ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL
ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Yana zaune awajen ko cikakken 10min ba’a dauka ba, wani Babban mutum da akalla shida Baba zasuyi sa’onni ya shigo cikin asibitin yana gyara Babban riganshi, farine mutumin sol yanada kiba dan yamafi Baba, shida wani dan saurayi dabazai wuce sa’an su Manaf ba dayay kama dashi dukansu fuskokinsu yanuna damuwa sosai, yana karasowa dafa kafadan Baba yayi yace “be strong my friend, Allah yabama Maryama lafiya, Allah yatashi kafadunta, Allah yasa kaffarane” tashi Baba yayi yanadan murmushi sanan yakalli yaron dake gaidashi yace “su Baban Baby girl Hafiz, Allah ya raya” ahankali yace “Ameen Baffa” sanan suka shiga ciki, har lokacin bacci take, da idanu Baffa yama Baba alamu su fito, suna fitowa yace “bazamu fitada ita wajeba ko har yanzu tanakan bakanta”.
I will talk to her idan ta farka, ahankali Baba yace “Allah yasa ta yarda” kara komawa sukayi wajen Dr ko akwai wani solution amman babu, dudda haka Baffa saida yakira some of the best Doctors dayasani a Abuja but is still same thing hakanan suka hakura.
Wajajen 3:00 na rana tafarka, dakin tabi da kallo kafin ahankali tafara yunkurin tashi dasauri Manaf da Mu’az suka dagota, ahankali Mu’az yace “kinajin yunwa Mama mezakici” dakin asibitin tabi da kallo kafin ahankali tasauke ijiyan zuciya tadanyi murmushi ganin duk sun damu tace “ya akayi bakuje aiki ba yau, laaaa is that Hafiz” tai maganan tana kallon Hafiz dake zaune kan kujeran gaban gadon yana kallonta cikeda tausayi, cikeda murna tace “zonan zoka nunamin hoton jikata nagani” dan murmushi yayi yataso yazo, wayanshi yaciro yafito da picture cute baby girl dinshi yabata karba tayi tace “Masha Allah tubarkallah, Allah ya rayamana kaga yarinya kaman Babanta Yan biyu” tai maganan tana nunamusu hoton kafin idanunta ya sauka kan time din wayan ganin karfe uku har da minti goma yasa dasauri tamikamai wayan takalli Mu’az tace “kiramin Dr yasallameni inkoma gida, Khairi takusan dawowa daga school” tana maganan saiga Baba da Baffa da Dr sun shigo tare, Baffa na ganinta yace “ya jiki Maryam” murmushi tayi tace “Alhamdulillah Baffa, ya ji kalle inasu Hajiya Asiya” kafinma taji amsanshi tace “Dr zokai discharging dina natafi gida” ahankali Dr yakaraso wajen yace “Hajiya kibari mu dubaki na kwanaki tukunna saimu sallameki” kallon Baba tayi sanan takalli Dr rai Adan bace tace “sallameni yarana banaso su dawo Bana gida Dan Allah” kallon Baba tayi sanan ahankali tace “daman Wanan ne shirinka idan ka kawomi asibitin arikeni” dasauri Baffa yazo wajen anatse yace “Maryam kalleni nan” ahankali tajanye idanunta dagakan Baba dake kallonta kuri takalli Baffa, anatse Baffa yace “Maryam kiyakuri ki zauna likitocin nan su cigaba da baki gudunmawa, zamanki agida zai karasa ciwon yazama worst ne, dan Allah maryam inhar kinajin magana ta” lumshe idanunta tayi sanan tabudesu ahankali tace “Baffa tun ina yarinya kasanni ban taba cemaka no ba, kome kacemin inayi dan haka yau Baffa dukanku anan zan rokeku alfarma, dagayau dan girman Allah kome zai sameni karku sake dawodani asibiti, Baffa nasan kalan chutan danake dashi, nasan metake nufi, da inzauna anan allurai da maganinsu yakarasa cinyeni gwara in koma dakina, I want to die adakina tareda yarana dakowa, I hate hospital and zaman asibiti shizaifi kasheni dawuri sama da komi, please Baffa dan Allah, idan baka yarda ba naji zan zauna, amman rokonka nake please Baffa” kowa na dakin saida jikinshi yay sanyi har Baffa, ahankali Manaf yakalli Baffa yace “Baffa please grant Mama wish, let’s just take her back home ko Hafiz” gyadamai kai Hafiz yayi da idanunshi sukai jajir, hakama Mu’az, ganin Baffa da Baba sunyi shiru dan su sunfiso tazauna a asibiti tasami lafiya yasa ahankali Dr yace “Alhaji kubarta takoma gida, idan anything come up ku kirani ni zandinga zuwa nadauki Wanan nauyin” ahankali Baffa yakalli Baba dakokadan baisoba, kallon kayakuri takoma gidan, hakan yasa ahankali Baba yace “shikenan” murmushi Mama tayi sosai nan da nan aka zaremata drop din sanan Dr yarubuta mata magunguna suka saya sanan suka dawo gida gabIaki dayansu.
???? ALKAWARIN ZUCIYA ????
✍???? M SHAKUR
Dan magana da M shakur
wa.me/+2347012181461
1️⃣5️⃣
Yasa hannunshi daya awajen kanta ya daki tafin hannunshi bayan hannunshi yadaki stairs din sanan yakai dayan hannunshi yakama waist dinta yajuyo da ita hakan yasa ta mirgino side tafado jikinshi.
Daga yaran, security, iyayensu dasuka biyosu da sauri, Gwoggo dakekan wheelchair duk sandarewa sukai danba karamin faduwa zatayi ba inda Allah bai kiyaye ba, yanda yakeji yanda take nishi a hannunshi yasa ahankali yazare hannunshi daga waist dinta gently yakai hannun kan fuskanta yadago fuskanta yana kallon face dinta yanda ta kankame idanunta gam gam cikeda tsoro pink lips dinta nawani irin shaking dayasa dimples dinta na lotsawa tana nishi sama sama dayake jinshi akan hannunshi, murya chan kasan makoshi while looking into her face yace “are you okay”? Muryan dataji yadaki dodon kunnenta yasa kadan kadan tashiga bude idanunta danta gasgata abinda taji kafin tabude su tass tadaura white fararen idanun nan nata manya manya dasukenan kaman an wanke da madara tadaura su akan fuskanshi, jitayi numfashinta ya makale somewhere in her throat ganin fuskanta dab da nashi yana kallonta as if he’s trying to check something, yatsanshi yakai saitin nose nata jin bata numfashi kawai takafeshi da manyan white eyes nata yasa dasauri yakalli security man din yanunamai jakanta dake kasa chan yace “give me her bag” dasauri yakawo jakanta yamikamai juye jakan yayi kasa inhaler ta yafado dasauri ya dauka yacire marfin yakai bakinta ahankali yace “breathe in Ummulkhair!” Wani irin bugawa zuciyanta yayi jin yanda yakira sunanta kaman sunanta dayakira ne yay reviving nata batasan lokacin datawani saki numfashinta data rikeshi amakogoronta ba yafito mai kara sanan taja inhaler, zagayesu mutane sukayi barinma parent din yaran da jikinsu yay sanyi ganin Yarinyar da yaranta suka ture is even asmatic, ganin yanda mutane suka cika kansu duk ana kallonta yasa ahankali takai hannunta batare data kalle fuskanshi ba tana kokarin karban inhaler daya rikemata abaki, ganin haka yasa gently yasakin mata ahankali yaran dasuke tsaye sukace “Anty sorry” dan murmushi tayi tana cire inhaler daga bakinta duk dasauri tana kokarin tashi tsaye, tsugunnawa Maman yaran tayi tace “rest a bit please” tai maganan tana maida mata kayan jakanta back aciki tareda daukan mata jakan ice cream dinta da sauri ta mike tsaye tana karban abubuwan ta daga hannun matan tace “I am okay thank u” Gwaggo dake kallonta tace “sannu kinji inane gidanku mukaiki nida jikana” dasauri tace “direbana na nan nagode Ma” sanan tawuce da sauri hartana tuntube tai wajen motansu da Adamu ya kwantar da kujera yanata hira awaya abinshi batare dayamasan meke faruwaba, saida yaga tabude motan ta shiga sanan yakoma wajen Gwaggo yatura keken sukai ciki tace “ohh yara da rashin wayau Hydar, inda badadan kaiba da sunja Yar yarinyar nan tafasa goshi wlh, itama yarinyar uwa batacin abinci yoo nakema wanan maganan haka rainon indomie ce daga ganinta, ace daga yan yara sun bangaje budurwan yarinya haka kawai sai faduwa uwa lagwani, ace yara suci tuwo suki duk irinku ne ai gashinan kaga yara sun taso basu da karfi ko kadan, kai Allah dai ya wadaran naka subaci, Allah dai yasa kai aure ka haihu, wlh tun yaranka na wata biyu zan fara basu lafiyayyen tuwo da miyan kuka dataji daddawa” hararanta yayi baima cemata komiba ya sassayi ice cream din sanan suka fito tace “minene Wanan abin danaga kanata matsamata abaki” kin kulata yayi yasa ta amota ya maidata gida sanan yafito yatafi aiki.