ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

 PROMISE OF THE HEART ????


    ✍????M SHAKUR

3️⃣

~Nigeria~
Wata babbar mace ce doguwa chocolate skin tsaye cikin wani lafiyayyen hadadden kitchen ginin zamani, tana sanye dawata doguwan rigan Atampa mai kyan bala’i ga kallabi daure akanta da kana gani kasan daura dankwalin kawai tayi amman hakan baihana kwantaccen black gashinta dake gauraye da farare lekowa ba, tana tsaye agaban wani hadadden babban gas a kitchen tanama wata yar aiki dake juya basmati rice a tukunya dawani wood spoon magana sukaji wata zazzakan murya dake ratsa zuciya na y’a mace ta kwala ma matar uban kira. “Mama nadawo, nakawo miki wasu kawayena ki gansu” wani irin kwashewa da dariya yar aikin dake juya abinci a tukunya tayi takalli Matar da aka kira da Mama datai tsaye kawai tama rasa ta cewa tace “Hajiya wlh tun ina iya kirga yawan kawayen Khairy harna bace a kirgan” kwafa kawai Matar da aka kira da Mama tayi tace “karasa juya abincin sai ki kwashe a warmer Ladid…..” bata idasa maganan ba aka kara rangadamata kira da wanan zakakkiyar muryan kaman ana busa sarewa. “Mamaaaa kina ina zoki gansu” dafa goshinta Matar tayi cikeda takaici tace “Allah nagode maka dakabani wanan yarinya, ina ganin Ummulkhairy ce zata bani hawan jini aduniyan nan” tai maganan tana fitadaga kitchen din ta hanyar bude kofa tafice, tana fitowa dining tai kicibus da yammata kusan su tara a zazzaune kan lafiyayyun kujerun falon suna maganganu suna hira suna kallon lafiyayyen hadaden falon dayaji Cubana furnitures, ganin Matar da kallo daya suka mata suka gane itace mahaifiyar Khairy yasa duk suka zubo daga kan kujerun cikeda girmamawa duk suka gaidata. “Mama ina yini, Mama barka da rana, Mama ina gajiya” lafiyayyen murmushi ta sakin musu tana karasowa tsakiyan falon tana bindi da kallo daidai tace “Masha Allah sassannunku da zuwa yammata yakaratu”? Kafin subata amsa wata kyakkyawan budurwa yarinya chocolate skin color, yar doguwa bachan sosai ba dabazata wuce 20yrs, skin dinta nawani kalan glowing fuskanta babu ko kuraje guda, tanada dan dogon hanci yet kuma dan karami dan diss afuskanta but fitacce, tanada manya manyan pure white eyes, idanunta are very big sunada wani kalan adorable spherical shape that is just damn gorgeous, dan kana kallonta the first thing dazasu fara daukan maka hankali a fuskanta are her big white eyes, ga eyelash dinta dogaye bakake cikakku, hakama gashin giranta, tanada goshi wanda kusan yarabu biyu ne rabi duk gashi ne dayake nan baki sidik sun kwanta daya karama fuskanta wani kalan kyau dan zaka dauka buzuwa ce sai dayan rabin kuma fatarta ne dayataho har gira, tana sanye da dogon rigan atampa itama da dan kwalinta akanta, tawani buga uban ihu da saida falon ya amsa gabadaya. “Mamaaaa” yanda ta kwala mata uban kiran nan yasa mahaifiyar nata tadago da kanta tareda juyowa ta zuba mata idanuwanta kurii irin na jama’a yaya zanyi da wanan yarinyar ne? Wani irin washe baki Khairy tayi cute saitin white teeth dinta suka bayyana tashiga saukowa daga stairs din dagudu kaman ba ita Mamar kema kallon zaki ganeba kawai tawani irin fada jikin Maman nata tana ihu sosai tana rawa ta kankame Maman kamkam. “Wayyooo Mama wlh nai missing naki, inata nemanki nadauka kin fita ne har hankalina yatashi ashe kina kitchen, Mama tun safe yau banganki ba awa nawa yanzu bansaki a idona ba karfe biyar fa, nai kewanki Maman mu, Mamana, I miss you Mommy Ummulkhaiyr” tai maganan tana kara kankamet Mama cikeda tsananin murna, dudda yanda Mama ke mugun kule da ita saida tai murmushi har cikin ranta duk cikin yaranta babu wanda ke sonta kaman yanda Khairy ke sonta, idan Khairy tadawo gida batanan wani zubin har zazzabi takeyi, Son da Khairy ke mata dabanne, gabaki dayan kawayenta baki suka sake suna kallon Khairy yanda ta kankame mamanta cikeda murna tana rawa kaman wata yar karaman yarinya, murmushi kawai Maman takeyi ganin yanda kawayen ke kallon Khairy sabida wayan nan wasu new set ne basu saba ganin haukanta agidaba yasa Mama tace “ke dalla cikani kije kitchen kitaya Ladidi ku kwaso abinci kiyi serving friends naki kuci” sakin Mama tayi ahankali tana murmushi dake bala’in kara mata kyau tana kallon Mama tace “tom Mama” sanan tawuce kitchen da ihunta ta shiga kitchen din. “Ladi kwas kwas!” Tsabagen yanda Ladidi tafirgita batasan lokacin data saki cokali data rike a hannunta kasa ba, kwashewa da dariya Khairy tayi ganin yanda Ladidi tafirgita, Ladidi ta watsa mata harara tana dafa kirjinta da hannu jin yanda yake bugawa tace “aniyarki tabiki Khairy bani zaki sawa bugawan zuciya ba wlh” dariya Khairy tayi tadauki spoon tazo kusa da ita tana kallon tukunyar tana murmushi tace “uhmm smells good, let’s have a taste” abincin tadeba takai baki tana lumshe ido, harara Ladidi tabita dashi tana kallon long full lushy eyelash dinta dazakaji kaman ka cire kasama naka sabida kyau, dan murmushi tayi tace “yayi dadi Khairy? Kinga nasa coconut milk dakikace nadinga sawa” bude idanu Khairy tayi ta kalleta sanan ta yatsine fuska tace “yayi dadi ba laifi amman ba kaman nawa ba” batarai Ladidi tayi hakan yasa Khairy tafashe da dariya tace “ki zubamana nida kawayena kizo ku gaisa” hararanta Ladidi tayi tace “Malama ki tsaya ki dauki abincinku ki kaimusu ba inda zani nagaji da gaisawa da kawayenki, nibansan ko kamfani gareki na kawaye ba” turobaki Khairy tayi tace “bakinciki kikemin kinga inada kawaye masu sona ke bakida kawa ko daya” dasauri Ladidi tanuna kanta tace “ni Khairy bakin ciki ana zaune lafiya, kawayenki sunfi dari, ni idan Allah yabani kawaye ko sama da biyu ne bansan yanda zanyi dasu ba” hararanta Khairy tayi tadauki Baban tray da Ladidi tajera musu different abinci akai a different plate guda 5 tafita dasu taje takai musu sanan tadawo ladidi na kallonta tace “yanaga kin dawo” akufule tace “su tara ne plus ni goma, kuma is just 5 plate of food nafita dashi” kasa magana Ladidi tayi kawai tashiga zuba wasu sababbi tass abincin yakare Ladidi tace “yayyinki suka dawo maizasuci” “oho” ta amsata akufule tafice abinta takaimusu abinci suka shiga ci suna hira shaaaa kakeji sun cika falon da hayaniya kadauka biki ake kowani liyafa aka hada, lekosu Ladidi tayi daga kitchen kwafa tayi tace “yo wlh ban kara daura wani girkin barima kiga tafiyata zanyi, masu gida nakema aiki ba kawayenki ba, yarinya kowani kare da doki kawayenki ne, mijinki zai sha fama Khairy” tai maganan tana komawa ciki, hada yan kayanta tayi a handbag dinan sanan tabi takofar kitchen tafice abinta daman inhar tagama aikin yamma indai Hajiya na sama tafiyanta take saidai in tana kasa ne saitaje tamata sallama tawuce.

Sai wuraren 6 sanan kawayen nata suka fito bayan takaisu sama sunma Mama sallama har compound tarakosu inda sukai parking motocin su duk suka shishiga, daya daga cikinsu taleko bayan tama motarta benz key tace “wai Khairy yaushe zaki farajan mota kine eh? Gamu duk mu munaja ke kadaine kullum driver ke kawowa” kaman zatai kuka tace “ba su Mama bane da Baba wai tsoro suke su barni nafara tuki wai nacika rawan kai kumafa na iya wlh Paddy” dariya dukansu sukayi wacce ta kira da Paddy tace “ke da karfin hali zakisa su barki kifara tuki wlh daukan mota kawai zakiyi wataran ki fice, Babe magrib tayi bari muwuce see you tomorrow at school” hannu tadaga musu tace “see yah girls” gateman dinsu yabude musu gate suka fice motoci biyar daidai kuma motocin yayinta na shigowa gida na Baban su biyeda su, washe baki tayi tana tafi ahankali tana kallon motar Baban su dake shigowa last tace “oyoyo Baba” motan na parking tai wajen motan da gudu batare databi na yayyinta da kallo bama.
???? PROMISE OF THE HEART ????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button