ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL
ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Hannun kujera Ammi tadaka cikeda bala’in dakin na amsa masifanta jikinta na girgiza tacigaba da magana. “Idan zuri’a kukeso kuhada abotanku yadawo tajini inace nan nan nan ga Batool nan diyar kace maisa baka hadata da Manaf ko Mu’az ba koma Maheer sai akan d’ana Zayn dina, kasan plan din danake dashi , buri danaci akan yaron nan nawa dazaka hadashi da yar gwal dinku? Kasan wace yarinya nakeso Zayn ya aura kasan matsayin Baban ta anan Nigeria kuwa kaga kyan Aisha? Wlh bazaka maidani karaman mutum a idanun kawata ba” takalli Zayn cikeda ihu tace “Zayn kalli fuskan mahaifinka kacemai bakason auren nan yanda sukayi suka hada auren subi haka su warware” shiru Zayn yayi kanshi nakasa shi bazai iyama cewa farin ciki yake ba ko bakin ciki all he knows is yaji dadin wanan labarin dayajita bagatatan haka kaman daga sama.
Baki Ammi tabude zata kara magana Baffa yadaga mata hannu cikin fushi, anatse yace “kinsan maisa duka wanan ihun dakike yi danki tozartani bazai taba bani kunya ba”? Dan murmushi yayi yace “sabida agaban dan uwana da yarana kike ko zaginane zaki iyayi” Baffa yasake murmushi yace “auren nan ba marigayiya kadai tai tunanin shi ba har mu nan, duk duniyan nan babu wanda zai rike Khairy amana kaman dan uwanta kuma Yayanta Zayn! Bata fita daga family ba zamu riketa amana dan dan uwanta take aure, banda kwanciyan hankali daya wuce nasan d’ana ke auren Khairy da mahaifiyarta tabani amana, nasanki karki manta na zauna dake tsawon shekaru danmu na farko shekarun shi 36 so babu wanda zai iya bada labarin halinki kaman ni, nariga nasan bakison mahaifiyar Khairy hakan zaisa bazaki tabaso auren shi da yarta ba abu nafarko dayasa naji bazan taba fadamiki ba kenan sai ranan da zan hada yaran nan nafada musu kisani kema, dan haka kome zakiyi kiyi Zayn mijin Ummulkhair ne nan da wata daya za’ayi walima ta tare agidanshi, kutashi kutafi” cikin yaran babu wanda ya iya cewa uppan duk mikewa tsaye sukayi banda Khairy data kasa mikewa tsaye tana kallon Baba idanunta sunyi jazur Baba shima yana kallonta, hannunta Batool takamo zata dagata tace “tashi muje Khairy” ahankali Baba yace “barta Batool” tashi yayi ahankali sanan yadauki wata yar jakan dake kusada shi yabude wani littafi yaciro tana kallon littafin ta tunashi Dairy Mama ne, karasowa gabanta Baba yayi ahankali sanan ya tsugunna agabanta yana kallonta, ahankali cikeda so dakuma tsantsar kaunar yarshi yace “Khairy kingan mu nan we are not bad parents idanma abinda kike tunani kenan, all abinda kikeji azuciyanki yanzu nasani, kina tunani tayaya aka miki aure tun kina karama baa taba sanar dake ba, auren ma da Yayan ki Zayn, wanda baki taba kallo da fuskan so ba, wanda bakisan koshi yana sonki ba” dan murmushi yayi yace “kituna babu aure mai albarka kaman wanda iyayenka suka zaba sanan suka maka banda haka kiyi tunanin auren nan mahaifiyarki dakikafi komi so aduniyan nan tahada ita tama miki shi Ummulkhair, and lastly mahaifiyarki tace nabaki Wanan abin ki karanta idan rana irin tayau tazo gashi” Baba yasamata book din a hannu, wani irin kankame book din tayi gam gam sanan Batool tadagata bin Batool kawai take suka wuce mota suka shiga suka zauna itama ahankali Anty Mariya tashigo taxauna tana kallona Khairy da idanunta suka bushe babu hawaye ko digi bazama ka iya tantance metake going through ba, chan saiga Baba yafito tareda Baffa motansu yazo yashiga yaja suka tafi sanan Baffa yawuce yakoma ciki biyoshi Ammi tayi tafara surfafa bala’i amman tak bai cemaHta ba.
4️⃣9️⃣
Bayan sunyi sallan asuba tareda Baffa da Zayn suka fito daga masallaci, tun bayan hatsarin nan haryau Baffa fushi yake da Zayn bayama amsa gaisuwan shi sai sa’i sa’i suna shigowa gida hannun Baffa Zayn yakama ahankali yace “Abba listen to me please” chak Baffa ya tsaya sanan ahankali yakalli Zayn din yay shiru, hannu Zayn yakai yakama kunnenshi ahankali yace “Abba nasan namaka laifi amman dan Allah ka yafemin and listen to me” wuceshi Baffa yayi zuwa kujerun dake garden na tsakar gidan masu kyau yazauna sanan yanunama Zayn daya daga cikin kujerun alamun yazo yazauna, ahankali yataho wajen yazauna yana kallon Abba, anatse Abba yace “Zayn shaye shayen ka bani kama laifi ba ubangijin daya hallito mu kamawa” murya chan kasa yace “Abba I know! Tun bayan abin yafaru I couldn’t live up to myself, Abba anytime naji inaso nayi I remember cewa abin yasa kanwata dat I care for wacce mahaifiyanta tabani amanan ta tace na kula da ita takusan mutuwa kan shan shishana, Abba ba lallai ka yarda ba wlh tun ranan ban kara marmarin shan shisha ba I even hated myself for shan shishan, Abba I am sorry” shiru Abba yayi yana kallonshi dan ya yarda da maganan shi dari bisa dari dan idanun Zayn basatabamai karya, ahankali Zayn yasa hannunshi yakama hannun Abba murya chan kasa yace “Abba I love Ummulkhairy tun kafin namasan da zancen auren and I want to promise you abu daya” yadanyi shiru sanan yace “Abba nasan bakada yanda zakayi ne daka tana auren mu tunda kagano ina shan shisha, Abba listen to me I have amended my ways wlh, and Abba namaka alkawari zan rike Khairy amana, bazan bari any harm to fall upon her ba, and I promise you Abba I will forever cherish and care for her batare dana bari Ammi ko anybody yatakurata ba and I will talk to Ammi zata yarda all those drama zata daina kaji Abba” hannunshi ahankali Baffa yakai kan bakinshi ya sumbace shi ahankali yace “Allah maka albarka Zayn” murya chan kasa yace “Ameen” tashi katafi, tashi ahankali Zayn yayi yawuce Baffa na kallonshi jiyayi duk wani nauyi da zuciyanshi yamai ya saukar tunda har Zayn din dakanshi yazo yay accepting mistakes nashi and promise to work on kanshi Abba jiyayi hankalinshi ya kwanta yanzu Ammi kadai tarage yasan ko itama she will come around.
All through ranan akan gado tayishi takasa fita school, takasa daukan wayan Aliyu takasa cin abinci gatanan ne kawai, wuraren magrib Anty Mariya tashigo dakin tana kallon Khairy dake kan gado maida kofan tayi tarufe sanan takaraso tazauna agefen gadon tana kallon idanun Ummulkhairy dasuka kumbura har lokacin hannunta takai tadagota tazauna sanan ahankali tace “maisa baki fadima Baban ki Aliyu kikeso ba” shiru Khairy tayi tana kallonta dan batasan ya akayi tasan aliyu takeso ba, ahankali Anty Mariya tace “nasan kinason Aliyu shima yana sonki tun a asibiti na karanci all of that, maisa baki fadiwa mahaifinki ba eh Ummulkhairy?” Ahankali tace “Anty kona fadamai is too late bazasu iya komi akaiba” shiru Anty Mariya tayi tana kallon Khairy she just wish tanada wani karfi dazata iya magance this whole case but her hands are tight, ahankali tace “Yaya zakiyi da Aliyu”? Wani irin ajiyan zuciya tasauke dasauri takai hannunta tashare hawayen daya zubomata sanan taja hancinta danji tayi majina zai gangaromata tace “zan gayamai gaskiya” ajiyan zuciya Anty Mariya tayi tace “to ki gaggauta fadamishi dan kinsan bai kamata kina magana da namijin daba naki ba ko” gyadama Anty Mariya kai tayi, ahankali Anty Mariya tashafa kumatunta tace “karki damu duk wanda yabi iyayenshi bayaci baya kinji” gyadama Anty Mariya kai tayi, Anty Mariya ta tashi tace “yanzu zan Aiko Batool da abinci yakawo miki kici” sanan tawuce tafice daga dakin, abinci Batool takawo mata kadan taci sanan tai sallan isha’i ta kwanta yau by 9 ma Aliyu yashiga kiranta, kallon wayan Batool tayi sanan ta tashi ahankali tafita daga dakin danta basu waje suyi magana, kasa daukan wayan Khairy tayi a third call dinne tadauka takai kunne.
Cikeda damuwa Aliyu yace “I am sick worried, Pickle what’s happening? Tun jiya I’ve been calling you baki dauka sokike ciwon zuciya yakamani” girgizamai kai tayi da sauri muryanta na rawa tace “n…..o” shiru Aliyu yayi hakan yasa dasauri ta taushe bakinta tana kokarin hana kanta kukan datakeji, yakai kusan 1min yay shiru kawai, kaman daga sama yace “waya saki kuka”? At this point zare hannun kawai tayi daga bakinta tafashe dawani irin kuka Aliyu knows her so well, if she’s happy yasani, if she’s sad yasani, if she cried yanajin muryanta yasani, shiru yayi yana sauraron kukan ta kaman yashiga wayan yazo inda take yakeji, almost good 2min yabarta tai kuka yanda takeso sanan ahankali cikeda iya lallashi yace “I always tell you I am here for you, why will you be crying haaa? Oya yishiru kinji” gyadamai kai tayi tana kokarin Hana kanta kukan, murya chan kasa ahankali yace “maiya sameki why are you crying”? Jitayi wani kukan yazomata tasake saki, cikeda damuwa sosai Aliyu yace “Pickle wai kasheni kikeso kiyi? U want my life eh? Kinsan yanda kukan ki ketabamin zuciya kuwa? Did you have any idea wlh idan kikaji ance I slump and die kece” rage sautin kukan tayi ahankali dan tasan ko karya daya baiyiba, cikeda lallashi yace “tell me menene, nazo gidanku naganki” dasauri ta girgizamai kai dan tasan wlh zai iya tace “a’a” ahankali yace “to what’s the matter”? Batasan yaya ma akayiba jitayi tace “cikina ke ciwo” tasake taushe bakinta jin takasa fadamai gaskiya for the first time yau tama Aliyu karya, shiru yadanyi sanan ahankali yace “sorry, is it MP? All this menstrual cramps shi?” Gyadamai kai tayi ahankali tace “eh” murya chan kasa yace “sorry, sannu, stop crying, kinsha magani kona siyo nakawo miki” ahankali tace “nasha” murya chan kasa yace “then it will stop soon, hey you this MP cramps I command you to leave my Pickle alone or I arrest you, nayi arresting nashi”? gyadamai kai tayi tana dan murmushi tace “eh” murmushi yayi jin tadanmai murmushi yace “okay MP u are under arrest for disturbing the peace and harmony na Miss Khairy, for taking away her smile and bringing her kukan banza back” dan dariya tayi, hakan yasa yace “yes koba kukan banza bane kikemin ba, idan kika ganni saiki kara wani narkewa kina kuka just to worry my heart Khairy angayamiki ban sani bane” at this point wlh tama manta itane mai kuka dariya tafara sosai, ganin haka yasa yace “haka ranan nazo asibiti u were very fine fa hira ma kike, kina ganina kika kokkobe fuska ashagwabe zaki faramin kuka sabida kawai ki rudani this girl keko don’t worry eventually zan saki kukan mai dalili” dariya tayi dan ita bamata gane last maganan ba, ahankali yace “kinci abinci”? Gyadamai kai tayi tace “but small baran iyaci dayawa ba” murya chan kasa yace “tom anjima idan yalafa sai ki karaci ko” tom, murya chan kasa yace “if it persist tell Batool tasa towel a warm water tamiki massaging abdomen it will stop” gyadamai kai tayi ahankali tace “tom” ahankali yace “gobe zaki school” girgizamai kai tayi tace “no sainaji sauki” Gyadamata kai yayi yace “okay, bari na barki kihuta idan pain din yadawo call me but don’t cry for me again” murmushi tayi tace “saina maka bye” dan dariya yayi ahankali yace “I love you Ummukhairi” katse wayan yayi dip, ahankali tajanye wayan daga kunnenta takasa koda kwakkwaran moHtsi.
4️⃣8️⃣