce yay tafiyan shi.

Okay Gidan yabida kallo sanan ahankali yafara tafiya zuwa gaban flat din ahankali yabude kofan ya shiga gidan wani haddaden kamshi yake banawasa ba, furnitures na ciki zaka dauka villa kaje, ganin babu kowa a falo yasan suna sama yasa yawuce wani hadadden daki dakenan kasa yabude kofan yashiga dakin shima yahadu yasha furnitures ga kanshi da dakin keyi ijiye komi yayi awajen sanan ya kwanta kan gado wayanshi yaciro yay dialing number ta amman harya gama ringing bata dauka ba hakan yasa yamata text.

“Suwaye tareda ke”?
Ko 1min text din baidauka ba tamai reply.
“Gwaggo, da Meena, da Batool da Amal, Ya Aliyu wai kwana zasuyi please kazo na ganka yau kwana nawa I didn’t see you”
Wani kalan murmushi yayi yana tunanin yanda zaiyi dawanan jarababbiyan kakan nashi, tashi kawai yayi yawuce sama Gwaggo yagani zaune falon sama dawani katon ghana masgo guda daya tana lissafin wani daki zata dauka adakunan dake saman tana ganin Aliyu tace “yauwa Gadanga zo bani dakina da kanka kagani naje najera wayan nan kayan a sip, gobe direba zai karasa kwasomin kayayyakina na jera adakin nawa” wani kallo Aliyu yamata daidai Meena tafito daga dakin da Khairy keciki ganin Ya Aliyu da Gwaggo yasa ta gimtse dariyan datakeji tazo wajen da sauri tace “Ya Aliyu Gwaggo tahada kayanta tass wai gidanka zata dawo dazama bazata iya rabuwa dakai ko Khairy ba” wani kallo Aliyu yama Gwaggo da itama kallonshi yake yace “wlh bazaki zaunamin agida ba ki koma chan gidan danki kicigaba da zama” nuna kanta Gwaggo tayi tace “ni zakama rashin mutunci” hararanta yayi yace “eh” cikeda masifa ta tafa hannu tace “yo idan ka isa Aliyu zoka korani daga gidan nan” wuceta yayi yay dakin dayasan Khairy keciki yabude dakin, Khairy na zaune kan gado an rufemata kai da lafaya ga Batool da Amal duk akan gado suna mata hira, ganin Aliyu yasa duk suka gaidashi, dan murmushi yayi yasa hannu a aljihu yaciro bandir na yan dubu guda biyar ya ijiyemusu akan gado yace “ka kudin siyan baki ina zuwa bari na ari Mrs Aliyu” yay maganan yana kama hannunta dayasha lafiyayyen lalle, ahankali tabiyoshi ta sauka kanta alullube yawuce suka fito daga dakin ganin yafito da Khairy yasa Gwaggo ta mike tsaye tace “ina zaka kaita kasayi kudin bakin bakin ne” ganin acike Gwaggo take dashi yasa ahankali yace “magana zamuyi da ita afalo Gwaggo, kuma ai nasaya ko Meena” dasauri Meena ta gyadama Gwaggo kai tace “ga kudin chan adakin” dasauri Gwaggo tace “muje ingani” tai hanyar dakin, dawani irin sauri Aliyu yaja hannunta suka sauka kasa zuwa dakin maida kofan yayi yarufe yasaka key yakai hannunshi ahankali Ya yaye gyalenta murya chan kasa yace “Assalamu Alaykum” wani irin murmushi Ummulkhairy tayi tai wani tsalle ta rungumeshi, wani irin fito da ita daga jikinshi yayi kawai Ya dauketa sama yana murmushi sosai yace “I miss this girl, me kikamin ne”? Sauketa yayi dawani irin sauri tazauna kan jikinshi tana kallon fuskanshi yanda yamata kyau ahankali tadaura hannunta kan kirjinta dayan hannunta kan kirjinshi tace “wani sirri ne da only this 2 zasu iya ganewa” hannunta yakama ahankali yamma hannun kiss yana kallonta kaman baitaba ganinta ba yanda takara kyau fatarta na taushi tana kamshi turare bana wasaba, jin Gwaggo na kwalamai kira yasa yace “bazata taba sani we are here ba, let’s go and perform ablution” gyadamai kai tayi suka wuce bayi alwala sukayo sanan suka fito dakin akwai dadduma kowani daki na gidan an ijiye dadduma hakan yasa suka shimfida sukai salla bayan sun idar yamusu addu’a yaHkama kanta yay addu’a sosai sanan ya warware mata gyalen.
7️⃣5️⃣

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button