ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Wuraren 4 tana zaune adakinta tana waya da Aliyu da this is the third time yake kiranta tun bayan text datamishi dazu kan ta yanke duk yadamu harda cemata zai dawo tahanashi karya dawo dudda haka yaki yarda, turo kofa Batool tayi tawani fado gadon tace “Malama Ya Zayn yace kifito kuje” ahankali tace “kije kicemai nafasa zuwa” hararanta Batool tayi tace “wacece Yar aikenki ni kinga tafiyata wajen Mom bye” Aliyu dakejin maganan su yace “waye Zayn? Ina zaku”? Dan yatsine fuska tayi tace “gidan mu zani wajen Baba, Ya Zayn kamanta Babban yayanmu dandan Baffan mune” dan ijiyan zuciya taji yasauke kafin ahankali yace “go and tell him u are not going, gobe Adamu yakaiki” gyadamai kai tayi tace “tom bari naje” katse wayan tayi ta ijiye kan gado sanan taja wani gyalen Batool data jefar kan gado tadaura akanta dababu dan kwali tazura silipas tawuce tafita”.

Yana zaune cikin mota yakafa black sun glasses a idanunshi kaman wani makaho yana kallon kofar flat din Mom, sai uban kamshi yake yasaka wani gizna mai ruwan toka ajikinshi kaman wani ango, bude kofan flat din Mom da akayi yasa ya gyara zama yana kallon flat din da kyau, fitowa tayi babu komi a hannunta sanye dawani pink bathroom slippers da kumbunan kafanta sukai Zara zara sukai kyau aciki, har lokacin tana sanye da gown din dake jikinta dazu, hannunta dataji ciwo saiwani kaffa kaffa take dashi kaman Yar yarinya daga ganinta kasan bata sabajin ciwo ba and she hates getting injured, fuskanta looks so innocent and so beautiful tana wani irin glowing idanunta subyi fari kal kaman tana wankesu da hypo, pink lips dinta ko daganan zaune amota da bakin glass dinan a idanunshi yana iya ganinsu, gani yayi ta tsaya takalli waya nan tsuntsayen dayagani anan barandan Mom acikin cage dinsu masu kyau dankoshi dazu dazai shigo saida ta tsaya ya kalli tsuntsayen dan sunyi kyau, murmushi tayi sosai da he could see all side dimples nata na lotsawa jerin gajejjerun white baby teeth nata sun fito tana kallonsu sanan ta tashi tajuyo tana saukowa daga staircase din, ahankali yakai hannunshi yadaura kan kirjinshi dayaji every step datai taking yana jinshi a heart dinshi, tunda yake shi he never baitaba jin haka on anygirl ba, shi baima taba tsayawa yakalli any girl kaman yanda yakalli Khairy yauba, he don’t know mesa kawai he just like how innocent she is, dan iska always know dan uwanshi idan yaganshi but anytime yakalli Khairy he sees yarinya that doesn’t know anything, yayi nisa acikin tunanin yaji tai knocking glass din motarshi wani irin daure fuska yayi batare daya saukarda glass din kasa ba yay unlocking car din hakan yasa tabude kofar motan kallo daya tamai sanan tadan sunnar da kai ahankali tace “Ya Zayn baranj…..” “you don’t talk to me daga waje get in kafin nabata miki rai” jitayi ranta yabaci ahankali tashigo motan tazauna zata fara magana yace “rufemin kofan mota” rufe kofan motan tayi ahankali kafin tai magana yatada motan yaja ana budemai kofa dasauri tace “Ya Zayn bazani ba shine abinda nazo nafadama” batare daya kalleta ba yace “idan munkai kidawo” dan jim tayi ranta nabaci, batare daya kalleta ba yace “sit belt Miss” jan sit belt din tayi tasaka sanan ahankali tamaida kanta tana kallon haDnya.
4️⃣2️⃣

Itadai shuuu kawai taji bamatajin maganganun mutane, sama kawai take kallo tana kallon watan dayay haske sosai ga stars ko’ina, hannun Zayn tarike gam daya bala’in rude ahankali tace “Ya Z…yn ni…..” ganin bata iya magana da kyau the more tana magana the more jini na bulbulowa ga wukan acikinta an hanashi yacire yasa yace “stop talking Ummulkhair” wani irin rawa jikinshi yakeyi maganganun da Mama tafadimai akunne kafin tarasu nadawo mai fresh akai. “Ka kulamin da Ummulkhairy Zayn, nabaka amananta, dan Allah, Khairy bata wani jin maganan yayyinta, Khairy nada fitina, tanada rashin ji, tanada fada, ka kulamin da ita, kasa idanu a al’amuranta, protect her for me, protect my little girl…..” maganan Khairy yadawo dashi daga duniyan tunanin dayaje jin takara kankame hannunshi tace “Ya Zayn zan mutu naje wajen Mama ne nima? Zan ganta ko, ga Mama nan ma tazo wlh” daidai nan aka taya Zayn dagata aka shigarda ita mota manager wajen yace “kai Yayanta ne” gyadamai kai Zayn yayi yama kasa magana, ganin yanda baya hayyacin shi yasa yace “bani wayanka nakira iyayenku” aljihun gaban riganshi yanunamai daukan wayan yayi shikuma Zayn ya kankame hannunta gam tunda yake baitaba jin what he is feeling now ba, kaman zaiyi kuka yakeji , yanaji kaman wukan yadawo cikinshi, sumbatu kawai take dayake daga wajen zuwa inda Baffa yace su kaita da nisa shidai Zayn kawai yagansu Awani private asibiti ga Drs kusan biyar agaban asibitin da nurses da gado ga Baffa da Baba da Yayyinta da yanzun nan sukabar gidan duka awajen, gasu Ammi da Batool duka ana jiransu, wajen motan sukayi Drs din suka shiga, wani torchlight suka haska suka kalli yankan da wukan kafin su dakansu suka dauketa suka sata agado Ahankali, amugun rude Baba da hankalinshi ya bala’in tashi yakama hannunta yana kiran sunanta. “Ummulkhairy gani nan inatare dake kinji” batare data bude idanunta ba tace “Baba karka damu….. wajen Mama zani” Baya Baba yayi zai fadi dasauri Baffa yatare shi sanan daya daga cikin Dr din yajuyo yakalli daga Baba har all the family dasukai zuru zuru yace “don’t worry yanzu X-ray zamu fara Muga inda wukan yay puncturing kafin muyi operation mucire she will be fine” hannun Dr Baba yarike idanunshi sunyi jajir yace “Dr save my Daughter, ban dade da rasa mahaifiyanta ba, dan Allah save my daughter dan Allah” gyadamai kai Dr yayi sanan yakalli Baffa dasu Manaf alamun su tafi da Baba sanan suka kamashi suka zauna, wajen Zayn da sai yanzu yasauko daga motan tayi tana kallonshi arude ganin jini a hannuwanshi da jikin kayanshi tace “are you okay Zayn dina”? Gyadamata kai kawai yayi kamo hannunshi tayi suka shiga asibitin duk suka zauna Baffa nabin Zayn din da kallo yanzu Khairys health first he don’t have time to go into details.

Batool dake zaune kusada Mom idanunta sunyi jajir ganin wayan Khairy data maida vibration da tun dazu bayan fitanta Aliyu ke kira yanzu ma da magriban nan sai kira yake yasa ahankali ta tashi dasauri Mom tace “ina zaki” ahankali tace “bayi” bayin datagani a reception tawuce sanan tashiga tamaida kofan tarufe tasaka sakata tsugunnawa tayi ahankali tana kallon wayan da Aliyu ke kira still kafin ahankali tai picking takai kunnenta.
“Pickle kinaso kibani heart attack ne, I’ve been feeling restless tun dazu, where have you been” ahankali Batool da muryanta kerawa sosai tace “Ya Aliyu” shiru yayi jin muryan daba na Khairy ba sanan gently yace “is this Batool”? Gyadamai kai tayi tace “y…es” jiyayi heart beat dinshi na bugawa ba kakkautawa jin yanda Batool ke kuka, adake yace “what happen to Ummulkhair”? Anatse dudda voice nata na breaking sabida kuka tace “dazu Baffa yace tabi Ya Zayn suje gidan su, tace bazata ba Bari taje tafadama Ya Zayn daganan I don’t know what happen suka tafi, shine dazun nan duk muna zaune muna dinner afalo wani mutumi yakira Abba yace wai manager wani guri ne that barayi sunyi attacking yaranshi an chakama Khairy wuka aciki…….” Wani irin fashewa da mugun kuka tayi, Aliyu jiyayi zuciyanshi na nema yafito tabaki lips dinshi nawani irin rawa yace “wher……i……my….Khairy….nw” cikin kuka tace “Baffa yafada musu clinic dinmu sun taho da ita yanzu, she’s still alive Dr sunce za’afara yin X-ray aga ina wukan yahuda kafin a shiga da ita operation, mutumin daya kira Abba yace ankama daya daga cikin barayin an ankaishi police station, Ya Aliyu Khairy tacemin you are police please those people should pay for what they did to Khairy, kaga Babanta yanzu kaman zai haukace Maman ta bata dade da rasuwa ba yanzu gashi itama ana nema akasheta, Ya Aliyu I don’t want anything to happen to Khairy” ahankali Aliyu yace “Ummulkhair will be fine” katse wayan yayi sanan ta tashi wanke fuskanta tayi tass kafin ahankali tabude kofa tafito.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button