ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL
ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Wani kalan shuuuuu taji kunenta nayi, itadai tasan taji koke koke, taji maganan Baba, su Ya Mu’az har maganan Ammi tasan taji sama sama kafin chan kuma taga tabude idanunta tana kallon kowa dake kanta, kala batace musu ba rarrafe ta shigayi har zuwa gaban gawan zama tayi dirshan tana kallon farin likafanin hannu tamika zatakai tabude saikuma tai shiru kafin ahankali tasa hannunta taja likafanin kasa fuskan Mama ya bayyana tai wani haske ga alamun murmushi tanayi wani kuri tayi da idanu kaman tahaukace sai kawai idanunta aukahau mata yana kaman Mama murmushi take mata dariya tayi sanan tajuyo ta kalli Maheer dake kuka tace “Ya Maheer dena kuka kaji zoka gani ga Mama nan namin murmushi, Mama bata mutu ba bacci take wlh gashinan zoka gani” babu zuciyan wanda bai tsinkeba adakin ahankali takai bakinta saitin fuskan murya chan kasa tace “Mama Mama, world best tashi kiji, Mama ai bacci kikeyi ko” tasake shiru, ganin ko motsi Mama batayi yasa tai tagumi tana kallonMama tace “zan jira harsai kin tashi kinmin magana” ahankali Baba yataho yazauna kusada ita dasauri tajuyo takalleshi kaman mai karantan wani abu akan fuskanshi, kafadan Khairy yakamo sanan ahankali yace “Ummulkhairy mamanki has been bathling with cancer for so long, blood cancer bataso kisani cus tasan abinda zakiyi kenan idan kikaji she has few days left, u will not take it likely, saisa taboyemiki all this while mamanki has been sick, seriously sick amman taki yarda kisani duk ciwon da mamanki keyi taganki she will pretend she is fine” hawaye masu bala’in dumi ne suka zubo mata dasauri tasa hannu tashare, ahankali Baba yace “karki sakawa Maman ki hakan nan Khairy inhar she’s your world best, kimata addu’a tasan tabar ya tagari aduniyan nan muje mukaita makwancinta, your mum is tired she need rest, go and pray for your mum” ahankali Khairy tasake matsawa kusada Mama she can’t believe Mama ne nan kasa addu’an tayi sai kuka ahankali tace “Mama dan Allah dagaske wai kin rasu?”, zuwa yayyinta sukayi kawai rungumeta ahankali Manaf yace “Mama tarasu Khairy pray for her” Ahankali tace “Mama Allah yajikanki Allah ya gafarta miki, Mama why did u leave me, shikenan bazan kara ganin ki ba, Mama maisa baki bari na rokeki kiyafemin ba, kullum ina cikin batamiki rai inta rashin ji, Mama Tayaya zan cigaba da rayuwa baki aciki Mama Innalillahi wa Innailaihi raji’un” tashi Baba yayi ahankali hakama Baffa dasu Ya Hassan da Hafiz dakuma Zayn zasu dauki Mama dan kaita waje salla, wani Zabura tayi zata tashi dasauri Manaf yariketa, Mom yabama ita tana wani kalan nishi hannu Mom tasa takarbi inhaler ta tace “Khairy Khairy” kaman zata haukace haka takeji da kyar ta iya kallon Mom tace “Mom na shiga uku, Mom Mama tarasu Innalillahi wa innailaihi raji’un, Mom wlh wlh ko….” kawai maganan yakakare takara suma, ruwa Mom tashafa mata a fuska tanamata addu’a, tafarfado ta sume tai having Asma attack haka tadingayi ahaka har akama Mama salla aka tafi da ita, Khairy bamatasan inda kanta yakeba tana jikin Mom, jikinta yay wani mahaukacin zafi dayasa Mom takalli Ammi dake zaune tanajan charbi tace “Hajiya kira Alhaji Dr yazo jikinta yay zafi dayawa, kuma suman nan datakeyi yay yawa” dan jim Ammi tayi sanan tadauki wayanta takira Baffa ta sanar dashi.
Bayan magrib Baba yashigo gidan tareda Baffa gaisawa yayi da matan dake falo dakemai gaisuwa sanan suka taho sama tundaga stairs yake kallon Khairy dake kwance akasa gatanan gatanan ne kawai baa cewa komi, tsugunnawa Baba yayi agabanta ahankali yadagota sharaf ta taso Mom yakalla yace “tayi salla kuwa”? Girgizamai kai Mom tayi, Baba zaiyi magana kawai tasaki wani sabon kuka mai bala’in tabarai dayasa kowa na dakin yazuba mata idanu tana taba zuciyanta kaman ta mutu takeji, kaman tai hauka takeji, kaman tadawo da hannun agogo baya takeji tama Mama duk abinda takeso batare datasa Mama fushi ba, duk su Baba magana suke mata amman harga Allah bata gane komi kunenta ma yadode, duk suna zaune ahaka tai kuka ta sume tadawo Dr yashigo gidan, allura kawai yamata aka samu tai bacci, Baba zai dagata Dr yace “ku kawo bargo kurufa mata, let her sleep anan” Baffa da kanshi yashiga dakinta pink bargonta da filonta yadauko yakawo Baba yakarba yasamata akarkashin kai sanan yarufa mata bargon yana kallonta yana kafin yasa hannunshi yacire rolling gyalen dake kanta ya ijiye gyalen agefe long kalaban ta suka bayyana duk akai shiru.
Hayowa saman sukayi duka yaran Hafiz na rike da jakanta daya dauko daga motanshi Dan dazu amotar tabari dakinta yabude ya shiga ya ijiye sanan yafito yasamu gefe daya yazauna afalon, suma su Hassan da Manaf suka zazzauna, ahankali Zayn ke hayowa stairs din da duk yay wani irin tsayawama waje yayi yin wata waya saisa bai shigo tareda kannen nashi ba,hayowa yayi kallo daya yama Khairy dake bacci akasa da aka lullube da pink bargo yadauke kai sanan yawuce gefen Ammin shi yazauna akasa tareda daura kanshi kan cinyanta hakan yasa tadaura hannunta ahankali tana shafa kanshi, kallon yaran Baffa yayi yace “kutashi kutafi gida mu muna nan” cikinsu duka babu wanda yay motsi, ahankali Ammi dake shafa kan Zayn tace “Son tashi katafi gida kahuta yau ka dawo daga tafiya” girgiza mata kai yayi ahankali yace “I don’t wanna go Ammi” kallon Hafiz Baba yayi yace “wuce katafi gidan ka Hafiz” girgiza kai yayi shima yace “Baba ai basu kadai bane kanwarta damai mata wanka duk suna nan” addu’a Baffa yayi dukansu sanan aka shafa, aka zauna turus duk wanda yaga su Baba da yaranshi saiya tausaya musu abinda kuma yahana yaran Baffa tafiya kenan Dan idan suka tafi gidan zai musu wani iri kai mutuwa batada dadi! Baba da Baffa sauka falon kasa sukayi sukuma yaran duk suna wajen kusan ahaka bacci ya kwashe kowa daga Ammi da Mom da duk suke kan kujera zuwa su Manaf dake bacci rabi rabi falon yarage only Zayn ne baiyi bacci ba dayake tattaba wayanshi maganan da Baffa da Baba keyi akasa yanaji.
Motsin da Khairy tayi cikin bacci yasa yajanye kanshi daga waya yazuba mata idanunshi kusan sai yanzu nema yake mata a very good kallo tunda yazo, hawaye yaga suna gangarowa daga gefen idanunta pink lips dinta na motsi sosai cikin bacci ta kankame pink bargon da aka lullubeta dashi tana maganganu da kana gani kasan mafarki take. “Mama Mama wai kin mutu? Ai baki mutu ba ko, bansan menama su Baffa dasukemin karya ba, Mama zansha madara, in dauka, Mama Mama Maaaaa….” Wani dogon ijiyan zuciya tasauke na kuka kalabanta daya na saukowa kan fuskanta, dauke kai yayi daga kallonta shi dabama danta ba mutuwan yajishi balle yaran data haifa, he can’t even imagine loosing Ammi God no please, Allah ya sassauta musu koma mesukeji a zukatan su.
Wuraren 4 daidai tabude idanunta daga kwance datake tana kallon saman dakin da kallo, the first thing daya fado brain nata is mutuwan Mama, ajiyan zuciya tasauke tana assuring kanta cewa mafarki ne tayi, juyoda kanta tayi tabi kowa na dakin da kallo, Hafiz nakan kujera yatakure yana bacci, Ya Manaf na zaune shima kan kujera yana bacci, Ya Mu’az ma haka Maheer ne kadai akasa yana bacci, sai Zayn da kanshi kekan kafan Ammi yana bacci shima kaman wani auta, Mom dake saitin inda take akan kujera tana bacci itama ta kalla ajiyan zuciya ta sauke zuciyanta na tsinkewa but she’s still in disbelief, bargon jikinta ya yaye ahankali sanan tamike tsaye da kyar cikinta namata wani irin ciwo na yunwa dan jiya all through babu abinda tasa abaka, tadade tsaye tana rikeda cikinta kafin ahankali tafara tafiya jelan kalaban kanta na lilo abayanta tai hanyar dakin Mama, ahankali tasa hannunta tabude kofan kaman a kunnen Zayn danshi baida nauyin bacci hakanan any movement kodan kara daza’ayi yana tashinshi da sauri yajuyo da kanshi yakalli kofan tana tsaye bakin kofa tarike handle na kofan da hannu tana kallon cikin dakin gashinta na lilo.