ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

    ALKAWARIN ZUCIYA ????


    ✍????M SHAKUR

5️⃣

Da asuba kafin Baba yawuce masallaci yashigo yatadata wanda hakan yakeyi kullum.
Da farinciki ta tashi yau sosai kaman ba itane ta kwana da fushi jiyaba, murna take sosai sabida yau zataje bikin kawarta Zainab.

Saida tai salla tai karatu sanan ta gyara dakinta tsaf tafito kasa ta sauka a kitchen ta tarda Mama tsaye zata fara aiki dawani irin gudu taje ta rungume Mama. “Mama good morning” murmushi Mama tasakeyi this is another aspect na halin Umma datakeso ko kadan batada riko, tureta Mama tayi tace “waike karyani kikeso kiyi” dariya tayi tace “Mama dadi nakeji yau bikin Zainab Kawata, Beaty wacce nai ankon ta kin tuna”? Baki Mama ta tabe tace “ina zan tuna wata Besty Bestotin kin sunfi dari, keda kullum cikin bikin kawayenki ake, idan babanki ya shigo kije ki tambayeshi izini baruwana da zuwa bikinki, bani tukunya nidai kiga” dasauri tadaukoma Mama tukunyar nan suka shiga hada breakfast tanama Mama surutu wuraren 8 suka gama komi suka jera a falo daidai nan su Baba suka shigo gidan duka zama sukai a falo suka shiga kari sai bayan an gama ta kwashe komi takai kitchen sanan tadawo da saurinta tazauna kusa da Baba, fuskanta kadai yagayamai dawani abu hakan yasa yace “Ya akayi Khairiyya?” Murmushi tayi tace “Baba yau bikin Zainab kawata shine nakeso nagayamaka” idanu Baba yazuba mata yace “amman kinsan yau yakamata kije gidan Baffan kiko” gyadamai kai tayi dasauri ahankali tace “Baba gobe zanje gidan tunda yau inada biki please naje Baba”? shiru yayi sai chan yace “ok kije, but by 4 kidawo gidan nan ban yarda kije kai Amarya ba” murmushi tayi tace “Baba ai daman bazanje ba itada za’akai Kano, kumama ana daura aure wai zaa tafida ita kaga kenan kafin 4 nadawo ma” jinjina kai Baba yayi yace “duk kincikani da surutu, okay to adawo lpy, ki kama kanki banson kula maza okay” dasauri tace “to Baba, bari naje na shirya to” tai maganan tana tashi tai sama, tashi Manaf yayi yace “bari naje na kwanta Mama” binshi Mama tai da kallo yawuce yafita shikuma Maheer da Mu’az Kwallo suka kunna a falon suna kallo abinsu, Baba kuma na duba wasu files dayasa Mama tadaukomai daga dakinshi.

Wanka tasakeyi sanan tashirya cikin wani hadaden ashobe, skyblue, dogon riga aka mata daya kamata daidai ita ya bala’in mata kyau, yabi jikinta sosai, zama tayi gaban madubi tana kallon kanta, dan tsaki tayi takai hannunta tana shafa siman rigan da akabi da net da kana iya hango tudun saman boobs dinta ahankali tace “I hate style like this dake nuna jikina, I will use gyalena narufe Mtsww” tasake jan tsaki sanan ta zauna tai wani lafiyayyen dauri dazaka dauka make up artist ce tayi, kwalli ta zizara sanan tadau wani lipgloss tasaka dayasa lips dinta shining pink din jiki yafito sosai dazaka dauka janbaki pink tasaka, wayanta dake gaban mirror kiran samsung note 22 ta dauka, ganin 10miss calls yasa tace “OMG guys gani nan zuwa kunata kirana” ganin battery ta yay ja yana nuna 10% left yasa takara jan tsaki tace “ohhh namanta bansa chaji ba” arayuwanta babu abinda take kiwuyan sawa irin chajin waya wani zubin sai wayan ya mutu russ ne shine zata dauka ma tasa a chaji, jefa wayan tayi a shinning handbag dinta dake ijiye kan mirror sanan tajawo wani hill na dolce gabana tasaka sanan tamike tsaye, dan karamin gyalenta tadauka ta warware sanan ta yafashi ta gaba tsaf yarufe mata kirji sanan tadauki turarukanta ta feffesa kafin ta maida komi yanda yake tafito lokacin 12:48PM.

Saukowa tashiga yi daga Mama sai Maheer afalon yana kallon wrestling shima Mu’az yatafi ya kwanta, kamshin dayaji yasa yajuyo ganin Khairy yasa yasaki baki yace “ke kece amaryan Wanan kwalliya haka, Wanan ko ranan aurenki banjin zaki irin wanan kyan ba” hararanshi tayi takalli Mama dake binta da kallo tace “Mama kin ganshi ko” hararan Maheer Mama tayi hakan yasa yay shiru itakuma takaraso wajen Mama tace “Mama zan tafi ina Baba?” Ahankali Mama tace “Ya kwanta, ga kudi ya ijiye miki” tanuna mata bandir na yan 200 dasauri tadauka tana murmushi tace “Allah sarki Babana he’s the best, Mama natafi” tai maganan tana wucewa zatai kofa, Mama tace “ke” dasauri tajuyo takalli Mama dake kallonta, Mama tace “kindaiji abinda Baban ki yace ko, 4 tamiki agida Umma, kuma ki kama kanki, baruwanki da maza ko abokan ango, saura kuma naji kin wuce wani gantalin daban, wlh kika saba any of them bikin dazakije na karshe kenan ban kara barinki fita” dasauri tace “Mama I promise, nida keda bukukuwa I will not jeopardize that Mama, bye, Mama zan kawo miki alkaki” hararanta Mama tayi tace “banso, wuce Direba na jiranki” kofa tabude tafice, Already Adamu Direba harya shiga cikin motan ita kawai yake jira, wata lafiyayyen bakar Benz tabude baya tashiga sanan tace “gidansu Zainab zamu Adamu” “to Hajiya” yay maganan yana tada motan yaja, saida sukahau kan titi sanan taciro wayanta dake nuna 9% yanzu sabida uban kiran dasuke mata, kafin tama danna wayan wani kira yashigo da suna Zainab, daukan kiran tayi tana dariya tace “Amarya kinsha kamshi da turare, kuma wani gida ne gani ahanya” shiru tayi sai chan tace “Okk” sanan tace “Adamu suna gidansu Amal wai” ahankali tace “to” dan babu gidan wata kawarta dabaisani ba, tafiya kai nisa sukayi sanan suka shigo wani hadadden estate daya cika da mutane kana gani kAsan biki ake wani Layi daban ya shiga sanan yay parking agaban wani hadadden gida, murmushi tayi tace “yauwa, Adamu bani key motan narike” dasauri yajuyo ya kalleta, ganin kaman yanaso yaganota yasa tace “zan taimaka musu dashine, ana kwaso one or two things dazamuyi amfani dashi, idan zan dawo zan kiraka saikazo mutafi” tai maganan tana mikamai hAnnu, ahankali yazari key motan yabata karba tayi tace “yauwa katafi to dan sai yamma zan kiraka” tai maganan tana fitowa daga motan shima fitowa yayi sanan tarufe motan ta danna lock tawuce cikin gidan abinta shikuma yawuce yatafi zuwa bakin titi ya tsaye abin hawa yahau.

Tun kafin tashiga gidan takejin tashin kida, murmushi tayi ta shiga gidan an gyara anyi decorating ga yammatan Amarya sai rawa suke suna hangota aka wani hau ihu. “Khairy, Khairy ta iso, ke join us” wani irin murmushi tayi kaman abinda take jira kenan dasauri tai dance floor din, DJ yasakan musu wani mad song rawa sukahau yi suna ihu suna hotuna idan kaga Khairy zaka dauka taje dancing school ne, suna haka saiga Amarya tafito wani mahaukacin ihu sukasa aiko tashigo itama sukahau rawa kaman mahaukata, Amaryan ta rungume Khairy tana mata magana a kunne, hakan yasa taciro wayanta tana video ganin wayan na nuna mata 1% yasa tai tsaki ta maida bag sanan taciro kudi tana ihu yara sai kallonsu suke taba manna ma amaryan. It was fun she love her friends and she loves wedding har buri takeci irin na shagulgulan da zaayi idan bikinta yatashi.
???? ALKAWARIN ZUCIYA ????

  PROMISE OF THE HEART ????


     ✍????M SHAKUR 

4️⃣

Kafin ma Baba yabude kofa tasa hannu tabudemai kofan jikinta har rawa yake tanajin dadi. “Baba oyoyo, Baba sannu da zuwa” wani magidancin mutum ne babba sosai yana sanye da babban riga yanada gemu dayacika da furfura, ga kuma katon ciki irin na manya wayanda suka manyanta dinan, exactly idanunsu iri daya da ita manya saidai nashi daya soma kankancewa sabida tsufa, wani kalan kyayataccen murmushi yasakin mata, cikin kamilallen muryanshi irin na magidantan nan yace “yarinyar Babanta” yay maganan yanajan dan hancinta, murmushi tayi sosai tace “sannu da zuwa Baba” fitowa daga motan yayi yace “to akwasomin kaya akai ciki” gyadamai kai tayi tace “to Baba” yawuce yana kallon yaranshi maza su uku da duk suke tsaye suna jiran fitowanshi, Manaf wanda yake Babba yanada 27yrs, sai Mu’az shima 27yrs twins ne shida Manaf saidai ba identical twins ba ko kadan ma basuyi kamaba idan baa gayamaka yan biyu bane bazama ka yardaba, Manaf na kama da Mama, Mu’az na kama da Baba, sai Maheer dakenan 24yrs, dukansu sun gama makaranta duk a company Baba suke aiki yanzu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button