ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.

wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp

This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️
5️⃣9️⃣

Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.

wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp

This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️

Daga Baffa, Anty Mariya, Baba da Mom babu wanda bai mata fada da wa’azi cikinsu ba, wajajen 6 Baba yace “wife kutafi da ita ta shirya motocin daukanta na hanya” gyadamai kai Anty Mariya tayi sanan suka dagata ahankali tana kuka sosai daki aka kaita wanka akasa tayi sanan aka bata ruwan turare tayi dashi sanan tafito shiryata sukayi cikin wani milk hadadden lafaya mai bala’in kyau, 6:40 hadaddun motoci sunyi layi gaban gidansu kowane mota dan sanda ne da full uniform keja dan duka boys sun Aliyu Dad yakira.
Tsaf aka shiryata bakaramin kyau tayiba aka lullubeta sanan aka fito da ita takasa daina kuka she can’t believe shikenan dagayau tabar gidan iyayenta rungume Baba tayi gam gam ana guda ana ayiriri sun dade ahaka shima Baba idanunshi sunyi ja sosai sanan yadagota yace “ya isa haka kukan kar kanki yayi ciwo” ahankali yakama hannunta yasaukar da ita kasa ana binsu suka fita tsakar gida har zuwa kofar gida da kanshi yabude kofar motan kafin ahankali yace “go in peace Ummulkhairy, ubangiji Allah yama aurenki albarka, ina rokon Allah to bless your new home yakuma haskaka rayuwan aurenki, go my daughter” yay maganan yana sata cikin motan ta zauna ahankali tana kuka, shiga motocin su Mom sukayi da kawayenta da Batool sanan aka tafi da ita.

Tsakanin gidansu Aliyu da nasu nada nisa sosai, dan sai wajajen 8 nadare sukakai, wowww Batool dake gaban motan tafadi ganin Babban gidansu Aliyu, an bude gate wato kudi nada kyau dudda su kansu basusan da bikin ba but they were able to pull something an zuba kujeru hadadun agidan ga DJ an kawo, yan uwa sun cika gidan ko’ina hayaniya ga girke girke abinci kala kala na yawo a tsakar gidan, kafin sufito daga mota Gwaggo da Mami dasukaci gayu na gani afada sukazo taransu idan kaga Gwaggo zaka dauka an mata bushara da Aljanna ne, fito da Khairy akayi daga mota kawai Gwaggo tafashe da kuka Dan she can’t believe Ummulkhairy ce aka kawomata amatsayin Matar Aliyu danta, taruwa akai kan Gwaggo dake kuka cikin kuka tace “ni kubani y’ata na rungume” murmushi su Mom sukayi sanan suka kawo mata Ummulkhairy dakenan alullube tawani irin rungumeta tana mata ruwan saman addu’a a godiya aka sanan tasaketa tace “kushigo” shigowa sukayi babban falon Mami aka fara kaita aka zaunar da ita atsakiyan dakin ana waka ana rawa Mami na murmushi ana cemata saita saya baki zata ganta, kudi Mami takawo da box na warwarayen zinare tadaura kan jikin Khairy ana ihu ana guda sanan aka bude mata fuskan Khairy kallon fuskan Khairy da idanunta ke kasa tayi sanan tamata addu’a kafin a dauketa akaita dakin Gwaggo, Gwaggo da dan kafafunta dababu lafiya rawa tahauyi Haba zokaga dariya sanan takawo turaman zani guda ashirin tabama Khairy da bandir na yan dubu dai dai guda uku, da zoben azurfa da warwaron azurfa da sarkan azurfa masu kyau sosai aka dinga guda, tashi Mom da Anty Mariya sukayi sukai sallama da su Baffa najiransu suzo aje aduba Aliyu, da Kyar Khairy tasakesu suka tafi sai kuka take sanan Kaka takaita dakinta dan fir tace “ita awajenta Khairy zata zaune har zuwa aliyu yaji sauki tanada dakuma daban daban dayawa a side nata, wani hadadden daki aka kai Khairy gadon ciki ma sabone fill dan dazu da rana Dad yasa wani furniture company suka kawo aka chanza komi na dakin aka fitarda nada zaunar da ita akai akan gado itada Batool da Amal kawarta sauran mutane duk suka tafi.

Wuraren 10 su Baba sukakai asibitin Dad, Dad dakanshi yazo yadauke su akasa yace “barkanku da zuwa” gaisawa sukayi suna sama Baba yace “yajikin nashi” ijiyan zuciya Dad yasauke yace “Alhamdulillah muje” sukai sama har zuwa wajen wani daki, bude kofan Dad yayi ahankali yashiga su Baba biyedashi Aliyu na kwance kan wani hadadden gado da kayan asibiti idanunshi akulle he’s attach to wani machine, salati su Baba sukayi, Baffa yace “what’s the plan yanzu” dan ijiyan zuciya Dad yasauke yace “wanan machine din shine taimakama heart dinshi to beat, beating na heart nashi is very slow, so yanzu dai gobe zamu fitardashi zuwa Oman akwai wani heart Dr achan he’s my very close friend tare mukai karatu a Ukraine yace nakawoshi Aliyu will be fine” dukansu ajiyan zuciya suka sauke Baba yace “In sha Allah zaiji sauki, please if u need anything we are here for you yanzu munzama family” murmushi Dad yamusu cikedajin dadin maganan su yace “Allah yabar zumunci nagode sosai” motsi da Aliyu yayi yasa dukansu suka kalleshi dasauri Baban yay wajen gado yana kama hannunshi yace “Aliyu, Hydar I am here can you hear me”? Wani irin bude idanunshi Aliyu yayi kadan da kana gani kasan baya cikin hayyacinshi sanan murya chan kasa yace “Um….mulk….hair” kafin yakara lumshe idanu kaman bashi ne yay motsi ba, sakinshi Dad yayi yadanyi murmushi yajuyo yakalli su Baba da jikinsu yay sanyi sosai yace “tun shekaran jiya haka yake saidai yadan bude idanu kadan yakira sunan Ummulkhairy yakoma” dan murmushi Dad yasakeyi sanan yakalli Aliyun yace “one thing I am sure of shine d’ana na bala’in son Ummulkhairy so thank you Alhaji dakuka auramai Ummulkhairy bazan taba mantawa da wanan kyautatawan dakukamin da d’ana ba” yay maganan yana juyowa yakalli su Baba daduk sukejin badadi suna addu’a Allah yabashi lpy, sun dade a asibitin sai wajajen 12 na dare sanan suka tafi, Baba da Baffa sun dade suna magana sanan kowa yawuce gidanshi.

Saida sukakai gida sanan Mom takalli Baffa kafin tafita daga cikin motan ahankali tace “one thing danasani cewa inaso gamedakai shine rashin yanke hukunci acikin fushi, nasan ba hurumina bane nan amman inaso na roki alfarma biyu daga wajenka” tai dan shiru tace “nafarko shine inaso kamaida Ammi and inaso kai kokari and look at her situation and understand her, batasan da Auren nan ba itace mahaifiyar Zayn, taci buri kan danta is understandable idan taki yarda da Auren nan kowa da kalan zuciyanshi, kuma yanda Zayn bai auri yarinyar nan ba barabonshi bace wlh inda rabonshi ne daba Ammi ba ko duk aduniyan nan ne basu isa suraba Auren nan ba, sai alfarma tabiyu shine ko’ina Zayn yaje ka kirashi danka ne, nasan yanachan cikeda damuwa yasa kazama karamin mutum da sauransu kanunamai bahaka bane yadawo gida, Auren Ummulkhairy ko rashin aurenta won’t change kai mahaifinshi ne yazo idan yanason wacce Ammi keso ya aura wato Aisha kaje ka nemamai Auren idan bayaso yakawo kowa yakeso ya aura, rayuwa batada tabbas kowa datashi kaddaran just look at Aliyu yanzu yanachan kwance rai hannun Allah yay giving up but Allah yaga zuciyanshi cikin sauki yabashi Ummulkhairy, komi yafaru nada dalili sometimes abinda mu iyaye kesoma yaranmu is not the best or Khair for them, I know u are hurt amman kayakuri and forget everything let this family continue to be in peace kaji”? Gyadamata kai Baffa yayi ahankali bude kofa tayi zata fita dasauri yakamo hannunta hakan yasa tajuyo takalleshi, ahankali yace “I am so lucky to marry a wife like you, Allah yamiki albarka” murmushi tayi tace “Ameen” sanan tawuce ta tafi shikuma yadan dade zaune a motan sanan yaciro wayanshi yakira number Zayn ringing yake yana gab da tsinkewa yadauka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button