ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Kallo daya Anty Mariya tamai taganeshi cikeda girmamawa tace “bismillah Aliyu shigo” hannunshi yasa ahankali yazare glasses na idanunshi sanan yakalli Anty Mariya ahankali yamika mata ledan hannunshi yace “sauri nake daman na shigo na duba mara lafiya ne bari naje” yajuya zai tafi dawani irin sauri Khairy data yunkuro daga gadon tana yatsine fuska sabida zafin datakeji inda aka mata dinki tace “Ya Aliyu!” Chak ya tsaya batare daya juyoba kirjinshi na tafarfasa dan ana bude kofan idanunshi suka sauka kan Zayn da yanda yaga yana kallon Khairy, juyowa yayi ahankali yazubamata mayun idanunshi hawayen dayaga sun taru a idanunta da yanda yaga tana yatsine fuska sabida tasowan datayi yasa yadago kafa ahankali yashigo dakin batare dayakai wajen gadon ba yay folding hannunshi akirji yana kallon kwayan idanunta da ita kadai zata iya fassara maganganun dake cikinsu asanyaye yace “lay ur back” gyadamai kai tayi kaman Yar baby shi, sanan takoma ahankali ta kwanta back, murya chan kasa yace “Ya jiki”? Ahankali kaman ba itane kemagana da dan kyau ba dazun nan tawani narke kaman wacce ke shirin fashewa da kuka yace “fine” kasa daurewa yayi zuciyanshi namai zafi da ciwo sosai, ahankali yace “meke miki ciwo”? Daga Anty Mariya har Zayn kallonta sukayi, gently takai hannunta tanunamai gefen cikinta, boyayen ijiyan zuciya yasauke sanan yajuya yace “lemme call Dr for you” yawuce zai fita, saida yakai daidai kofa tasake kiranshi amugun hankali. “Ya Aliyu” chak ya tsaya still, kafin chan batare dayajuyo ba yace “I will get the Dr for you, sai anjima Anty” dasauri Anty Mariya tace “sai anjima Aliyu an gode” kallon Khairy yayi nakusan 1min dayaga takife kanta a filo sanan yatashi shima yakalli Anty Mariya yace “bari naje anjima zan dawo” murmushi tayi tace “tom Zayn angode” sanan yawuce yafita, Anty Mariya da takaranci komi that just happen in this room tasauke ijiyan zuciya ahankali tana kallon Khairy datai kaman tana bacci taji anbude kofa Dr yashigo.

Aliyu na gab da tada motanshi yaji anyi knocking glass din motar, juyowa ahankali yakalli wajen ganin Zayn ne tsaye yasa ahankali ya danna botur yasaukar da glass din motar yana kallon Zayn din da idanunshi dasuka dan chanza launi, folding hannu Zayn yayi akirji dan idan baiyi hakaba ayanda kirjinshi yaji yana tafarfasa da mugun kishi zai iya dambe da wanan dan sandan, cikin wani yanayi na rashin mutunci yace “what’s between kai da kanwata”?Wani kallo Aliyu yamai ido da ido kaman yazaro bindigarshi ya bindige Zayn yakeji, akufule yace “go and ask ur sister” wani irin kallo Zayn yamai ganin kome yake takama dashi shima haka Aliyu yake takama dashi yasa awulakance yace “stay away from this hospital and stay away from my sister, I don’t want you handling case din barayin nan zanzo nasa abama wani dan sandan, duk randa nakara ganinka anyway near my sister law zai rabamu” wani matsiyacin kallo Aliyu yamai kafin yadau bakin glasses dinshi yasa a idanunshi yakalli Zayn din awulakance yace “I am the law! So do your worse” yana maganan yadaga glass din motanshi sama yawani ja motar da mahaukacin gudu yafita dashi daga asibitin yanaji kaman zai mutu da bakin kishi.

Kwana uku Khairy takara a hospital aka sallameta gidansu tace zata Anty Mariya kaman an mata kyauta, fir Batool tace itama gidan Baba zata koma babu wanda yahanata suka koma wajen nan tabama Khairy labarin all abinda yafaru har jinin da Aliyu yabata sanan tace taji Baffa yace ankama duka barayin sun saida motan Zayn din amman an samo motan itama, sanan Zayn suka dinga bi tun ranan farko daya fara zuwa Variety suka ganshi suke binshi dan sunga big boy ne.

Wuraren 11 nadare tai dialing number Aliyu harya katse bai daukaba saigashi yakirata dawani irin sauri tadauka ahankali yace “Pickle” murya chan kasa tace “Ya Aliyu ina yini” ijiyan zuciya yasauke yace “ancemin an sallameki yau ko hope u are good” shiru tadanyi kafin ahankali tace “Ya akayi kasan an sallameni” murya chan kasa yace “I come everyday to check on you dudda bana shigowa dakin” wani kalan murmushi tayi tanason Aliyu over ko Allah ma yasani, murya chan kasa taji yakira sunanta. “Ummulkhair!” Dan faduwa gabanta yayi dan wani irin faduwa gabanta yaje most time idan yakira sunanta haka, murya chan kasa tace “na’am” dan shiru yayi nakusan good 1min, sanan ahankali yace “is there anything between you and dan uwanki Zayn da I don’t know about” dan zaro idanu tayi dan bama tagane kan tambayan ba hakan yasa takasa ma magana, ahankali yasake maimaita tambayan. “Akwai soyayya tsakanin ke da Zayn ne?” Wani irin zaro idanu tayi adan rude tace “ni? Nooo a’a wlh, why will you ask me such question”? Dan shiru yayi sai chan taji yasauke ijiyan zuciya yace “abar maganan tunda kince no I believe you” tsoro taji yadan shigeta ahankali tace “Ya Aliyu are u fine” ijiyan zuciya yadan sauke sanan da kyar yace “I am now!” Yasake yin shiru saikuma chan yace “remember I told you I am a very very jealous person, banda yan uwanki danasan kun fito ciki daya su Manaf I can’t stand inga any man on this earth yana baki any affection look, Khairyyyy I love you don’t you get that, I am crazy and obsess dake” dan murmushi tayi sai yanzu tama gane maganan dayake yadauka ita da Ya Zayn soyayya suke saisa duk yay wani iri Ya Aliyu nada mugun kishi kam, dan murmushi tayi tace “Ya Aliyu kai kadai nakeso aduk duniyan nan, nima I am obsess with you, saisa nama zuciyana alkawari kai nata ne, THE PROMISE OF MY HEART is you” murmushi yadanyi kafin ahankali yace “Khairy inaso naturo iyayena suga Baba” dasauri tace “Ya Aliyu dan Allah kabari nakarasa school kagafa baifi 2month yaragemin ba nama fara project ta online nake turama professor na yana dubawa, kaga I want to enjoy my wedding ayi event kala kala nai rawa kasan na iya rawa” dan murmushi yayi yace “so I heard” dariya tayi tace “dagaske fa” hira tadinga mai kaman ba ita aka sallamo daga asibiti ba harsaida yasaki zuciyanshi sosai sanan wuraren 1 yasata tai bacci badan taso ba.

Kusan kullum sai Zayn yazo gidansu batasan mesa ba kofan tambayan da Ya Aliyu yamata ne hakanan saita fara gujemai, dazaran yazo tagaidashi zata wuce dakinta zatajishi dasu Manaf suna hira afalo Baba ma yadawo duk suhade sai dare yake barin gidan amman ita bata taba saukowa, kullum tana zuwa school tadage da project dinta Maheer natayata yi yanzu ma haka tana chapter 4.

Yau duka duka saura 14 days sufara final exam dinta tadage da karatu sosai, at the same time Baba da Baffa da abokanen su sukaje nemawa Manaf Auren Aisha, Mu’az kuma Auren Maimuna sanan washe gari sunday Baba yasa dukansu su shirya dan gidan Baffa zDasu yau zasuyi family meeting.
4️⃣5️⃣

Faduwa gabanshi yayi ahankali yafara kokarin saukar da kanshi kasa dan ko kadan bazai iya ya kalli kwayan idon Abban yamai karyaba, cikin kakkausan murya Baffa yace “look at me Zayn bance ka saukarmin da kanka kasa ba” ahankali yakalli Baffa, cikin fushi Baffa yace “Zayn shaye shaye kakeyi”? Dawani irin sauri Ammi takalli Baffa jin kalman shaye shaye tace “wai Alhaji sabida Yar gwal dinku da aka chakama wuka dan tana tareda d’ana shine haryakai afara tuhuman d’ana da shaye sha…..” dagamata hannu da Baffa yayi afusace yasa takasa karasa maganan cikin kakkausan murya yace “kimin shiru Rabia’atu, I am not ready for sakarcin ki this morning” sanan yamaida kanshi kan Zayn yace “daya daga cikin offisoshin dayamin yan tambayoyi yasanar dani agaban Variety Pot kai parking motanka kashiga ciki Khairy kabarta amota anan waje, wajen babu abinda ake saidawa sai kayan shaye shaye da kayan maye daban daban Innalillahi wa innailaihi raji’un Zayn yaushe kafara shaye shaye tarbiyan danamaka kenan shaye shaye!” Baffa yay maganan yana kallon fuskanshi dan fuskan Zayn bayatabamai karya, kallonshi kadai yakara tabbatarmai da yes shaye shaye yaje yayi, Baffa jiyayi ranshi na tafarfasa yace “Zayn tayaya zaka dauko mace, Yar yarinya ka ajeta gaban wajen da ake shaye shaye da kasan criminals nanne majalissan su, kashiga ciki kaje shaye shayen ka kabarta inba sakarci da rashin hankali irin naka ba” Baffa yadanyi shiru yana kallonshi kafin cikin ihu da saida gidan ya amsa yace “inda yarinyar nan tamutu tayaya kakeso na kalli mahaifinta dabai dade da rasa matarshi ba iyye? Tayaya!” Baffa yay ihu da saida Ammi tadaura hannunta aka, Baffa yace “kasan menene tsakanina da Baffan ka mahaifin Khairy kuwa?? Bamuda dangantaka ta jini amman duk duniyan nan ko yan uwana basukai Baffan ka matsayi, kima da daraja awuri naba, azuciyata ba daduka duniyan nan Zayn, duk duniyan nan banida kaman Baban Khairy, bakuma zan taba samin kaman Baban Khairy ba, kabani kunya Zayn kabani kunya, kayi karatun addini kasani cewa shaye shaye is haram, duk wani abu aduniyan nan dakesa maye haramun ne annabi yahana sha, bari Khairy ta warke zaka sha mamaki” Baffa yay stairs dasauri Zayn yatashi zai bashi hakuri amman ina harya wuce hakan yasa yadawo yazauna yadaura hannunshi akai, saida Ammi taji rufe kofan Baffa sanan takalli Zayn da duk yabi yadamu ahankali tace “karka damu kasan mahaifinka bazai taba iya fushi dakaiba relax I will talk to him, kaga abinda yasa banson yarinyar nan ba banmason hadinka da ita, nasan cewa zaka dauketa kaje gidansu da ita dana sani ai da bazan taba bari kadauketa ba, akan me zata wani jazawa d’ana bakin jini, har ana kiran d’ana da dan shaye shaye, Zayn dina dako hayaki bayaso, mtswww aikin banza wlh ko ganinka nasakeyi a inda take saina cimaka mutunci Zayn nagaya maka baka ba ita dagayau” saida Ammi tagama surfafamai bala’i sanan ta tashi tai sama yadade zaune awajen sanan ahankali yatashi yafita daga dakin zuwa nashi dakin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button