ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Yau rabonta dajin muryan Aliyu sati daya chur kenan dan gashi nan wata asabar din ta zagayo, exam ma adaddafe take tabashi hakuri harta gaji yaki hakura dudda kullum saiya mata text yasata tayi karatu but other than that shiru kakeji, har dan ramewa tayi dayake ansan exam take babu wanda yabama abin attention, yau tunda gari yawaye Mom tasata ta shirya taje tagaida matan Baba da tuni akai biki harta tare, bataso taje amman bazata iya cewa no ba hakan yasa ta shirya dan yau at the same time zaa raba gadon Mama abinda yasama bataso taje kenan.

Parking direba yayi acikin gidansu gani tayi gidansu ya chanza an sake penti, Baba tagani akujera a tsakar gidan da alamu shan iska yake yasa farin jallabiya ga flask don shayi agabanshi dawasu papers yarame sosai ganinta yawani fadada murmushin fuskanta yabude mata hannu dawani irin gudu tazo batai wata wata ba tawani rungume shi she miss baba so much, sun dade ahaka sanan tasakeshi yazauna kan kujeran dake kusada shi tace “Baba ina yini” murmushi yamata yana tana kumatunta yace “Khairy na ya jarabawa next week zaki gama ko” gyadamai kai tayi yace “yaushe zaki dawo gida” gidan tabi da kallo sanan ahankali tace “bayan jarabawa Baba” Gyadamata kai yayi sanan yadauki papers dake gabanshi yabata yace “ga gadon Maman ki nan dakika samu na filaye biyu dakuma gidan kifinta guda daya, sai kayayyakin ta, duk wani abu na Maman ki daidai da cokali an raba, duk suna store, su Manaf duk sunkai nasu gidan marayu sunyi sadaka dasu naki kome kikace ayi dasu haka zaayi” ahankali tace “Baba akai gidan marayu, kayanta na sawa zan cire wanda nakeso sauran sai akai” Gyadamata mata kai yayi sanan ahankali yakama hannunta yace “I am here for you Khairy okay, hope bakida any damuwa” dan murmushi tayi tace “Baba I am fine Allah kuwan, ina su Ya Manaf” “sun tafi office” gyadamai kai tayi ahankali tace “ina new Mom”? Yadade yana kallonta sabida yanda tafadi sunan kafin ahankali yace “tana ciki” tashi tayi tace “bari naje nagaidata” tawuce ciki Baba yabita da kallo, ahankali tabude kofar falonsu wani sanyi yamata sallama tadade tsaye kafin ta shiga cikin falon daidai da foot mat nabakin kofa an chanza har tv bango an chanza komi tatas kaman ba gidansu ba kaman ba falon Mama ba, abin was so strange, mutuwa mutuwa wlh karshe ne! yanzu shikenan this falo is not for Mama again na wata ne, Anya zata iya cigaba da zama agidan nan kuwa Anya bazata koma da zama gidan Baffa gabaki dayaba Dan what she is feeling right now jitayi kaman ta kurma ihu hatta labule duka bana Mama bane jin kuka yazo mata sosai dawani irin sauri tajuya zata fita taji ankirata. “Ummulkhairy” chak ta tsaya, sanan takai hannuwanta ta goge hawayen dasuka zubomata daga idanunta tass kafin ahankali tajuyo, sabuwar matan Baba tagani batada wani makusa Babba ce itama amman daga gani Mama ta girmeta sosai, doguwa da ita kana ganinta kaga natsassiyar mace, murmushin dole Khairy ta kakalo ahankali tace “ina yini uhnnn” tama rasa sunan dazata kirata dashi murmushi matan tayi daidai takaraso gabanta hannunta tasa ahankali takama hannun Khairy tace “sunana Mariya, maisa kika tsaya anan bakin kofa keda falonku shigo mu gaisa” taja Khairy cikin falon danne kukanta Khairy tayi sosai sanan ta zauna akan kujeran da Mariya ta zaunar da ita sanan tace “ina zuwa” dasaurinta ta wuce kitchen tafito da drinks a tray takawoma Khairy ta ijiye sanan tasake zama kusada Khairy data kasa kallonta dan wani iri takeji, ahankali takai hannunta tadaura kan cinyan Khairy cikeda tausayawa tace “ina tunamiki da mahaifiyanki ko” dauke kai Khairy tayi da sauri tana kokarin danne hawayen dake gab da zubowa tace “uhn uhn” ahankali Mariya tace “Khairy I am so sorry about your mother’s death, Allah ubangiji ya haskaka makwancinta, Allah yasaka mata da gidan aljanna” ahankali Khairy tace “Ameen” murya chan kasa tace “Khairy mijina na farko nima yarasu so I understand pains dinki sabida yarana suma sunma mahaifinsu kuka, at first da akazo nemama babanki aurena nariga nai alkawari bazan kara aure ba but danaji matarshi tarasu tabar yara abinda yasa na aure mahaifinki kenan sabida inaso nazama uwa ga yaranshi dan ni bansami chance dinan nama yarana hakaba” dasauri Khairy takalleta tana share hawayen daya zubomata, Gyadamata kai tayi tace “bayan rasuwanshi iyayenshi suka karbe yaran, kafin naga yarana yanzu sai Hutu Hutu akawosu sumin kwana biyu, tuntuni naso nazo dakaina ma har gidan Baffan naku ko Baban ki ko yayyinki sukawoni nadawo dake gidan mahaifinki, Khairy just know this, nasan ba lallai ki daukeni ko ki kalleni a matsayin mahaifiyanki yanzu ba saidai a matsayin kishiyaneuwa, I want to assure u ke y’ata ce Khairy, u can come to me for everything and anything, zan rikeki da yayyinki amana kaman yaran da na haifa, bazan taba cutar daku ba kinji” Gyadamata kai Khairy tayi sanan ahankali tace “thank u” hannu Mariya tasa tashare mata hawayen sanan tace tashi muje sama binta Khairy yayi Baba dake kofa yaji komi baitaba jin sonta aranshiba sai yau, tunda akai auren basuma taba kwana daki daya ba dan gani yake kaman yacuci Mama amman yau yakudiri aniya komi zai chanza zai saki ranshi da ita.

Khairy bata bar gidan ba sai bayan sallan magrib shima saida matan Baba tasa tamata alkawari dazaran tagama jarabawa zata daDwo gida.
3️⃣4️⃣

Saida sukaci suka koshi sanan suka ture ga uban abinshi sun rage akwai wayanda bama sutaba ba ahankali yace “shall we?” Gyadamai kai tayi yatashi hakan yasa itama ta tashi suka fito maiikatan eatry namai godiya suka wuce motanshi yabude mata shiga tayi sanan yamaida kofan yarufe yadawo yazauna yatada motan suka bar wajen bini bini yake satan kallonshi ganin sunzo wonderland yasa tawani ware idanunta aljihun motanshi yasa hannu yaciro mata 2 ticket dinsu yamika mata Wanan Karan takasa boye excitement dinta tace “wowwwwww Ya Aliyu I am so sosoooooo happy thank uuu” u welcome baby yay maganan yana shiga ciki parking yayi a inda ake parking sanan yafito itama fitowa tayi she’s so happy datama kasa boyewa zagayowa yayi ta inda take yace “are u happy” gyadamai kai tayi tana dan tsalle tace “yes thank uuu” murmushi yamata yace “let’s go” ciki sukayi yariga yay recharging card nasu yace “me and u competition yau zamuyi kin yarda”? Gyadamai kai tayi tace “and I will win cus I am a born winner” murmushi yayi yace “let’s see then” da bumper cars suka fara suka shiga, both of them were literally screaming suna bubbuge juna da motan shi kanshi Aliyu baitaba sanin he could do this childish play ba sai yau, bugeshi tayi motanshi yakoma baya tahau ihu ta waigo tanamai gwalo kwafa yayi sanan yatashi yafita itama fitowa tayi tana tsalle sosai kaman Yar yarinya tace “I won yayy” hararanta yayi yay gaba dasauri tabishi sukaje next game dayakeso suyi shooting target, indai target ne babu wanda yakaishi but da gangan yabarta shima taci wayyo Ummulkhairy kaman zata zuba ruwa akasa tasha dan dadi, ice cream yasaya mata takarba tanasha saida yajiraa ta shanye sanan suka shiga wajen 3D zasu buga car race, nan ma ita taci, yanda takemai dariya ko shi kanshi baisan ta iya dariya hakaba she was really feeling herself, ta iya game sosai sabida su Maheer dan sunayi a gida, all games na wajen nan saida tayi har teddy bear saida taci katuwa tadauki abinta tana dariya, hararanta yayi yay gaba dasauri tabishi tace “Ya Aliyu wait, fushi kake sorry but I told you I am a winner” juyowa yayi yace “nine looser ko” hannu tadaura akan bakinta tana hadiye dariyan dake zuwa mata tace “uhm’uhm” hararanta yayi yace “let’s go waje kiga wanda zamuyi I promise u will be the one to loose” dasauri with confidence tace “eh muje” tabishi dasauri gaban rollercosta taga sunje koda tana yarinya bata yarda tai abin nan ba sabida tsoro hakan yasa ta ware idanu, magana taga Aliyu yayi da mutanen sanan yazo inda take tsaye yace “harkin fara tsoro ne” turamai baki tayi tace “never” dan bakinta data turamai yakalla saikuma ahankali yace “mutafi to aga who will lost, and yarinya kikamin kuka ko” dasauri tace “ni Bana kuka saikace wata baby” dariyanshi yahadiye dan he already saw d fears a eyes nata, yace “let’s go” tana bite dashi suka shiga wajen, ganin tsoro a fuskanta yasa bai bari ta shiga wajen one person ba, two sitter slot suka shiga na mutane biyu, zama yayi sanan itama tashigo tazauna kusadashi ahankali sakamusu abinda zai rike mutum yahanasu faduwa yayi sukadai akan makeken roller coaster dinan sanan Aliyu yakalleta yace “kin shirya” gyadamai kai tayi gabanta na faduwa tim tim, juyowa Aliyu yayi yakallesu yace “we ready” ajiyan zuciya tasauke hakan yasa yay dan dariya yaciro wayanshi yana bude camera yace “I need evidence” turo baki tayi tana hararanshi sanan aka kunna abun, rawa hannunta yafara tun kafin su fara moving, kawai jitayi sunyi sararin samaniyan Allah wani kalan ihuuu tayi. “Wayyoooo Ya Aliyu banyi banyi nafasa, huuuuu wlh nafasa kayakuri” tai maganan tana kankame idanunta jin kaman hanjin cikinta zai fito shiko dariya kaman zai mutu yana musu video, jin suncigaba da sama abin nawani chillarasu kaman zai kaisu lahira yasa kawai tawani kankameshi tana boye fuskanta akan kirjinshi. “Innalillahi, Ya Aliyu zanyi fitsari, wlh u won, Dan Allah kayakuri kace subari wayyooo Allah na na shiga uku, Ya Aliyu zan mutuuuu” alamu yamusu da hannu dasu kashe jin yanda heart nata ke beating, amman har suka dawo kasa bata saniba ta kankameshi gam gam tana cewa zatai fitasari, yadade yana zaune ahaka feeling her ajikinshi kafin ahankali yace “sokike kimin fitsarin ajiki cus we are down already” dago kanta tayi daga jikinshi ahankali kaman matsoraciya kallon idanunshi take dake cikeda dariya sanan takalli ko’ina ganin suna kasa, dan hararanta yayi yace “matsoraciya kawai harda kuka” dan turo baki tayi sanan akunyace tasake takoma gefenta, ciremusu abin rike mutum din yayi sanan yabude sit din yafita dagangan yashiga duba jikinshi yace “hope bakimin fitsarin ajikina ba” rufe fuskanta tayi da hannu tace “ni banyi ba” sanan ta sauko tagefenshi tabi da gudu tai restroom dan tagani wajen dasuke zuwa, shikuma yawuce dan sayomusu snacks yana kallon video daya musu awayanshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button