ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL
ALKAWARIN ZUCIYA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp
This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️
5️⃣2️⃣
Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.
wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp
This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️
Harsukakai gida kuka Gwaggo takeyi hakan yasa Dad yakai Gwaggo side dinta yace “dan Allah Gwaggo kidena kuka kar Aliyu yagane idan yaji sauki saimu fadamai gaskiya dan Allah Gwaggo” bakin zani takama ta warware ta fyace majina tace “Abdul nafi kowa sanin yanda Aliyu keson yarinyar nan tunda harkaga yadauki yarinyar nan dungurungum yakawomin, Allah kai zurfin cikin nan aiko kasan yana sonta tayaya zamu gayamai jibi ne bikin yarinyar nan eh”? Ahankali Baba yace “Gwaggo Aliyu zai hakura daga baya yaji sauki dakaina zan mishi bayanin komi kinji kema kiyakuri bari naje nadubo shi” gyadamai kai Gwaggo tayi tace “tom jeka” fita yayi daga dakin Meena dake uwardakan Gwaggo dataji komi komawa gadon Gwaggo tayi da gudu takwanta kaman kai bacci tana hadiye kukan datakeji Gwaggo tashigo dakin ganinta tana bacci yasa tace “Alhamdulilah nasan inda munafukan nan taji zata iya zuwa tafadimai” tai maganan tana daukan kwaryan maganinta tana dafa bango tafito falo tazauna kurban maganin tayi sanan tabuga tagumi ahankali saikuma tafashe da kuka wiwi.
Ahankali Dad yashiga side din, ganin Aliyun na bacci yasa yadan sauke ijiyan zuciya sanan yajuya zai fita daga dakin kaman daga sama yaji Aliyu yakira sunanshi. “Dad”juyowa Dad yayi ahankali wearing a smile a face nashi sanan yakarasa gaban gadon yace “kai Aliyu ashema nasan mahaifinta nine Dr Maman Ummulkhair kafin tarasu” ganin yanda Dad kemai murmushi yasa ahankali yaji wani karfi yazomai da karfinshi ya yunkura yatashi zaune yana jingina da gado, murmushi Dad yayi yace “ance jibi zata dawo daga kauyen wai rasuwa aka musu saisa suka tsaya, Babanta da Yayyinta kadai ne agida ita da Amaryan Baban nachan kauye, kana damun kanka ne for nothing, danaji haka shine nace okay bayan sun dawo kaima lokacin kaji sauki garau basai muje dakai a nemo aurenta ba, so get on ur feet yarona” dan murmushi yama Dad ahankali yace “thank you Dad” murmushi Dad yamai ya shafa fuskanshi yace “bari naje nadan kwanta tunda yau bazanje aiki ba” gyadama Dad kai yayi ahankali yawuce yafita wani dan karfine yaji yazomai ahankali yatashi yana dafa bango dan har yanzu kanshi na sassarawa yashiga bayi alwala yayi sanan yafito dadduma ya shimfida yayi salla sanan yakoma kan gadon yasake kwanciya yana lumshe idanu.
Wuraren 1 aka bude kofan dakinshi lokacin yanakan dadduma ya idar da salla, Meena ce tashigo dauke da tray da mug na coffee kekai dakuma sandwich agefe karasowa gabanshi tayi akan dadduman ijiye tray din tayi sanan tazauna ahankali tace “Ya Aliyu namaka coffee” muryanta dayaji yasa yakalleta dasauri ganin yanda idanunta sukai jaa yasa ahankali yace “what happen?” Girgizamai kai tayi dasauri sanan tace “bakomi sha coffee please kaci abinci kaga kai kadai gareni” tai maganan hawaye na zubomata gyara zama yayi yana kallonta dan murmushi yayi da kyar sabida yanda kanshi keciwo yace “are u like this sabida banda lafiya”? Girgizamai kai tayi dasauri tana kokarin danne kukanta amman takasa tafashe da kuka sosai dayasa yarike hannuwanta yace “menene Amina?” Kallonshi tayi cikin kuka da bakinciki tace “Ya Aliyu Ummulkhairy ta yaudareka jibi ne bikinta” wani irin daran kaman karan kararrawa yaji zuciyanshi nayi dasauri yakalleta dan baigane inda ta dosa ba, ahankali tace “dazu naji maganganun su Dad da Gwaggo dake kuka sosai afalo bayan sun dawo daga gidan su Khairy, babu inda Ummulkhairy taje tana gidansu bikinta za’ayi ranan Saturday dinan jibi dawani Yayanta Zayyanu inji Gwaggo dan tun dazu sambatu takeyi tana kiran sunanshi, Ya Aliyu I am very very sad for u kaman in kashe kaina nakeji sabida nasan yanda kakeson Khairy, su Dad basuso su fadama wai saika warke amman Bikin Ummulkhairy ranan satur……..” “stop it!” Aliyu yadaka mata wani mummunan tsawa dasaida takoma baya dasauri, runtse idanunshi yayi batare daya budesuba yace “leave this room Meena” dawani kalan sauri Meena ta tashi tafice tana goge hawayen datakeyi, Aliyu yakai kusan minti ashirin zaune inda yake he’s trying yafadama kanshi maganan da Meena tagayamai karyane na Baban shine gaske, kunnenshi keeps hearing bikin Khairy jibi ne Ya Aliyu, wani irin mikewa tsaye yayi kaman zaki car keys dinshi dake kan gado da wayanshi yadauka yawani fice kanshi nasarawa amman bayamaji tsabagen fitinannen kishinn dayakeji azuciyanshi, motanshi yashiga gateman nabudemai yaja motan feee yawuce, gudun dayake akan hanya zaka dauka yazare ne cikin ikon Allah yakawo har kofan gidansu Khairy awani irin hankali yay parking yana kallon kofar gidan dayaga anyi pentin shi gate din gidan a bude ana shiga dasu kanopi da kujeru cikin compound din ana jerawa hannunshi ahankali yadaga yadaura kan kirjinshi dayaji yanamai zafi sosai kaman an zuba garwashi akai, wani irin rawa da bari jikinshi yafara yana kalle kalle baimasan maiyakeyi ba, wani irin bude kofan motan yayi marfin kaman zai balle sanan yasauko daga motan, duk wanda zaiga Aliyu zaisan baya cikin hayyacin shi, shiga gidan yayi yana kalle kalle ko’ina, dayake mai gadi baya wurin yana wajen masu saka kanopi yana tayasu aiki yasa Aliyu yawuce ciki yana kallon banner dasuke kokarin makalawa abango an rubuta #KhaZy saikuma a tsakiya ansa Ummulkhairy weds Zayn! Jiyayi gabaki daya kwakwalwan shi yafara boiling babbabaaa, bayamaji da kyau chak bakumaya gani da kyau ya tsaya kaman wanda yasami tabin kwakwalwa yawani irin kwalamata kira babu ko shakka ko tsoro atattare dashi. “Ummulkhairrrrrrr!” Wani irin amsawa gidan yayi da su kansu masu aikin saida kowa ya tsaya chak suka juyo suna kallonshi.
Ummulkhairy na zaune dasu Batool da Anty Mariya da Besty afalon sama ana mata lalle akafa daya dan yanzu aka fara, cikin besty yafito tai kyau sosai kaman daga sama taji muryan Aliyu harcikin kashin zuciyanta taji yanda yakirata dawani irin sauri ta zabura tamike tsaye zumbur tana kalle kalle tama manta lalle ake mata hakan yasa daga mai lallen harsu Besty sukace “ke lpy”.
“Ummulkhairrrrrrrree!” Aliyu yasake kiranta akaro nabiyu da gidan ya mugun amsa danko su Anty Mariya saida sukaji dan kaman yay using microphone it was so audible, dawani irin gudu Ummulkhairy tajuya tai stairs su Anty Mariya da Batool suka biyota dasauri, wani irin bude kofan falo tayi tafito ido da Aliyu tayi da Aliyu dake tsaye tsakar gidansu idanunshi sunyi jajir kaman jini wallahi, fuskan Aliyu dakenan fari kal yau fuskanshi yay ja shima, wani irin zufa naketomai akowani bangare na fuskanshi.
Fuskanshi kadai tagani taji zuciyanta ya tsinke she saw his pain and agony Wanan kuma shine abinda yasa she avoided him takasa fadimai, ahankali tadaga kafa zata tafi wajenshi Besty tarike hannunta, muryanta nadan rawa tace “Besty, Anty Mariya dan Allah kubari naganshi nagayamai gaskiya please, kar wanda yabiyoni lemme talk to Ya Aliyu” karbe hannunta tayi sanan ahankali tashiga sauka daga stairs din tana wani irin kallonshi kaman yanda yake kallonta suma ma’aikatan kowa yacigaba da aikinshi ganin anma San mutumin sunsan juna tunda ga amaryan tafito taganshi, yanda taga Aliyu kaman zaki yasa takasa karasawa gabanshi, dan nesadashi ta tsaya ayanda taganshi kaman zai Chaka mata wuka yake murya chan chan kasa dake mugun rawa tace “Y……Ya Aliy……” bata karasa maganan ba jin wani fizgo hannunta dayayi kaman zaki kawai yashiga janta dawani irin sauri kaman jirgin sama su Mom Anty Mariya dasu maigadi damasu aiki suka biyosu amman ina! Kafin suma fito waje Aliyu yajefata amota yaja motan da arnen gudu ma’aikatan nabin motan dagudu, arude Anty Mariya datafito har waje ba hijabi ba mayafi takalli su Batool da Besty arude tace “kubani wayaZna nakira Baban ku Aliyu yasace Khairy Innalillahi wa innailaihi raji’un”.
Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.