ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Bangaren Gwaggo shima yanada girma sosai, da sallaman nan nashi chan kasan makoshi yadaga labule ya shiga dakin ko kadan Gwaggo dake zaune tana kada lagwani bataji alamun shigowan mutum ba kawai karan kwas kwas na takalmin dake kafanshi taji akan tile din dakinta afirgice takalleshi tana “Innailaihi wa innailaihi raji’un, waikai Aliyu wani irin murdadden yaro ne eh, bama wanan ba dan ubanka koma ka cire shegen takalmin nan naka dazaka shigomin dashi falo ina salla a ko’ina afalona dan tsarki ne dashi wlh” ko kallonta baiyiba saima hawa kan dogon kujeran ta dayayi yay kwanciya abinshi yanadan lumshe idanu, ijiye komi Gwaggo tayi tamike tana gyara zani tazo kanshi zatahau mai bala’in idanunshi daya lumshe tabi da kallo ganin sundanyi ja yasa tace “kai yaron nan zazzabi kake yine”? Dan bude idanunshi kadan yayi yakalleta dauke kanshi yayi yaki kulata, dasauri ta kalli agogo ganin ko shabiyu batayiba yaron da dazun nan dasafe yafita aiki yasa tace “wlh bakada lafiya Hydar zo meke damunka”? takai hannunta da duk audugan lagwani yake kai zata tabamai fuska dasauri yatashi zaune yace “karki tabani da hannun dattin nan Gwaggo” dan sassauta murya tayi kaman ba ita kemai ihu ba cikeda damuwa tace “meke damunka eh Hydar? Duk wanda yasanka yana ganin Wanan idanun naka yasan bakada lafiya, meke maka ciwo” tashi daga kan kujeran yayi yace “tunda bazaki barni nai bacci ba bari na barmiki dakinki” yay maganan yay hanyar fita tana kwalamai kira kaman badashi takeba, cikeda damuwa tace “ai idan bakaji nawa ba zakaji na ubanka, yaro sai bakin zurfin ciki da shegen share mutane sabida yaga nadamu dashi” duk yanajin ta tana surutunta bai amsata ba flat dinshi yawuce bude kofa yayi yashiga cikin dakin da babu abinda yakeyi sai kamshi ko’ina a gyare kaman babu wanda ke zama adakin, bedroom nashi yawuce yana shiga adaddafe yacire rigan yan sandan ya Yar anan kasan dakin sanan yazauna takalmin kafanshi yacire yazaro wayanshi yadaura saman side drawer sanan ahankali ya kwanta yanadan yatsine fuska bala’in ciwon kai yakeyi daya rasa na menene amman sai uban dauriya, har bacci yasoma daukanshi yaji wayanshi na ringing da kyar yadaga hannunshi yakai wajen wayan dauka yayi batare dayama kalli screen dinba yakai wayan kunne ahankali yace “Hello” daga tachan bangaren muryan wani magidanci ne yace “Aliyu meke damunka?” Dan yatsine fuska yayi yanaji kaman ya rufe Gwaggo da duka akan me zata fadiwa Abba dan gyara muryanshi yayi yace “Abba I am fine” cikin rashin gamsuwa Abba yace “Aliyuuu” dagashi sai Abba sukasan meaning din anytime yakirashi da Aliyuuu hakan yasa gently ya fuzar da dan iska ahankali yace “Abba kaina hurts so bad” anatse Abba yace “is that all”? Ahankali yace “yes Abba” “okay I am coming yanzun nan nadubaka” dasauri yace “no Abba I am fine kazauna please zansha magani” dan jim Abba yayi yace “Aliyu haryau banga wanda yakaika tsanan magani ba” sanin tsaf Abba zaibar hospital yazo yasa yace “Allah Abba zansha I promise” cikeda gamsuwa dan yasan Aliyu baya promise yaki cikawa yace “okay kasha I will call Ogan ka zance mai yabaka the rest of today da gobe kahuta, this work is draining you Aliyu banason shi, anyway that will be another day talk, kasha maganin ka kwanta” ahankali yace “to Abba” Allah kara sauki kaji gyadama Abba kai yayi tareda katse wayan, hannunshi yasa yajawo drawer gefen gadon shi sanan yadauki paracetamol ya ballo guda biyu yana kallon maganin a hannunshi kaman yay amai, yadade yana kallon maganin sanan yasa hannu yadauki goran ruwan dake kan side drawer yabude kurba yayi sanan yajefa maganin da kyar ta hadiye sanan yasa goran abaki saida yasha kusan duka ruwan sanan yaji maganin yatafi ahankali ya ijiye goran kafin yakoma ya kwanta ya lumshe idanunshi bai wani dade ahakaba bacci ya kwasChe shi.
1️⃣6️⃣

Free page
???? enjoy

Kofan dakinta tabude ahankali ta shiga tanabin dakin da kallo yanda ko’ina tsaf tsaf an gyaramata sai kamshi dakin yake, shiga ciki tayi sanan tamaida kofan tarufe kafin awani irin gajiye cikeda sanyin jiki tasaki handbag dinta akasan dakin tafada kan gadon batare data cire takalmin kafanta ba tawani kalan kankame jikinta tanajin wani irin sanyi na shiga jikinta, she don’t even know why amman hakanan fuskan police man dinan take gani a idanunta muryan shi namata yawo a kunne da kanta gabaki daya yana kiran sunanta Ummulkhair breathe in, runtse idanunta tayi gam gam tana feeling yanda bones nata ke cringing to each other tana ganin fuskanshi namata yawo a idanu kafin idanunta suna hasko lips dinshi wani kalan ihu tayi. “Ahhhh stop!” dasauri ta tashi zaune tana wurwurga kafafunta cikeda damuwa tace “Stopppp noooo what’s wrong with me”? Wani irin zabura tayi ta tashi tsaye kawai tawuce dasauri tafada bathroom, wanka tayo sanan tafito daure da towel tana tunanin yaushe Mama zatasa amata Kitso dan gashin ya isheta daga tsifemata jiya, wani simple dogon Riga tasaka sanan tasaka hijabi tai salla tana idarwa tafito falo tawuce ganin duk basu tasan sun tafi masallaci sallan magrib, dinning tawuce zama tayi tana bubbude kula rice tazuba kadan sanan tasa nama tafaraci saida tacinye sanan takai plate din kitchen kafin tafito ahankali tai stairs, knocking dakin Mama tayi sanan tabude kofan ganin Mama akan gado ta lullube da bargo yasa tashigo da sauri tace “Mama menene” wani kalan kallo Mama tamata tace “bacci zanyi nagaji” hawa gadon tayi tana kallon fuskan Mama tace “Mama kibari ayi isha’i tukunna nima bacci nakeji” gyadamata kai Mama tayi tana kallon gashinta tace “weekend zakiyi kitso tunda ke kin dawo yarinya daga tsife miki kai kanki yadawo kaman na mahaukaciya” gyadama Mama kai tayi tana hamma, ganin haka yasa Mama tace “Oya tashi kije kiyi sallan to gashinan ana kira saiki kwanta tunda kin gaji, kinmasha ice cream din” girgizakai tayi agajiye tace “gobe zan sha Mama nagaji, gud night world best” night my baby girl, Mama tai maganan tana binta da kallo wucewa tayi tafice daga dakin tana salla ta kallabi tahau gado sai bacci.

Da asuba tana tashi salla tafarayi sanan takoma bacci dan yau batada lectures sai 10 and she wants to sleep sosai cus kanta yay clearing tadena all this banzayen tunanin nan datakeyi.
Karan wayanta yatadata by 9, da kyar ta iya bude idanunta ta kalli wayan rabon data danna wayanta hartama manta one thing dabai dameta aduniya kenan ba waya, she’s not just a phone person, itadai barta da physical surutu, yawo rawa haaba anan ake samin Khairy, hannunta tamika da kyar tadauko wayan ganin Besty yasa taji duk wani kalan bacci datakeji yafice daga idanunta dasauri tai picking call din tace “Iyye su Besty Amarya ai nadauka kin manta dani yar rainin hankali saisa na shareki banma nemekiba” kuka Besty tasaki awaya dayasa dasauri ta tashi zaune adan tsorace tace “ke menene Besty, what happen? Kinasa inajin tsoro why are u crying?” Cikin wani kalan muryan ban tausayi Besty tace “Khairy wlh nafasa auren mutumin nan kasheni zaiyi tun ranan da aka kawoni abu daya ake har yau nagaji” dan ware idanu Khairy tayi tanajin maganan wani banbaram itadai barta da rashin ji but duk wani harka na maganan banza da Iskanci bata aciki, adan kunyace cikedajin nauyin magannan tace “to ba ance ana sabawa ba” tai dan shiru saikuma ta turo baki tace “idan yaki kihadashi da Maman ku” wani gajeren tsaki Besty taja cikeda masifa kaman tabugama Khairy dundu tace “I don’t even know why I called u you are crazy Khairy, da zancen party ake da yanzu kingama tsara komi, lemme call Amal” tana maganan ta katse wayan, hararan wayan Khairy tayi ta ijiye saikuma chan kaman ta tuna wani abu wayan ta dauka dailing number Besty tayi back ringing daya tadaga, ahankali tace “sorry Besty kinji I seriously don’t know what to tell u or how to advice u” cikin muryan damuwa Besty tace “wai Khairy when will you learn all this stuff eh, u are just hella wired Umma, u are just leaving life kaman bamace ba gashi duk munata aure Khairy keko saurayi bakida shi sai wanan Wizzy dake binki” hararanta Khairy tayi tace “nacemiki kidena hadani da wanan yaron” dan dariya Besty tayi kaman ba itane mai kuka yanzun nan ba tace “naji nadena, yanzu dai kinyi wani saurayin”? Dan shiru tayi kaman mai tunani harta bude baki zatai magana saikuma tai shiru hakan yasa Besty tace “ohhh wowww, Khairy this is something new, tell me who is he? Dan tunda nake dake duk aka miki tambayan saurayi direct kike cema mutum baki dashi wanan dakika kasa magana tell me wayeshi” dan murmushi tayi tayi dan juyi akan gado tana dan lumshe ido saikuma ahankali tace “wlh Besty banda kowa kawaidai wani Police man ne naketa haduwa dashi this days amman ko magana bamayi kawai dai he always saves me from trouble ne I don’t know if that means anything amma dai ba soyayya muke ba ko magana ma bamayi” ahankali akuma natse Besty tace “ohh my Goddd! Khairy kinji yanda harwani natsuwa kikayi kina bani labarin police man dinnan kuwa, My world Khairy you love me! Wlh….” Dan yatsine fuska Khairy tayi dasauri tace “stop it! Mutumin dabanma sanshi ba, yaushe zaki dawo school nidai” dariya Besty tayi sosai tace “tunda u are avoiding maganan ai ba matsala, this weekend zai dawo dani but every weekend zai dinga zuwa” gyadamata kai Khairy tayi tace “sai kinzo bye” tai maganan tana katse wayan da sauri dan tasan Besty bazata taba hakura da topic dinan ba, ijiye wayan tayi ahankali sanan ta mirgina zuwa dayan gefen gadon tana tunani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button