ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Hannun kujera Ammi tadaka cikeda bala’in dakin na amsa masifanta jikinta na girgiza tacigaba da magana. “Idan zuri’a kukeso kuhada abotanku yadawo tajini inace nan nan nan ga Batool nan diyar kace maisa baka hadata da Manaf ko Mu’az ba koma Maheer sai akan d’ana Zayn dina, kasan plan din danake dashi , buri danaci akan yaron nan nawa dazaka hadashi da yar gwal dinku? Kasan wace yarinya nakeso Zayn ya aura kasan matsayin Baban ta anan Nigeria kuwa kaga kyan Aisha? Wlh bazaka maidani karaman mutum a idanun kawata ba” takalli Zayn cikeda ihu tace “Zayn kalli fuskan mahaifinka kacemai bakason auren nan yanda sukayi suka hada auren subi haka su warware” shiru Zayn yayi kanshi nakasa shi bazai iyama cewa farin ciki yake ba ko bakin ciki all he knows is yaji dadin wanan labarin dayajita bagatatan haka kaman daga sama.

Baki Ammi tabude zata kara magana Baffa yadaga mata hannu cikin fushi, anatse yace “kinsan maisa duka wanan ihun dakike yi danki tozartani bazai taba bani kunya ba”? Dan murmushi yayi yace “sabida agaban dan uwana da yarana kike ko zaginane zaki iyayi” Baffa yasake murmushi yace “auren nan ba marigayiya kadai tai tunanin shi ba har mu nan, duk duniyan nan babu wanda zai rike Khairy amana kaman dan uwanta kuma Yayanta Zayn! Bata fita daga family ba zamu riketa amana dan dan uwanta take aure, banda kwanciyan hankali daya wuce nasan d’ana ke auren Khairy da mahaifiyarta tabani amana, nasanki karki manta na zauna dake tsawon shekaru danmu na farko shekarun shi 36 so babu wanda zai iya bada labarin halinki kaman ni, nariga nasan bakison mahaifiyar Khairy hakan zaisa bazaki tabaso auren shi da yarta ba abu nafarko dayasa naji bazan taba fadamiki ba kenan sai ranan da zan hada yaran nan nafada musu kisani kema, dan haka kome zakiyi kiyi Zayn mijin Ummulkhair ne nan da wata daya za’ayi walima ta tare agidanshi, kutashi kutafi” cikin yaran babu wanda ya iya cewa uppan duk mikewa tsaye sukayi banda Khairy data kasa mikewa tsaye tana kallon Baba idanunta sunyi jazur Baba shima yana kallonta, hannunta Batool takamo zata dagata tace “tashi muje Khairy” ahankali Baba yace “barta Batool” tashi yayi ahankali sanan yadauki wata yar jakan dake kusada shi yabude wani littafi yaciro tana kallon littafin ta tunashi Dairy Mama ne, karasowa gabanta Baba yayi ahankali sanan ya tsugunna agabanta yana kallonta, ahankali cikeda so dakuma tsantsar kaunar yarshi yace “Khairy kingan mu nan we are not bad parents idanma abinda kike tunani kenan, all abinda kikeji azuciyanki yanzu nasani, kina tunani tayaya aka miki aure tun kina karama baa taba sanar dake ba, auren ma da Yayan ki Zayn, wanda baki taba kallo da fuskan so ba, wanda bakisan koshi yana sonki ba” dan murmushi yayi yace “kituna babu aure mai albarka kaman wanda iyayenka suka zaba sanan suka maka banda haka kiyi tunanin auren nan mahaifiyarki dakikafi komi so aduniyan nan tahada ita tama miki shi Ummulkhair, and lastly mahaifiyarki tace nabaki Wanan abin ki karanta idan rana irin tayau tazo gashi” Baba yasamata book din a hannu, wani irin kankame book din tayi gam gam sanan Batool tadagata bin Batool kawai take suka wuce mota suka shiga suka zauna itama ahankali Anty Mariya tashigo taxauna tana kallona Khairy da idanunta suka bushe babu hawaye ko digi bazama ka iya tantance metake going through ba, chan saiga Baba yafito tareda Baffa motansu yazo yashiga yaja suka tafi sanan Baffa yawuce yakoma ciki biyoshi Ammi tayi tafara surfafa bala’i amman tak bai cemaDta ba.
4️⃣7️⃣

Ahankali take shiryawa dan ita ko kadan bataso taje gidan Baffan dan bamataso su hadu da Zayn dataga Kwanan nan wani mugun kallo yake mata kaman zai hadiyeta, Batool da harta gama shiryawa tace “wai bazakiyi sauri ba kinata abu ahankali kaman bakida kayan ciki” hararanta tayi tace “dalla chan” bude kofa Anty Mariya data shirya tayi takalli Khairy tace “har yanzu baki gama ba” gyalen abayan data saka tadauka baki tace “na shirya Anty” sanan tadauki jakanta Batool ta tashi suka fito zuwa compund ganin Ya Manaf da Mu’az yasa tai wani murmushi cikeda tsokana tace “angwaye wai kwana nawa aka saka ne” hararanta Baba daya fito yayi yace “ban fadamusu ba sai munje gidan Baffan su zasuji” dariya tayi tace “wlh Baba duk sun kosa” hararanta Manaf yayi yashiga motan shi yace “karki sake kizo motana Batool taho kinji” dasauri Batool tai wajen, Baba yace “manta dasu muje motana kinji” gwalo tamusu suka wuce tashiga motan Baba, Anty Mariya na gaba ita kadai abaya sanan suka wuce batasan mesa ba hakanan taji gabanta nafaduwa dum dum dum, daura hannunta tayi kan kirjinta tana addu’a azuciyanta tana kallon hanya ahaka har sukakai gidan Baffa, Babban falon Baffa sukaje, tunda tashigo taga Zayn na kallonta kaman zai hadiyeta dawani irin sauri tadauke kanta tagaida Ammi data amsata ciki ciki sanan tawuce wajen Mom tazauna kusada kafanta Batool ma tazauna awajen tana gaida Ya Hafiz dake zaune kusada matanshi yana rikeda Babyn su dake bacci, gasu Hassan a zaune kowa a zaune, Baffa na zaune kusada Baba

Ahankali tadago kanta hada idanu sukayi da Zayn dataga yasakin mata wani cool smile dasauri tadauke kanta takalli Baffa dake gyaran murya.
Anatse Baffa yabude taron nasu da addu’a sanan yace “jiya munje gidan iyayen yarinyar da Manaf dakuma Mu’az sukeso su aura, Alhamdulillah komi ya daidaita bamu sanar daku komi gabe da abin bane sabida akwai abinda mukeso musanar daku wanda dukanku nan babu wanda yasan maganan dagani sai Baffan ku nan” yanuna Baba saikuma “marigayiya mahaifiyan ku Manaf” yanuna su Manaf, tsit dakin yayi, gyaran murya Baba yasakeyi yace “an sakawa Manaf da Mu’az ranan aure kimanin sati hudu wato wata daya kenan” murmushi duk akayi Hafiz najan bayan rigan Manaf dake murmushi cikeda tsokana yana kabarda hannunshi sanan anatse Baffa yace “yara nata aure amman asalin Babban yayan gidan nan shiru” dariya Hafiz yayi Ammi ta ballamai harara, anatse Baffa yace “gawata labari” sanan ahankali yafara magana yace “shekaru ashirin dasuka wuce abaya, lokacin Zayn yashiga JSS 1, Hafiz na primary school, su Hassan na Hussaini sune yara alokaci dudda suma primary suke, Maryama wato mahaifiyan Ummulkhairy ta haifi Ummulkhair” Baffa yadanyi shiru, ajiyan zuciya yasauke yace “bayan an haifi Khairy Maryam was very very sick, after series na test and investigations alokacin ne aka fara gano cewa mahaifiyar ki nada blood cancer!” Shiru kakejin dakin kaman ruwa ya hadiye kowa, ganin Baffa yakasa magana yasa ahankali Baba yace “Maman ki was very very scared Khairy son da Mama kemiki tun ranan dakika fado duniya ne, bansan mesa ba kodan agidan marayu ta taso tana matsayin ya mace batasan kowa nata ba tai wahalan rayuwa, kodan sabida taga kema mace ce batason kiyi wahalan rayuwan datayi gashi ance tanada cancer bazatai wani rayuwa mai tsawo ba dan lokacin bama agama sanin kan treatment na blood cancer ba yasa ranan cikin dare ina bacci akan kujera naji Mamanki ta tabani tana kiran sunana” Baba yadanyi shiru ahankali yace “bude idanu nayi naganta zaune kan gadon asibitin rikeda ke a hannu” Baba yakarayin shiru yadan fuzar da iska nai dumi, Ahankali yace “Maman ki was very very sick jikinta yay bala’in zafi tacemin tana ganin one of this days zata mutu dan haka nakira Baffa nacemai idan zai taho yazo mata dasu Manaf dake gidanshi wajen Ammi nacemata to ganin hankalinta atashe yake sanan takara kallonki” Baba yay shiru yace “tana kallon fuskanki tacemin batason Ummulkhairy tasha wahala, sanan duk duniyan nan banda ni babu wanda ta yarda dashi kaman Baffan ki tasan ko Bana duniya sai inda karfinshi yakare akan yarana sabida haka tanason ta aurar dake tun yanzu datake da ranta a inda ko yanzu yanzu tafadi tamutu zata tafi batada damuwa” Baba yakara yin shiru kowa na kallonshi, handkerchief yaciro daga aljihu yakai kan idanunshi dan ko kadan bai son yay kuka agaban yaran shi, kafadan shi Baffa ya matse sosai yakalli yaran yace “Baban ki yadauka awanan daren Maman ki zata rasu, bayan tamai maganan nan tasashi yakirani awaya, kunga acikin kuryan darenan haka nashiga mota nazo asibitin nan, cikin tsananin zazzabi tana rike dake a hannunta tace tanaso tabani amanarki sanan tana neman alfarma wajena…..” wani irin faduwa gaban Khairy dake kallon Baffa chass takeyi dabama tasan na miyeba, ahankali Baffa yace “Maman ki tace tanaso nahada Ummulkhair da Zayn babban dana wanda Mamanki takeso sosai sun shaku da mamanki sama da su Hafiz ma, tace tanaso nahada ku aure” Zayn da tunda aka fara maganan kanshi ke kasa sai alokacin yadago kanshi yakalle Babanshi dake Magana, Baffa yace “jikin Maman ki yay zafi yay tsanani duk mun zaci zata rasune, Gyadamata kai nayi na nuna amincewa na, tace mukaita masallaci adaura auren, I remember Baban ki yafita waje yadauko keken guragu muka daurata akai muka gungura keken har zuwa masallacin dake asibitin nan dayake nan kaman ba dare ba jama’a duk suna zazzaune some a kwance iri masu jinyan nanne, da sauransu limamun muka kira mukamai bayanin komi ya matukar tausayama Maman ki sanan aka gungurota aka shiga da ita masallaci tana rike dake a hannu limam yadauki microphone aka tada duka mutanen dake bacci” tsinkewa gaban Khairy yahauyi yana dawowa daidai hakama Batool, Ammi, Zayn dakuma Anty Mariya, kowa na kallon Baffa, murya chan kasa Baffa yace “all I had was 20k ajikina haka na bayar kudin sadaki dani da mahaifinki limamin masallacin mahaifiyar ki jama’an dake wajen suka shaida daurin aure tsakanin Ummulkhair Ahmad Muhammad da Zayn Abdullahi Gabas akan sadaki naira dubu ashirin!”
Khairy jitayi numfashinta zai dauke kunenta yay dummm kaman ta sume ne kaman tafice hayyacinta ne oho ita kanta bazata iya tantance wani yanayi take ciki ba, daga Baba har Baffa murmushi sukayi suka kalli juna, Baffa yace “inda ace Baffan nan naku nada yara mata dayawa zansa yarana maza duka su aurensu sabida inaso muhada zuru’a wanan amincin dake tsakanin mu na abota takoma na jini, saisa bayan mun daura auren muka yanke shawarana sai yaranmu sunyi girma sun mallaki hankalin junansu zamu sanar daku, yanzu ma bikin su Manaf ne sabida munaso muhada bikin su da kuma taron bikin su Zayn ayi atare saisu tare nan da wata daya lokacin Ummulkhairy itama tagama jarabawa tagama makaranta ko aminina” gyadamai kai Baba yayi yana wani irin murmushi, Ammi dajitayi komi na duniya ya tsaya mata chak takalli mijin nata, cikin wani irin masifa tace “Alhaji na dauki cikin Zayn na wata tara, na tsugunna na haifo dana dakaina batare da wata ko wani yatayani ba ninasan ciwon kan d’ana nasan wahalan danasha na tarbiyantan dazai ka kama shekaru kusan ashirin kenan kama d’ana aure baka sanar dani ba wlh wlh wlh kayi kadan!” Ammi tama Baffa magana babu ko shakkan shi guda akan idanunshi dayasa kowa yakalleta shima Zayn yakalleta uppan Baffa baice mata ba hakama Baba duk kallonta suke da Mom da Anty Mariya dasauran yaran.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button