ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL
ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Sakin hannunta yayi dawani irin sauri tajuya gabanta nafaduwa dum dum Batool sai hadiye dariyanta take ganin yanda duk Khairy ta birkice sanan suka wuce suka shiga flat dinsu, suna shiga Batool tafada kan kujera tana dariya tana kallon Khairy datai kuriii jikinta har lokacin bai dawo daidai ba, kallonsu Mom data fito daga kitchen tayi tace “ya akayi” cikeda dariya Batool tace “Mom Khairy taje takankame Ya Zayn tadauka nine saura kiris yamaketa bakiga yanda dukta rude” hararan Batool Mom tayi tace “wlh daya makemin mu danama mai godiya, yara daga tashinku kunbi gida kuna guje guje ko kayan bacci baku cireba ku wuce kuje kuyi wanka kuchanza kaya kafin na sassaba muku” Khairy tafara gaba kafin Batool tabita abaya, hartahau stairs sanan tajuyo takalli Mom tace “Mom yaushe Ya Zayn yadawo”? Batare da Mom takalleta ba tace “around 2 nadare ya shigo gidan nan kuna bacci lokacin” wani irin tsalle Batool tayi tace “yanzun nan bai wanka zanje nasame shi Mom yabani kudin ankon Na’ima” “kinfi kusa” Mom tai maganan tana shiga kitchen abinta itakuma Batool tajuya tai dakinsu, shiga tayi ganin babu Khairy afalon yasa tafada kan gado tana jiranta tafito daga wankan.
Fitowa Khairy tayi daure da towel dinta pink akirji ko kallon Batool din batayiba tawuce wajen wardrobe dinsu, tashi Batool tayi zaune tana kallonta tace “towai fushi kikedani danna tadaki daga bacci sorry to” juyowa tayi ta balla mata harara tace “ni gidanmu zan ma koma Wanan da wanchan Yayan naku yafaramin gorin gida daga ganina bazan dauka ba” dasauri Batool ta tashi dan idan akwai abinda ta tsana shine taji Khairy tace zata tafi gidansu, dasauri ta tsaya kusada Khairy dake shafa mai ahankali tace “ke dalla don’t mind Ya Zayn, wlh Ya Zayn nada bala’in kirki barshi dai da iyaji da kanshi amman yanada kirki kinga duk wulakanci Ammi baya biyemata wlh, Bakiga yana shigowa nan ya gaida Mom ba dudda Ammi bataso shi baruwan shi kuma yana sonmu, yana bani kudi koban tambayeshi ba hakama Zara’u, har dakinshi tana zuwa taitamai surutu wlh baida wulakanci, dan Allah karki kara cewa zaki tafi” kwafa tayi tajuya mata baya tanasa bra sanan tajuyo binta da kallo Batool tayi tace “ke Khairy ai wanan Bra yamiki kadan, kinada nono wlh Khairy kaman muyi musanye” dan tsaki tayi tadau riganta tana sawa, Batool cikeda tsokana tace “iyye su Ya Aliyu zai more” dawani irin sauri tajuyo zata dakamata duka ihu Batool tayi tawuce dagudu tafada bayi, dan murmushi tayi tana kallon kanta a madubi saikuma akunyace tamake kafada tace “ni bazan ma taba bari yaganni bama rigaba balle ma yaganni” karasa shiryawa tayi abinta cikin wani plain dogon rigan atampa ja batare data daura dan kwali ba tafito zuwa saukowa tayi kasa Mom ce kadai tanashan tea a dinning dayaji kayan kamshi ganinta yasa tace “ko kefa jibi yanda kikai kyau” dan murmushi tayi Mom tace “oya zoki zauna kiyi breakfast” karasowa wajen tayi tace “Mom ni indomie zandafa” baki Mom ta tabe tace “Allah dai yay wadaran naka yabaci, nidai kinga tafiyata bari naje natado Baban ku daga bacci, yadan kwanta shima yazo yay kari” kitchen tawuce itakuma Mom tai sama abinta.
Wani karamin tukunya tadauko sanan tashiga store dinsu tadauko indomie daya da kwai guda daya tafito sanan ta tara ruwa tukunna gas don tadaura sanan tawanke kwan a tap tazo tasaka a ruwan pot din tarufe pot din sanan takoma store, albasa tadauka awajen, wani black wukan datagani ijiye tunkwal shikadai a store din tadauko tace “hala Mom ta manta da wukan nan a store ne baga wajen wukake duk suna nan ba” takalli cabinet din wukansu wucewa gaban tap tayi tadauraye wukan sanan tasa wukan ta yanke kan albasan sanan tabare albasan tass, kafin tasa wukan taraba albasan biyu ta ijiye rabi akasa sanan tadauki rabi daya tasa wukan tafara yankawa cirrrr wukan yawani irin yanketa a tafin hannu lafiyayyen yanka dayasa batasan lokacin data saki wani azababben ihu ba daga wukan har albasan nafadi akasa daidai lokacin Zayn na shigowa falon yana sanye da 3quater dawata faran riga, jin ihu acikin din Mom yasa yay kitchen din dasauri ganin Khairy tana yarfe hannunta da jini ke tsayaya ya diddiga ko’ina a kitchen din tana ihu tana kuka ga wuka da albasa akasan kitchen din yasa yay kitchen din da sauri hannunshi yasa ya karbe hannun nata data yanke dasauri yay tap da ita kunna tap din yayi ya tare hannun kasan ruwa wani kalan fashewa da kuka tayi zata kwace hannun amma yaki yana wanke jinin daidai lokacin daga Mom har Baffa dasukaji ihunta sun shigo kitchen din dasauri wukanda Mom tagani akasa yasa tai salati. “Innalillahi waya fito da wukan daga store” cire hannunta Zayn yayi daga tap but still jini zuba yake ganin haka yasa Baffa yace “kawo first aid kit dinan Wife” fita Mom tayi daga kitchen din, ahankali Zayn dake rikeda hannun yakalli fuskanta yanda take kuka da yanda har gumi yafeso agoshinta dan ita anytime she’s stress or in pain tuni zakaga gumi yaketo mata a goshi, yanda gumi yasa gashin gaban goshinta ya kwanta ga hawaye na gangarowa daga idanunta datake gogewa da bayan dayan normal hannunta idanunta duka suna kan hannun da jini kefitowa dagakai yasa yaji beat din heart dinshi na raguwa, ahankali kaman wanda wani abu ke controlling yakai hannun saitin bakinshi kafin ahankali yadaura bakinshi kan hannun wajen yankan yanashan jinin yana kallon fuskanta, wani irin sanyi taji bakinshi yayi akan yankan kaman yadaura ice akai shiru yadena mata zafin dayake dawani irin sauri takalleshi tana ware manyan idanunta duk wani hawaye datakeyi ya tsaya chak Baffa dake bayansu tsaye ya tsaya chak yana kallonsu daidai nan kuma Mom tashigo dagudu tace “gashinan Zayn” firgigit! Kaman wanda yadawo hayyacin shi, bakinshi yazare dagakan ciwon, sanan yana rikeda hannun nata yakarbi spirit din da Mom kebashi yazuba mata akan hannun wani kalan ihu tayi dasauri yashiga hura mata hannun da iskan bakinshi hakan yasa tai shiru, auduga yakarba daga hannun Mom yadaura kan hannun sanan yasa plasta akai kafin ahankali yakalli Baffa yace “Abba akaita tayi tatanus injection” Dawani irin sauri Khairy tace “Baffa no dan Allah dan Allah Baffa kar Amin allura” dan dariya Baffa tayi yace “Khairy Khairy, ai Khairy tun tana yarinya batasan allura wuce kije ki zauna wai mema tazo yi a kitchen din” Mom tace “wai indomie zataci ga abincin normal mutane amman Khairy indomie zataci wuce tafi nadafa miki, wukan nan sabida yanda nasan kaifinshi yasa naboyeshi a store ko ya akayi tafito dashi oho” Mom tai maganan tana daukan wukan itakuma ahankali tawuce tafita hannun namata zafi, Baffa yakalli Zayn dayadan saci kallonta yace “let’s go Son, yaushe kashigo” dan murmushi yayi yace “yanzun nan nazo gaida Mom ne shine naji yarinyar chan na ihu kaman bera”
Juyowa dasauri Khairy tayi jin ita yake kwatantawa da bera, mugun kallo Baffa yamai yace “karka kara kwatantamin y’a da bera” zama tayi a dinning ahankali Baffa da Zayn suka wuce falo suka zauna akan kujera.
Baffa yace “yanzu tunda kagama komi yaushe zaka fara company and start managing everything, I want to retire nima nahuta” anatse yace “Abba bari nadan huta” atsanake Baffa yace “I am giving you just 2 weeks to rest Zayn am I clear” gyadama Baffa kai yayi cikeda girmamawa, saikuma chan yamike tsaye ahankali yace “bari naje wajen Ammi” gyadamai kai Baffa yayi yace “okay yaushe zakaje gaida Baffan naka” dan ware idanu Khairy tayi jin ana maganan gidansu, ahankali Zayn yace “anjima da yamma” ganin yanda Khairy ke kallonsu yasa yace “zakije” dasauri ta gyadamai kai tana murmushi kallon Zayn Baffa yayi yace “to kaje da Khairy idan zaka tafi” dasauri daga Zayn din har Khairy suka kalli juna dan bata taba tunanin Baffa saice Zayn yaje da ita ba ita tazaci kawai zaice taje idan ta shirya Adamu yatafi da ita, wani kalan mugun kallo Zayn yamata sanan yawuce yafita daga daDkin.