ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Popcorn yasai musu, unsweetened yasaima kanshi dan baicin sugar shi ko kadan itakuma yasaimata mai milk sanan yazauna yana jiranta.

Fitsari tayi sanan tafito tanadan murmushi ita kunya ma takeji, tana cikin tafiya taji an kwalamata kira Ummulkhairy dasauri tajuyo, ganin class governor dinsu yasa tadan tsaya tana murmushi shima yakaraso wajenta da sauri yana rikeda cotton candy guda biyu a hannunshi da alama bashi kadai bane, ganinta yasa yace “wow kema kinzo shakatawa” murmushi tayi tace “eh Governor ya aiki ya shirin exam” ahankali yace “Alhamdulilah” yana kallonta ganin yanda tai kyau yadade yanason Khairy amman yakasa gayamata dan yake yayi yace “u look good Khairy” murmushi tayi tace “thank you bari naje” tajuya zata wuce dasauri yabiyota gabanta yasha sanan yamika mata one cotton candy dake hannunshi yace “atleast take this” girgizamai kai tayi tace “no thank you Governor” dasauri yace “I insist Allah saikin amsa, nawane dana little sister na dama, nakoma nakara sayowa, idan baki amsa ba zanta binki ne wlh” badan taso ba bataso taga kaman wulakanci tamai wanan ma daya rantse saita amsa yasa gently tamika hannu takarbi wanda yake bata sanan tace “thank u” tawuce da sauri binta dawani irin mayen kallo yayi sanan yace “see you on Monday Khairy” ko tankashi batayiba dasauri take tafiya kanta akasa dan tabata lokaci tabar Ya Aliyu chan, jitayi ajikinta ana kallonta, ahankali tadaga kanta, Aliyu tagani tsaye rikeda pop corn guda biyu a hannu, fuskanshi kadai tagani ya tabbatar mata da yaganta tareda class governor dinsu, jitayi kawai jikinta yahau rawa sakin cotton candy don tayi akasa sanan ta taho da sauri kafin takaraso gabanshi gani tayi cikeda bacinrai yawani irin jefar da pop corns din akasa yajuya fuuu kaman zaki yawuce dasauri tabishi tana kiranshi. “Ya Aliyu Ya Aliyu” amman ko waigowa baiyiba har wajen dayay parking mota kafin ta isa wajen dan one step dinshi shine like 3 or 4 step nata harya shiga mota wani irin jan motanshi yayi Saura kiris yabuge wasu yarama ita kanta saida tai ihu Allah yakiyaye bai bugesu ba yafita daga wajen da balDa’in gudu.3️⃣6️⃣

Yauma hartai bacci Aliyu bai kirata ba ita at this junction tama fara tsoro haka Aliyu keda fushi, abinma haduwa yayi yataru yamata yawa hakan yasa ta tashi da zazzabi jikinta zafi gashi hancinta yatoshe mura, wuraren 7:30 tafito kasa, ganinta wani iri yasa Mom tace “meke damunki idanunki sundan kumbura da hancinki” ahankali tace “mura ne” jin yanda take magana da hanci yasa Mom tace “Ayyah sannu zoki breakfast bari nakowa miki maganin mura” kunu tadeba tafara sha bata wani dade ba Mom tasauko rikeda maganin mura karba tayi tasha sanan takarasa shanye kunun ta tashi tama Mom sallama ta tafi.

Tun kafin sukarasa wajen parking space din ta hango Aliyu tsaye yay wani irin bala’in kyau yakara haske kaman wani balarabe, yana sanye da uniform din yan sanda jingine da motanshi yay folding hannunshi a kirji yana kallon motansu tunda ta doso, idanunshi sun fada ciki kadan kana ganinshi kasan shima yawahala yan kwanakin nan kaman yanda itama ta wahala.

Jitayi wani abu yazomata wuya amman ta danne, parking Adamu yayi hakan yasa tafito daga motan ahankali kallonshi tayi kaman yanda yake kallonta, hawayen dataji yazo mata yasa takauda kanta gefe dasauri taredakai bayan hannunta tashare sanan ahankali tadaga kafanta tafara tafiya wuceshi tayi ahankali kaman bata ganshi ba dawani irin sauri yasha gabanta hakan yasa chak ta tsaya batare data dagokai ta kalleshi ba dan dazaran ta kalleshi zata iya kuka kuma bataso tayi, ahankali tace “excuse me please I have exam by 9” dan ijiyan zuciya yasauke tareda lumshe idanunshi jin muryanta sanan ahankali yabude su yadaura akanta, murya chan kasa yace “Ummulkhair!” Wani abune yataso mata tundaga cikinta harzuwa wuyanta dataji inbata amayar dashiba zata iya mutuwa dago idanunta dasukai jaa tayi sun cikada kwala tace “don’t call my name again Ya Aliyu, nadauka ai kadena daukan wayana, kadaina kirana, kadaina texting dina? Why are you here then? Mekazo nema wajena”? Kallonta yake idanunshi sundanyi ja, jiyayi zuciyanshi na tafarfasa, ko kadan baiso yanunama Khairy fushin shi that’s the reason why he avoided her yamaki wayada ita, wani irin zuciya yakawomai wuya ciki wani irin harsh tone that’s not loud yace “kinmin laifi and kina fushi dani? Why would you talk to anyman har kina karban abinshi why?!” Yamata wani kalan ihu da saida tadan firgita tadan koma baya tana kalle kalle tagodema Allah dababu kowa awajen, zuciyanshi yanuna mata yace “kinsan what you did to me? To my heart haaa? Why will you talk to anyman why?? Akanme zaki tsaya kinama wani namiji magana bayan kinsan I love you! My heart beats for you! You are my life! U are my happiness! You are my everything Khairy haaa” yanda idanunshi taga sunyi jajir saida abin yabata tsoro kaman zai daketa, jijiyoyin kanshi sun fito, bayan hannunta tasa tagoge hawayen daya zubomata kafin ahankali tace “Ya Hydar akanme zakai tunanin wani abu bayan nacemaka class governor dinmu ne, is it my fault we bumped into each other that day? Ya Aliyu akanme zakai tunanin wani nakeso bayan nariga nama zuciyata alkawari cewa ita taka ce, zuciyata, gangan jikina, ruhina duka nakane Ya Aliyu Wanan shine ALKAWARIN ZUCIYA na, akan me zakai tunanin bana sonka uhmm”? Hawayen daya zubomata ta share, kawai tawuce fuuuu hannu yamika zai kirata amman yakasa cikin wani irin fushi yadaki motanshi da kafa shikanshi baisan mesa yake da mugun kishi nan ba.

Adaddafe tai exam din ranan, inda ace batai karatu ba dababu abinda zata iya rubutawa sabida yanda babu abinda kemata dadin nan, bata taba sanin haka akeji idan akai fada da masoyi ba sai yau, she miss Aliyu badly, she just miss him.
Tana gama paper tafito bata tsaya jiran su Besty da Amal ba sabida yanda batajin dadin komi ga jikinta yakara zafi, fitowa tayi yanda takeji batajin zama ta iya jiran Adamu yazo daukanta ba hakan yasa tafara tafiya tai hanyar gate, wani irin shan gabanta da mota Aliyu yayi tana ganin motan tajuya zata chanza hanya da sauri yafito baima tsaya mata magana ba hannunta yaja ganin mutane yasa tabishi dan ayanda yake zai iya cewa daukanta zaiyi gaban mutane idan bata bishi ba, bude mata yayi tashiga batare data kalleshi ba sanan yamaida kofan yarufe yazagaya yashiga mazaunin direba yaja motan, batare data kalleshi ba tace “kana fita daga gate kasauke ni natare cab natafi gida” kallonta yayi da jajayen idanunshi cikin husky voice dinshi yace “idan naki fa” hannunta tadaura akan fuska tafashe da kuka sosai cikin kuka tace “I said I am sorry, I don’t have anything to do with class governor munhadu ne by accident, he said yazo wajen da sister shine, and he insisted saina karbi candy hannunshi, I don’t wanna be rude koyaga namai wulakanci saisa na amsa, nabaka hakuri kaki hakura what do you want from me, what do you want from me?” Wani irin fizgota taji anyi da bala’in karfi, dawani irin sauri tabude idanunta jikinta na rawa, tuki Aliyu yake da hannu daya akan titi amman ya fizgota da karfi tana jikin kafadanshi yakai hannunshi ta waist nata yariketa gam ajikinshi takasa kwace kanta yana kallon hanya, dasauri takalli hanyan jikinta narawa tace “Ya Aliyu dan Allah zamuyi accident kayi parking” gangarawa gefen hanya yayi yawani kalan taka burki kaman motan zai kife kankameshi tayi tareda runtse ido gam gam jikinta narawa still, habanta dataji ankama yasa tabude idanunta ahankali, hada idanu sukai da Aliyu da idanunshi sukai ja faduwa taji gabanta nayi, cikin wani irin murya yace “you ask wat do I want from you” gyadamai kai tayi tana wani irin shakkan shi, wani kallon fuskanta yake ahankali yace “I want you Ummulkhair! I want you so bad saisa my heart can not stand yaga kinama any namiji magana, zuciyana yakusan bugawa ranan I had an accident” dan zaro idanu tayi cikeda mamaki, lumshe idanu yayi sanan ahankali yakai fuskanshi dab da nata yana kallonta dawani irin sauri ta lumshe idanunta gabanta nafaduwa dasauri dasauri yadade yana kallon fuskanta ahaka kafin ahankali yadaura goshinshi kan nata yanajin saukan numfashinta akan fuskanshi, cikin wani whispering voice dake nuna so yace “I am sorry for hurting you, I couldn’t help it, Ummulkhair ina sonki da yawa and Aliyu is a very very jealous man bayin kaina bane, can you put up with me? I can’t help it bazan iya magance kishina akanki ba, zaki iya rayuwa dani eh Ummulkhair?” Jitayi zuciyan ta gabaki daya yasaki gyadamai kai tayi ahankali tace “but don’t ever hurt me the way you did by not answering and responding to my calls, Ya Aliyu I….Love yhuu” this is the first time tafadimai kalman daya dade yakeso yaji daga bakinta, ahankali yace “you are the PROMISE OF MY HEART Khairy” ahankali tace “Ya Aliyu nima kaine ALKAWARIN ZUCIYA ta” ahankali yamata peck a forehead sanan yakai hannunshi yashare mata fuska tass sanan gently yasake ta yamaidata kujeran datake kafin ahankali yatada motan zuwa pharmacy, magunguna yasayo mata da ruwa da kanshi yabata sai kallonta yake sanan yadawo motan yatada har anguwan su Baffa yakawota nesa da gida yay parking sanan yakalleta, kallonshi tayi sanan ahankali tabude motan tasauka tawuce saida yaga shi ganta gida sanan yatada motan yabar anguwDdan.
3️⃣7️⃣

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button