NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL

NEEHAL COMPLETE HAUSA NOVEL BY Zeey Kumurya

NEEHAL
By
Zeey Kumurya

Da sunan Allah mai kowa mai komai, Allah ka sa yanda na fara rubuta Littafinnan lafiya na gama shi Lafiya, Allah ka ba ni ikon rubuta abun da zai amfanar da Al’umma Ameen._

Kamar yadda na yi alƙawari yau zan fara sakin sabon book ɗina NEEHAL, gashi na cika alƙawarin, sai dai ba na jin daɗi hakan ya sa za ku ga page d'in kaɗan, nima ba haka na so ba, ina buƙatar addu'ar ku???????????? Masoya.

0️⃣1️⃣
…………A ƙaton parking space d’in gidansu driver’nsa wanda ya kasance soja kamarsa ya yi parking rantsatstsiyar motar da suke ciki, driver’n ya fito da sauri ya zagaya ɓangaren da yake ya buɗe masa motar, ya ɗan ja baya tare da sara masa irin nasu na sojoji, a hankali ya ziro da santaleliyar ƙafarsa ta dama, bayan 3 seconds ya ziro ta hagun itama tare da fitowa gabad’ayansa fuskarsa babu walwala ko

kaɗan kamar kodayaushe, kai kawai ya gyad’awa driver’n ya fara tafiya cikin takunsa na ƙasaita da isa, part ɗin mahaifiyarsa ya nufa direct, duk inda ya gilma sojojin dake kai kawo a farfajiyar gidan na sara masa, kasancewar mahaifinsa shima GENERAL ne na sojoji, hannu kawai yake d’aga musu.


Da sallama ƙasa_ƙasa ya shiga main parlour na part d’in Mama, Mama da mahaifiyarta Hajiya dake zaune a parlorn suka amsa masa suna binsa da kallo, Hajiya tana washe baki ta ce “Aminullahi! sannunka da zuwa, ashe da rabon zamu haɗu da tuni yau na tafi baffanku ya ce in bari sai Monday zai zo mu tafi” ya

ɗan saki fuska ya ce mata “Yawwa, ina yini” idanunta na kansa ta ce “Lafiya k’alau, ya aikin?” ba tare da ya amsa mata ba, ya zauna a kujerar dake fuskantar ta su ya dubi mahaifiyarsa wadda suke tsananin kama da

shi tamkar an tsaga kara ya ce “Ina yini Mama” ya ƙarasa zancen yana dafe kansa tare da taune lips d’insa na ƙasa dan maganama wahala take masa” Mama data k’ura masa ido ganin yanda ya rame ta ce “Lafiya k’alau, yau sai yanzu kazo har ina shirin kiranka in tambayeka ko this week ba za ka zo ba, Dad ma kafin ya fita yanata ta tambayarka” ya gyad’a mata kai kawai tare da kwantar da kansa a jikin kujera ya lumshe

fitinannun idanunsa, Hajiya data saki baki da hanci tana kallonsa ta ce “Aminullah cuta kayi acan Lagos ɗinne naga duk ka zabge ka rame haka, kamar wanda ke zaune cikin guggun mayu?” Shiru yay mata kamar ba da shi take ba , A ɗan fusace Hajiya ta ce “Nifa matsalata dakai jarababben miskilancinka na tsiya, ana maka magana kana yiwa mutane banza” nanma shirun ya kuma mata, Mama ta tab’e baki ta maida kanta akan wayarta dake hannunta, Hajiya ta dubeta ta ce “Ke kuma Fatima wacce irin uwa ce ke?

Kina kallon yaro ya dawo a haka, ai kya tambayesa ki ji me ya samesa ya yi irin wannan zabgewa haka” Mama ta d’ago da kanta tana duban Hajiya ta ce “Amma fa Hajiya kinsan halinsa, ko zan kwana ina tambayarsa abin da ke damunsa idan bai ga dama ba, ba faɗamun ze yi ba, kema kuma gashi kin tambayesa ya miki shiru” cikin faɗa Hajiya ta ce “To kuma sai abiye masa, ai ba dan shi zaki yi ba” Mama ta ce “Hmmm, Hajiya Ameen fa ba yaro ba ne yasan ciwon kansa” Hajiya ta ce “Sai kuma ki yi, amma dai wannan rashin kula ne gaskiya, ace kiga yaro haka ki nuna masa halin ko in kula, ni tunda ya rainani ai ba ze bani amsa ba dama, amma ke tunda ke kika haifeshi dole ya sanar miki” Mama ta mata shiru ta cigaba da sabgarta, Hajiya ta cigaba da mitarta da masifarta.

Wata kyakkyawar budurwa ce take sakkowa daga kan steps d’in dake parlour’n, sanye take cikin wani wandon jeans dark blue wanda ya kama jikinta sosai, sai riga t_shirt pink colour, babu ɗankwali akanta, kawai ta tufke gashintane cikin ribbom, hannunta riƙe da waya tana latsawa da earpiece sanye a kunnenta, Mama ta d’ago jin takunta tana kallonta fuska a daure ta ce “kar ki kuskura ki ƙarasomun nan a haka”

NEEHAL ta d’ago da kanta daga kallon wayarta da take ta kalli Mama sannan ta juya ta koma inda ta fito ta na turo baki gaba, Hajiya ta keb’e baki ta ce “Oh ni Zainabu, Allah kanunamun ranar da wannan yarinya za tai hankali ta san ta girma” Neehal ta koma ɗakinta tana kwab’e fuska ta ɗakko after dress ta ɗora a kan riga da wandon jikinta tare da sanya hula a kanta ta ƙara fitowa ta dawo falon ƙasan, Hajiya ta ce “To

ba ki fi kyan gani ba yanzu, amma da kinfito kamar wata y’ar arna” Neehal ta turo baki gaba, ta na ƙoƙarin zama kusa da Mama ta lura da Ameen dake zaune yanda yake tun d’azu, waro manyan idanunta tayi waje cikin murnar ganinsa ta ce “Yayana yaushe ka zo?” Ameen wanda tun sanda ta ƙaraso falon ya buɗe idonsa yake kallonta ta ƙasan ido baice komai ba, Neehal ta koma kusa dashi ta zauna, dama tunda ta shigo falon taji k’amshinsa amma bata lura da shi ba saboda mitar da Hajiya take mata, ta tattaro duka nutsuwarta saboda sanin halinsa ta ce “Yaya ina yini” bai tanka mata


ba, sai idanunshi daya mayar ya lumshe kawai. Neehal ta ɓata fuska ta tashi daga kusa dashi ta koma kusa da Mama, Hajiya ta ce “Wannan mugun hali naka Aminu Allah ya sauya maka shi da gaggawa, yarinyar ta taho da murnarta tana maka magana amma ka shareta, saboda baƙin hali irinnaka” Mama ta dubi Neehal data kwanta mata a jiki ta ce “To mage, sai yanzu kika tashi daga baccin?” Neehal ta ce “Um” Mama ta ce “K’arfe nawa zaki aiki?” Neehal ta ce “Around 4” Mama ta ce “Sai ki tashi ki shiga kitchen for lunch, kinga 2 ta kusa” Neehal ta kwab’e fuska sosai tana barin jikin Mama ta ce “Tom” Arayuwar Neehal bata k’aunar

aiki ko kaɗan, musamman ma girki ta fi tsanarshi, gashi in dai tana gida ita take yi, Mama ba ta yi, masu aiki dama wanke_wanke da shara kawai suke yi sai kuma ɗan tayayyar aiki, dan ko Neehal tana School ko gurin aiki Mama ke girkinta da kanta. Neehal ta mik’e tana duban Mama ta ce “Me zan dafa?” Mama ta ce “ki yi abun da zai yi sauri dan kar ki yi late gurin aiki, akwai ma soyayyen kayan miya na soya ɗazu, ki haɗa miya kawai sai ki dafa wani abun simple a ci da miyar” Neehal ta ce “Toh” tare da nufar hanyar kitchen.

Hajiya ta ce “ki yi sauri da’Allah kar yunwa ta kashemu” Neehal bata bi takanta ba ta shige kitchen. Mama ta mik’e tana duban Ameen ta ce “Mit me in my room” batajira amsarsa ba tayi hanyar step, a hankali ya mik’e ya bi bayan Maman, Hajiya ta bishi da kallo cikin tausayinsa kamar zatayi kuka ta ce “Aminu Allah ya baka lafiya, bari jenal ya dawo gaskiya a san abin yi, tunda ita uwarta ta ka shashashace”

Mama tana duban Ameen dake zaune a gefenta a bakin gado fuskarta babu wasa ta ce “Ameen me ke damunka?” Shiru ya yi tare da sunkuyar da kansa, Mama cikin takaicin shirun da yay mata ta kuma cewa “Ameen da kai nake fa, ko ba ka jina ne, kasan bana son wannan iskancinnaka ko, ana maka magana ka na jin mutane ka yi musu banza” Jin yanda Mama ta yi magana a fusace ya sa shi d’agowa ya na duban

Maman cikin muryarsa mai daɗin amo da sanyi ya ce “Babu komai Mum” ya ƙarasa zancen ya na taune Pink lips d’insa na ƙasa tare da maida idanunshi ya lumshe ya na sauke numfashi a hankali. Mama ta bishi da wani irin kallo cike da takaici gami da mamakin halinsa na zurfin ciki, tun yana ɗan ƙaraminsa haka yake, miskilancinsa da zurfin cikinsa ya yi over. Mama ta sauke numfashi cikin ƙoƙarin ganin ta danne tata damuwar, cikin sanyin murya mai nuni da rarrashi ga wanda akewa ta fara magana, “Al’Ameen!” Ta kira sunanshi a ɗan kausashe, bata jira amsarsa ba ta cigaba da magana da faɗin, “Ameen, Ni mahaifiyarkace duk duniya ba ka da kamata kamar yadda nima ba ni da kamarku, ko kaɗan ba na son ganinka cikin damuwa, amma kuma 2 years kenan idan ban manta ba kullum cikin damuwa nake ganinka, ka faɗamun menene damuwarka ko na samu nima hankalina ya kwanta” buɗe idanunsa da suka yi nauyi ya yi ya saukesu akan fuskar Mama wadda take kallonsa itama, matsowa jikinta ya yi ya kama hannayenta

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page