ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

“Eh Gwaggo ina jinki sorry ba shareki nayiba, Abban nake jira nariga nakawo shi…” ahankali tashiga dagoda kanta kaman wata mara gaskiya cikeda kunya jin mutum na wayanshi ta tsokano fada tazo tafada jikin shi, kanta akasa ahankali sadaf sadaf tashiga fitowa tana matsawa baya kafin gently kanta nakasa batare data kalleshi ba tace “thank you” sanan ahankali tajuya tashiga tafiya har lokacin gabanta nafaduwa sosai. “You!” Taji kaman daga sama mutumin yakirata chak ta tsaya batare data juyoba, “turn around” taji muryanshi anatse yet with authority batasan mesaba amman kasa ketare abinda yace tayi tayi hakan yasa gently tajuyo sanan ahankali tadaga fuskanta takalleshi, wani dogon saurayi ne fari sol dashi kaman balarabe yana sanye da jumper na farar shadda bugaggiya kanshi babu hula gashinshi akwance baki sidik sai kyalli yake hannunshi rikeda iPhone 13 yazubamata idanu dababu alamun wasa daidai da digi acikinsu, hakanan jitayi takasa jure kallon mutumin dataga kaman ta sanshi amman ta manta a ina ta sanshi ta sauke kanta kasa, anatse yace “the next time I will see you making trouble I will arrest you!” dasauri tadago kanta ta kalleshi saida yafidi kalman arrest sanan police din ranan yafado mata arai, dauke kai yayi daga kallonta sanan yabude kofar motan daya tsaya jikinta ya shiga ciki tareda rufe marfin motan da sauri dayadan firgitata sanan ahankali tajuya tacigaba da tafiya ahankali.

Samin kanshi yayi da binta da kallo ta madubin motan, yanda take tafiya ahankali har lokacin bata dawo daidai ba, sanan ahankali yadauke kanshi daga kallonta jin wayanshi na ringing again screen din yakalla ganin Grandma yasa yabude motan yafito yace “this woman will not allow me leave in peace”.

Garden din takarasa tun daga nesa kawayenta dasuka hangota suka kwalamata kira hakan yasa takarasa zuwa inda suke zama tayi sanan tadauki bottle na ruwan dake gaban Farida tabude takai bakinta ta kwalkwale duk kallo suka bita dashi, saida ta shanye goran ruwan tass sanan ta ijiye tana sauke ijiyan zuciya, Farida tace “daga ina kike haka duk kinyi zufa kaman kin fito daga yaki” dan yatsine fuska tayi kaman bazatai magana ba ganin yanda suke kallonta yasa tace “Ahmad na mara shine yabiyoni and someone…..” tadanyi shiru kafin ahankali tace “wani mutumi yataimakeni” atare dukansu all the 5 friends sukace “wani mutumi” shiru tayi sai chan tace “oho nima ban sanshi ba” dukansu dariya sukahau yi dasauri takallesu tace “me” hada baki sukayi sukace bakomi, sharesu tayi kawai cus she doesn’t even feel okay batasan mesa ba, duk suna zaune wata kawarsu tashigo eatery dagudunta tana haki tace “kufito kugani yan sanda sun shigo school dinan anzo ana kwashe su Ahmad da Gang dinsu” dasauri Farida tace “ke haba let’s go video it musashi a internet” dukansu tashi sukayi itama ta tashi tabisu suka fice daga cikin garden din, van suka gani na police gaban wani eatry dake kusada garden din dasuke ciki, dasauri suka karasa gaban eatry din student sun cika wajen suna kallon Van din police, suna tsaye wajen dayay cha da mutane sukaga an fito da Ahmad da akasamai handcuff a hannu an sashi a van din sai abokanen shi na dazsu dasuka biyota guda biyu saikuma wasu guda biyu daban yan sandan sun fito dasu ana sakasu a van din saiga police man dinan shima yafito daga eatry har lokacin yana sanye da kayan dazu farin shadda waya a kunenshi still, hada idanu sukayi batasan mesaba jitayi gabanta yafadi dasauri ta sauke kanta kasa tareda juyawa ahankali tamabar wajen bata kara juyowa ba kawai tai hanyar class nasu, daidai lokacin ana shirin fara wani lecture kujera tasamu atsakiyan ajin ta zauna sanan tabude jakanta taciro note nata da pen aka fara lecture ko kadan takasa concentrating batasan mesa ba she just keep seeing police man face din da what happen today, gabaki daya all through da day har yamma ita kanta tasan yau ba school tazo ba takasa natsuwa tunanin shi da komi yacika mata kai, wuraren 5 na Yamma Adamu direba yazo daukan ta shiga motan tayi ahankali tace “Adamu please kafara kaini Coldstone nasayi ice cream nasha saimu wuce gida” cikeda girmamawa yace “to Miss Khairy” daura kanta tayi akan kujeran tajuyar da kanta tana kallon hanya tareda fuzar da ijiyan zuciya, she just hope tanashan ice cream dinan sanyin shi zaisa brain nata yay sanyi tadena all tunane tunanin datakeyi tun safe.

Agaban wani Babban joint na coldstone Adamu yay parking hakan yasa tabude motan tafito ta shiga ciki, daidai wani Babban Jeep na shigowa wajen parking yayi kusa da Benz da Adamu ke ciki, bude gaban motan yayi yafito ahankali wanan karan yana sanye da kayan yan sanda Rolex din dake daure a hannunshi yakalla shidda saura, sanan yazaga zuwa boot din jeep din yabude keken guragu yaciro ya ijiye ya maida boot din yarufe sanan yadawo bangaren baya yabude motan wata kyakkyawan tsohuwa ce fara sol kaman balarabiya zaune abayan tasaka Riga da zani irin na tsofaffi anmai dinkin Bubu kafafunta da hannayenta sunsha lalli, hannunshi yamikamata batare dayace mata uppan ba hararanshi tayi tana kama hannun nashi tamike tsaye da kyar tana masifa tace “idan kaga dama kai gaba dani dagayau har jibi Ice cream dai saika kaini nasaiwa jikoki na ja’irin yaro kawai” ko kala baice mata ba da taimakonshi ya daurata akan keken sanan yamaida kofan bayan yarufe da karfi tace “kama balla motan baban karfi, ubanka zai sayamin wata Alhamdulilah Allah yamai arziki rufin asiri danasha takaici” cikeda masifa yace “wlh Goggo in baki shiru ba anan zan barki na shiga ciki nasayo” wani kalan murmushi tayi tamaka bakinta tace “yo ai nadauka gaba kake dani to muje nadena” dan murmushi kadan kawai yayi sanan yashiga turata zuwa gaban entrace din dakenan divided into 3, staircase ne gefe da gefe sai tsakiya a bit sloppy floor dazaka haura ka shiga cikin shagon, daidai lokacin security na budewa Khairy kofa tana fitowa rikeda paper bag na ice cream din dakuma handbag dinta rataye a shoulder dinta, saiga wasu yara su biyu maza dabazasu wuce 8yrs ba suna guje guje kowanne rikeda ice cream dinshi dayan kawai ya mamayi brother shi ya fizge ice cream din hakan yasa brother yay ihu yabi dan uwanshi da gudu Khairy dabude mata kofa kenan tasa kafa tafito zata fara sauka daga staircase din kawai yaran suka fito suka mugun bangajeta dayasa ita kanta tasaki wani irin ihu kafanta ya gicce abunku da tiles kawai ta kifo zata fadi da mugun sauri Gwaggo tace “Subhanallahi” dawani irin sauri yasaki wheelchair Gwaggo daidai kanta zai daki dakaIUlin stairs din…1️⃣7️⃣

Free page
Ahankali yake tuki ganin ya shigo cikin estate dinsu, saida yakarasa gaban wani dankareren gate sanan ya danna horn, budemai gate da akayi yasa yaja motan zuwa cikin gidan dakeda bala’in kyau kuma babban gaske ga flowers dasuka karama gidan kyau sosai, parking yayi abangaren parking sanan yakashe motan yana kallon cikin gidan dababu kowa sai gardener dinsu daketa yayyanke flowers yana gyara su, yakai kusan 1min cikakke zaune a motan yay shiru sanan ahankali yabude kofar motan yafito yamaida kofan yarufe sanan yafara tafiya dai dai yawuce zuwa babban flat dakenan shine first flat a gidan, bude kofa yayi ahankali tareda sallama chan ciki sanan yashiga babban falon da babu kowa ciki, falon ya bala’in hadu yaji furnitures, saikuma dan kara dayakeji a kitchen da alamu mai aikice ke wanke wanke, juyawa yayi zai fice kaman daga sama yaji ankirashi. “Aliyu” dan juyoda kanshi yayi ya waigo, wata matace doguwa mai jiki fara kal da ita taci gayu da sarkan gwal a wuyanta wacce bazata wuce 40 ba tana sanye da lace ja da baki ke saukowa daga benen, kallo daya yamata yadauke kai yace “barka da rana Mami” dan murmushi matan tayi sanan takalli agogo bangon falon ganin is just 11 yasa tace “Lafiya kadawo gida ware haka Aliyu”? Batare daya kalletaba ahankali yace “lpy lau Mami” gyadamai kai tayi tana kallonshi still tace “tom shikenan, mezakaci a aiko maka dashi”? Batare daya kalleta ba har lokacin yajuya yace “zanci abinci wajen Gwaggo” yana maganan yajuya yafice tareda rufo kofan binshi da kallo tayi ta jikin window falon har saida yay side din Kaka yabace mata daga gani sanan tasami kujera ta zauna tanadan karkada kafa tunda take bata taba ganin wanda uniform na police kemai kyau kaman Aliyu ba, haryau tarasa maisa Aliyu yawani zama police ba yaron dayay lafiyayyen karatu yakuma gama da good result, kwanciya ahankali tayi tana kwalama Yar aikinta kira dan tazo ta danne mata kafa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button