ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL
ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Wuraren 6 tafarka daga bacci daga Mom har Baffa daya shigo dubasu da asuba saida sukaji dadi ganin yanda tai bacci sosai yau dan this last few days dudda ana mata allura bata tabakai war haka bata tashi ba 4 ta tashi ko 3 nadare ma.
Kalle kallen data shigayi yasa Mom data shigo dubata tace “Khairy ya akayi me kike nema? Kin tashi” Dasauri zuciyanta na bugawa fast fast tace “Mama ina take?” Shiru Mom tayi tana kallonta hakan yasa tafashe dawani irin kuka tace “wlh ba karya nake ba Mom naga Mama adakin nan takwana tareda ni I was even holding hannunta sabida idan kuka tashi kugani, kuma tace bazata kara tafiya tabarni ba” hannu Mom tasa tadafa cinyanta ahankali tace “Khairy idan aka rasu an rasu kenan mutum baya dawowa, sabida rasuwan Mama na ranki saisa kike mafarke mafarke, Mama tarasu, you had a dream about her, tashi kije ki dauro alwala kiyi salla” tashi tayi ahankali tana goge hawayen dasuke zubomata tai bayi, fitowa tayi daure da alwala tai salla, da kyar tasha kunun da Mom tabata shima kadan sanan Mom tabarta da su Batool da Zara’u daketa musu surutu Khairy na kallonsu kuri kaman tazare itakuma Mom ta sauka kasa.
Knocking akayi tareda shigowa dakin, Zayn ne yana sanye da kananun kaya yay kyau yana zuba wani uban kamshi, ganinshi yasa Mom tace “Zayn shigo mana zoka zauna” karasowa yayi cikin falon cikeda girmamawa yace “Mom zan tafi” dasauri Mom tace “harzaka koma” ahankali yace “eh something come up dole nakoma dama 1week naso nayi amman bazai yuba” murmushi Mum tayi tace “Allah sarki to Allah kiyaye hanya, Aida nasan yau zaka tafi dana maka su dambun nama wlh yanzu sai yaushe kenan” dan shiru yayi yana tunani sanan yace “let’s just say 2month intotal nagama komi” ahankali Mom tace “Alhamdulilah Alhamdulillah komi yay farko zaiyi karshe Allah bada sa’a Allah ya kiyaye hanya” Ameen yace yana tashi har waje Mom tarakashi Baffa dasu Hafiz suka daukeshi a mota har zuwa airpDort.
3️⃣1️⃣
Murmushi yamata sanan yamika hannunshi yadauki jakanta wayanta yaciro yakunna yace “this phone should always be on” gyadamai kai tayi ahankali tana kallonshi Ya Aliyu is just….bamatasan taya zatai describing nashi ba, he’s just everything datake so, he’s so cool, calm, religious, selfless, caring, loving and above all very handsome. “will you marry me?” Kaman daga sama taji yajefo mata tambayan dan tayi nisa a tunanin shi while looking at him, ware manyan idanunta tayi da sun soma washewa, ijiye wayan nata yayi akan cinyanshi dayagama saita mata dan komi na ciki ya hargitse sanan yadaura mata mayun idanunshi akan nata, ahankali yace “zaki taimaki Aliyu Hydar ki aureshi yazama mijinki?” Batasan mesaba but wani kalan bala’in kunya ne taji ya lullubeta dasauri takai hannayenta duka biyun tarufe fuskanta dashi tana murmushi sosai kaman ba Khairy ba, dan murmushi yayi ganin yanda tambayan shi yabata kunya, matso da fuskanshi saitin fuskanta data rufe da hannayen ta yayi kaman mai whispering yace “I want to go and seeaBaba fa” girgizamai kai tayi tareda makemai kafada batare data bude fuskanta ba hakan yasa yace “what”? Awani irin shagwabe kaman Yar baby one year tace “ni karkaje wajen Baba yanzu” dasauri yana kallon long yatsun hannunta masu bala’in kyau da fararen kumbunanta kal kal yace “sai yaushe” ahankali kaman bataso tafadi maganan tace “sai nagama second semester exam dina nagama school” dan shiru yayi kaman mai calculating dan yamai nisa, dan yatsine fuska yayi yace “to but will you marry Aliyu”? Shiru tayi kaman bazatai bashi amsaba yana kallonta sai chan yaga ta gyadamai kai wani irin murmushi yayi ya dunkule hannu yadaki iska yace “yessssss!” Juyamai baya tayi akunyace tana daukan jakanta ahankali tace “mutafi inada class by 2” dan murmushi yayi ganin kunyanshi takeji dan tace zata aureshi, yace “ok” tashi tayi ahankali tafice daga wajen murmushi yasakeyi ya kwashe dadduman dasauran abubuwa yafito, discarding nasu yayi sanan yazo yasameta tsaye jikin motan tana kallon wasu tsintsaye dake wasa jikin bishiyan wajen, ga gidajensu birjik a wajen da alamu kiwonsu ake awajen, abayanta ya tsaya yana kallon tsuntsayen shima murya chan kasa yace “u like them”? Gyadamai kai tayi da sauri batare data cire idanunta daga kansu ba, wani mutum dakaman shine mai gadin wajen yakira da hannu ko kadan bamata lura ba dan hankalinta nakan tsuntsayen datake kallo, kawai gani tayi mutum yafito dawani basket cage na gidan tsuntsu yazo wajen bishiyan cikin sauki taga yakamo guda biyu yana kokarin sawa ciki, dasauri tace “Ya Aliyu meyake yi wanchan mutumin”? Ahankali yana tsaye kusada ita yace “I don’t know let’s see” saka tsuntsayen yayi a basket din sanan yataho dasu gabansu da sauri yamikama Aliyu yace “officer gashinan macen da namijin ne kaman yanda kace” hannu yasa ya karba sanan ya ijiye akan motan Khairy tabishi da kallo, hannu yatura a aljihu yaciro wallet kudi dayawa yaciro yamikama guy din godiya yamai sanan yawuce, hakan yasa yamaida wallet din aljihunshi kafin ahankali yadauki cage din yajuyo yana kallon Khairy dake kallonshi yamika mata yace “take” wani cute smile tasaki sanan tasa hannu takarba tana kallonsu tana murmushi sanan tadago kanta takalli Aliyun dake kallonta tace “they are so cute, they’re so tiny and adorable” matsowa kusada ita yayi yana kallonsu shima acikin cage din sanan ahankali yace “mace da namiji ne, this is Aliyu Hydar” yanuna mata namijin, sanan yanuna mata macen da yatsa yace “and that’s the lady, Miss Ummulkhair” wani kalan murmushi tayi she’s so happy bata taba zatan dan tace tanaso zai sayamata ba harma guda biyu, fuskanta yakalla yanda take murmushi tana kallonsu, ahankali yace “are you happy Pickle”? Juyoda fuskanta tayi takalleshi, gyadamai kai tayi ahankali tace “I am very happy” “mutafi to”? Gyadamai kai tayi da sauri tace “a ina zan ijiye idan zan shiga class”? kofar motan yabude mata shiga tayi dan shiru yayi kaman mai tunani sanan yace “I will keep them for you harki gama class, how does that sound” “perfect” tafadi tana girgiza case din dake jikinta dan suyi attempting flying wani dadi taji tace “yayyyy they’re flying, Ya Aliyu kalli” kallonsu yayi yana mamakin yanda abin kesata murna, maida kofan yayi yarufe yanajin wani kalan sanyi aranshi, duk wani damuwa da kunci dayakeji yatafi ganin yanda take murmushi looking happy.
Shigowa motan yayi yatada yaja motan kusan every minute and second saiya juyo ya kalleta yanda take wasa da tsuntsayen sosai, yana bala’in son Khairy shi kanshi baisan adadin son dayake mata ba, ahaka har sukakai school dinta around 15min after 1 na rana, parking yayi hakan yasa takalleshi daidai shima ya kalleta, dan sunnar dakanta tayi akunyace yace “2 zaku shiga class ko?” Gyadamai kai tayi, what time zaki gama lectures yau, ahankali tace “5” dan ajiyan zuciya yasauke yace “yanzu jeki salla a mosque kafin ku shiga class, I will come back later nakawo miki birds dinki kitafi dasu gida, what do u want me to get for u when coming back?” Girgizamai kai tayi tace “babu komi” jakanta tadauka sanan tadan saci kallonshi ganin kallonta yake kaman yauya fara ganinta yasa tajuya da sauri tareda bude kofan tafita tafara tafiya dan murmushi yayi yakafeta da ido yana kirga step dinta waiting for something, kaman taji kiran da zuciyanshi kemata juyowa tayi dudda motan is tinted but samin kanta tayi damai waving hannu dan tasan yana kallonta sanan tajuya da sauri tawuce feeling so happy da shi can not even deny, bata taba sanin she can feel this happy ba bayan rasuwan Mama gashi she’s feeling it.”