ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Free page

Da taimakon Mom tai wanka ta chanza mata kaya zuwa wani simple atampa doguwan Riga sanan tasata tai salla itadai tasan tai salla amman bamatasan metakeyi cikin sallan ba kotana karatu dakyau kobatayi jikinta yay munannan zafi, kwanciya tayi kan dadduman Mom tazo dagata tayi tacire mata hijabi tace “kwanciya akasan ya isa haka nan kar sanyi ya shigeki zoki kwanta akan gado” Mom ta kwantar da ita kan gado ta kwanta lamo kan gado hawaye nabin idanunta suna sauka kan katifan, hannu Mom takai tana sharemata hawayen ahankali tace “Khairy nasan mekikeji aranki yanzu haka amman kisani kome yan uwanki sukayi da mahaifinki sabida mamanki sukai hakan, shi mara lafiya ana so ana cikamai wishes nashi, barinma mara lafiya kaman na mamanki, Mamanki ita ta haifeku duka idan she choose ke kadai zata boyemawa rashin lafiyanta believe me tanada reason nata maybe taga Kece mai weak zuciya u can not take it, and believe me yanzu idan nagayamiki Wanan abin dakike yi yanzu is not what she wants Khairy, be strong dan yanzu Kece maman su yayyinki, kinyi tunani what Baban ki is going through yanzu haka, matarshi dasuka tsufa tare bata kuma dawanne zaiji dake koko da rasuwan da akamai? Khairy ki kwantar da hankalinki kinji, bari na sauka kasa na hadomiki ko shayi ne kisha” Mom tashafa kanta kafin ta tashi daga kan gadon tawuce tafita daga dakin su Manaf zasu shiga tahanasu.

Ranan haka aka wuni Khairy gatanan gatanan ne, takasa cin komi kotaci amai straight, rasuwan Maman ta yabi gari bama asan ya kawayenta sukaji ba before you know it kawayenta suka cika gidan harda Besty duka dakinta aka kawosu kallonsu kawai take kaman ta haukace, babu wanda take amsa gaisuwan shi, duk wanda yazo gaisuwan bazaiyi kuka ba amman dazaran kaga Khairy saikai kuka kawayenta sunyi kuka sunyi kuka harsun gaji, Besty tunda tazo take rungume da Khairy da jikinta kaman wuta tana kuka da kyar ta iya tauna kosai guda da Besty tabata abaki ahaka dare nayi suka tafi.

Hakanan yaji ya bala’in damu cus yakira Khairy yanaganin miss calls din daya sunkai 20 maybe but all ba amsa same with text messages nashi ba reply, he don’t know why but kasa jurewa yayi tashi yayi daga office din nashi yadauki car keys dinshi yafito wajen police station din, motarshi yashiga yajata yafice daga police station din, he don’t even know why he’s driving to layinsu Khairy but yasan zuciyanshi keeps pulling him to go there dudda bawai shiga gidansu zaiyiba, ahaka har yazo layin, kofar gidansu yagani tsaitsaye da maza sanan gashi an bude gate an saka canopy a compound din ga tabarmai maza sun zazzauna, hakanan yaji kirjinshi yabuga dum! Waje yasamo yay parking motarshi yadade zaune sanan ahankali yafito ya tsaya jikin motanshi yana kallon jama’a dake shiga da fita gidan yakasa zuwa, yana tsaye awajen Ya Mu’az yafito tareda wasu friends nashi dasuka zomai gaisuwa, shiga motansu sukayi suka wuce daidai zai juya yakoma ciki idanunshi suka sauka kan Aliyu dake tsaye jikin motanshi yay folding hannunshi yana kallonshi tunani yafara inda yasanshi kafin daga baya kanshi yagayamai police man din ranan nan takowa yayi zuwa inda Aliyu yake tsaye yamikamai hannu dasauri Aliyu yabashi hannu yace “meke faruwane wucewa zanyi naga mutane gate abude shine nai parking, what happen?” Aliyu yasake tambayan Ya Mu’az heart nashi nabugawa, ahankali Ya Mu’az yace “Maman mu ce ta rasu, muje nakaika ciki kaman Baba gaisuwa” Ya Mu’az yay maganan yana gaba binshi abaya Aliyu yayi har zuwa cikin gidan har inda Baba yake kan tabarma tareda Baffa dawasu abokanen arziki Mu’az yakai Hydar, Baba nada gane mutane kallo daya yana Hydar yace “Aliyu” hannu yamikama Baba anatse yace “Baba yahakuri, Allah yajikanta Allah yamata rahama” ahankali Baba yace “Ameen Ameen Allah yayimaka Albarka” sanan yakalli Baffa yace “Wanan ne officer dana gayamaka ranan da Khairy tai shirmen nan yadawo da ita gida” dasauri Baffa yace “Allah sarki, yaro mai hankali angode Malam Aliyu, gashi Ummulkhair ba lafiya da an kirata kamata gaisuwa nasan zataji dadin hakan” gyadama Baffa kai yayi yakasa magana kirjinshi na bugawa dum dum, kafin da kyar ya iya tashi yamika musu hannu yace “bari nakoma wajen aiki” addu’a su Baffa sukamai sosai sanan yajuyo Ya Mu’az biyeda shi har waje zuwa wajen motanshi sanan Ya Mu’az yace “mungode Allah bada lada” murmushi yamai tareda gyadakai har Ya Mu’az yajuya zai wuce yaji yakasa hakura ahankali yace “Ya Ummulkhair take”? Juyowa Ya Mu’az yayi yakalleshi cikeda damuwa yace “not good at all” yay shiru yana kallon Hydar din dayaga ya tsaya yaki tafiya yana kallonshi kaman yana jiran yace wani abu ahankali Ya Mu’az yace “Mama had cancer all this while Khairy bata sani ba cus Mama tahana afadi mata, as it is now kaga yau uku this is the third day da abinci bai shiga bakin Khairy ba, she’s not handling the whole thing very well, she’s not doing okay, kuka suma asma attack duka yahadu mata kaman zatai hauka takeji, kasan she’s very very close to Mama, naji Baffan mu yana cewa yau zasu wuce da ita gidansu Dan gidan nan is not helping her at”. Gyadamai kai Aliyu yayi idanunshi sunyi ja yakasa magana juyawa Ya Mu’az yayi yCawuce ciki.
2️⃣9️⃣

Free page
Ganin yarinyar nan da Mamanta tarasu dayaga antaho da ita gidansu dazu dazasu dawo dan he can’t even remember her name yasa yadan ware idanu yana binta da kallo yanda take sauka daga kan staircase din gaban flat din Mom, babu takalmi akafanta babu dan kwali akanta kalaban kanta na lilo atsakiyan bayanta, daga ita saidan rigan bacci pink mai hannun taliya daya tsaya a guiwanta, ganin yanda take tafiya one one as if she’s trying to hold something yasa yadanja karamin tsaki yace “God am I a baby sitter now” jin tace Mama kijirani tai hanyar gate yasa yadanja tsaki yatashi dasauri ganin tai hanyar gate, dawani irin sauri yasha gabanta batare dayace kalaba yay folding hannunshi a chest dan ihu yaso yamata but to his biggest suprise gani yayi gabaki daya idanunta are close is she sleeping walking or what? Yatambayi kanshi daidai ta iso gabanshi babu any tazara tsakanin shi da ita tsayawa yayi yana kallonta just to feed his curiosity yaga mezatayi, wani kalan heart melting murmushi tasaki daya bala’in lobar da dimples dinta all the 2 yabayyana set na white teeth dinta, pink lips dinta nawani kalan shinning kafin ahankali takai duka hannayenta biyun tadaura kan hannunshi daya rungume a kirji takama cikin muryanta kaman na baby tace “Mama kinjirani, Mama I miss u, karki kara tafiya ki barni kinji Mama” tai maganan tana warware hannunshi daya rungume a kirji tasaukar da hannun kasa sanan gently takara tako one more step ta shige cikin jikinshi tai wrapping two hands nata around his back tawani kalan kankameshi tana sauke ijiyan zuciya dahar cikin brain dinshi saida yaji ahankali tace “Mama bacci” tunda yake in his life what he just felt now baitaba jinshi ba, sandarewa yayi hannunshi sauke akasan batare daya iya komiba yanajin saukan ijiyan zuciyanta akirjinshi yana kallon tsakiyan kanta da yanda gashinta ke lilo sabida iskan dake kadawa da yanda heart dinta ke biting each beat yana jinshi anashi heart din, yakai kusan 2min ahaka she’s still holding him tight batare data kara magana ba, ahankali yadaga hannayenshi dayaji sunyi sanyi kaman basa functioning kuma yakai saitin hannunta abayanshi zai kwance yanda tadaure hannun abayanshi, kankame hannun tasakeyi saikuma yaji tasaki kuka dabaida kara ko kadan. “Baran sakeki ba Mama, ina sakinki cemin zasuyi kin mutu, Mama nakusan haukacewa da suka fadamin haka ni nasan baki mutu ba, ni ajikinki zanyi bacci anan dakinki zanyi bacci, I will not allow u to leave me ever again and go” yanda hawayenta kebin kirjinshi yasa yaji zuciyanshi ta tsinke shifa baicika tausayin mutane ba but for the first time jiyayi yarinyar nan tabashi tausayi sosai ahankali yakomar da hannunshi batare daya rabata dashi ba, yadan dade ahaka sanan gently yadan duka tareda ita yasa hannayenshi the two yadauketa ajikinshi kankameshi tasake yi gamgan tana kara gyara zaman kanta akirjinshi yana kallon fuskanta saida tagama sanan ahankali kaman yadauki Kwai yafara tafiya har zuwa flat din Mom, shiga ciki yayi daman kofan abude yake yay stairs da ita yana mamakin yanda batada nauyi kaman yadauki paper, dakin Batool dayagani a bude ya tabbatar mai daganan tafito, shiga cikin dakin yayi dudda ko’ina da duhu but he could see sabida hasken window dake nuno compound nasu gently ya tsugunnawa kaman yanda ake kwantar da baby haka ya kwantar da ita kan gadon zai zame hannunshi yaji ta chapke hannunshi da sauri tana sheshekan kuka kaman yanda jarirai kema mamansu takai hannunshi kirjinta ta kankame sosai kaman idan tasaki hannunshi something will happen to her, wani dauuuu yaji a brain dinshi kaman an watsa acid a alkaline environment, dan gabaki daya a boobs nata ta kankame hannun nashi, he could basically feel sign na her sleeping nippy, karya fizge hannun tahau kuka ne this is middle of night a ganshi adakin nan saisa yakeyi ahankali, gently ya tsugunna jikin gado, wani kalan zufa yaji yana ketomai shi kanshi baisan mesa ba this is not the first time yake feeling boobs na mace why is hers different, why so much effect, ahankali yakai dayan hannunshi yadaura akan fuskanta yana shafa kumatunta he don’t even know what to do samin kanshi yayi da hura mata iskan bakinshi a fuskan wani irin ijiyan zuciya ta sauke tasaki hannun nashi kadan bakaman yanda ta kankame hannun a kirjinta da farko ba, ganin haka yasa yacigaba da hura mata iskan yana shafa kumatun nata dayaji yamafi na jariri taushi sanan gently yashiga janye hannunshi kafin yay nasaran janye hannun duka sanan ya dauke hannun kan fuskan nata dawani irin sauri yatashi yafice yaja kofan nasu ahankali sanan yasauka kasa yafice waje abinshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button