ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Koda sukakai gida kasama fitowa daga motan Khairy tayi duk Baba na kallonta da taimakon Anty Mariya da Batool suka fito da ita sanan suka shiga ciki Anty Mariya tace “tafi da ita dakinku Batool” wucewa da ita sama Batool tayi sanan tajuyo takalli Baba zatai magana Baba yadaga mata hannu anatse yace “Zayn shine best husband da Ummulkhairy will ever wish for, please karkimin wata magana aikin gama yariga yagama beside auren nan mahaifiyanta tamata shi” shiru Anty Mariya tayi tana kallon Baba saikuma ahankali tace “ok” sanan tajuya tawuce sama abinta.

Suna shiga daki Batool tazaunar da ita abakin gado sanan tamaida kofansu tarufe tasa key sanan tazo gaban gadon da gudu tazauna akasa kanta tadaura kan kafan Khairy tace “Khairy why are you not crying Innalillahi wa innailaihi raji’un, yanzu Khairy kefa matan aure ce, matan Ya Zayn, Khairy what about Aliyu? Ya Aliyu yaya zakiyi dashi? Khairy I am so sad for you not because Ya Zayn is a bad person but because of soyayyan da kukeyi da yanda kike sonshi da yanda Ya Aliyu yake sonki, Khairy how are you going to tell him eh? How”? Sai alokacin wasu kalan hot hawaye suka zubomata, jikinta harwani tsuma yake tana kuka mara sauti itama Batool kasa hanata kukan tayi saima rungumeta datayi suna kuka sosai, sun dade ahaka ganin asma ta na neman tashi yasada sauri tasaki Khairy tawuce tadauko mata inhaler ta dake kan drawer takawo mata tace “shaka and stop crying” ahankali ta shaka but takasa daina kukan, wani kalan bakin ciki da damuwa ne taji ya lullube mata zuciya littafin Mama ma sai kallonshi take takasa karantawa, da kyar da daddare ta iya shan tea tana zaune kallon wayanta kawai take idanunta sunyi jazur sun kumbura, wuraren 10 Batool tai bacci ta barta, tana zaune awajen tana kallon wayan shadaya nayi wayanta yahau ringing wani irin lumshe idanu tayi batare data kalli screen dinba hawaye taji sun zubomata sharrrr ajiki, tunda tasan Ya Aliyu kullum doki take yakirata yaune rana na farko dataji tana tsoron tadauki wayanshi ma dan gani take dazaran yaji muryanta zan gane and tayaya zata iya fadamai Wanan bakin labarin da tasan halinshi yanda yakeda mugun kishi idan wani abu yasameshi this night fa, kozata fadamai labarin nan she needs to think it through sanan tasami hanyan dazata iya fadamai batare datai breaking heart nashi ba dan batason wani abu yasameshi.
Wani kiran nashine yashigo ahankali tadauki wayan, maida wayan silent tayi gabaki daya sanan tasauka daga kan gadon ahankali tadauki littafin Mama, gaban wardrope taje tazauna ahankali akasa tana rikeda book din tana kallo tsoron ma karantawa take hawaye ta share dasauri sanan tabude book din ahankali tafara ni tana karantawa.

Tunda aka haifeta Mama tafara rubuta mata book dinan, taushe bakinta tayi jin wani mugun kukan dayake zuwan mata, sanan tacigaba da karanta littafin page after page, Mama na bata labarin komi wahalan datasha rayuwa kafin tahadu da mahaifinta, da ranan da ciwonta zai tashi da ranan da ciwonta zai lapa haka takebin littafin nan word by word tana taushe bakinta hartakai pages na karshen dataga yanayin rubutun mama ma ya chanza.
“Ummulkhair bansan maisa ba but anytime nake rike da littafin nan dakuma alkalamin nan babu abinda bana iya fayyace miki, yanzun nan kika fita kika tafi makaranta, lokacina yakusa ni kaina inaji ajikina saisa nace bari namiki Wanan one final rubutun. Ummulkhairy inaso kisani cewa duk cikin yaran dana haifo duniya babu wanda nakeso kaman ke! Nasan ance babu kyau uwa tafadima yaranta tafison Wanan kan Wanan nafadamiki hakane sabida inaso ki natsu aduk lokacin da Littafin nan zai sameki. Khairy ni mahaifiyanki nine na zabamiki miji Zayn sanan umarnina ne agareki kiyi zaman aure dashi!” Wani irin sakin book din Khairy tai akasa kawai tashi tayi dagudu tafada bayi ta kunna ma kanta shower tana wani irin kuka tamai sosa zuciya ahankali tace “Mama whyyyyyyyy? Mama Ummulkhairy ki Ya Aliyu takeso, Mama whyyy” wani irin kukan datayi batajin koda Mama tarasu tayi irin kukan nan ba, takai kusan awa daya abayin karkashin ruwa kuka take sanan da kyar ta lallashi kanta tafito bayan ta tube kayan tadauki towel tadaura akirji tabude kofa Littafin taci karo dashi ahankali ta tsugunna tasa hannu tadauka sanan tabude tacigaba da karantawa.
“Nasan bama kiwani san Zayn da kyau ba amman tun kina yarinya Zayn na bala’in sonki kuma yanaji dake, Zayn nada tausayi, yanada Imani sanan yanada kirki ni mahaifiyar ki na yarda da Zayn, karki tunani babu soyayya a tsakaninku so yakanzo daga baya, Khairy kaman yanda nafadi miki abaya na zaba miki Zayn ne sabida inaso hankalina ya kwanta aduk inda nasami kaina nan gaba dan haka y’ata don’t reject Zayn! Accept him and accept the marriage do that for me Ummulkhairy, do it for world best Mom dinki! Karki tadama Baban ki hankali ko yayyinki trust me nasan Baban ki will be going through alot kinsan kuma farin cikin ki shine farin cikin mahaifinki da yayyinki karki basu damuwa kinji Khairy na” Awani irin hankali ta gyadama Mama kai wasu sansanyar hawaye nabin idanunta suna saukowa kasa sanan tasake kallon book din.
“Allah yamiki albarka, inhar kayi abu for the sake of iyayenka dan ka farantamusu rai Allah zai albarkace ki, sanan zai baki kome kikeso cikin sauki, Khairy don’t stress your heart kiyi tunanin anything kibi umarnina dana mahaifinki bazaki taba tabewa ba Allah yamiki albarka daga mahaifiyanki Maryama”

Ahankali ta maida littafin tarufe sanan ahankali ta tashi tamike tsaye jinta take kaman iska zai kadata tafadi wardrobe tabude tadaga karkashin kayanta ta tura littafin sanan tajawo wani dogon Riga tasaka na bacci kafin tazo gado ahankali ta zauna tana kallon wayanta, ahankali tasaka hannu tadauka sanan ta danna 5miss calls tagani na Aliyu saikuma messenge, message din ta danna ahankali.
“Pickle are you sleeping? Maisa kikai bacci dawuri haka? Wait are you fine are you okay? Wani abu namiki ciwo ne??? Umm I am worried”
Hawayen daya gangaronata ta share ahankali sanan gently tashiga scrolling tundaga farkon message din dasuka farama juna harzuwa na yau tana karantawa wani irin jefar da wayan tayi kan gado takifa kanta kan gadon tana kuka, idan ta tuna Aliyu ta tuna yanda yake sonta da yanda yake mugun kishinta saitaji she can’t hurt him, bazata iyaba bazata iyaba! Ganin tana nema ta shige yasa tashaki inhaler ta sanan ta tashi tashiga bayi tadauro alwala wato idan kaga bala’i rasa bacci kake hijabi tasaka kawai tahau kan dadduma tana kuka tana fadima Allah komi itadai tasan tanata salla wajajen asuba barawon bacci yasaceta anan kaHn dadduman.
5️⃣0️⃣

Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.

wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp

This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️

Ranan ma bacci barawo yasace ta da kyar ta tashi dasafe tai salla, tana zaune da safe ita kadai akasa taji an bude kofanta hakan yasa takalli kofan Baba ne, shigowa dakin yayi hakan yasa ahankali tace “Baba ina kwana” zama yayi akasa kusada ita shima ahankali yana kallonta yace “yauma bazaki school ba” gyadamai kai tayi ahankali tace “bama komi sai ranan exam zanje” shiru yayi yana kallonta hakan yasa ta saukarda kanta kasa, ahankali yakai hannunshi yatallabo fuskanta yana kallon kwayan idanunta yace “have you been crying Ummulkhairy”? Dan murmushi takakalo sanan ta girgiza mai kai, baki Baba yabude zaiyi magana dasauri ta girgiza mai kai tana hadiye miyau sanan tasa hannunta ta goge hawayen daya zubomata da sauri sanan takalli Baba murya chan kasa tace “Baba nariga na karanta Littafin Mama na karanta komi naciki” shiru tadanyi sanan tasauke ijiyan zuciya ahankali, murya chan kasa tace “Baba babu abinda bazan iyama mahaifiyata aduniyan nan ba she’s my number one dan haka karkaji komi” tasakeyin shiru tana saukar da ijiyan zuciya ahankali tace “I accept Ya Zayn amatsayin mijina wanda kuka auramin Baba” tai maganan tana danne hawayen ta, wani irin farin ciki dataga ya lullube fuskan Baba yasa tasakinmai murmushi ahankali, rungume ta yayi yana mata addu’a sanan yacirota yace “kome kikeso nasaya miki Ummulkhair kifadamin ko yaushe I will buy it for you, I know Maman ki is very very happy dake, Allah miki albarka, bari naje nafadima Anty ki dan ta shirya tafiya Dubai yomiki shopping zaki bita kutafi tare” girgixamai kai tayi tace “zanyi karatu for final exam Baba” “ohhh hakane nama manta tsabagen farin ciki bari naje” Baba yay maganan yana fita daga dakin cikeda farinciki datama dade bata ganshi da irinshi ba tun Mama nada rai, hannu tasa tashare fuskanta ahankali tace “Ya Aliyu I am sorry” ko kadan batasan tayaya zata fadima Ya Aliyu ba ita batamajin zata iya fadamai ba bama tasan tayaya zatai avoiding nashi ba tana zaune tana tunanin Batool tashigo dakin ganin idanunta sunyi jajir yasa Batool tamaida kofan tarufe tazo inda take zaune akasa tazauna tace “Khairy zakije kisawa kanki wani ciwo ne wai, kin fadama Ya Aliyu”? Girgizamata kai tayi cikin muryan kuka tace “Batool I don’t know Tayaya zan fadamai, I can’t hurt Ya Aliyu, I can’t hurt him, I don’t even want to imagine what he will go through Idan yaji wanan zancen, banson wani abu yasameshi” ta karashe maganan tana goge kwalla duk Batool na kallonta tace “to tayaya zakiyi avoiding nashi yanzu I am sure sabida shine kika kasa zuwa school, Khairy you need to think of something” hawaye tadan share sanan takalli Batool tace “na chanza SIM card”? Dasauri Batool tace “ko kin chanza SIM card ai yasan gidan nan, saidai” tai shiru dasauri Khairy ta kalleta tace “saidai me”? Ahankali Batool tace “call him up kifadamai zakuyi tafiya kauyen su Mama garin kuma babu service gobe zaku tafi ba lallai idan yakira yasameki ba saiki kashe wayanki kawai, karki kara zuwa school din saikun fara exam baduk idan kina exam baya zuwa school wajen kiba” gyadamata kai Khairy tayi tace “to kingani dazaran an gama exam din karki kara fita kawai nasan idan aka kaiki gidan Zayn zai chanza miki layin waya shikenan, idan bai ganki ba daga baya yaji kinyi aure zai hakura” shiru Khairy tayi tana kallon Batool Wanan shine simplest thing datasan zata iya dan she can never ever hurt Ya Aliyu, hannu Batool tasa akan fuskanta ta sharemata hawayen tace “kirashi yanzu” ahankali tadauki wayanta tai dialing number Aliyu, saida wayan ya katse sanan yakirata back, ahankali yace “good morning Miss Khairy yaya jikin I was about calling you Boss dina yarikeni a office annoying man kawai, cikin yadena ciwo”? Gyadamai kai tayi ahankali tace “eh” sanan tai shiru dukan cinyanta Batool tayi hakan yasa dasauri tace “Ya Aliyu zamuyi tafiya yau” dan shiru yadanyi kafin ahankali yace “ina zakuje”? “Kauyen su Mama zamu” ahankali yace “ina ne kauyen”? Dan shiru tayi tana kallon Batool data Balla mata harara dan tana jin maganan Aliyun daga inda take, ahankali tace “uhmmm namanta sunan kauyen, nataba zuwa sau daya da ita secondary school” ahankali yace “ok yaushe zaku dawo”? Murya chan kasa tace “sai Baba yafada I don’t know” hararanta Batool tayi hakan yasa tace “Ya Aliyu kauyen babu network” danjim yayi kafin ahankali yace “Tayaya zan dingajin muryan ki to” hawaye taji yazo mata ahankali tace “nima bansani ba” jin yanda muryanta yayi zatamai kuka yasa yace “to shine zakiyi kuka? Ki tambayi Baba sunan kauyen saiki fadamin kafin kutafi duk randa naji nagaji da rashin jin muryanki I will just enter road and come cus I can’t survive this life banganki ba kuma banji muryanki ba, so don’t cry okay” ita kanta jikin Batool wani sanyi taji yayi ko itane she can’t hurt a guy kaman Aliyu haka with pure heart gashinan so cool and calm. Ahankali Khairy tace “okay” murmushi yadan mata yace “mai kukan banza, lemme get back to office kafin boss dina yay firing nawa in the middle of minute nadauki excuse nafito, bye I love you Miss Khairy” ya katse wayan da alamu sauri yake ajiye wayan zatayi taga kiranshi yashigo ahankali tadauka gudu taji yanayi yace “I forgot to tell you Allah kiyaye hanya, kidauki mosquito cream, insecticide and mosquitoe net kauye akwai sauro I don’t want them biting you, and go with indomie da some cereal incase bazaki iyacin abincin kauye ba, and again go with some bottle water karkisha ruwan rafi kinji, take care of yourself for me kinji Ummulkhair” gyadamaikai tayi ahankali tace “naji Ya Aliyu thank you” dan murmushi taji yayi sai chan taji ya tsaya dagudun yace “shitt! Pickle my heart kinda feel sad, I guess I am missing you already, zanyi missing Khairy na very very so so sooo much” murmushi tayi tace “me too” sanan tace “Ya Aliyu ka koma meeting bye bye” takatse wayan dasauri sanan tafada jikin Batool tace “Batool na shiga uku ina cikin tsaka mai wuya yaya zanyi da ALKAWARIN ZUCIYA NA?” Bubbuga bayanta Batool tayi tace “kaddaranki kenan kiyakuri Khairy” da kyar ta lallashi Khairy, sanan tadauki wayan Khairy tacire SIM card dinta tawuce bayi amasai ta Kefa SIM card din tai flushing dan that’s the only thing dazata iyama Khairy dan yasan yanda so yake lokacin dazata kunna wayan nan takira Aliyu bazata sani ba and she needs to let him go dan tanada mijinta, dawowa dakin tayi kawai ta rungume Khairy suna kuka sosai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button