ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Sai wajajen 6 nasafe sanan Dr yay discharging Aliyu, ahankali yafita daga dakin boys dinshi biyedashi juyowa yayi yakallesu yace “ku tafi mota ina zuwa” saramai sukayi sanan suka wuce shikuma yakarasa zuwa ICU din, dayake Baba da Manaf sun tafi masallaci ganin tai bacci babu kowa awajen, ahankali ya tsaya gaban glass din yay folding hannunshi akirji yana kallonta, yakai kusan 3 good minute yana kallonta sanan yajuya ahankali yawuce yafita daga asibitin masallaci yafara shiga yay salla sanan yagaisa dasu Abba yamusu sallama.

Kwananta biyu a ICU aka dawo da ita normal daki sabida yanda takeda saurin warkewan ciwo, Baffa dasu Mom tun safe sukazo harda Batool da da kyar Mom takadata tawuce school daga wajen, sanan Matan Baba da Khairy take kirada Anty Mariya ta gyaramata jiki da towel da ruwan dumi sanan aka chanza mata kaya zuwa wani simple gown baby pink da hula baby pink sanan aka maidata gado tai kyau kaman wata yar karaman yarinya tea Anty Mariya tabata tasha dan yunwa takeji Baba sai murmushi yake cikeda jin dadi da kyar Baffa yabashi duk suka tafi aiki akabarta da Anty Mariya kadai.

Saida ta shanye tea sanan ta kwanta tana rikeda teddy da Maheer yasayo mata na Mickey Mouse tana murmushi Anty Mariya tace “Maheer yamaidake yar yarinya ko” dan murmushi tayi sanan ahankali dan bata iya magana da karfi tace “ina wayana Anty”? Ahankali tace “wayanki na wajen Batool” dan yatsine fuska tayi dasauri tace “menene wani abu namiki ciwo ne” girgiza mata kai tayi ahankali tace “ni gida nakeso mutafi” fuskanta Anty Mariya tashafa tace “Dr yace at this rate dakike warkewa very fast maybe gobe ko jibi ma zasu iya sallaman ki jikinki nada kyau Khairy” Gyadamata kai tayi ahankali Ya Aliyu takeson kawai tagani tasan yanata kiranta, knocking kofarsu akayi dawani irin sauri tadago kanta he just feel inama ace Ya Aliyu ne zai shigo, ahankali aka turo kofan aka shigo Zayn ne yana sanye da riga da wando na jeans dasukamai hadadden kyau idanunshi sanye da bakin glasses idanunshi nakan Khairy datai lamo agado tunda ta kalleshi sau daya tacire idanu tana shafa teddy data rike, she looks super cute kaman ka saceta ka gudu ga dakin datake ciki very fine dan hospital suit ne harda kujera doguwa da fridge da ac ga tv, an rufe mata kafa da bargo, ganinshi yasa Anty Mariya tai murmushi tace “barka da zuwa Zayn shigo mana” tai maganan tana tashi dagakan wani hadadden plastic chair dake gaban gadon Khairy takoma kan lumtsatsen 3 sitter tazauna, ahankali Zayn yashigo yace “ina yini yamai jiki” murmushi tayi tace “jiki Alhamdulilah ai taji sauki, gashinan ta damemu ita a sallameta takoma gida kasan duk kyan asibiti babu mai son asibiti ga waje zauna mana ka tsaya” karasawa yayi gaban plastic chair datake nunamai ya zauna ahankali sanan ya ijiye katuwan ledan daya taho dashi kafin ahankali yasa hannunshi yazare bakin glasses din idanunshi yakalli Khairy daidai itama tadan kalleshi dasauri tadauke idanunta sanan ahankali tace “ina yini Ya Zayn” harcikin brain dinshi yaji muryanta daurewa yayi yadake yace “how are you feeling now”? Batare data kalleshi ba tace “fine” kallonta yacigaba daya kaman wanda baitaba ganinta ba, yatsun hannunta da fararen kumbunanta yabi da kallo da yanda take rike kafan teddy, kafin ahankali yasauke kanshi kan lips dinta dayay wani irin mahaukacin pink sunadan motsi sabida yanda take motsi ga gashin gaban goshinta daya kwanta lub lub tunda yake baitaba tsayawa yakurema nace kallo haka ba sai Khairy he loves everything every single thing about her, baitabajin zuciyanshi ya girgiza akan mace ba sai akanta kaman yadauketa yatafi da ita dakinshi suyi rayuwan aure yakeji she’s so innocent, kana ganinta kasan yarinya ce dabatasan komi ba about all this iskanci life da sauransu knocking kofan da akayi yasa yadawo daga king tunanin dayake, tashi Anty Mariya tace “tace suwaye kuma Kodai Babanki bai yarda yabi Baffa sun tafi aiki bane” tai maganan tana bude kofan daga Khairy dake kwance har Zayn suka juyo dan ganin waye akofan, ahankali Anty Mariya tabude kofan Aliyu ne tsaye gaban kofan yana sanye dawata sky blue yadi mai bala’in kyau hannunshi rikeda wani Leda na Buba popsicles yana wani irin bala’in kamshi idanunshi sanye da bakin glasses yanabin dakin da kallo kafin idanunshi su sauka kan Khairy dake kan gado tana kallonshi wearing one big smile akan fuskDta.
4️⃣7️⃣

Ahankali take shiryawa dan ita ko kadan bataso taje gidan Baffan dan bamataso su hadu da Zayn dataga Kwanan nan wani mugun kallo yake mata kaman zai hadiyeta, Batool da harta gama shiryawa tace “wai bazakiyi sauri ba kinata abu ahankali kaman bakida kayan ciki” hararanta tayi tace “dalla chan” bude kofa Anty Mariya data shirya tayi takalli Khairy tace “har yanzu baki gama ba” gyalen abayan data saka tadauka baki tace “na shirya Anty” sanan tadauki jakanta Batool ta tashi suka fito zuwa compund ganin Ya Manaf da Mu’az yasa tai wani murmushi cikeda tsokana tace “angwaye wai kwana nawa aka saka ne” hararanta Baba daya fito yayi yace “ban fadamusu ba sai munje gidan Baffan su zasuji” dariya tayi tace “wlh Baba duk sun kosa” hararanta Manaf yayi yashiga motan shi yace “karki sake kizo motana Batool taho kinji” dasauri Batool tai wajen, Baba yace “manta dasu muje motana kinji” gwalo tamusu suka wuce tashiga motan Baba, Anty Mariya na gaba ita kadai abaya sanan suka wuce batasan mesa ba hakanan taji gabanta nafaduwa dum dum dum, daura hannunta tayi kan kirjinta tana addu’a azuciyanta tana kallon hanya ahaka har sukakai gidan Baffa, Babban falon Baffa sukaje, tunda tashigo taga Zayn na kallonta kaman zai hadiyeta dawani irin sauri tadauke kanta tagaida Ammi data amsata ciki ciki sanan tawuce wajen Mom tazauna kusada kafanta Batool ma tazauna awajen tana gaida Ya Hafiz dake zaune kusada matanshi yana rikeda Babyn su dake bacci, gasu Hassan a zaune kowa a zaune, Baffa na zaune kusada Baba

Ahankali tadago kanta hada idanu sukayi da Zayn dataga yasakin mata wani cool smile dasauri tadauke kanta takalli Baffa dake gyaran murya.
Anatse Baffa yabude taron nasu da addu’a sanan yace “jiya munje gidan iyayen yarinyar da Manaf dakuma Mu’az sukeso su aura, Alhamdulillah komi ya daidaita bamu sanar daku komi gabe da abin bane sabida akwai abinda mukeso musanar daku wanda dukanku nan babu wanda yasan maganan dagani sai Baffan ku nan” yanuna Baba saikuma “marigayiya mahaifiyan ku Manaf” yanuna su Manaf, tsit dakin yayi, gyaran murya Baba yasakeyi yace “an sakawa Manaf da Mu’az ranan aure kimanin sati hudu wato wata daya kenan” murmushi duk akayi Hafiz najan bayan rigan Manaf dake murmushi cikeda tsokana yana kabarda hannunshi sanan anatse Baffa yace “yara nata aure amman asalin Babban yayan gidan nan shiru” dariya Hafiz yayi Ammi ta ballamai harara, anatse Baffa yace “gawata labari” sanan ahankali yafara magana yace “shekaru ashirin dasuka wuce abaya, lokacin Zayn yashiga JSS 1, Hafiz na primary school, su Hassan na Hussaini sune yara alokaci dudda suma primary suke, Maryama wato mahaifiyan Ummulkhairy ta haifi Ummulkhair” Baffa yadanyi shiru, ajiyan zuciya yasauke yace “bayan an haifi Khairy Maryam was very very sick, after series na test and investigations alokacin ne aka fara gano cewa mahaifiyar ki nada blood cancer!” Shiru kakejin dakin kaman ruwa ya hadiye kowa, ganin Baffa yakasa magana yasa ahankali Baba yace “Maman ki was very very scared Khairy son da Mama kemiki tun ranan dakika fado duniya ne, bansan mesa ba kodan agidan marayu ta taso tana matsayin ya mace batasan kowa nata ba tai wahalan rayuwa, kodan sabida taga kema mace ce batason kiyi wahalan rayuwan datayi gashi ance tanada cancer bazatai wani rayuwa mai tsawo ba dan lokacin bama agama sanin kan treatment na blood cancer ba yasa ranan cikin dare ina bacci akan kujera naji Mamanki ta tabani tana kiran sunana” Baba yadanyi shiru ahankali yace “bude idanu nayi naganta zaune kan gadon asibitin rikeda ke a hannu” Baba yakarayin shiru yadan fuzar da iska nai dumi, Ahankali yace “Maman ki was very very sick jikinta yay bala’in zafi tacemin tana ganin one of this days zata mutu dan haka nakira Baffa nacemai idan zai taho yazo mata dasu Manaf dake gidanshi wajen Ammi nacemata to ganin hankalinta atashe yake sanan takara kallonki” Baba yay shiru yace “tana kallon fuskanki tacemin batason Ummulkhairy tasha wahala, sanan duk duniyan nan banda ni babu wanda ta yarda dashi kaman Baffan ki tasan ko Bana duniya sai inda karfinshi yakare akan yarana sabida haka tanason ta aurar dake tun yanzu datake da ranta a inda ko yanzu yanzu tafadi tamutu zata tafi batada damuwa” Baba yakara yin shiru kowa na kallonshi, handkerchief yaciro daga aljihu yakai kan idanunshi dan ko kadan bai son yay kuka agaban yaran shi, kafadan shi Baffa ya matse sosai yakalli yaran yace “Baban ki yadauka awanan daren Maman ki zata rasu, bayan tamai maganan nan tasashi yakirani awaya, kunga acikin kuryan darenan haka nashiga mota nazo asibitin nan, cikin tsananin zazzabi tana rike dake a hannunta tace tanaso tabani amanarki sanan tana neman alfarma wajena…..” wani irin faduwa gaban Khairy dake kallon Baffa chass takeyi dabama tasan na miyeba, ahankali Baffa yace “Maman ki tace tanaso nahada Ummulkhair da Zayn babban dana wanda Mamanki takeso sosai sun shaku da mamanki sama da su Hafiz ma, tace tanaso nahada ku aure” Zayn da tunda aka fara maganan kanshi ke kasa sai alokacin yadago kanshi yakalle Babanshi dake Magana, Baffa yace “jikin Maman ki yay zafi yay tsanani duk mun zaci zata rasune, Gyadamata kai nayi na nuna amincewa na, tace mukaita masallaci adaura auren, I remember Baban ki yafita waje yadauko keken guragu muka daurata akai muka gungura keken har zuwa masallacin dake asibitin nan dayake nan kaman ba dare ba jama’a duk suna zazzaune some a kwance iri masu jinyan nanne, da sauransu limamun muka kira mukamai bayanin komi ya matukar tausayama Maman ki sanan aka gungurota aka shiga da ita masallaci tana rike dake a hannu limam yadauki microphone aka tada duka mutanen dake bacci” tsinkewa gaban Khairy yahauyi yana dawowa daidai hakama Batool, Ammi, Zayn dakuma Anty Mariya, kowa na kallon Baffa, murya chan kasa Baffa yace “all I had was 20k ajikina haka na bayar kudin sadaki dani da mahaifinki limamin masallacin mahaifiyar ki jama’an dake wajen suka shaida daurin aure tsakanin Ummulkhair Ahmad Muhammad da Zayn Abdullahi Gabas akan sadaki naira dubu ashirin!”
Khairy jitayi numfashinta zai dauke kunenta yay dummm kaman ta sume ne kaman tafice hayyacinta ne oho ita kanta bazata iya tantance wani yanayi take ciki ba, daga Baba har Baffa murmushi sukayi suka kalli juna, Baffa yace “inda ace Baffan nan naku nada yara mata dayawa zansa yarana maza duka su aurensu sabida inaso muhada zuru’a wanan amincin dake tsakanin mu na abota takoma na jini, saisa bayan mun daura auren muka yanke shawarana sai yaranmu sunyi girma sun mallaki hankalin junansu zamu sanar daku, yanzu ma bikin su Manaf ne sabida munaso muhada bikin su da kuma taron bikin su Zayn ayi atare saisu tare nan da wata daya lokacin Ummulkhairy itama tagama jarabawa tagama makaranta ko aminina” gyadamai kai Baba yayi yana wani irin murmushi, Ammi dajitayi komi na duniya ya tsaya mata chak takalli mijin nata, cikin wani irin masifa tace “Alhaji na dauki cikin Zayn na wata tara, na tsugunna na haifo dana dakaina batare da wata ko wani yatayani ba ninasan ciwon kan d’ana nasan wahalan danasha na tarbiyantan dazai ka kama shekaru kusan ashirin kenan kama d’ana aure baka sanar dani ba wlh wlh wlh kayi kadan!” Ammi tama Baffa magana babu ko shakkan shi guda akan idanunshi dayasa kowa yakalleta shima Zayn yakalleta uppan Baffa baice mata ba hakama Baba duk kallonta suke da Mom da Anty Mariya dasauran yaran.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button